Showing 339001 words to 342000 words out of 352722 words
maida numfashi da haki take cewa.
"Oyoyo Ummey na yau kam daɗi zai kasheni".
Itama Ummey wani irin ruggume ta tayi cikin tsantsar jin daɗi da tsananin so.
Tace.
"Oyoyo Shatuna Boɗɗona mangana yar al'barka."
Sai kuma tayi saurin janye jikinta jin yadda ɗan cikin yake wutsul-wutsul da sauri ta kamo hannun ta.
Ita kuwa Shatu hawayen farin ciki take zubdawa.
Inna Amarya kuwa taburma ta shimfiɗa musu a tsakiyar gidan.
A ƙarƙashin inuwar bishiyar mango da bishiyoyin ayaba suka zagayeshi hakan ya bada daddaɗan inuwa mai sanyi.
Da sauri Ummey ta ajiyeta.
Ruwan sanyin da Inna Amarya ke miƙa mata ta amsa ta bata.
Ba musu ta amsa ta kafa kai dan hakin da takeyi yasata jin ƙishi.
Gefenta Junainah ta zauna.
Ummey kuwa gabanta ta zauna Inna Amarya kuma gefenta.
Junaidu kuma shigar da kayanta ɗakin Ummey yayi kana ya fito ya gaisheta sannan ya tafi.
Ita kuwa Shatu a hankali ta zame ta kwanta ta ɗaura kanta bisa cinyar Ummeynta cikin sanyi tace.
"Alhamdulillah yau gani ga Ummey na".
Murmushi Ummey tayi kana ta shafa cikinta tare da cewa.
"Shatu ki dena wasa da jikinkifa, kada kije ki tadawa kanki naƙuda lokacin ta baiba".
Cikin jin ɗan kunya tace.
"Toh Ummey itama ai yau tana farin cikin ganinki".
Sai kuma tayi maza ta miƙa zaune.
Jin muryar Bappa na cewa.
"A a a masha ALLAH yau gani ga Shatu na".
Cikin sauri ya iso inda suke gefenta ya zauna ita kuwa hijabinta ta gyara tana ɗan rufe cikinta alamun kunya tace.
"Oyoyo Bappa na".
Cike da jin daɗi yace.
"Sannu Shatu na.
Nanfa suka fara gaggaisawa da hirar yaushe gamo, ɗaya Bayan ɗaya haka take tambayar ahlinta wato ahlin Abboi.
Su iro ma suna dawowa aka zauna ana hira.
Inna Amarya kuwa da Ummey gidin murhu suka koma sunata haɗa miyar jumma'a.
Junainah kuwa na liƙe da ita.
Sai salla ne kawai yake ɗagasu a wurin.
Sai bayan sallan isha'i kuma duk suka zauna bisa taburma suna hira suna cin abinci.
Cikin nitsuwa Shatu ta juyo ta kalli Bappa dake gefe dashi dasu Iro yayinda farin wata ya haskasu ras, numfashin ta ɗan fesar tare da cewa.
"Bappa na ya lbrin su Yah Giɗi na".
Tayi mgnar hawaye na ciko mata ido".
Cikin sanyi yace.
"Wlh Shatu jikina na gaya min su Giɗi suna gab da baiyana.
Dan wayewar asuban yau nayi mafarkinsu wai Mijinki ya dawo min dasu da hannunshi.
In sha Allah kuwa suna kan hanya da izinin ubangiji tabbas suna hanya, muci gaba da Addu'o'in da muka sabayi".
Cikin gamsuwa da jin sanyi tace.
"In sha Allah kuwa."
Nan sukayi ta hira maƙota nata zuwa Binto budurwar Ya Gaini tazo haka Hari.
Sune basu shiga sai kusan ƙarfe sha biyu na dare.
Yau ko Junainah batayi bacci ba.
Suna shiga suka kwanta, Ummey na kan ɗaya gadon ita kuwa Shatu ita da Junainah suna kan ɗaya gadon.
Cikin sanyi Ummey tace.
"Uhumm Shatu ya mai gidan naki da mutanen gidan naku?".
Dogon numfashi ta sauƙe tare da cewa.
"Uhumm Alhamdulillah Ummey yana lfy yace in gaidaki shima zaizo da tarema zamuzo to sai aka kai wasu asibitinsa sunyi hatsiri".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Allah ya basu lfy".
Amin tace kana a hankali ta gyara kwanciyarta tare da jawo hand bang ɗin ta hannun tasa ta fito da cakuleti masu daɗi ta miƙa Junainah da sauri ta amsa ta ɓare tasa a baki.
Ita kuwa Ummey ta kalla tare da cewa.
"Uhmmm mutanen gidansu kuwa masu cike da sarƙaƙiya da mugunta suna can sunata fama da muguntarsu.
Kai Ummey gidajen sarauta akwai wuyan zama".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Ke dai ki dage da addu'a in sha Allah babu abinda zai sameki".
Cikin gamsuwa tace.
"In sha Allah kuwa, shima Yah Sheykh yana yawan mana addu'o'in".
Kai Ummey ta jinjina cikin gamsuwa.
Dai-dai lokacin kuma.
Sheykh ne tsaye tsakiyar falonshi gaba ɗaya ya rasa me ke mishi daɗi.
Tsaki ya ɗan ja, tare da cewa.
"Gidan ba daɗi".
Sai kuma ya zauna bisa kujera, a karo na biyar ya kuma kiranta stiil bata ɗagaba.
Sabida wayar na sailent kuma tana cikin hand bang ɗin ta.
Allah ya sani ta mance da batun wani suyi waya dashi.
Dogon tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"Yayi kyau Aish wato kin samu su Ummeynki ni kin mance da nima".
Haka dai ya kwanta yanata jan tsaki a haka yayi bacci.
Ita kuwa da Ummey kusan kwanan zaune sukayi ranar.
Koda asuba sukayi salla wani hirar suka kuma buɗe wa.
Harda Bappa daya shigo.
Nan ta jawo jakar da Sheykh yace tsarabar Junainah ne.
Tana buɗe wa daga sama ta samu wata leda cike da kayayyakin kwalam na makwaɗaita irin Junainah.
Sai kuma wasu irin tsala-tsalan turame atamfa da Shadda da lashi da hijabai guda biyar-biyar iri ɗaya alamun na Ummey da Inna Amarya.
Sai kuma wasu dogayen riguna masu kyau guda biyar irin na larabawa da alamun na Junainah ne sai dai zasu ɗan mata tsawo kaɗan.
kana sai takalma na manya da kamar na Junainah.
Sai kuma wasu irin yadin Getzner masu kyau kala biyar sai manyan al'kyabba guda biyu da alamun na Bappa ne.
Sai kuma kuɗi a cikin ko wanne kaso alamun kuɗin ɗinkin ne, sai can ƙasar jakar kuma turaruka ne masu tsadar gaske da sabulai da mayukan shafawa.
Ido kawai suke zuba mata.
Ita kuwa cikin jin daɗi tace.
"Gashi inji Yah Sheykh".
Cikin jin daɗi Junainah ta fara tsalle da ribibi kan kayan zaƙin sam batama kula kayan suturun ba.
Bappa da Ummey da Inna Amarya data shigo musu da karin kumallo kuwa cikin fulaku da kawaicin fulanin kwarai sukace.
"Kai Shatu ya zakiyi ki barshi yayi mana irin wannan hidimar haka".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummey kawai kusa mana al'baka".
Cikin sanyi suka haɗa bakin cewa.
"Allah ya muku al'baka ya sauƙeki lfy".
Amin Amin tace tana jawon akoshin ɗumamen gashesshen naman.
Nan Bappa ya fita su kuma suka zauna suka fara cin abinci.
Ranar ma dai haka suka wuni hira, sam ko ta kan wayarta bata biba.
Yauma kamar daren jiya haka sunata hira.
A ɗaki duk da kusan sha ɗaya ne.
Sheykh kuwa a hankali ya fito falo inda Ummi da Juwairiyya suke zaune dan Juwairiyya ta shigo dubata Ummi da jiki a haka nan a hankali yace.
"Ummi gidan shiru ba daɗi".
Da sauri Juwairiyya ta kalleshi tare da son gimtse dariyarta.
Kana a hankali tace.
"Ai fa kam gidan ba daɗi fa Sheykh".
Kanshi ya ɗan jinjina kana yace.
"Ummi ki shirya gobe zamuje Rugar Bani".
Cikin jin daɗi Ummi tace.
"To Allah ya kaimu".
Amin Amin yace yana mai juyawa ya koma falonshi yana maici gaba da kiran Shatu.
Dai-dai lokacin kuwa Shatu kwance take gefen Ummey cikin kula Ummey ta kalli cikin nata tare da cewa.
"Ya kai wata nawa Shatu?".
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
"Bakwai".
Kai ta gyaɗa cikin gamsuwa tare da cewa.
"Masha Allah, zan haɗa miki mgnin zaƙi ki fara sha yana sauƙaƙa naƙuda".
Cikin gamsuwa tace.
"Toh Ummey na".
Sai kuma tasa hannunta ta jawo hand bang ɗin ta ganin haske da sauri ta fito da wayarta.
Cikin juya ƙwayar idanunta ta amsa kiran tare da karawa a kunne a hankali tace.
"Assalamu alaikum".
Wani irin sassanyan numfashi ya fesar tare da cewa.
"Wa alaikassalam yah Aishhhhhhhh".
A hankali ta ɗan juya ta kalli Ummey tare da yin ƙasa da murya tace.
"Ina wuni".
Cikin narke fuska yace.
"Aish nayi fushi dake".
Da sauri tace.
"Na tuba".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Wato kin samu su Junainah kin mance dani ko? Kin barni da kewa gaba ɗaya gidan ba daɗi".
"Murmushi tayi tare da cewa.
"Junainah ce take shagaltar dani".
Da sauri yace.
"Okay to ki shirya gobe da wuri zamu zo ɗaukari".
A hankali tace.
"A a dai kam Hamma".
Kauda zancen yayi da cewa.
"Ya Baby na tana Lfy ko".
"Alhamdulillah tana lfy".
"Masha Allah".
Yace kana sukaci gaba da hira
Daga bisani sukayi sallama.
Ita harda Allah gani take zai barta tayi koda mako ɗaya ne.
Koda ta juyo taga tuni Ummey da Junainah sunyi bacci.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi Bedroom yana mmkin tsawon lokacin da sukayi suna hira.
Allah ya sani bai taɓa zato da tunanin shaƙuwarsu ta kai hakaba saida bata kusa dashi.
Washe gari bayan anyi sallan la'asar.
Suna fitowa suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Suna shiga abincin rana sukaci kana suka fito cikin shiri suka shiga mota.
Jalal ke tuƙi Sheykh na gefensa.
Jamil kuwa na baya kusa dasu.
Ummey kuwa tana can baya sit ɗin ƙarshe.
Waya takeyi da Umaymah tana sanarmata cewa gasu nan kan hanya.
Ƙarfe huɗu da kwata dai-dai suna bakin ƙofar gidan Bappa.
A hankali sukayi parking cikin nitsuwa Sheykh ya buɗe marfin gefensa kana ya zira ƙafarsa ta dama ya fito.
Da sauri Bappa ya miƙe tsaye ganin Sheykh.
Hakama Junaidu.
Shima Sheykh da sauri ya nufi Bappa Jamil da Jalal na biye dashi a baya.
Ummi kuwa yanzu ta buɗe marfin motar ta fito.
Ciken girmamawa Sheykh ya miƙawa Bappa hannu tare da ɗan rusunawa.
Cike da mutumtaka Bappa ya bashi hannun fuska cike da fara yace.
"A a a a masha ALLAH maraba lale marhabin da baƙin kirki kai sannunku da zuwa".
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gasheshi yayinda Junaidu kuwa ya rusuna yana gaida Sheykh.
Cikin tsananin karramawa Bappa ya juya yace.
"Maraba lale kushi go ku shigo daga ciki."
Cikin sanyi Sheykh yace.
"Bappa nanma yayi ai".
Da sauri ya jujjuya kai tare da cewa.
"A a Muhammadu kada muyi haka da kai maza ku shigo ciki, ai nanma gidane".
Yana faɗin haka ya juya yayi cikin gida.
Dole tasa Sheykh ya bisa a baya.
Kana Jalal da Jamil na biye dashi.
Ummi kuwa na biye da bayansu.
Haka nan sukeji suna mararin shiga cikin gida.
Yayinda gaba ɗaya zuciyarsu ke bugawa da sauri-sauri.
A hankali Sheykh ya sako ƙafarsa ta dama cikin gidan dai-dai lokacin kuma ya yayi ido biyu da....!
By
*GARKUWAR FULANI*
[4/12, 8:34 PM] Maman Aslam: Agogon hannunsa, ƙarfe 11:30 pm na dare har yanzu Shatu bata shigo inda yakeba.
Idanunsa ya rumtse da ɗan ƙarfi,
tare da gyara kwanciyarsa, ya mai jin wani irin zazzafan kishi na taso mai.
Allah Ya sani yana jin ciwo da zafi acikin zuciyarshi, har yanzu idan ya tuno yanayin tashin hankali da kuma tausayi da rauni’n da ya gani a fuskar Shatu, lokacin dasu Jalal ke dukan wannan taƙadirin tsohon saurayin nata.
Mchewww yaja wani dogon tsaki a fili yace.
"Sabida shine zata barni ni ɗaya a ɗaki kamar wani marar galihu?"
Muskutawa yayi tare da fesar da zazzafar iska ta bakinsa, sosai yakejin kuna acikin zuciyarsa, wanda kuma duk akan Kishin Shatou’n da yakeji ne.
A haka dai bacci b’arawo yayi awon gaba dashi bayan yayi ta juye-juye.
Ita kuwa Shatu tunda suka dawo ta gaza tsaida hawayenta.
Allah Ya sani bata taɓa jin son Yah Ba'ana aranta ba, bata kuma jinsa a matsayin saurayin da take buri da fatan aure, sai dai tasan tabbas tana mishi so irin na ɗan uwan taka.
Tana jinshi tamkar su Yah Al'ameen dasu Yah Giɗi.
Tana mishi so irin na ƴan uwa musulmai da son ya gyara rayuwarsa ko ya samu rabauta ranar gobe kiyama.
Kuka sosai takeyi, rungume da Afreen damunta da yarinyar tayi ne kuma yasa ta fito da ita.
A falo ta samu Ummi zaune ita da Jalal.
Cikin disashewar murya tace.
"Ayyah Ummi ga Afreen kaina ciwo ina so inyi bacci ta hanani".
Da sauri Ummi ta miƙo hannu ta amsheta tare da cewa.
"Tasha mamanta ai ko?".
Kai ta gyaɗa mata alaman “Eh.”
Jalal ne ya ɗan kalleta sosai fuskarta, ta kumbura tayi jazir idanunta kuwa sunyi tib tib.
A hankali ya maida kanshi ga Ummi yana mai ci gaba da cewa.
“Ai daga can Rugar tasu cibiyar bincike na jiha muka kaishi.
Alhamdulillah kuma shida bakinshi ya amsa dukkan laifukansa tare da yin bayanin komai, ya tabbata cikekken mai laifi da ake nema ido rufe, yanzu
kai tsaye ba ɓata lokaci za'a kaishi kotu ta yanke mishi hukunci ranar Monday da izinin ubangiji.”
Cikin sanyi Ummi tace.
"Allah sarki, Allah yasa ya samu da sauƙi".
Miƙewa Jalal yayi tare da cewa.
"Wani da sauƙi kuma Ummi ai yadda yayi ta kashe mutane, da sace dabbobin su shima kasheshi za'ayi a rage mugun iri a duniya".
Jin hakanne kuma yasa cikin sauri Shatu ta koma ɗakinta.
Bisa kan gadonta ta kwanta tare da kifa kanta kan pillow, wani irin sassanyan kuka ne ya kwace mata.
Lokaci daya Komai ya fara dawo mata sabo, tun randa ta fara ganin Yah Ba'ana da kuma yau da tayi mishi kallon da take tsoron kada ya zama na ƙarshe ne.
Saboda ita dai bata taɓa sanin cewa yana sata da kashe mutane ba.
Haka ta dinga sak’e sak’e acikin zuciyarta, a ranar dai haka suka kwana kowa da abinda ke damunsa.
Washe gari kuwa, ranar Lahadi, Sheykh yana gida wuni zur amman Allah bai sa yaga idon Shatu ta fito ba.
Wannan abun ya ƙara ingiza mishi zafin kishinsa, ji yakeyi tamkar yayi ta ihu dan takaici.
Bayan sallan azahar ne.
Ya dawo a falon ya samu Ummi da Aunty Juwairiyya da Mamey.
Wacce kuma ta shigo ne dan ta duba Shatu, da yawan kuka ya sakar mata zazzafan zazzaɓi da ciwon kai.
To ta fito daga d’akin Shatou d’in kenan, suna zaune afalo ya dawo.
A hankali ya ɗan sunkuyo ya shafa kan Afreen dake cinyar Mamey.
Tare da cewa.
"Mamey ɗazu naje kina bacci".
Tana kallon yadda yake shafa kan Afreen yana cewa.
"Allah ya miki al'barka".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To masu ƴaƴa kaima Allah yayi maka al'barka".
Cikin jin daɗi yace.
"Amin Amin Mamey na".
Murmushi tayi kana tace.
"Muna son mgn da kai".
Da sauri cike da biyayya yace.
"Toh Mamey gani".
Miƙewa tayi ta nufi waje, shikuwa gyara al'kyabbar dake jikinshi yayi tare da bin bayanta.
Kai tsaye Part ɗin Abbanshi ta nufa yana biye da ita a baya.
Da sallama suka shiga.
Murmushi Abba yayi tare da miƙa hannunshi ya amshi Afreen daketa raba ido.
Ita kuwa Mamey gefenshi ta zauna.
Da sauri ya zauna gabansu a ƙasa bisa Austrian carpet, ya tanƙoshe sawunshi ya fuskancesu da kyau.
Gyaran murya Abba yayi tare da zuba mishi ido, wanda haka yasa shi yin ƙasa da kansa.
Shiru-shiru basuyi mgna ba, hakane yasa ya sake ɗago kanshi da sauri yayi ƙasa da idonshi sabida ganin daga Abban har Mameyn ido suka zuba mishi.
A hankali ya fara motsa lips ɗin shi yana cewa.
"Astaghfirullah!!".
Ya fara tubawar ubangijin mu.
Kafin ya tubarwa iyayen nasa dan hakan da sukayi ya rauna tashi sabida bai san laifinsa ba.
Su kuwa sun mishi hakane dan su sa mishi rauni da kuma halarto da biyayyarsa.
Karo na uku ya kuma ɗagowa ya kallesu.
Kawai sai ya tankwashe kansa bisa kafad’arsa murya cike da rauni yace.
“Dan Allah Abba Mamey kuyi haƙuri ku gafarceni idan wani laifi nayi muku, ku sanarmin dan in kiyaye gaba kada in maimaitashi".
Sai kuma ga idanunshi sunyi rau-rau sun fara wani sheƙi alamun hawaye na tsastsafowa daga cikinsu.
Cikin tsare murya da fuska da kauda wargi Abba yace.
“Muhammad!”
Da sauri murya na rawa yace.
"Na'am Abbana".
Sai kuma ya kalli Mamey da itama ta kirashi.
Amsawa yayi tare da zuba musu ido.
Kai titsiyewar iyaye akwai sa rawan jiki da fargaba a zuciyar ɗan adam.
Cikin tsananin kausasa murya Abba yace.
“Ina bukatar in baka umarni kayi wani abu, ban saniba ko zaka iya min biyayya ko bazaka iyaba".
Cikin sauri ya kalli Mamey da tace.
"Ni umarni nake so in baka".
Da rarrafe ya ƙara matsosu cikin rawan murya yace.
"Abba matuƙar dai abin da zaka sani bai saɓawa umarnin Ubangiji da tsarin Addinin Musulunci ba, in sha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka da izinin Ubangiji."
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe cikin yanayin gamsuwa.
Shi kuwa a hankali ya kamo hannun Mamey, cikin sanyi ya had’a su ya tallafe haɓarshi sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya murya na rawa yace.
“Tsawon shekaru goma sha uku ina kuka dare da rana kuka na cikin zuciya, ina so in ganki da idona ma Allah bai bani Dama ba.
Nakanji wani irin daɗi na musamman in Umaymah ta bani umarnin inyi abu kai tsaye, sai inji kamar ban rasa uwar da zata tirsasani yin abinda ya dace ba.
Mameyna bani umarni da izinin ubangiji zanbi zan miki biyayya".
A hankali tasa hannunta tsakiyar kanshi tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka".
Da sauri yace "Amin". kana ya kallesu yace.
"Menene umarninku?."
Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.
"Umarninmu shine ka amshi mulkin Masarautar Joɗa, da Lamiɗo yake son yin murabus, ka yarda ka mulki masarautar Joɗa domin kawo gyara da tsari irin na addinin musulunci, Ni Umarnine kai tsaye nake baka".
Mamey ta kare zancen.
Abba kuwa cewa yayi.
"Ni kuwa al'farma nake nema".
Abun ya zo mishi amatuk’ar bazata amman kuma saidai umarnin iyaye ya wuce wasa.
Wani irin kukane mai rauni ya kwace mishi, take hawaye ya soma kwarara akan fuskarsa, cikin raunanniyar murya yace.
“Mamey zanyi na amince zan mulki masarautar Joɗa, Abba kaima kace umarnine kawai na amince zanyi muddin hakan zai saku farin ciki".
Cikin tsananin jin daɗi suka ɗaura hannunsu a kanshi tare da sa mishi al'barka.
Sai kawai ya kife kansa bisa cinyar Mamey murya na rawa yace.
“Kuyi min addu'a da bakunanku masu al'barka, ku roƙa min Allah ya bani ikon zama adalin shugaba mai tausayin al'ummar sa, ku roƙa min Allah ya bani ƙarfin zuciyar yin mulkin, sannan ku roƙa min Allah yasa
kada giyar mulki ta bugar dani, ta sani danasanin muku biyayya ranar gobe kiyama, ku roƙa min Allah yasa talakawa suyi farin ciki da alfahari dani a matsayin shugaban su".
Ya ilahi ya mujibadda'awati.
Su kansu su Abba tausayin shi ya rufesu, domin yanzu suka gano abinda yasa yake tsoron mulki da gudunsa.
Cikin sanyi sukayi ta jero mishi addu'o'i.
Yana amsawa da.
"Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati".
Daga nan Abba yayi ta bashi baki da bashi ƙarfin guiwa.
Dole sai kiran sallan la'asar ne yasa suka fito suka nufi masallaci.
Bayan kuma sun idar da Sallah’n sun fitone.
Abba ya sanarwa Lamiɗo da Galadima yadda sukayi.
Sujjadar godiyar Allah Lamiɗo yayi sabida baiyi zaton abun zaizo da sauƙi haka ba.
Shi kuwa Sheykh Part ɗinsa ya koma.
Junainah da Mimi yaran Aunty Juwairiyya ya wuce a falo,
har yaje bakin ƙofar shiga falonshi ya juyo yace.
"Junainah zo".
Da sauri tace “To”
ta biyo bayanshi.
A falon ya tsaya a hankali yace.
"Ina Adda Shatu ?".
Cikin sanyi tace.
"Tana ɗakinta".
Da sauri yace.
"Kuka takeyi ne?".
Kai ta ɗan gyaɗa mishi alaman “Eh”
Uhummm kawai yace kana yace.
"Jeki".
Ƙarfe tara dai-dai na dare ya fito daga Bathroom ɗinsa cikin shirin bacci.
Shiru yayi jiyo muryar Afreen nata kuka a falo.
Da sauri ya jawo al'kyabba ya ɗaura akan men sleeping dress d’in dake jikinsa.
Direct parlor’n ya fito.
"Ummi lfy kuwa meke damunta?".
Yace yana zama kusa da Ummin.
Cikin damuwa Ummi tace.
“Wlh tun ɗazu kuka takeyi,
to uwar kuma Maman ba ruwa, saboda tun shekaran jiya bata wani ci abincin kirki ba".
Cikin ɓacin rai yasa hannunshi ya amshi Afreen, daketa wawure-wawuren hannunta tana kaiwa baki alamun yunwa.
A kafaɗarsa ya saɓa ta tare da miƙewa ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Ita kuwa Shatu tsananin ciwon