Showing 300001 words to 303000 words out of 352722 words
shaƙar numfashi ka sauƙaƙa mata shi al'farmar Annabi da al'ƙur'ani."
"Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati my Dear".
Ya faɗa yana share mata hawayen fuskarta da hannunshi na hagu.
Su kuwa saura kab ajiyan zuciya sukayi tare da cewa.
"Alhamdulillah"..
Sai lokacin ya ɗan kalli Aunty Rahma dake gefen Shatu tana zubda hawaye a hankali yace.
"So sorry my Aunty in Sha Allah babu komai likita yace, da shayar da ita shi akayi zaifi mata illa yanzu kuma shaƙane an mata duk wani taimakon gaggawa daya kamata".
Cikin gamsuwa ta gyada kai.
Sai kuma ya ɗan taso tsaye sai lokacin yaga yawansu.
A hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
"Gimbiya Aminatu in sha Allah daga yau wannan al'adar zata kau a masarautar Joɗa dama duk wasu tarkacen al'adun daba addiniba ki gayawa Lamiɗo".
Cikin jin daɗi tace.
"Ai ba ita kaɗai ba in dai ka yarda ka mulki masarautar Joɗa duk wata al'ada na masarautun gargajiya kana da damar datsesu ka wanzar da Sunnah".
Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe.
Tabbas masarautar Joɗa tana buƙatar sabon Sarki sabon tsari sabon zubi bisa koyarwar musulunci da sunnar manzon Allah a kauda bidi'a a kawo sunna.
To amman shi baida ra'ayin mulki.
Cikin sanyi yace.
"Gyaran ba lallai sai ni ɗaya zan yi shi ba ai, kuma ko bani ke mulkiba zan iya bada shawara in an yarda a amsa".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Idan dai har kana son kauda al'adun a wanzar da sunna to dole ka mulki masarautar Joɗa da kanka".
Kanshi kawai ya jingina jikin kujerar kana a hankali ya sunkuyo yana kallon Shatu dake cewa.
"Baiyi mulki Bama Umaymah ana neman ransa da na ahlinsa".
Lamiɗo da Galadima dake shigowa ne dan jin lbrin abinda ya faru a bakin Jalal ne.
Suka haɗa baki wurin cewa.
"Ƙi gudu sa gudu, Shatu ke muke zaton zaki bashi ƙarfin guiwa kuma sai ki karaya da wuri haka."
Da sauri su Umaymah kab suka ja da baya suka basu wurin zama.
Suna zama dai-dai lokacin kuma Shatu ta zare mamanta daga bakin Afreen ɗin cikin tsoron ganin yadda ta ke ɗan yunƙuri tana kwaro amai.
Da sauri Sheykh ya matso tare da cewa.
"Innalillahi".
Ita kuwa Shatu ɗagota tayi da sauri ganin yadda taketa yunƙirin kakarin amai ba ƙaƙƙautawa.
Da sauri Gimbiya Aminatu ta matso tana cewa.
"Subahanallahi"
Shi kuwa Sheykh wayarshi dake cikin al'jihun rigarsa ya zaro da sauri ya kira Dr Lukman Ibrahim yana ɗagawa yace.
"Dr Baby fa sai amai takeyi ba tsayawa".
Da sauri Dr Lukman Ibrahim yace.
"Alhamdulillah tasha Mamanta ko?".
"Eh tasha, tana shane ma ta fara aman".
Ya bashi amsa.
"Yauwa haka akeso Sheykh ba komai yanzu duk kaifin gubar ya karye ta harar dashi yanzu zatayi bacci kuyi mata wonka da ruwan sanyi.
Tana farkawa kuyi mata wonka da ruwan sanyi kuma zata dawo dai-dai da izin Ubangiji".
Da sauri ya katse kiran bayan yace.
"Ok thanks Dr".
Ita kuwa Shatu ajiyan zuciya ta sauƙe tare da meda kanta ta jingina da kujera ganin ta bar aman.
Shi kuwa Umaymah ya kalla tare dayi mata bayanin da Dr yayi mishi.
Da sauri ta iso garesu ta amshi ƴar kana ta wuce Bathroom.
Wonka tai mata da ruwan sanyi ɗan kwalinta ta wore ta naɗeta a ciki.
Tuni tayi bacci kafinma ta fito da ita.
A hankali ta zauna bakin gadon Shatu gefen Aunty Amina da Khadijah dake waya da Abboi Appansu kenan tanai mishi bayanin duk abinda ya faru.
Cikin tashin hankali da mamaki Abboi yace.
"Subahanallahi, kai wannan gida nasu akwai sarƙaƙiya.
yanzu ina Parvina?".
A hankali tace.
"Tana falo can naji kamar harda Lamiɗo ma yazo da kanshi, amman yanzu yarinyar gata nan ta farfaɗo harma tayi bacci".
Cikin kula da son ahlinshi especially Parvina a hankali yace.
"In sha Allah nida Dedden ku da Al'ameen zumu zo gobe gobe da izinin ubangiji, dama tun tuni ma shiryawa hakan, in Parvina ta shigo kice ta kirani".
Da sauri tace.
"Toh Appa".
Guntun murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Babanku kika gayawa ne?".
Cikin alamun karaya da lamarin gidajen sarauta tace.
"Eh Umaymah".
Kai kawai ta gyaɗa tare da gyarawa jaririyar kwanciya.
Aunty Amina kuwa sunkuyowa tayi tana kallon fuskar Babyn.
A falon Shatu kuwa sosai Lamiɗo ya kwantar mata da hankali kana suka tafi Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.
Bayan ta shiga ta ƙara duba Babyn.
Umaymah kuwa fitowa falon tayi suka zauna a nan.
Ita kuwa Shatu bedroom ta koma ta konta tasa yarta a gaba tofi takeyi mata tana kallon fuskarta Allah ya sani ji takeyi kamar bata tsiraba shiyasa har yanzu hanjin cikinta ke kaɗawa.
A hankali ta jawo wayarta.
Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya faru ya ɗaura da cewa.
"Dama can gobe zamu zo ko ba komai zanzo inga amryata, inga mummunace ko kekyawa".
Ya ƙare mgnar da ƴar raha da son kontar mata sa hankali.
Murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya kawomku lfy Appa na, da Ummey na da Junainah take kamafa".
Tayi mgnar cikin jin kunya duk da yawan shaƙuwa dake tsakaninsu.
Murmushi yayi tare da kallon Dedde dake jin duk tattaunawar da sukeyi yace.
"Ato kekkyawace sadaki ta garken shanun Bappa zai bata".
Dariya sukayi baki ɗayansu kana sukayi sallama da juna.
Daga nan kuma Bappa ta kira, wanda tun ɗazu Abboi ya shaida masa abinda ya faru yana ɗagawa yace.
"Shatu na ya jikin Aisha ƙaramar dai?".
A hankali ta ɗan shafa kan Afreen tare da cewa.
"Alhamdulillah Bappa na ba komai ta samu lfy gatama tana bacci".
Cikin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah ga Ummeynki tun ɗazu hankalinta a tashe yake".
Amsa Ummey tayi cikin kula tace.
"Boɗɗo na me sukayi miki?".
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ummey na so sukayi su kashe miki jikarki tun baki ganta ba, dan Allah da Manzonsa Ummey na kizo gobe".
Cikin kaɗuwa da begen son ganin Shatu da ƴar tata tace.
"In Sha Allah Gobe za muzo tare da Abboi da izin Ubangiji".
Cikin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah naji daɗi na, Gobe ina cikin gatana".
Su kuma ta kalli Umaymah da ta shigo yanzu tare da cewa.
"Alhamdulillah Umaymah na Gobe Ummey na zatazo da Bappa na da Deddena da Abboi".
Cikin wani irin masha'hurin farin cikin alamun son tabbatuwar wani abu Umaymah tace.
"Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Haka dai akayi wunin sunan jiki a mace da abinda ya faru.
Sai can da yamma ne da Afreen ɗin ta farka daga baccin suka ganta lfy lau kafin hankalin kowa ya kwanta.
Nan Umaymah suka fito da kayan suna na gani na burgewa, da aka haɗawa mai jego da Ɗiyarta.
Kayan da Sheykh yayi musu kuwa abin sai dai ace son barka.
Gaba ɗaya wunin yau shima ya kasa fita ko nan da can tunda akayi sallan Jumma'a ya shigo ya wuce Side ɗinsa.
Bini-bini ya kira Shatu ko Umaymah ya tambayi jikin yarinya.
Bayan sun dawo sallan la'asar ne.
Jalal ya biyoshi har cikin falonshi, gefen Haroon ya zauna kana a hankali yace.
"Shima sarkin al'adun sunan harda shi a sahun Magauta sai dai biya shi Hajia Mama tayi da dubu ɗari bakwai daga baya yace min tace in ƴar ta rasu zata cikata mishi dubu ɗari uku ya zama one million".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Ikon Allah ikon gaske, wai ita wannan shegiyar matar meyasa bazamu fito mata a fili bane mu nuna mata mun san komai mu kuma juyo kanta".
Cikin taune lips Sheykh yace.
"Uhumm bazaku gane bane,".
Da sauri Umaymah dake shigowa tace.
"Ni na gaji bazamu gane me ɗin ba kuma".
Cikin wani irin yanayi mai rauni cikin sanyi murya na rawa yace.
"Affan ina ɗagawa Hajia Mama kafane sabida Affan ina jin takaici in na tuno a cikinta Affan ya fito, ku kun san waye Affan kun kuma san asalin zahirin gskyar so da ƙaunar da yake mana, kunsan yadda yake faman faɗa da yaƙin sauya mahaifiyarshi daga mummunan ɗabi'a eh zuwa kekkyawan ɗabi'a.
Ta yaya zanci zarafin ta al'halin Affan ya ɗaukeni matsayin Uba ya ɗaukeni ciki ɗaya muka fito,kada ku manta son da Affan kewa Mameynmu Jalal ka duba tarin son da Affan yakeyi muku kaida Jamil.
Ko a lahira wani kanci al'barkacin wani.
Ina barine sabida ko Affan zai samu nasarar juya halinta".
Ya ƙarashe mgnar hawaye na zubo mishi.
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tabbas sun san waye Affan ko su Jalal basa so da shaƙuwa dashi kamar Affan.
A hankali yace.
"Duk abinda nasa Affan zaiyi minshi babu musu koda baya son abin duk inda na aikeshi zaije min duk abinda na bashi zaɓi zaɓina yake bi, Affan da kanshi ya fara nuna min baya son inci abincin Hajia Mama wacce take uwace a garesa, yayi hakane sabida zargin tana samin abu a cikin abinci.
Yasha yin kuka yana mgiya in ya tareta tana wani abun me zanyiwa Affan in nuna mishi halaccin ɗan uwantaka banda in rufawa mahaifiyarshi asiri".
Shiru yayi ganin kiran Affan daya shigo wayarshi.
Jiki a mace itama Umaymah ta zauna.
A hankali ya kara wayar a kunne bayan a amsa kiran.
"Assalamu alaikum Hamma Jabeer".
Affan ya faɗa cikin tsananin so da ladabi ga ɗan uwan nasa.
"Wa alaikassalam Affan kana lfy".
Sheykh yayi mgn yana mai jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
Murmushi Affan yayi cikin yanayin shi na Happy mood yace.
"Alhamdulillah Hamma Dr Akarmakallu Yah Sheykh, mun sauƙo lfy".
Jingina bayan sa yayi da kujera tare da cewa.
"Alhamdulillah Affan Allah yayi ma al'baka".
Da sauri yace.
"Amin Hammana".
Sai kuma yace.
"Jamil ne yazo ya daukomu a airport to yanzu mun biya mun sauƙe Yah Sulaiman da Malam Abubakar.
To gani tare dasu Giɗi ɗin yanzu su ina zamu kaisu, umarni nake jira Hamma?".
Cikin sanyi yace.
"Alhamdulillah Affan ku dawo dasu masarautar Joɗa ku wuce dasu Part ɗinsu Jalal a sauƙesu a can.
Bawa Jamil wayar".
Da sauri yace.
"An gama sir yadda kace haka za'ayi ga Jamil ɗin".
Ya kare mgnar yana miƙawa Jamil wayar.
Saƙale wayar yayi da kafaɗarsa tare da cewa.
"Assalamu alaikum Yah Sheykh".
Gyaɗa al'kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
"Wa alaikassalam Jamil ka kaisu part ɗinku ɗakinka ka nuna musu Bathroom suyi wonka.
Aunty Rahma zata kawo musu abinci ka tabbatar sunci sun ƙoshi.
Sannan Jalal zai ɗauki Dr Kabir zaizo ya dubasu in sunada matsalar lfy zai kula da komai".
Cikin gamsuwa Jamil yace to yana kallon kekyawar fuskar Giɗi ta madubin motar.
Shi kuwa Sheykh a hankali yace.
"Toh Umaymah a hakan ta yaya zan tozarta mahaifiyar Affan wanda duk munin halinta uwa dai uwace."
Cikin rauni Umaymah tace.
"Wannan hakane Jazlaan amman Hajia Mama tanayi mana illa a rayuwa".
Sosai jikin Haroon yayi sanyi.
Shi kuwa Sheykh Jalal ya kalla tare da cewa.
"Kaje Valli ka taho da Dr Kabir".
Jiki a mace Jalal yace to kana ya miƙe ya fita.
Umaymah na biye dashi a baya, har taje bakin ƙofar fita a hankali yace.
"Ayyah Umaymah Ɗiyar taki ta kawo min ɗiyar tawa mana in ganta".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Toh".
Shi kuwa Haroon da sauri yace.
"To bari in baka wuri dan nasan dai uwar ɗiya za'a gani ba ɗiyaba".
A hankali yace.
"Mutun da abinsa".
Dariya Haroon yayi kana ya nufi ƙofar da zata sadashi da Garden.
A hankali ta turo ƙofar Bedroom ɗinsa.
Tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Cikin wani irin happy yace.
"Wa alaikissalam".
sai kuma ya juyo ya fuskanceta tare da buɗe mata hannunshi.
Cikin sauri ta faɗa jikinshi ruggume da Afreen haɗe su yayi ya ruggume tare da cewa.
"Alhamdulillah ya Allah ka tsare min ahlinna ka cika mana farin cikinmu".
"Amin ya Allah". Ta faɗa a hankali sai kuma ya jawo hannunta suka zauna a bakin gadon.
Cikin narke fuska yace.
"Nayi fushi Aish tun ɗazufa na aika kizo baki zoba sai yanzu".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Malam sallan la'asar nakeyi".
Cikin sauri ya kalleta tare da cewa.
"Kai haba dai Aish da gaske shine baki gaya minba yaushe kika fara salla".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Yoh ai dama ina salla".
Lakace hancinta yayi tare da cewa.
"Batun gsky dai my dear yaushe kika samu tsarki?".
Cikin nitsuwa tace.
"Yau da safe, nai wonka naci gaba da salla tunda naga jinin biƙin ya ɗauke na samu tsarki".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Masha Allah, jego yayi kyau kenan Boɗɗo na, dama wasu matan kafin satin sunama sun samu tsarki sun fara salla, kinga kema kina ɗaya daga cikinsu wasu kuma sai anyi arba'in ma, wasu har hamsin suna likin.
Koda yake ke dama al'adarma kwana uku kikeyi ko".
Kai ta gyaɗa mishi.
Hannunshi ya cusa ƙasan pillow'nshi tare da zaro key ɗin sabuwar mota dal a leda.
Kamo hannun ta yayi ya danƙa mata key ɗin tare da cewa.
"Al'ada kwana uku baƙi kwana bakwai kai naji daɗi na, na more".
Da sauri ta buɗe tafin hannunta tare da kallon key ɗin sai kuma ta lumshe idonta jin ya manna mata tattausan lips ɗinsa a goshi ya sake mata sassayan kiss.
Tare da cewa.
"Taki ce motar sai dai bani son kiyi tuƙi nafi son a jamin ke, sai daifa bana miji zai jamin keba.
Sara taki zata zama yar rakiyarki mai jan mota da tayaki kula da Babynmu, duk inda kuke in bana kusa daku.
Gimbiya Aminatu zata bamu wata mai girki".
Cikin wani irin farin cikin ta ruggumeshi gam-gam a jikinta.
Da sauri yace.
"Wayyo Aish zaki danne Mimi na".
Da sauri ta kwantar da Afreen gefe, kana ta faɗa jikinshi ta rungume shi.
Murmushi yayi mai cike da farin ciki cikin wasa yace.
"Zaki bani abin daɗi?".
Da sauri tace.
"Ban workeba".
Dariya mai ɗan sauti yayi tare da haɗe bakinsu wuri guda.
A part ɗinsu Jalal kuwa.
Yah Giɗi Seyo Gaini ne zaune bayan duk sunyi wonka, sun saka sabbin kayan da Jamil ya zaro musu cikin durowarsa.
Cikin wani irin yanayin jin daɗin duniya da kuma bege da kewar iyaye da ƴan uwa wanda da sun cire tsammani.
A hankali Yah Giɗi ya kalli Jamil dake miƙo mishi turare yana cewa.
"Kai masha Allah sai kunga yadda kukayi kyau, farinku ya ƙara fitowa".
Cikin rauni Giɗi yace.
"Dan Allah bawan Allah, nan ina muke ne? Kuma ina wanda muka dawo dashi? Sannan ina za'a kaimu? Wayasa aka fito damu?".
Da sauri Jamil ya zauna gabanshi kamo hannun shi yayi a hankali yace.
"Nan kuna cikin Ɓadamaya ne, cikin masarautar Joɗa, wanda kuka dawo dashi kuma Yayana ne Affan ya tafi ƙofar matarshi.
Wanda ya taimake ku yasa aka fitar daku kuma babban Yayanane Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa.
Yana nan matarsa ta haihu yau akeyin suna. Sai in ya nitsu zaizo wurinku shi zai gaya muku ina za'a kaiku".
Wasu irin hawaye ne suka tsunkowa Gaini murya na rawa yace.
"Alhamdulillah kowa yace yaya zaiyi ya manta da Allahu wahidun ƙahharar sarki buwayi gagara misali mai badawa mai hanawa mai raya mai kashewa mai kawo sauƙi cikin tsanani mai yaye tsananin duhu ya wanzar da haske".
Ido Jamil ya zuba musu cike da so da ƙaunar su, sai kuma ya kalli Seyo da yake zubda hawaye cikin sanyi yace.
"Ko wanne hali ahlinmu ke ciki".
Da sauri Jamil yace.
"Yanzu muje falo kuci abinci kunji dan Allah ku bar kukan".
Kasan cewar ya haɗa su da Allah yasa ba musu suka tashi.
Amman badon hakaba farin cikin da suke ciki ya kori yunwa bare ƙishi.
A tsakiyar falon suka zauna.
Jamil da kanshi ya zuba musu abincin da Aunty Rahma ta kawo musu.
Sukaci suka sha.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallan magriba.
Nan sukayi al'wala kana Jamil ya jasu sukayi jam'i.
Shatu kuwa bata bar ɗakin Sheykh ba saida ya tafi masallaci.
Ta fito cike da farin ciki.
Aunty Amina da Khadijah da Umaymah da Hibba ta samu a falonta Umaymah ta miƙa wa key ɗin tare da cewa.
"Umaymah Yah Sheykh ya saya min mota".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Kana duk sukayi al'wala haramar salla.
Ƙarfe goma da rabi.
Duk baƙi sun watse.
Sai su Umaymah da su Aunty Amina.
A falon Shatu suke suna hirarsu cikin salama Ummi na ruggumi da Afreen.
Umaymah kuwa na haɗawa Shatu tea da fifitashi da kyau.
Aunty Rahma kuwa kitso Khadija keyi mata.
Junainah da Ishma kuwa suna can babban falon da Hibba da Jalal.
Sara da Larai da indo hadimar Aunty Juwairiyya kuwa tattare kitchin sukeyi da kimtsa ko ina na gidan.
Sheykh kuwa a hankali ya jawo wayarshi daya tattare wacce yake waya da Hajia Mama da ita.
Kiranta yayi.
Tana amsawa yace.
"Ƴar ta mutu ko?".
Wani irin gigitaccen tsaki taja tare da cewa.
"Inafa ta mutu na dai ji ta suma amman wannan Shegen yaron duk abinda nayi a kanshi ko matarsa yanzu dama yar tashi abun baya tasiri.
Sannan babban tashin hankali na, shima Sarkin al'adun suna bai dawoba.
Kuma wayarshi na shiga baya ɗagawa, tsorona kada dai sun ganeshi".
Cikin sauya muryarsa ih zuwa muryar Jahan yace.
"A a ba dai kamashi ba kam, sai dai ko in yana jin tsoron amsa kiran nakine sabida kada kiyi mishi faɗa tunda ƴar bata rasuba kada kice bai iya aikinsa bane a ganina fa shine yasa baya amsa kiran naki".
Cikin tashin hankali tace.
"Ni babbar matsala ma yau tunda gari ya waye hankalina yake a tashi zuciyata na tsinkewa gaba ɗaya tsoro ya rufeni ji nakeyi wani mugun abu yana tunkaro rayuwata, naje gidan boka kuma ya koroni shima sai tsalle yakeyi yana kaɗe jikinsa
Wai komai na gab da dawo mana".
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi a ransa yake zaton ko shiryace zata zo mata, haka yasa yace.
"Sai gobe zanzo muyi mgn in kaiki gidan wani sabon boka".
Da sauri tace.
"To".
Daga nan ya katse kiran.
Kana ya miƙe ya fito falo, a hankali ya kalli Jalal da Hibba tare da cewa.
"Jamil fa".
"Yana Part ɗin mu".
Jalal ya bashi amsa".
To yace kana ya juyo ya kalli Yah Jafar da yanzu ya shigo kenan.
A hankali ya tsaya gaban Sheykh.
A hankali suka lumshe idonsu a tare, da sauri Sheykh da Jalal da Hibba suka matso kusa dashi sosai jin yana cewa.
"Jabeer zuciyata na tsinkewa tun jiya sai inji kamar wani abu zai faru".
Cike da mamaki Jalal yace.
"Wlh nima tun jiya zuciyata ke tsinke kirjina yaita bugawa".
Wani irin rumtse ido Sheykh yayi tare da cewa.
"Nima abinda naketa fama dashi kenan tun jiya, to da Aisha ta suma sai nai zaton ko abinne ke samin tsinkewar zuciya.
To kuwa still abin bai bariba saima ƙaruwar da yakeyi yana tsananta".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To kuyi ta addu'a hakama Umaymah da Mamma da Aunty Rahma sukace suna ji".
Kai suka gyaɗa gaba ɗaya.
Hannun Yah Jafar ɗin Sheykh yaja suka nufi Part ɗin su Jamil.
Su kuwa su Jalal zama sukayi suna kallon Ishma da Junainah daketa sabgoginsu.
A hankali Sheykh ya zauna tare da kallon Jamil dake zaune tsakiyarsu Giɗi a hankali yace.
"Ka barsu su huta mana".
Cikin sanyi Jamil yace.
"Allah ko Hamma Jabeer ina so in tafi wurin Khadijah ma sai inji zuciyata na tsinkewa kamar dai zan samu wani abu".
Cikin kula Sheykh yace.
"Uhmm duk haka mukeyi kaita mai-maita innalillahi wa innailaihi rajiun".
To yace.
Shi kuwa Sheykh nitse ya kalli Gaini da zai kai sa'an Affan.
Cikin kula yace.
"Sannunku da hanya".
A tare sukace sannu.
Jamil ne ya ɗan kallesu tare da cewa.
"Shine babban yayanmu Sheykh da yasa aka fito daku".
Da sauri suka ɗan gyara zama suka matsoshi tare da cewa.
"Allah sarki bawan