Showing 327001 words to 330000 words out of 352722 words
mu samu irin tagwayen Nana Faɗima".
Da sauri tace.
"Uhum wuya".
Kissing lips ɗin ta yayi tare da cewa.
"Ke ai yar baiwa ce nine zanke mana laulayi da naƙuda".
Murmushi tayi tare dasa tafin hannunta ta tallabe kanshi a hankali tace.
"Harda naƙudar ma Yah Sheykh".
Da sauri yace.
"Sosai ma kuwa ai na Afreen ɗinma ni nayi naƙudar ke ba kallonki kikeyi hankali konceba..".
Dariya mai sauti tayi sabida lbarta mata yadda yaji a lokacin da karayar da yayi ya ƙara da cewa.
"Mata kuna jin azabar duniya akan hayhuwa bamu da abinda zamuyi muku kuji sanyi sai kyautata muku da nuna muku soyayya in kuna matsayin matanmu iyaye kuwa ayi musu biyayya da tausayawa da kulawa shine kaɗai tukuicin wahalarsu dan bazamu taɓa iya biyansu ba inaji kamar ko wuta Mamey tace in shiga zan shiga dan biyayya sabida azabar da naji wanda nasa irinshi koma fiye da haka taji.
In matsayin yarane kuma mu jiƙansu mu sosu mu kula da amanarsu da Allah ya bamu".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Yauwa niko Yah Sheykh inada tambaya".
Rigarta ya fara turawa sama yana shafa cikinta tare da cewa.
"Allah yasa na sani Boɗɗona".
Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da yin murmushi kana tace.
"In sha Allah ma ka sani".
Murmushi yayi tare dasa yatsarshi cikin hudar jibiyarta tare da cewa.
"Uhum ina jinki".
Kai ta gyaɗa kana tace.
"Yauwa Dr dama ina son kayi min ƙarin bayani ne kan batun laulayi cikin Afreen da kai tayi."
Murmushi yayi tare da cewa.
"To ina jinki tambayi in baki amsa in na sani".
Muskutawa tayi ta fuskanceshi da kyau tare da cewa.
"Bayanin sanadin faruwar haka.
Nake son sani.
Don yana da kyeu mugane dalilin hakan.
Shin yawan shaƙuwace da soyayya tsakanin ma'aurata kawai ke sa hakan ya faru.
Ko kuma wani biology ne na Ubangiji?.
Yake sa miji yayiwa matarsa laulayin ciki a wasu lokuta?".
Murmushi mai cike da shauƙi yayi tare da cewa.
"Eh wato kina son kiji ba'asin miki laulayi ko irin kin huta ɗin nan".
Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa.
"Eh mana kaga in zakayi ta mana laulayi da naƙuda to ko duk shekara zan haihu ba matsala."
Lakace hancinta yayi tare da cewa.
"Uhum".
Kiss ta manna mishi a goshinsa tare da cewa.
"Dan Allah gaya min".
Zamanshi ya gyara kana yace.
"Toh Aish ba yawan shuƙuwa ko soyayya ba ne ke sa miji yayiwa matarsa laulayi.
Asali ma ai dangantakar ba tsakanin matar da mijin ba ne.
Dangantakar tsakanin ɗan ne da ubansa."
Sai kuma ya ɗan ƙara jawota jikinshi tare da cewa.
"Samuwar ɗan, ana nufin kamar yadda ya shafi uwar kai tsaye, to haka kuma ya shafi uban.
Don haka, irin yanayin da ta ji saboda zuwan yaron, shi ma yakan iya jin hakan.
Sai dai kawai nasa bazai kai yawan na uwar ba, saboda ta fi shi kusance da ɗan, kasancewar yana jikinta kin gane ko?."
Cikin gamsuwa ta gyaɗa kai tare da cewa.
"Na gane na gamsu.
To kuma batun naƙuda fa da kace kayi min.
Shin dama na miji kan ji ciwon naƙudan matarsa kamar yadda wasu mazan ke jin ciwon laulayi ciki ne?
Ko dai kwatakwata babu wannan!?".
Kanshi ya ɗan cusa tsakanin wuyanta da kafaɗarta tare da shaƙar ƙamshin jikinta cikin fahimtarwa yace.
"A dai iyakar abinda muka sani zuwa yanzu, wanda kuma bincike da gwaje-gwace likitocin duniya suka tabbatar shi ne, namiji ba ya iya jin ciwon naƙuda.
Sai dai yakan jin tsananin damuwa da ciwon rai ne, maimakon ciwon jiki da raɗaɗi da mai naƙudar take ji.
Sai dai bincike ya tabbbatar da cewa yana da tasiri sosai wurin sauƙaƙa wa matar ciwon naƙudar, idan zai kasance tare da ita har ta haihu".
Da sauri tace.
"Kamar yaya to dan yana kusa da ita zataji ciwon ya sauƙaƙa?".
Kai ya ɗan ɗago ya kalleta tare da cewa.
"Domin idan ya zauna a gunta, musamman in zai riƙe mata hannunta ko ya riƙa ɗan shafa goshinta yana yi mata sannu kamar dai yadda nai miki ta miki lokacin kina naƙudar gab da haihuwar.
To tabbas zataji sauƙi da sassaucin naƙudar da samun haihuwa a sauƙaƙe da izinin ubangiji.
Saboda yayin da suka kasance a haka, jikin matar yana samar da wani sinadari da ake cewa oxytocin , wanda yake sanadin tsattsafowar wannan ruwa mai tsantsi to zai sauƙaƙa fitar yaron daga jikinta.
Da iznin Allah".
Cikin gamsuwa ta sauƙe numfashi tare da cewa.
"To kai kuma kace harda ciwon baya kaji ranar da zan haihu a lokacin ma meya kawo hakan?".
Cikin sanyi ya jujjuya kanshi tare da cewa.
"Allahu ahlamu, kawai abinda nasa a raina wannan wani ikone da ƙudurar ubangiji daya gwada a kanmu wanda tabbas na taɓa riskar makamancin lbrin miji yayiwa matarsa naƙuda, to amman dai a likitance bamu ganoba tukun, dan haka wannan fagene na ubangijin sammai bakwai da ƙassai bakwai, shiyasa nasan zafi da ciwon da mata kanji yayin haihuwa".
Cikin gamsuwa tace.
"Ayyah sannu Yah Sheykh".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ke kam ba cewa kikayi in dan zanci gaba dayi miki laulayin ciki da naƙuda ba, ko duk shekarama ki haihu ba matsala ko".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Eh mana".
Murmushi yayi tare da jawota jikinshi yana mai sa hannunshi ɗaya zai zare boxes ɗinsa.
Fahimtar inda ya dosane yasa ta miƙe da sauri tare da cewa.
"Bari inje wurin Ummey na naji alamun Afreen ta farka".
Fuskarshi ya kwaɓe tare da cewa.
"Kai Aish ni dai banjiba".
Cikin son zille mishi tace.
"Kaji can muryarta tana kuka".
Komawa yayi ya kwanta
Cikin jinjina ƙudurar ubangiji yace.
"Toh ɗaukota kuzo".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Toh". Kana ta fita.
Tana fita ya maida kanshi bisa pillow'nshi yana tasbihi da girman zatin Allah daya samar da cikekkiyar dangantaka tsakanin uwa da ɗanta ta yadda ko bata tare dashi in zaiyi kuka ko ya tashi bacci.
Mamanta zai sanar mata.
Ita kuwa Shatu tana zuwa ta wuce bedroom ɗin Ummi.
Umaymah da Ummin kawai ta samu sunata hira da dariyar Abba daya shigo da kansa ya kira Mamey wai tazo su gaisa da abokanshi, daga nan yayi Part ɗin shi da ita wanda yake kusa da nata.
Umaymah na kwance Afreen na gabanta Ummi kuwa zaune.
A hankali ta zauna gefensu tare da cewa.
"Umaymah Ina su Ummey".
Kai Umaymah ta juya tana danne dariyarta tace.
"Sun tafi Side ɗin ta".
Da sauri tace.
"Harda Mamma".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
"Bakiga tun da yamma Mamma da Rahma sukaje suka gyara komai na Part ɗinta ɗinba.
Sabida Abban yasa an kawo mata sabbin kayan ɗaki sannan anyi duk abinda ya kamata".
Jinjina kai tayi tare da cewa.
"Ayyah".
Sai kuma tace.
"Bari inje in kwanta".
Sai da safe tayi musu.
Ta fita ta tafi.
Ishma da Hibba ta samu kwance bisa gadonta tuni sunyi bacci da alamun Hibba wayama takeyi tayi baccin.
Gefenta ta kwanta.
Su kuwa su Umaymah sukaci gaba da hira.
Sai kusan ƙarfe biyu ne da Afreen ta tashi Umaymah ta kaita ta bata mama tasha kana ta dawo da ita wai karta hana uwarta bacci.
Alhamdulillah fa komai na tafiya yadda ya kamata rayuwa ta miƙa.
Gsky tayi halinta.
Jadda da Sitti da Babansu Aunty Juwairiyya sun koma.
Haroon ma da Jannart sun da Hibba sun koma.
Saura Umaymah da Mamma Aunty Rahma.
Tuni Mamey ta koma Part ɗin ta.
Hajia Mama kuwa ta tabbata mai suffa hudu kafar ladin kogi, hannun fiffigen tsuntsuwar Boleru idanu na Duji, sauran jiki na mutun.
Ta zama abar kallo Abba kuwa ya danƙara mata saki.
Affan kuwa yana nan lfy da ƴan uwanshi.
Yanzu Shatu ta kusa wata ɗaya.
Wanda ya kama satin su Umaymah uku da zuwa kenan.
Abboi kuwa dasu Bappa sunje ga iyayen Rafi'a sun nemi aureta ga Al'ameen an basu kuma.
Kana su Bappa kuwa sun nemawa Salmanu auren Hasfi an kuma basu.
Zaune suke Umaymah Mamey Lamiɗo Galadima Abba
A hankali Lamiɗo ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh Alhamdulillah komai ya wuce ya zama tarihi.
Manufar taruwarmu anan a kan Masarautar Joɗa ne.
Na gama zama da duk manyan fada mun gama tsaida zance duk kowa ya gamsu da batun Jabeer ya mulkin Masarautar Joɗa.
Toh amman inda gizo ke saƙan kun san ɗan naku, na kira sarki Jalaluddin akan batun to shi mgn ɗaya yayi cewa yasan Jabeer mai biyayya ne ga Khadijah da take ƙanwar mahaifiyarshi ma bare ke Aisha da Habibullah da kuke iyayensa yace ya sani tabbas in kuka cewa Sheykh ya mulki masarautar Joɗa ku bashi umarnine ba shawaraba tabbas zai yarda".
Cikin gamsuwa Galadima yace.
"Haƙƙun wannan haka yake tabbas zai yarda bisa dole bisa umarnin iyayenshi".
Cikin sanyi Mamey tace.
"In kuna son in bashi umarni zan bashi kuma nasan zai min biyayya to amman meyasa baza'a bawa wani cikin ƙannen mahaifinshi ba sai shi".
Shiru sukayi baki ɗayansu jin Lamiɗo na cewa.
"Sabida ina son masararutar Joɗa ta tsarkaka ta rabu da duk wata al'ada daba addiniba.
Na sani babu mai iya sarrafa Masarautar Joɗa ya juyata daga bahahuwa zuwa ba damiya ya kauda al'adar bidi'a ya wanzar da sunna sai shi.
Zai gyara masararutar ta yadda za'a dena zalama da son cutar da juna bisa kujerar zai sauyata ta yadda sai mai cikekken ilimin addini ne zai iya mulkarta."
Cikin gamsuwa Mamey tace.
"In sha Allah zaku sameni mai biyayya bisa umarnin ku na in bashi umarni kuma na sani zai min biyayya".
Cikin jin daɗi sukace to.
"Allah ya shige mana gaba".
Amin Amin sukace.
Sai kuma suka nitsu jin Lamiɗo na cewa.
"Alhamdulillah yanzu Ita matarshi ta kusa gama wonka tana gamawa zukjne Rugar Bani suyi kwana ɗaya daga nan su dawo su shirya suje Ƙasar Cameroon wurin iyayen Shatu kuma zasuje da Aliyu (Dr Aliyu) kenan da Basiru da Galadima domin su nemawa Jamilu auren Khadijah ƙanwar Shatu".
Cikin jin daɗi Mamey tace.
"Alhamdulillah to Allah ya kaimu".
Amin Amin sukace.
Sai kuma Abba yace.
"Jalal kuwa mun gama mgna da Abban Haroon kan batun Jalal da Hibba".
Cikin tsananin jin daɗi sukace.
"Alhamdulillah daga nan suka watse taron.
Washe gari su Umaymah suka koma.
Alhamdulillah yau Shatu ta gama arba'in.
Sosai Afreen tayi kuɓul-kuɓul da ita gwanin burgewa ta cika tayi kyau in ka ganta kamar yar wata biyu.
Sosai kuwa Shatu tasha gyara na musamman daga wurin Ummi da Mameynta.
A can ƙasar Cameroon kuwa.
Ba'ana ya gama shirin dawowarsa kab.
Wanda da azatonsa zai kaishi watanni uku sai gashi cikin wata biyu ya gama shirinsa.
Kana ya kamo hanya.
Yau Alhamis da misalin ƙarfe tara na dare yayiwa Rugar Bani diran miki...!
Ban samu nayi editing ba
By
*GARKUWAR FULANI*
Dirar mikiya tare da tawagar shi wanda Baroon na ciki.
A bakin titi motar ta sauƙesu kana suka ƙaraso cikin Rugar tasu da ƙafa.
Dai-dai bakin mashigar Rugar Bani ɗin suka tsaya, sabida ganin uban gayan tafiyar ya tsaya.
A hankali ya lumshe idonshi, tare da shaƙan sassayan iskan garin dake kaɗawa yana ratsa jiki.
Hannunshi ya buɗe ya waresu, ya tanƙwashe kansa bisa wuyanshi cikin muryar dake nuni da gskyar abin dake binne can ƙasan zuciyarsa yace.
"Uhummmmmmm ko wani ɗan adam yanada yanki na musamman da yake cikin bugun zuciyarsa.
Ni kuwa Rugar Bani ce bugun zuciya ta.
RUGAR BANI itace mahaɗin soyayya da Mata. Allah ka sani kaine ma sannin sirrin zuciyata ina son Shatu son da ni kaina ban san adadinshi ba.
Son da bana yiwa kaina shi.
Mata itace cikon farin cikina ban taɓa son wani abu a duniya sama da Shatu ba ya Allah ka yafe min kura-kuraina na baya, ka bani ikon samun Shatu, ka tsare min imanina duk da nasan.
Ban fiye aikata aiyukan gsky ba a rayuwata.
Amman son Shatu gsky ne a cikin zuciyata kuma tuban da nayi gsky ne.
Ya Allah ka jiƙaina ka tausaya min ka cika min burina ka ƙaddara Mata ta tabbata matar aure na, in rayu da ita inuwa ɗaya.
Domin itace sanyin idaniyata in ka samar min ita rayuwata zata inƙanta."
Ya ƙarashe mgnar cikin rauni da rawan muryar kana wasu irin tafasassun hawaye suna masu kwarya mishi.
Sheykh kuwa dake jin duk abinda Ba'ana yake faɗa bisa kiran da Baroon yayi mishi.
Da ƙarfi ya rumtse idanunshi, yana mai jin wani irin azabebben kishi mai masifar zafi da ƙuna yana caccakar zuciyarsa.
So yake ya tashi yaje suyi hira da Mamey'nshi Amman gaba ɗaya yanayi shi ya hautsine kishi ajalin maza.
Domin in mu mata kumallonmu ne tofa su maza yakan iya karsu.
A can Rugar Bani kuwa, cikin rauni Ba'ana yaci gaba da magana cikin sanyin jiki da raunin da bai taɓa riskar shi ba yace.
"Na sani na yarda akan komai ni bazan amsa sunan mai gsky ba ko mai tausayi amman akan tubana da Shatu ni mai gsky ne! Ya Allah ka mallaka min Shatu na yarda na gane babu wani sihiri ko tsafi ko boka ko dodon tsafin da zai mallaka min ita sai kai sarkin da bashi da tamka sarki buwayi gagara misali sarkin kowa na Annabi baban zara".
Kawai sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya daga idanunsa rusunawa yayi ya durƙusa bisa guiwowinsa ya kafa kanshi cikin sassayan yashin garin.
Ya saki wani irin raunataccen kuka.
Gaba ɗaya yaran nashi shiru sukayi cikin tarin mamaki da tsantsar gaskata soyayya ba ƙarya bace shirya kuma ta Allah ce dan tuni sun san yabar komai na tsafi saidai wasu abubuwan dake jikinsa basu karyeba kamar ɓacewa har yanzu yana iya ɓacewa.
Saida yayi kuka mai tarin yawa kana suka miƙe suka nufi cikin gari.
A tsakiyar wurin garken al'ummar Rugar Bani ɗin ya tsaya ya juya gabas da yamma kudu da arewa.
Kana a hankali yace.
"Duk da son hanaku ci gaba da nakeyi, ya rigada Allah ya lamunce muku kuna ci gaba da izininsa."
Kai tsaye garken Bappa ya nufa bayan duk ya sallamesu sai Baroon kawai.
A hankali yasa ƙafarshi ya ratsa tsakiyar garken cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Bappa".
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali da firgici Bappa ya miƙa tsaye.
Tare da cewa.
"Na'am Ba'ana".
Giɗi da Seyo ne dake gefenshi suma suka miƙe da sauri cike da tsoron me zai faru.
A hankali ya zame ya zauna gaban Bappa kana a hankali yace.
"A nan a tsakiyar garken nan na rayu da ita tsawon shekaru goma sha biyu, na rayu da sonta kan gsky.
Koda komai ƙaryane Bappa ka yarda ina son Shatu son da bana yiwa kaina".
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Bappa ya zauna jiki a mace hakama su Gidi da Baroon.
Cikin nitsuwa yace.
"Ba'ana yaushe ka dawo?".
Murya na rawa yace.
"Bappa yanzu na shigo Rugar Bani ko gidanmu ban jeba, ina so ka yarda cewa da gaske ina son Shatu".
Yadda yayi mgnar yasa Bappa jin wani irin rauni da tausayinsa a hankali yace.
"Na yarda Ba'ana na sani kana son Shatu".
Da sauri yace.
"Bappa ka tuna kun min al'ƙawarin aura min ita".
Da sauri Bappa yace.
"Na tuna Ba'ana ban manceba to amman al'ƙawarin Allah ya ture namu ya rigada Allah ya tsara Shatu ba matarka bace."
Cikin sauri ya miƙe yana cewa.
"A'a a'a bana son jin haka".
Yana faɗin haka yana yarfa hannun a haka ya nufi cikin gari Baroon na biye dashi a baya.
Shiru Bappa da su Giɗi sukayi cikin tarin rauni.
Shi kuwa Ba'ana a tsakiyar gidansu ya zauna gaban Bukar da Bugulu mahaifiyarshi.
Cike da mamaki suke kallonsa jin yadda yake kuka babu sassauci.
Cikin tsananin tausayi da so irin na iyaye da yaransu.
Sukayi kanshi cikin kula Bugulu tace.
"Ba'ana yau ranar farin cikine a garemu ba ranar kuka ba.
Kada kayi kuka muna cikin farin cikin ganin juna".
Ba mgn sai kuka.
Da sauri Bukar ya jawoshi jikinshi tare da cewa.
"Gaya min me ya saka kuka haka?".
Cike da rauni yace.
"Karo na forko dai a rayuwata Baba zan roƙeku in kuna da hali ku aura min Shatu ku dawo da ita gareni".
Ganin tsananin tashin hankali da yake cikine yasa sukace.
"To kwantar da hankalinka ina shine kawai burinka zamu dawo maka da farin cikin ka".
Da sauri yace.
"Allah Baba?".
Kai ya gyaɗa mishi cikin tausayinsa.
Shi kuwa jin hakane ya zame ya kwanta ya ɗaura kansa bisa cinyar babanshi yana sauƙe numfashin kuka shima Baroon gefe ya zauna.
Sheykh kuwa cikin tsananin tashin hankali na kishi ya rumtse idanunshi da ƙarfi.
Kana ya taune lip ɗinsa na ƙasa.
Shatu ce zaune ita da Mamey har cikin ɗakinta Afreen na hannun Ummi.
A hankali Mamey tace.
"Shatu".
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Mamey tare da cewa.
"Na'am Mamey na".
Gyara zama tayi tare da cewa.
"Shatu batun mijinki ne, nake son kisa baki a lamuransa".
A hankali tace.
"Mamey waɗannen lamuran ne?".
"Shin kina son Mijinki ya mulki masarautar Joɗa?".
Ta jefa mata tambayar kai tsaye.
Da sauri Shatu ta zubawa Ummey nata ido ta karanci yanayinta na ƴan wasu daƙiƙu kana a hankali tace.
"Mamey in dai kuna so ya mulka to nima zanso, hakan sai dai ina tsoro kada a sabautamu".
Da sauri Abba dake shigowa yace.
"A'a Shatu in sha Allah babu komai babu abinda zai faru sai al'khairi.
Burinmu ya mulki masarautar Joɗa ne dan ya gyara ta zama Tsarkakkiyar masarauta mai wadatar sunna da ƙarancin al'adun bidi'a".
A hankali ta gyaɗa kanta tare da cewa.
"Shi kenan Abba Allah ya sanya al'khairi yasa hakan ya zama ci gaba ga Musulunci da musulmai".
Amin Amin sukace.
Kana ta ɗan yunƙura zata tashi.
Ganin Abba ya shigo yana amsar Afreen tare da cewa.
"Ƴar lukuta".
Murmushi tayi kana ta kalli Mamey dake cewa.
"Ki fara nuna mishi amfanin ya mulki masarautar bisa hikima ta yadda zaki sa mishi abin a ransa ba tare da yaji dole akayi mishi ba".
Da sauri tace.
"Toh Ummeyna".
Har ta isa bakin ƙofar kuma sai ta tsaya jin Mameyn na cewa.
"Umurnine fa Shatu ki fara daga yau".
Ajiyan zuciya mai sauƙi ta sauƙe tare da cewa.
"In sha Allah kuwa Mamey".
Tana fita Ummi na biye da ita a baya.
A bakin ƙofar shigowa suka haɗu da Sheykh shida Affan.
Wuce sukayi kana su kuma suka fita.
Kai tsaye har bedroom ɗin suka wuce.
Suna hira ta tsakanin iyaye da yaransu.
Da sauri Sheykh ya ɗan ɗago ya kalli Mameynshi tare da sakin murmushi jin tana cewa.
"Jabeer wannan gemun haka ka ɗan rageshi mana ga saje ga gemu".
A hankali yace.
"Mamey bai min kyau bane?".
Da sauri tace.
"A'a wlh yayi maka kyau sosai ma fiye da zaton mai zato sai dai yasa kayi kwarjini da yawa ni kaina sai inji kana min kwarjini".
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
"Uwa mai daɗi Allah ya bar mana ke Mameynmu".
Dariya Abba da Affan sukayi tare zubawa Sheykh ɗin ido jin yana cewa.
"Toh gemu da saje ku kiyayi kanku da sa Mameyn Jabeer ganin kwarjini mai yawa".
Jamil da Jalal da Yah Jafar Imran dake shigowa ne suka haɗa baki wurin cewa.
"A to a haɗa harda mu dan muma kansu mana kwarjini yana mana yawa Hamma Jabeer".
Murmushi yayi kana suka shigo suka zauna suna hira cikin jin daɗi.
So a nanne yaji kaso 30