Showing 90001 words to 93000 words out of 352722 words

Chapter 31 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30758

wurin yanayi mishi.
Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa.
Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa.
"Dokar gasa banda susa".
Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa.
"To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah".
Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa.
"Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?".
Arɗo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ƙarfi yaja.
Shi kuwa Ba'ana wani irin masifeffen ƙaiƙayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi.
Yayi wani irin gantsarewan da yafi na ɗazu.
Wani irin azabebben zafi da raɗadine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya.
Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi.
Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haɗa data forkon.
Ya damƙesu a hannun hagunshi.
Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa.
Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa.
A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ƙafar hagu.
To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya riƙe mahaɗin al'kyabbar jikinshi da hannun damanshi.
Gyara tsayuwarshi yayi kana ya ɗaga bulalar da ƙarfi ya zubawa Ba'ana a tsakiyar bayanshi.

Wani irin azabebben ihu mai ƙarfin amo da karaji Ba'ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaɗiya.
Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi.
Arɗo Bani kuwa a gabansu Lamiɗo ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al'ƙibila yayi sujjada.
Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daɗi yakeyi.

Hakama duk sauran dottawan.
Shi kuwa Ba'ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi.
Wani irin tsalle ya buga da ƙarfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba'anansa miƙewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sinƙo mishi, zafi yakeji har cikin ƙoƙon kanshi da zuciyarshi.
Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ƙarfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi.
Wanda gaba ɗaya rugar saida kowa ya jiyoshi.
Ƙabilar ɓachama kuwa gaba ɗaya suma kuka suka saka.
Shi kuwa Ba'ana da ƙarfi ya faɗi ƙasa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al'janu.
faɗuwanshi ƙasane yasa Jabeer rusunowa ya rinƙa tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba'ana yakeyi cikin azaba da karaɗi da kuka yake cewa.
"Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni.
Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah."
Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya ɗiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje.
Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama,
Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba'ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu.
Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba ɗaya.
Barmuji ne ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa.
"A dokar gasa Shaɗi in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faɗi a gasa kaci.
Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba."
Wani irin busar sarewa da al'gaita kana da kiɗe-kiɗen tsantsar farin ciki, al'ummar Rugar Bani suka farayi.
Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da Arɗo Bani da Galadima miƙewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi.
Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zuƙata.
Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya shaƙo Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari ɗaya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba'ana.
Lamiɗo kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi.

Koda su Galadima suka ruggumeshi, Arɗo Bani kuwa kama hannunshi yayi ya ɗaga sama alamun yaci gasar Shaɗin.

A haka suka iso gaban Lamiɗo hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al'barka.

Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki.
Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daɗi.
Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an ɗauka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi.

Jan gefe makaɗan suka sabi, da sauran zugar jamar gari.

Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga.
Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ƙan raƙuma.
Lamiɗo kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer ɗin dake kusa dashi baya jinshi.

Bisa umarnin Arɗo Bani ne aka rinƙa fito da ƙwaran nono da fura da dambu da ƙwaran zuma,
Ana kawowa su Lamiɗo.

Wanda fadawa da dogarai ne sukasha.

A hankali Jabeer ya kalli Lamiɗo cikin gajiya yace.
"To ai sai ku tashi mu tafi ko!".
Shiru Lamiɗo yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa.
"Mu tafi ko".
Galadima ne yace.
"Ai bamu gamaba".
Cikin sauri Haroon yace.
"To meya rage kuma?".
Galadima ya buɗe bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya ɗan kalli motocine da mamaki yace.
"Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda". (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda)
Sai kuwa ya juyo ya kalli Lamiɗo cikin nitsuwa yace.
"Lamiɗo lfy kuwa?".
Kanshi ya gyaɗa mishi alamar eh Lfy kau.
Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas.
Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu.
Da sauri ya juyo ya kalli Lamiɗo da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin Lamiɗo na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"To wannan ƙus-ƙus du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daɗin yinshi."
Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar.
Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune.
Wanda tuni Arɗo Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su.
Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiɗa.

Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaɗun Jabeer tare da sanya mushi al'barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya.
Kusa dashi Abbanshi ya zauna,
Kana Jalaluddin ya zauna kusa da Abban.
Lamiɗo kuwa na kusa dashi shida Galadima.

Da sauri Haroon dasu Jamil kan sukabi bayan fadawan da suka nufi motocin da sukazo yanzu da ido.

Shi kuwa Sheykh Jabeer ido kawai ya zubawa wayarshi.
Yana wasu aiyukanshi a ciki.

A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Haroon dake taɓashi.
Da yatsa Haroon ya nuna mishi gabanshi.
A hankali ya juya kanshi ya kalli inda Haroon ke nuna mishi.
Fadawane da hadimansu keta jido katon-katon ɗin sweet ga kuma fufun goro shima sunata jidowa suna ajiyewa a gabansu Arɗo Bani.

Cikin mamaki ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Me za'ayi da wannan kuma? Kamar wanda suka zo ɗaurin aure!".
Da sauri Galadima yace.
"Eh ashe ka gane ai ɗaurkin auren ne".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Aure kuma? To auren waye?".
Lamiɗo ne ya kalleshi cikin isa yace.
"Auren Muhammad Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa!".
Wani irin yunƙura Jabeer yayi zai miƙe, cikin tsananin haɗe fuskarnan tamkar zatayi aman jini ya kalli Lamiɗo tare da yunƙurin miƙewa yace.
"Zancen banza kenan a wurin banza, ai wlh baka isaba, wlh Lamiɗo kafa kiyayeni kanafa shigemin rayuwa, ka fita hanyata ka fice min a ido kar in rintsa da kai fa kadafa ka bari in juyo kanka".
Ya ƙarishe mgnar da miƙewa tsaye. Sai kuma ya juyo jin an kamo hannunshi an medashi zaune, a fusace ya kalli inda yaji anja hannun nashi ganin Sarki Jalaluddin ne ya riƙo hannunshi ya sashi kuma tsuke fuskarsa cikin faɗa yace.
"Jadda sakarmin hannu bana so! Bana son abinda kuke min da rayuwata, wlh gwarama kun tashi mun tafi, dan babu ruwana dan Ni bazanyi aure ba".
Da sauri ya juyo jin muryar Abbanshi yana cewa.
"...!

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, sai in saki cikin Normal group wanda a kwana talatin za'a gama littafin. Ko kuma kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Sai in saki a Special Group inda cikin mako biyu kacal za'a gama Part 1 da izinin ubangiji.
By
*GARKUWAR FULANI*


"Muhammad!". Ya kira babban sunanshi tare da jawo hannunshi, ya zaunar dashi bisa kujerar da ya tashi a kai.
Cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin aikatawa, ya kalli Mahaifin nashi, kana ya juyo ya kalli Lamiɗo da Galadima gefen damanshi ya juyo ya kalli Jadda cikin rauni ya kuma kalli mahaifin nashi tare dayin ƙasa da murya yace.
"Abba kada ka bari su ɗaura auren nan, dan Allah kace musu su bari, kada su ɗaura".
Ya ƙarishe mgnar cikin tashin hankali da ɓacin rai da tarin rauni a fuskarshi.
Cikin zuba mishi ido Abbanshi yace.
"Meyasa? Sabida me za'a bari!? Meyasa baka so!?."
Kanshi ya jujjuya tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya ya fuskanci mahaifin nashi cikin sanyi yace.
"Ni dai bana so. Abba dan Allah kada ka bari suyi.
Bana son garin nan bare mutanen cikinsa, kuma bawai haka banza naƙi auren nan ba, Abba inada matsala, Please Abba na tuba dan Allah kace su bari. In yaso a ɗaura da wani amman banda ni kam".
Lamiɗo ne ya kamo hannunshi cikin isa yace.
"Auren' nanfa, kamar ma an ɗaurashi an gama, domin babu wani abu ko wani mahaluƙin da ya isa ya hana wannan ɗaurin auren, gwarama ka kontar da hankalinka. Tunda ka iya jure bulalin aiko tabbas dole ka aureta, babu shakka dole sai ka aureta, bazai yiwu a dakeka a kantaba sannan ka barmusu itaba."
Cikin jin haushin wannan fitinenne tsohon ya kwace hannunshi daya riƙe tare da cewa.
"Haka kenan kullum zanyi ta wahala a bisa wasu dalilanka da bana addiniba, me ruwanka da dukan da akayi min, ba dai kai-kasa dole aka dakeni ba".
A hankali Galadima yace.
"Eh da kuma bakayi kukaba, baka guduba, yau kuma kasa yayi kuka ya gudu ai dole ka aure matar da a kanta aka haɗaku gasar, tunda mu dai ba sakarkaru bane, bare ace bamu san dokar gasar Shaɗi ba."
Wayyo Jabeer ji yakeyi tamkar ya mammake tsoffin nan dan tarin baƙin ciki. Rai a ɓace yace.
"Bakufa fini sanin kainaba, tunda nace muku bana son aure, bazan kuma yi aureba, to ku barni mana, rayuwata ce ko taku, ko dole ne duk wata matsalata da sirrin rayuwata sai kun sani! Nace muku bana son wannan garin na tsani garin bana son mutanen garin karankatab ɗinsu.
Bani babu su, in kuma kukayi gangancin cusa min wata muguwar yarsu, tabbas! lallai ilaihin! A kanta zan rama sauran bulali ashirin da wancan ƙaton gardin ya min, hamsin, ni a talatin ya gudu".
Kai Jadda ya girgiza tare da cewa.
"Ka rama mana kaida matarka, ka rama ka kuma jinyace ta".
Shiru sukayi sabida jin muryar Dr Aliyu da kuma Galadima da Arɗo Bani da Bappa suna tabbar wa juna lfyar yaransu, cikin Mamaki ya kalli Galadima dake cewa.
"Muma ɗanmu lfyarshi lau, Namiji ne".
Cikin sanyi Jabeer yace.
"Ji maƙaryacin tsoho, wai lafiyata lau, ko yaushe ya zama likita ya gwadani. Harda wani karkacewa yana zuba ƙarya ko farin gemunshi bai martaba-ba".
Jin Abbanshi ya daki gefen ƙafarshi ne yasashi yin shiru.

A nan a gabanshi a gaban mahaifinshi. A gaban dubban al'ummar fulani makiyaya daketa tsastsafo tako wani sashi na duniya, a kuma gaban Lamiɗo da tawagarsa hakama Jalaluddin da tawagarsa.

Aka ɗaura auren Muhammad Jabeer da Aysha. Bisa koyarwan addinin Musulunci.

Sosai su Jalal, Jamil, Hashim, Haroon, Sulaiman. Sukayi mamakin wannan aure na ba zata. Ba zato ba tsammani.
Bayan an gama dai-dai-ta komai an ɗaura auren ne, kuma.
Lamiɗo ya kalli Arɗo Bani, cikin girma da ƙasaita yace.
"Yanzu zai tafi da matarshi."
Cikin sanyi da al'hini Bappa yace.
"Allah rene yanzu kuma!?".
Galadima ne ya amshi zancen da cewa.
"Haƙƙun yanzu zamu tafi da ita!".
Arɗo Bani ne yayi murmushi mai cike da jin daɗin yace.
"To ba laifi ai, muje a fito muku da ita".
Shi kuwa Bappa ido ya zuba musu.
Dan shi a zatonshi ba yau zasu tafin mishi da Shatunsa ba.

Nan duk suka ɗunguzuma, suka shiga motocin. suka nufi ƙofar gidansu Shatu.

Ya Salmanu kuwa, tuni ya shiga cikin gidan su.
Ya shiga ɗakinshi yana ta kuka kamar yaro. Bai tsamci haka abin kan iya juyewa ba, Ba'ana ya rasa Shatu shima ya rasata.

Suna isa ƙofar gidansu, duk motocin suka tsaya.
A hankali Bappa da Arɗo Bani suka kutsa kansu cikin gidan.

A tsakar gidan suka samu.
Shatu na zaune dan dawowarta kenan, hannunta tasa ta tallabe haɓarta ta zubawa su Junainah ido, shigowarta gida kenan daga dawowarta.
Cikin Ɓadamaya su Binto suka shigo gidan a guje suna ce mata wai an ɗaura aurenta da ɗan sarkin da akayi gasar Shaɗi dashi.
Jin hakane yasata yin murmushi tare sauƙe dogon ajiyan zuciya na gajiyar tafiyar da tayi, ido ta lumshe tare da cewa.
"Auren kuma wasane, da zai zama an aura min wani wanda ba'a san halinshi ba, ko ƴar tsana ma ai ba'a aurar da ita a hakaba bare ni".
Ta faɗi mgnar cikin fargaban ganin yadda suketa rantse mata. Duk da bawai ta yarda da zancensu bane. Junainah kuwa dariya takeyi tare da ɗan tsalle-tsallenta tana cewa.
"Yeeh Auren Addana yazo, zanyi gayyan fati muyi gaɗa".

Cikin zuba musu ido, ta zauna gefen, Ummey dake ta Binta da ido, cikin sanyi tace.
"Ummey na dawo! Ya jikin naki!?."
Da sauri ta gyara zamanta tare da zubawa Ummey ido, cikin mamaki take kallonta ganin idanunta nata zubda hawaye ne, yasata cikin ruɗani da tashin hankali da fargabar abinda ke shirin faruwa da ita da rayuwarta.
A kiɗime tace.
"Ummey meya sameki? meya saki kuka? Jikin ne yake miki ciwo?."
Sam Ummey bata iya mgna ba, sai kukan da takeyi,
hakanne yasa zuciyar Shatu karaya, cikin rauni wasu hawaye masu ɗumi suka fara tsiyayo mata.
Hakan ya ƙara ingiza kukan Ummey hakama,
Junainah sai ta raɓa gefensu tayi, zurui a zatonta aure abun daɗi ne ba kukaba to gashi taga su kuma kuka sukeyi.
Sosai Shatu takeyin kuka mai tarin dalilai.
Suna isa Bappa yasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyi yace.
"Taso kizo".
Ido cike da hawaye ta mike tsaye bisa umarnin Bappa.
Shi kuwa Bappa cikin sanyi ya kalli Ummey da Junainah yace.
"Kada kuyi kuka, kuyi mata addu'o'in samun nasara a cikin wannan al'amari, muyi mata fatan aurenta ya zamo haske ne a rayuwarsa shi mijin da ahlinshin baki daya, fatanmu aurenta ya zamo ƙungiyar da zata jawo gskya cikin raminda aka binneta ya fito da ita kowa ya gani."
Shiru Ummey tayi sai hawayen da suke kwaranya.
Hakama Shatu hawayenta wani na korar wani.
Ita kuwa Junainah faɗawa jikin Ummey tayi sukaci gaba da zubda hawaye.

Bappa kuwa hannunta yaja suka juya suna nufi hanyar fita.
Da kayanta na ɗazu wanda taje Genaral Hospital Ɓadawaya dasu, hatta hand bag ɗinta na rataye a kafaɗarta wayarta na ciki.

Cikin mamaki take bin bayan Bappa, tare da yin taku a hankali tana bin bayanshi yadda yake jan hannunta.
Arɗo Bani kuma na biye dasu a baya.

Suna fitowa ƙofar gidan, Haroon da Jalal suka juyo suka kalli juna,
Cikin tarin mamakin ganin kamar yarinyar ɗazuce.


Shi kuwa Sheykh Jabeer yana zaune cikin motar, shi ɗaya dan duk sun fita.
Da sauri ya dafe saitin ƙahon zuciyarshi jin ta tsananta bugawar da yakeyi.
A hankali ya maida bayanshi ya jingina da sit ɗin tare da rufe idonshi.
Yana mai jin sanyin A/C na ratsa mishi jiki da jini da zuciya.
Amman duk da haka zuface ke tsastsafo mishi a jikinshi sabida bugun da Zuciyarshi keyi ya wuce misalin.

A hankali ya juya kanshi ya kalli gefen hagunshi inda yaga motar Jadda da kuma Dr Aliyu ne da Barrister Kamal ke jere a wurin.

Bappa kuwa a hankali yake taku, yana nufo inda Lamiɗo ke tsaye Dogari na riƙe masa da laima, Ɗanzagi da fadawa na zube a kasa.

Ita kuwa Shatu cikin rawan jikin jin idanun mutane na yawo a jikinta dan ma Allah yasa akwai niƙab a fuskarta.
Take bin bayanshi. Shi kuwa Sheykh Jabeer yadda suke ƙara matso inda yake haka bugun zuciyarshin keta tsananta.
Suna isa gaban Lamiɗo Bappa ya miƙawa Lamiɗo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace.
"Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer.
Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka.
Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ƙarfin guiwar baku aurenta.
Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta".
Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace.
"Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu ɗaukanta, dan in danƙa amanarta a hannun macce yar uwarta.
Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin ƴaƴan mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma ɗiya irin Shatu ɗiyace da take da nasabobi masu yawa a gareni".
Cikin gamsuwa Lamiɗo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni niƙab ɗin fuskarta ya jiƙe jilak da ruwan hawaye.

Cikin Dattaku Lamiɗo yace.
"In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ƙanwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta Joɗo, baƙoma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina".
Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace.
"To Ngd matuƙa".
Arɗo Bani ne ya dafashi tare da cewa.
"Ka sanya mata al'barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba."
Sosai Haroon ya zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye.

A hankali su Bappa suka ɗan ja da baya.

Shi kuwa Lamiɗo ya juya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login