Showing 27001 words to 30000 words out of 352722 words

Chapter 10 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30709

wanda duk wanda ya daka dasu ƙarshe mutuwa yakeyi ko ya haukace, to a karon nan zamuce babu shaɗi domin ai shi shaɗi al'adace ba shariya ba.
Zamu kuma bawa salmanu dakarun tsaro masu bibiyar lamuranshi a sirri dan gudun kada ayi mishi yankan rago kamar yadda akayiwa Hashimu duk da dai bamu da sanin shin Ba'ana ne koko kafuran Ɓachamawa ne".
Da sauri ɗaya daga cikin dottawan yace.
"Yo ai shima Ba'ana kusan kafurin ne, tunda baya salla kuma matsafine".
Bappa ne ya nisa tare da jan dogon numfashi mai tsawo sannan yace.
"Bazai yardaba duk yadda za'ayi sai yace dole ayi bulalin Shaɗi, kana kuma muddin akace baza'ayi Shaɗi ba to haƙƙun zai kashe Salmanu kisan da bazamu samu huja ko madafaba".
Shiru sukayi baki ɗayansu cikin kamala da nitsuwa da rauni Bappa yace.
"Kaɗan kenan daga illar riƙo da Al'adar daba addini ne ya tanadar dashi ba".
Ardonne yayi gyaran murya cikin sanyi yace.
"Ya Allah ka kawo mana mafita kan wannan bawa naka Ba'ana daya zame mana masifa a rayuwarmu".
Ɗaya daga cikinsu wanda tunda suka zauna baiyi mgna bane ya gyara zama tare da cewa.
"Gashi shi kamar ibilis yake, ya rigada ya gama dafa kanshi wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa".
Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba'ana wato Chubaɗo yana cewa.
"Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma'jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba'ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani."
Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace.
"To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?".
Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace.
"Eh na sani".
Cikin sauri sukace.
"Bulalin inane a wacce ƙasar suke?".
Cikin tsoro yace.
"Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba".
Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi.


Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira.
Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja'eh da kuma Malam Umaru.
Sun shiga jimami mai yawa.
A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba'a sake kashe wani ba a cikinsu.

Yau tun da yamma Ba'ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace,
Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen.

Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu,
A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace.
"Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa.
Ga buzuna zauna a kai".
Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin.
Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta,
Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa.
"Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce".
Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa.
"To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?".
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
"In an nemi mijinki ba'a sameshiba dole kanki za'a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki".
Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace.
"Ingo ki fara shan wannan".
Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta.
Cikin takaicin halinsa tace.
"Me wannan kuma?". dariya yayi tare da cewa.
"Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso".
Cikin sanyi tace.
"Sai dai in na koma gida zansha".
Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace.
"Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi".
Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba'ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta.
Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Mata nayi miki kyau ne?".
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye.
Saida ta goge bakinta tace mishi.
"Na shanye kazo". Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace.
"Me kika gani a ciki?".
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Nono fari ƙal mana".
Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa.
"Me kika gani?". Tura baki tayi tace.
"Farin nono mana". Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani".
Ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Sha kuma?".
Kai ya jijina mata kana yace.
"Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu".
Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha.

Wani irin wawan zabura tayi jiki na tsuma da karkarwa cikin tsananin firgita da tarin tsoro ta sake kwaryar....!

By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 8

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘


Kada dai ku mance Free page ne, yana kuma gab da karewa.


*Ga mai buƙatar saya ga number ta, 09097853276 turo ɗari uku ko dubunki ɗaya kacal domin samun damar karantawa cikin salama, Ga Ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin biya sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in ba halin turawa ta ac bisa dole turo katin mtn.*



Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar.
Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba'ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?".
Gaba ɗaya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata.
Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin ɗaga murya yace.
"Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki".
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"Ban yardaba me ka shayar dani?".
Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam.
Kawai sai tasa mishi kuka.
Cikin tashin hankali yace.
"Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba.
Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba".
Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa.
"Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce".
Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai".
Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma.
A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haɗe tare da cewa.
"Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi.
A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama.
Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi?
ko dai wani kikeso ba niba?".
Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
"A a ni kam babu wanda nakeso."
Kanshi ya ɗan rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace.
"Dawo ki zauna".
A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna,
shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa.
"To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun Arɗo Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake".
Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa.
"A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani.
Makaranta kai kuma baka hanaba".
Cikin haɗe fuska yace.
"Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaɗi bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso".
Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace.
"Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba'ana kada ka yarda da ƙaryar mutane".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Uhum kinga nan cikin ranɗar nan, to bulaline wanda nake shaɗi dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaɗi basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe,
Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa'ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba".
Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa.
"Ya Ba'ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba".
A hankali yace.
"Eh ai yau kam zaki haɗu dashi".
Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa.
"Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla."
Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata.
"To Mata jirani inzo in rakaki Mana".
To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi.

Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta ɗan tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo,
cikin jin daɗi ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa.
"Bari inje wurinsu Ya Giɗi, in tayasu ɗaure shanun".
Murmushi yayi kana yace.
"To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba".
To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma.
Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa.
"Yaya sannunku da dawowa".
Da sauri Giɗi da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa.
"Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?".
Da ido ta nuna musu Ba'ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su.

Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi.
Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi.
Har saida Giɗi yace.
"Heyy Ya ba'ana Ubanka na kiranka".
Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa.
Shi kuwa Ba'ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo.

Cikin sakalci da gajiya Giɗi ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace.
"Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon ɗaure shanu ba, ga Shatu zata tayaku".
Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata ɗaure dabobbin suna ɗan dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu.
Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida.
Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa.
"Ya Giɗi tareni, na gaji ga damunku".
Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke.

Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya ɗauke kana ya buɗe kwaryar, ludeyi ɗaya ya sa musu a ciki.
Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa.
"Ya Giɗi kama ka bani". Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba.
Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata,
Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da ɗan uwanta tsokonta Giɗi abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace.
"Ya Seyo zauna ga fili."
To yace kana ya zauna suka fara sha,
Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace.
"To wai mu aka kawowa ko kune?".
Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi,
Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya ɗauki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace.
"To ni naci girma".
Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa.
"A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi". Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi,
Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi,
Cikin kula yace.
"Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu,
Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace.
"Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla".

To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.

Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al'wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci.
Yayinda ko wanne garke an bar mutun ɗaya sabida tsaro...

Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.


Suna zaune, yaro yayi sallama, yace.
"Wai ana kiran Shatu a woje".
Ummey ce ta ɗan juyo ta kalli yaron tare da cewa.
"Wake kiranta?".
"Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne".
Yaron ya faɗi.
Da sauri Ummey tace.
"A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo".
To yaron yace kana ya juya ya fita.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa.
"Yace wai ince mata, ta fito woje".
"Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa".
Sai kuma Inna ta ɗan kalli Shatu tace.
"Tashi kije ai mun gama aikin ma".
Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma,
kwano ta ɗauko a konɗonsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu.
Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon.
A hankali ta ratsa gefen su Ya Giɗi ta wuce.

Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da Arɗo Yabani ya tabbata.

Suna fita suka sameshi zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasu.
Da sauri Junainah ta isa gareshi tare da cewa.
"Oyoyo yaya Salmanu".
Ajiye kwanon tayi a gefenshi.
Da sauri yasa hannunshin suka tafa da hannunta data miƙa mishi, cikin sakin fuska da nitsuwa yace.
"I miss you ƙanwali".
Dariya mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
"Miss you too my dear".
Dariya mai sauti sukayi a tare cikin jin daɗi wanda aka kira da Salmanu ya lakace hancin Junainah tare da cewa.
"Alhamdulillah alama ta nuna ƙanwaliya tana zuwa makaranta babu wasa".
Cikin jin daɗi tace.
"Sosai ma ya Salmanu yanzu ajiyana huɗu fa, yanzuma dan hutu mukeyi, kuma gashi ko a gidama Ina karatu".
Jinjina mata yayi da hannunshi kana, ya jawo kwanan data ajiye tare da cewa.
"Ƙanwaliya me kika kawo mim ne?".
Cikin murmushi tace.
"Gasheshen naman tattabarune Ya Salmanu barima in koma ciki inci rabona inci na Addana".
Kafin ya ankarama tuni ta juya da sauri tayi cikin gida.


Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da kallon Aysha dake jingini


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login