Showing 291001 words to 294000 words out of 352722 words
Alhamdulillah kada kayi kuka, Abba kaga ikon Allah ko Yah Jafar yayi mgn a yau yayi hamdala yace ya godewa Allah daya nuna masa wannan ranar muma muce mun godewa Allah mana sai ya ƙara mana wata ni'imar domin indan Allah yayi maka wata ni'imar ka gode mishi sai ya ƙara maka da wata, muce Alhamdulillah".
Kusan a tare gaba ɗayansu sukace.
"Alhamdulillah".
Harda shi Yah Jafar ɗin.
Ya ilahi wannan shine kyautar Allah.
Juwairiyya kam hawayenta yaƙi barin zubowa.
Lamiɗo kuwa a hankali ya dawo kusa dashi hakama Galadima, sai ya zama sun sashi a tsakiyarsu.
Abban da Sheykh kuwa suna gabansu da sauran Juwairiyya da Ummi kuwa suna gefe".
Cikin nitsuwa Abba yace.
"Jafar! Jafar!! Jafar!!!".
Shiru babu amsa.
Da sauri Lamiɗo ya jujjuya mishi kai tare da cewa.
"A a barshi, dole sai a hankali komai zaiyi dai-dai."
Sai kuma ya gyara zamanshi ya kalli jikokin nashi ya juya dama da hauni kana cikin yin ƙasa da murya yace.
"Toh wannan al'amari ya zama sirri tsakaninmu har zuwa ɗan wani lokaci kada ku gayawa kowa na cikin masarautar Joɗa".
Da sauri sukace "To".
Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin ya ɗauki Jaririyar ya miƙa Lamiɗo ita.
Addu'o'in yayi mata sosai kana ya miƙawa Galadima ita, sannan Sheykh ya ɗauƙeta ya miƙa Abba ita cikin murmushi yace.
"Aisha ta tafi Aisha ta dawo".
Murmushi Ummi tayi sabida tuno irin tarin son da Abba kewa Mamey wanda shiga goma zai zaka jishi yana kira Aisha! kaxa Aisha kaza da kaza yayi kaza ko?,".
Shima addu'o'in yayi mata kana, suka ɗan tattauna kaɗan suka tafi.
Su Jamil kuwa suma ɗaya bayan ɗaya suka amsheta.
Cikin murmushi da tarin son yarinyar Jalal yace.
"Masha Allah da Ishma take kama".
Da sauri Jamil ya amsheta tare da cewa.
"Kace da Mamey take kama tunda Ishma dai da Aunty Rahma take kama Aunty Rahma Kuma da Mameynmu take kama".
Da sauri Affan ya amsheta tare da cewa.
"Masha Allah wlh da Mamey take kama, Alhamdulillah Yusuf ƙarami yayi kamu".
Ɗan shi kenan takwaran Hamma Yusuf ɗin Zahra dariya sukayi baki ɗayansu.
Kana Aunty Juwairiyya ta amshi yarinyar ita da Ummi suka nufi ɗakin Shatu.
Suna shiga suka sameta zaune bakin gado da alamun waya takeyi da Rafi'a.
"A a bazan gaya miki ba sai kinzo kiga mai aka samu".
Tayi mgnar tana amsar Babyn da Aunty Juwairiyya ke miƙo mata.
Ita kuwa Rafi'a cikin tarin jin daɗi tace.
"Ai kuwa gobe da sassafe zan muku sammako".
Da sauri tace.
"Rafi'a baza kizo mu kwana ba".
Cikin dariyar jin daɗi ta e.
"Zan dai zo gobe kam da wuri".
Daga nan sukayi sallama.
Ita kuwa Ummi abinci ta zuba mata mai rai da lfy cimar jegon gaske.
Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar ɗanyar kuɓewa tasha man shanu da yajin daddawa da nama.
Sosai ta tasata gaba taci.
Ita kuma Juwairiyya tana riƙe da Ƴar.
Bayan taci tuwon ne kuma Ummi tasa mata gashin da yaketa tururi yaji yaji tana fifita matashi dan yayi sanyi.
Kana ta haɗa mata kunu da zuma ta bata, tanaci tana ɗan korawa.
A hankali ta ɗan jingina bayanta da gado a hankali tace.
"Ummi na ƙoshi".
Da sauri tace.
"A a Shatu ƙara sashi kada kice zakiyi jegonku na yaran zamani jego da soyayyan Arish da tea".
Cikin sanyi tace.
"Allah Ummi cikina zai fashe".
Jin hakane tace.
"To sai anjima ki ƙara".
Gyaɗa kai tayi kana ta gyara zamanta.
A can falon kuwa su Jamil duk Dinning area Suka nufa, suka zauna suka fara cin abinci.
Yah Sheykh kuwa falonshi ya wuce, wayarshi liƙe a kunne wanda Bappa yake kira.
Shi kuwa Bappa a can Rugar Bani yana zaune a tsakar gida Junainah na gefenshi su Ummey na gefenta.
Da sauri Junainah ta miƙo mishi wayar da dama Game takeyi da ita.
Amsa yayi da sauri ya amsa kiran.
Gyara zamanshi yayi jin muryar Sheykh na cewa.
"Assalamu alaikum".
Cikin kulawa yace.
"Wa alaikassalam Muhammad".
Da sauri ya zauna bisa kujera cikin tarin jin daɗi da son tsohon da tausayinsa yace.
"Na'am Bappa na Ina wuni".
Fuska ɗauke da murmushi yace.
"Lfy lau Alhamdulillah Muhammad ya su Lamiɗo ya Abbanka dasu Jalal duk suna lfy koma?".
"Alhamdulillah Bappa duk suna lfy cikin farin ciki".
Ya bashi amsa yana murmushi.
Shi kuwa Bappa cikin kula yace.
"Yah Shatu na?".
Murmushi Sosai yayi kana yace.
"Alhamdulillah Bappa Shatunka ta girma yau ɗazu da yamma gabanin magriba ta zama uwa".
Cike da tsananin farin ciki Bappa yace.
"Masha Allah! Alhamdulillah yaushe ta haifu mata na samu ko aboki mai tayani kiwo?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"A a Bappa wannan Gimbiya ce amrya ka samu".
Cike da farin ciki Bappa yace.
"Alhamdulillah Allah ya raya mana bisa imani".
"Amin Amin".
Yace yana mai jin muryar Junainah tana cewa.
"Ayyah Bappa bani shi Adda Shatu ce ta haihu?".
Cikin kula yace.
"Bappa a bawa Junainah waya".
To yace kana ya miƙa mata wayar, tare da juyowa ya kalli Ummey cikin murmushin yace.
"Alhamdulillah Shatu ta sauƙa lfy an samu ƴa mace yanzu da yamman nan".
Wani irin ajiyan zuciya mai sanyi Ummey ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah yau kam zanyi bacci hankali na konce Shatuna ta haihu lfy".
Murmushi Inna Amarya tayi tare da cewa.
"Wlh kuwa kai Alhamdulillah Metai fi haka daɗi kaji kawai ɗan ka ya haihu lfy".
"Wlh kuwa fa". Cewar Bappa.
Sai kuma suka juyo suna kallon Junainah dake tsalle tana cewa.
"Alhamdulillah Hamma Jabeer kace dani takeyin kama?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Junainah".
Cikin dariya tace.
"Allah shi ƙara dama kullum Addana sai tace wai ta fini kyau wai inada dogon bakin kwaɗayi, ni kuma kullum ince Allah yasa ta haifi irina ai zata dena cemin mummunan".
Dariya yayi sosai kana yace.
"Toh gobe dai zaki zo mana ko?".
Da sauri tace.
"Eh zanzo Bappa na da Ummey ma zasu zo".
Katse kiran tayi kana ta miƙawa Bappa wayar.
Shi kuwa kiran Abboi yayi ya kara wayar a kunne tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
"Wa alaikassalam".
"Barka da dare Abboi".
"Barka dai Bappa Shatu." Abboi yace yana murmushi tare da kallon Dedde dake gefensa.
Cikin jin daɗi Bappa yace.
"Alhamdulillah yau Shatu na ta hau matakin uwa ta sauƙa lfy mun samu ɗiya mace".
Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da jin daɗi Abboi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kai yau naji labari mai daɗi masha Allah. Kace lallai zuwa Nigeria ya kamani".
Da sauri Bappa yace.
"Sosai ma kuwa, yanzu dai su waye zasu fara zuwa".
Da sauri yace.
"Khadijah da Amina ƙanwar Deddena Shatun, dama nayi mgnar da mijinta tun kwanaki to yanzu kuwa zan kirashi in sanar mishi anfa yi haihuwar ba mamaki gobe ko jibi su taho da safe zuwa gidan naka.
Kaga da azahar sai su wuce masarautar da iyalin taka".
Cikin gamsuwa Bappa yace eh hakan yayi.
Yana katse kiran yayiwa Ummey bayani cikin gamsuwa tace.
"Eh hakan yayi amman in Amina da Khadijah sun zo suje da Junainah ni sai bayan suna sai inje ko".
Cikin gamsuwa yace.
"Eh amman bayan suna da kwana ɗaya zakije in anyi suna kamar yau sai gebe kije ko".
"Eh hakanma yayi". Tace cikin jin daɗi.
Shi kuwa Abboi a ya juyo ya kalli Dedde ya mata bayani.
Sosai ta shiga cikin farin ciki a take ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Nan ta gaya Khadijah ta fara shiri Addanta ta haifu.
A masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya a daren labarin haihuwar Shatu ya karaɗe ko ina lungu da saƙo na masarautar.
Riskar wannan lbrin a kumnunwan Magauta yayi masifar tada musu hankali.
Hajia Mama kuwa a dare cikin masifar tashin hankali ta wuce gidan bokanta.
Tana shiga tace.
"Meyasa ne wai ku bokaye babu wasu maƙaryata a duniya sama daku, ya mukayi da kai da shaiɗanun makaranka maƙaryata. Shin ba cewa sukayi randa aka haifi yarinyar a wurin yanke cibiya zasu kashe min itaba".
Cikin wani irin masifeffen razana ta daka tsalle tayi baya, sabida wani irin razanenne tsawa da bokan ya daka mata da ƙarfi.
Cikin ɗaga amo yace.
"Ke tafi daga can waya isa ya cutar da wanda Allah ya kare, dama ai na gaya miki babu abinda da zai samu cikin nan sai al'khairi.
Amma da yake ke tinkiyace ƙidahuma kikazo kina min ihu a kai in zaki iya cutar da itan ke kije ki gwada mana".
Cikin tashin hankali gano tayi asarar kuɗaɗenta a banza ta juya ta fita tana cewa.
"Tabbas sai na kashe yar nan babu shakka bazata rayuba".
Shi dai boka tsaki yaja.
Ita kuma ta juyo ta dawo hankali a masifar tashe.
Shi kuwa Sheykh yana gama mgn da Bappa DSS ɗinsu ya kira.
Cikin hikima da iya sarrafa harshe yace.
"Sir naga wasu yaran da akayi nasarar kamasu da laifin kinnafin ko?".
Jim kaɗan yayi tare da cewa.
"Eh yaran fulani masu kiwo ko?".
Da sauri yace.
"Eh su waɗanda akasa suka amsa laifin da ba nasuba akan dole."
Da sauri yace.
"A a kamar yaya laifin da ba nasuba?".
Cikin nutsawa ya gyara zamanshi kana yayi mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi ɗazu.
Cike da al'hini irin yanayin nan na ba'a mugun sarki sai mugun bafade ogan nashi yace.
"Kai Malam ni bansan da zancen nanba, kawai nasan kotu ta bada beli babu batun a nemo wasu a basu laifin da ba nasuba".
Da sauri Sheykh yace.
"Ni nasan baka saniba dan na yarda da adalci ka yanzu me abun yi a kan lamarin yaran nan?".
Cikin takaicin yadda wasu jami'an tsaron kasar nan suka zama azzalumai yace.
"Dole zamu kai zancen kotu ayi bayani a gaban al'ƙali a kawo Sulaiman ya bada shaida, da kuma sauran ma zauna magarƙamar".
Cikin wani irin jin daɗi sanin muddin mgnar taje kotu.
Komai zai iya dai-dai yace.
"To ka taimaka musu a meda case ɗin yaran zuwa kotu".
Cikin nitsuwa yace.
"Toh ba matsala".
Suna gama wayar kuwa ya fara bincikan lmrin a afaren ya turawa wani al'ƙali rahoton.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin Shatu.
Tuni tayi wani baccin gajiya.
Ummi na kwance gefenta.
A hankali yace.
"Ummi bakuyi bacci bako?".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To ita dai mai jego tayi sai nida ƙawar tawane muke hira".
Murmushi yayi kana ya matso.
Miƙawa mishi yar tayi, amsa yayi, ya zauna a bakin gado gefen Shatu.
Addu'o'in ya farayi yana tofa mata.
Kana a hankali ya kalli Shatu data buɗe ido a hankali tana kallonsu.
fuskar yarinyar ya kalla yadda taketa wawure-wawuren hannunta.
Cikin nitsuwa yace.
"Ummi yunwa nefa ya hanata bacci".
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Ita kuwa Ummi da sauri tace.
"Yauwa tunda ta tashi ta bata maman ta tsotsa".
Kai ya gyaɗa kana yasa hannunshi ya kamo na Shatu ta tashi zaune.
Ɗaura mata yar yayi bisa cinyarta, kana yace.
"Bata Baloon ɗin tasha".
Cikin ɗan yamutsa fuska tace.
"Daga yanzu?".
Da sauri yace.
"Eh".
Ya ƙare mgnar yana tattaro rigarta yayi sama dashi, tare da ɗan ɗago kan Baby ya saita bakinta da nimple ɗin ya manna mata.
Ai kuwa da ƙarfinta ta damƙi nimple ɗin.
Wani irin zillo Shatu tai tare da yarfa hannun cikin sakin ƴar ƙara tace.
"Wayyo Allah na Yah Sheykh zafi".
Da sauri ya saki dariyar mugunta.
Hakama Ummi dariyar suke mata.
Ita kuwa cikin kunya ta ɗan sunkuyo tana kallon yadda ƴar taketa zuƙam nonon da har yanzu bai tsastsafo da ruwaba.
Haka nan taji wani irin son yarinyar yana shiga ta.
Tsawon 5 minute tana tsotsar bakin nimple ɗin ta,
wanda saida yayi ja yayi tsami a hankali tace.
"Zafi wlh zata cinye min nimple".
Murmushi yayi tare da lakace hancinta kana ya janye kan yarinyar.
Ya kwantar da ita, ai kuwa gajiya da tsotson yasa tayi bacci.
Ita kuma Shatu meda breast ɗinta cikin riga tayi kana ta koma ta konta.
Sunkuyowa yayi kansu yayi musu addu'a.
Kana ya juya ya fita yana cewa Ummi.
"Sai da safe".
Allah ya bamu al'khairi tace.
Amin yace yana fita.
Yana komawa ɗauki shi yayi shirin bacci kana ya kira Haroon da ibrahima sukayi hira sosai cikin farin cikin.
Daga nan ya kwanta.
Washe gari da safe.
Gimbiya Saudatu ce zaune a falon Shatu.
A hankali ta fito ruggume da yar a hannunta sunyi kyau sosai cikin shigar tasu.
Especially Babyn da aka shiryata cikin wasu kayan sanyi masu taushi red color and white masu masifar kyau da taushi, tayi lib a ciki.
A hankali ta kalli Shatu dake miƙo mata ƴar amsa tayi tare da cewa.
"Masha Allah, ƴarinya kam kekkyawan sai dai Allah yasa kada ta gaji Rashin kunyar uwarta da ubanta".
Sheykh dake shigowa ne yace.
"Ai kuwa zata gada dan kyan ɗan ya gaji iyayensa".
Cikin watsa mishi harara tace.
"Kai matarka ta haihu ka girmama bazaka bar yiwa manya rashin kunya bane wai?".
Da sauri ta juyo ta kalli Shatu dake cewa.
"Toh ai kema baki bar rashin kunyarba bare mu".
Cikin ta kaici tace.
"To uwar fitsara ke kiji da jegon ma mana tukun".
Murmushi tayi tare dasa hannun ta amshi babyn da take miƙo mata tare da cewa.
"Allah ya raya".
Karo na forko a rayuwar Sheykh da yaji Gimbiya Saudatu ta mishi addu'a ko mgn mai kyau.
Cikin jin daɗi yace.
"Amin ngd".
Tsaki taja tare da watsa musu harara ta fita.
Murmushi yayi mai sauti ƙana ya iso gareta.
Ya ruggumeta ita da Babyn cikin raɗa yace.
"Ana Uhubbuk ya habibi Da'iman".
Murmushi tayi dan bata gane da ita yakeba, a zatonta da yar tasu yakeyi.
Shi kuwa ganin bata gane bane sai ya share tare da cewa.
"Ɗazu nazo kuna bacci".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ummi ta gaya min".
Da sauri ya janye jikinsa gareta, jin Muryar Mom Maman Imran wacce itace matar Abbansu ta uku.
A daƙile ya amsa sallamar tata, sai ya kuma saki fuskarsa ganin harda Abbanshi da cingam ɗinsa amaryarsa kenan.
Bayan su zauna ne Shatu ta miƙa musu ƴar ɗaya bayan ɗaya, cikin murmushin Mom tace.
"Masha Allah, tana kama da kakarta".
Amaryar Abban ta miƙawa amsa tayi tare da cewa.
"Kekkyawar Baby Allah ya raya amaryar Habibullah".
Da sauri Abba yace.
"Uwar gida dai, ai kece amarya kam".
Kauda fuska Sheykh yayi kamar baya wurin.
Haka dai sukayi musu Barka suka tafi.
Haka kuma mata da maza bayi da hadimai keta yiwa Sheykh Barka a duk sanda ya gilma cikin masarautar.
Rafi'a kuwa tazo wanda zuwanta yasa Shatu ƙara sakewa sosai gashi Khadija tace mata gobe zasuzo da sassafe, dan jirgin dare zasu biyo da yauma zasu isota.
Alhamdulillah kuma bayan sallan isha'i suka iso.
Salmanu ne ya ɗauke su ya kaisu Rugar Bani, shima zai kwana can saida safe zai taho dasu.
A masarautar Joɗa kuwa abin mamaki kowa yazo barka yaga baby ammma.
Banda Hajia Mama, Mami Matar Affan kuwa kusan nan Part ɗin Shatu ta wuni dan suna masifar ɗasawa.
Washe gari da safe, Aunty Amina ƙanwar Dedde da Khadijah ƙanwar Shatu da Inna Amarya da Junainah suka shirya zuwa masarautar Joɗa.
Inda Ummey ta haɗawa Shatu man shanu, kwan zabbi yajin daddawa dana borkono da zuma da madarar shanu, ko wanne mai yawa suka taho mata dashi.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai Salmanu yayi parking a asalin babban gate ɗin masarautar Joɗa.
A hankali ya juyo ya kalli Khadija dake gefensa yace.
"Kira ta ki gaya mata kun iso a turo masu shiga daku".
To tace kana ta kira Shatu.
Tana ɗagawa tace.
"Assalamu alaikum ƴar uwa rabin jiki kun isone?".
Da sauri tace.
"Eh mun iso muna babban gate ki turo azo a shigo damu naga masu jajayen rigunar nan sai kallonmu suke tayi".
Da sauri tace.
"Toh ba matsala bari yanzu Jamil ko Jalal zaizo".
Tana faɗin haka ta katse kiran, tana ruggume da Babyn ta nufo falon.
Tana fitowa ta hangosu can bisa.
Dinning table suna yin breakfast harda Yah Jafar.
Da sauri Ummi ta nufi inda take tare da cewa.
"Yah dai Shatu kina son wani abune?".
Gyara riƙon da tayiwa Babyn tayi tare da cewa.
"Eh Ummi dama su Junainah ne suka zo, suna can babban gate to inaso a shigo da sune".
Da sauri Ummi tace to kana ta juyo tana ƙwalawa Sara dake kitchin kira.
Da sauri ta fito tare da cewa.
"Na'am".
Cikin kula tace yauwa dan Allah jeki can bakin babban gate ki shigo da baƙi".
Da sauri tace to kana ta fita.
Tana isa tace su shigo da motar har Salmanu yace a a sai kuma yace to sabida tuno akwai kaya.
A hankali tayi gaba motar na binta a baya suna kutsa hancin motar cikin masarautar Joɗa.
Junainah ta sauƙe wani irin masifeffen ajiyan zuciya kamar dai irin ka dade kana neman abu baka samuba ka samu.
Wani irin daɗi takeji na musamman yana ratsa mata jiki da zuciya.
Haka nan taji tsikar jikinta yana tashi tsaye.
Har bakin Part ɗin su. Sukayi parking.
A hankali suka fito.
Shi kuwa Salmanu kayan nasu ya fitar ya ajiye bisa barandar dake bakin ƙofar falon tare da cewa.
"Toh ni zan juya in kin shiga Khadijah kiyi mata barka".
Da sauri Khadijah tace to.
Kana ta sunkuya ta ɗauki jarkan man Shanu Junainah kuwa galam ɗin zuma ita kuwa Sara ta ɗauki kwaryan ƙoyayen.
Inna Amarya kuwa jarkan madarar shanu.
Sara ce a gaba Junainah na biye da ita a baya sauran na biye dasu.
A can cikin falon kuwa dai-dai lokacin Sheykh ya fito Falon gefen Shatu ya zauna.
Jalal kuwa tsaye yake gefensu yana kallon Babyn dake hannun Sheykh su Jamil Affan Yah Jafar kuwa suna Dinning area.
Haka nan sukeji zuƙatansu na harbawa da ƙarfi da ƙarfi.
A hankali Sara ta buɗe ƙofar tare da turo kai tana mai sallama.
A hankali Junainah ta sako ƙafarta cikin falon tare da buɗe muryarta sama tace.
"Assalamu alaikum Adda Shatu".
Wani irin ratsa amon sautin muryar ta kunnuwansu Jalal Jamil Jafar Sheykh sukayi tare da juyowa da sauri suka fuskanci bakin ƙofar ɗakin.
Dai-dai lokacin Junainah ta shigo cikin falon.
Cike da mamaki Sheykh Jabeer, Yah Jafar, Jamil, suka zuba mata ido tare da haɗa baki wurin cewa.
"....!
Littafin GARKUWA na kuɗine akwai Normal group 300, akwai Special Group 1k babbancinsu a wurin yawan posting ne ga ac no 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa.
Sai kuyi screenshort na Debit Alert ɗin sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276 ƴan Normal group in baki da halin biya ta ac zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.
By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin zuba mata ido tare da mamaki muryarta da kamanninta suka haɗa baki wurin cewa.
"Wa alaikassalam".
Shatu kuwa da sauri ta miƙe tsaye tare da nufosu cikin farin cike take cewa.
"Oyoyo Allah sarki My Junnu".
Da gudu Junainah ta ƙara sa inda take ruggume juna sukayi suna dariya.
Da sauri Shatu ta ɗan ɗago kanta ta kalli Khadija date cewa.
"Wato ma Junainah kawai kika gani ko Adda Shatu shekara biyu baki ganniba ko ki kulani".
Da sauri ta saki Junainah ta ruggume Khadijah tana dariya tare da cewa.
"Oh Dija ƙorafi".
Ita kuwa Junainah dariya tayi tare da cewa.
"Oh su Adda Dija kishi akeyi dani".
Cike da mamaki da kuma farin cikin ganin Junainah Ummi ta kalli Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
"Lalako jaɓɓama mon poi".
Da sauri Shatu ta ture Dija cikin tarin so ta ruggume Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
"Aunty Amina Inna Amarya marabanku."
Da sauri suka ɗan juyo jin Sheykh