Showing 324001 words to 327000 words out of 352722 words

Chapter 109 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30805

hawayenka gasu Yah Gaini Seyo da Giɗi".

Duk sauran mutanen falon duk suka ɗago kansu.

Ido cikin ido Shatu tayi da Yah Giɗi'nta abokin tsamarta.
Wani irin yunƙura tayi ta miƙe tsaye tare da cewa.
"La'ilahaillaha Muhammadu rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam Alhamdulillah Bappa gasu Yah Gaini".
Jin kalaman Shatu ne yasa Bappa dayake sunkuye ya ɗago kanshi yana kalli bakin ƙofar shigowa ya sauƙe kwayar idanunshi kan.....!



Kuyi haƙuri da typing errors ina cikin ciwon kai nayi typing ɗin a daddafe.



Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300.
A yawan posting ne babban cinsu 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa in kin tura sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo min ta whatsApp 09097853276 ƴan 3oo in naki da halin biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ku turo min ta whatsApp ɗin 09097853276.

By
*GARKUWAR FULANI*


: Ya sauƙe idanunshi kan Giɗi Seyo Gaini.
Cikin wani irin yanayin tarin farin ciki mai sanya rauni.
Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mishi.
Da sauri ya yunƙura ya juyo ya fuskanci al'ƙibila. Sujjadar godiyar Allah yayi kana ya ɗago yana mai zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu da sauri ta ƙarasa garesu, kawai sai ta faɗa jikinsu baki ɗayansu, tare da sakin raunataccen kuka.
Cikin rauni da yanayin kula Seyo wa mai tausayi kamar uwa yace.
"Shatu dena kuka, mu godewa Allah".
Sai kuma ta kalli Yah Giɗi cikin sanyi ta ruggume shi tare da cewa.
"Tunda na rasaka kusa dani na rasa abokin faɗa da tsama, shiyasa lokuta da dama ina jin daɗin inyi taƙaddama da Gimbiya Saudatu dan sai yana tunamin ta ƙaddamar mu, da Yah Giɗi na abokin faɗana".
Cikin zubda hawaye shima Giɗi yayi murmushi tare da janyeta jikinshi kana yace.
"Nayi kuka a lokuta ma banbantan da bazan iya ƙididdiga ba sabida tunoki da rayuwarmu".
Hannun tasa ta share hawayenta kana ta kalli Yah Gaini wa mai matsayin Uba cikin kulawa da yanayin rayuwarta yace.
"Shatu ina Ba'ana ko mun samu nasarar rabuwarki dashi".
Da sauri tace.
"Yah Gaini Allah ya rabamu da Yah Ba'ana".
Cikin tarin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah".
Dai-dai lokacin suka isa gaban Bappa daketa zubda hawaye.
Zama sukayi a gabanshi gaba dayansu huɗu.
A hankali Giɗi ya sunkuyo ya kwantar da kanshi bisa cinyar Bappa tare da sakin sassayan kuka a hankali yace.
"Bappa mun ganka kaida Shatu ina Innarmu ina Ummey ina Junainah ina Yah Lado?".
Da sauri Ummey tasa hannunta ta rufe bakinta jin kuka zai kubce mata.
Sai dai tuni sautin kukan ya fito.
Da sauri Giɗi ya rarrafo gabanta murmushi yayi still Ido na zubda hawaye a hankali yace.
"Alhamdulillah Ummey Junainah ina Innarmu da Yah Lado".
Cikin kuka Junainah ta faɗa jikinshi tare da cewa.
"Arnan Ɓacama sun kashe Innarmu sun kashe Yah Lado sun kashe mutane da yawa na rugarmu".
Da sauri Giɗi ya juyo ya kalli Ummey cikin tashin hankali da kubcewar kuka.
Gaini da Seyo suma kuka mai rauni suka sake ganin Bappansu yana jinjina musu kai alamun zancen Junainah hakane".

Shiru falon sukayi baki ɗayansu sai sutin kukan Giɗi, Shatu, Junainah, Ummey, Seyo, Gaini. Raunin da kukansu ya sauƙar a zuciyar Bappa ne yasa shima sakin kuka dan yau sai sukaji gaba ɗaya rasuwar Yah Lado da Inna ta dawo musu sabuwa.

Sosai Shatu keyin kuka tana durƙushe ta tanƙwashe sawunta, hakama Ummey.

Gaba ɗaya kab falon saida idon kawa ya ciko da ƙwalla.

Cikin Rauni Sheykh ya matso inda Shatu ke durƙushe gaban yayun nata, cikin sanyi ya kalli Bappa Ummey murya a raunace yace.
"Tabbas bansan irin ƙunar da kakaji a cikin ranka ba Bappa amman nasan kwatankwacin kamannin ƙunan rashin ɗa, a suman da Afreen tayi naji ciwo da ƙuna a zuciyata tamkar ban taɓa farin cikiba, nasan zafin rashin uwa, amman ban san zafin rashin mataba dan kamin gatan bani Mar'atussaliha ta zame min GARKUWA tana sani farin ciki a duk lokacin da nake cikin baƙin ciki."
Shiru yayi sai kuma ga hawaye shar-shar a idanunsa cikin rauni yace.
"Na samu komai da nake nema a rayuwata daga gareka ka bani mata ta gari, Allah ya azurtamu da samun ƙaruwar arzin haihuwa sanadinka Ummey na ta dawo.
Inama! inama! ace Inna da Lado ɓata sukayi ba rasuwa ba, da tabbas zanyi iyakar iyawata in dawo maka dasu da izinin ubangiji.
To amman wannan hurumin ubangijin sammai da ƙassaine.
Kayi haƙuri Bappa Allah ne ya baka Inna matsayin mata ya ɗauketa ya sauyama da ƴar uwarta kuma Allah shi ya baka Lado ya ɗauke shi kuma ya killace maka Seyo Gaini Giɗi, wanda wata ƙil da suna Rugar ba'a sacesu ba da an kashesu.
Gashi yanzu Allah ya dawo maka dasu.
Bappa kace Alhamdulillah ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka sai ya ƙara maka wata a kai.
Kayi haƙuri ka bar kuka kaga kukanka na ƙara ingiza nasu".
Ya ƙare mgnar yana sa hannunshi cikin tafin hannun Shatu yana murza a hankali.
Cikin gamsuwa da jin sanyi a ransa Bappa yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Su Giɗi suma sukace.
"Alhamdulillah". Hakama su Lamiɗo kab falon sai suka fara mai-mai-ta hamdala.
Ai kuwa cikin ikon Allah duk ƙuna da ƙuncin da zuƙatansu keyi a take Allah ya sauƙaƙa musu shi.
Cikin gyaran murya Lamiɗo yace.
"Alhamdulillah komai yayi forko zaiyi ƙarshe duk abinda yayi tsananin tabbas zaiyi sauƙi Allah mun gode maka daka ara mana rai da lfy".
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Sheykh dake kallon agogon hannunshi sabida jin anyi kiran sallan azahar.

Cikin tarin jin daɗi Abbansu Sheykh ya matso kusa da Bappa da Abboi murya cike da tarin jin daɗi yace.
"Bappa Abboi dama duk al'ummar Rugar Bani da Rugar Arɗo Babayo ngd matuƙa Ubangiji yayi muka sakayya da gidan al'ljanna mafi ƙololuwa girma.
Shatu Allah ya dafa miki ya tsareki dake da ahlinka".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Shi kuwa Bappa Sheykh ya kalla tare da cewa.
"Muhammad Ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi da kulawarka Alhamdulillah ga mahaifiyarku da ƙanwarku Allah ya bamu aron rai da lfy da ikon dawo muku dasu lfy".
Cikin jin daɗi Ummey tace.
"Bappa dani dasu ya kamata muyi godiya ba kuba kun gama min komai a duniya musamman Alhaji Abboi da matarsa Dedde sun min karar bani yar su duk da tarin son da sukeyi mata, suka amince muka dawo da ita nan, kana suka bawa Jabeer na aurenta."
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu tare da cewa.
"Kin min komai kin juya min Jabeer daga bauɗeɗɗen mutun zuwa dai-daice gashi yanzu har fara'a yakeyi ga Jalal na shima ya zama mai fara'a Jamil kuma ya nitsu.
Sai dai yanayin Affan nane ke min ciwo a rai, Affan ka dena kuka kajiko Shalelen Mamey".
Cikin rauni Affan ya matsota ɗaura kanshi bisa cinyarta yayi tare da sakin kuka.
Gaba ɗaya kowa yasan takaicin abinda mahaifiyarsa tayine yake sashi kukan.
A hankali Lamiɗo yace.
"Kayi shiru Affan ita rayuwa kowa abinda ya shuka zai girba".
Daga nan dai kuma akayi gaishe-gaishe.
Kana mazan duk suka tafi masallaci.
Matan masarautar Joɗa kuwa irinsu Gimbiya Saudatu da Gimbiya Aminatu dasu Mom da Samira duk ko wacce ta koma part ɗin ta cike da al'hinin sharrin ɗan Adam.

Matan kuma duk kowa tai al'wala sukayi salla, kana suka sake fitowa falo suka zauna suna cin abinci.

Affan kuwa Part ɗin shi ya koma ganin tashin hankali da yake cikine yasa Mami meda hankalinta gareshi.
Shi kuwa Rumaisa yayarshi ya kira tana ɗagawa yace.
"Uhummm tunda kullum kece kike zuga Hajia Mama kuna cutar waɗanda basu damu da kuba sai ki shirya kizo kiga halin da Mama ke ciki na girbar aiyukanta data shuka".
Cikin tashin hankali Rumaisa tace.
"Affan m.."
Bai bari ta ida zancenta ba ya katse kiran.

Su Sheykh kuwa dasu Haroon falon Sheykh Suka wuce.

Bayan anyi sallan la'asar ne,
Dedde ta kalli Ummey cikin kula tace.
"Toh Ummeyn Shatu mu zamu koma Rugar Bani, sai jibi zamu koma Cameroon da izinin ubangiji Allah ya kiyaye gaba ya tsaremu".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Yanzu-yanzu zaku tafine?".
Cikin nitsuwa Dedde tace.
"Eh ai su tuni ma sun shiga mota nida su Khadijah suke jira".
Da sauri Umaymah tace.
"Ayyah ni kuwa ina son ku gaisa da Sittinmu da Jadda kafin ku tafi".
Da sauri Mamma tace.
"Ai sun iso suna Part ɗin Lamiɗo.
Amman yanzu zasu iso".
Da sauri Shatu tace.
"Toh Dedde am ki ɗan jira ku gaisa mana".

Suna cikin mgnar Sitti da Jadda suka shigo.
Allah sarki iyaye sai gashi Ummey a tsakiyarsu suna kuka gaba ɗayansu an rasa mai rarrashin wani.
A hankali Sheykh da Haroon suka shigo falon cikin tsiya Sheykh yace.
"Toh Alhamdulillah Jadda ni dai burina ya cika ko yau in kana son tafi ka gaida na gaba tunda kaga Mamey na ta dawo ta sameku cikar farin cikinta kusa mata al'barka".
Dariya sukayi baki ɗayansu kana su Dedde suka matso aka gaggaisa.
Sannan Jadda ya fita ya koma wurin su Lamiɗo.

Cikin sanyi Shatu ta kalli Deddenta Aunty Amina Hafsi Khadijah waɗanda duk suke cikin shirin tafiya.
A hankali tace.
"Allah sarki da mu ƙara kwana mana, yanzu kuma in kun tafi shikenan sai yaushe ni na zama a nan ina gefe duk ƴan uwa suna Cameroon".
Da sauri Ummi tace.
"Kema kina tare da yan uwanki ga Ummeynki ta dawo kusa dake ga kuma Junainah gani ga Hibba".
Da sauri suka kalli Jamil da ke cewa.
"Kuma zan auro mana Khadijah ma ta dawo nan zaku bani ita ai ko Dedde".
Ya ƙare mgnar cikin yanayinsa na wasa da dariya da kowa.
Murmushi Dedde tayi tare da cewa.
"Ai an baka ma Jamilu".
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Junainah kuwa a hankali ta matso kusa da Ya Giɗi tare da cewa.
"Ummey ni dai zan tafi tare dasu Yah Giɗi ban gaji da ganinsu ba".
Cikin jin kewar juna Ummey tace.
"Kije Junainah nima in Sitti na da Jadda sun tafi zamuzo tasu Mamma".
Da sauri tace to.
Kana ta kalli Shatu da tai shiru tana kallonta tare da cewa.
"Kada ki damu Addana nima zanke zuwa masarautar Joɗa".
Da sauri Jalal yace.
"Zaki dawo dai Junnu gamu ga Abbanmu ga Adda Shatunki ga Ummey".
Da sauri ta kalli Sheykh tare da cewa.
"Toh Yan Junaidun fa".
Dariya mai sauti Sheykh ya ɗan yi tare da cewa.
"Shima zai dawo nan".
Nan dai suka fito gaba dayansu dan yiwa su Dedde rakiya.
Jadda kuwa harda kuka yayi yana yiwa su Abboi da Bappa godiya.

A hankali Salmanu wanda yazo wurin ɗan Hafsi ne ya ɗan matso kusa da Ummey ƙasa yayi da murya tare da cewa.
"Ummey ki roƙa min su Abboi a bar mana Hafsi mana".
Dariya Ummey tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kuce duk ma zamu kwasosu mu dawo nan dasu".
Da sauri Salmanu ya shiga mota.
Shi kuwa Yah Al'ameen gefen Shatu ya ɗan kalla tare da yafitota.
Bayan Sheykh suna ɗan ratsa a hankali yace.
"Wannan ƙawar taki Rafi'a fa, da batunta yasa su Abboi zuwa gobe zasuje su zanta da manyanta sai jibi zamu koma".
Cike da mamaki tace.
"Lahh Yah Al'ameen ashe mgnar taku har ta kankama".
Da sauri yace.
"Ke da Allah ni kada kimin shele".
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
"Toh sai na gaya ma kowa yaji".

Da sauri ya biyota ita kuwa cikin dariya tace.
"Ummey ashe Yah Al'ameen da Rafi'a munahikai ne soyayyar sirri sukeyi".
Dariya Sheykh yayi tare da juya mata ido alamun ai kema soyayyar sirri kikayi.

Haka dai suka shiga motocin suka tafi cikin farin ciki da kewar juna.


Cike da farin ciki suka koma cikin falon.
Da sauri Umaymah ta amshi wayarta da Ishma ke miƙa mata.
Amsa kiran tai da sauri ganin Abbansu Sheykh ne.
"Assalamu alaikum Abban Jazlaan".
Da sauri Abba dake part ɗin shi ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh wai Umaymah ni sai yaushe zan samu in gaisa da Yayar takune kun taru kun riƙe min ita da hira".
Dariya mai sauti Umaymah tayi tare da cewa.
"A a sai mun koma mana".
Da sauri yace.
"A a dan Allah kada muyi haka dake, kinga yara na cike nan ki kirata gefe kice mata ina kiranta".
Murmushi tai tare da cewa.
"Nawa zaka biya".
Dariyar jin daɗi yayi tare da cewa.
"Kujerar hajji tayi miki".
Da sauri tace.
"Sosai ma kuwa yanzu kuwa zan cika aiki".

Tana gama wayar ta yafito Mamey suka tafi ɗakin Ummi ta gaya mata.
Cikin jin kunya Mamey tace.
"A'a kinga dama ke tsiyarki yawane da ita Khadijah ya da girmana kuma ana cike yarana da jikoki ku wani kawo min batun inje gareshi".
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
"Toh shike nan ni dai yar aikece.
Cikin yanayin tarin shaƙuwarsu ta ya da ƙanwa Mamey tace.
"To ai dai ya bari sai dare ko".
Da sauri Umaymah tace.
"Ohoh anaso ana kaiwa kasuwa".
Hararan wasa tayi mata kana ta fito.

Nanfa sukaci gaba da hira.
Ana gab da kiran sallan magriba.
Suka juyo ehu da kururuwar Hajia Mama da faɗe-faɗen da takeyi.
Da sauri Sheykh ya nufi ɗakin daya rufeta, yana buɗeta.
Ta fito tanata yayyarfa hannunta tare da cewa.
"Wayyoooooooo zan zama tsuntsuwar Boleru".
Da sauri yabi bayanta tuni ta iso falo.
Tana kaɗan yatsun hannunta da sun fara komawa na tsuntsuwar Boleru.
Cikin tsoro da mamaki da tausayi Mamey tace.
"Innalillahi Jabeer kamanninta fa na sauyawa".
Da sauri ya iso, yana mai kara wayarshi a kunne sabida kiran da yayiwa Affan.
Yana ɗagawa yace.
"Affan kazo kayi maza kazo".
Cikin tashin hankali da tsoro Affan yace.
"Toh".
Yana fitowa yayi kiciɓis da Rumaisa a tare suka nufi.
Part ɗin Sheykhhhh.

Umaymah kuwa Abba da Lamiɗo ta kira ta gayawa.
Kusan duk a tare suka iso.
A tsakiyar falon suka sameta.
Tana yayyarfa hannunta tare da cewa.
"Na ji daɗi zan zama tsuntsuwar Boleru zanyi ta firewa kamar jirgi".
Sai kuma ta kalli Sheykh da yake ta karanto Ayatul shifa yana tofa mata. Dariya tayi tare da cewa.
"Kai bar ɓata lokacin ka a kaina ai al'haƙine kuikuyo ya dawo kaina wayyo ni Halima naga ta kaina".
Da sauri Rumaisa ta iso gareta ihu tasa tare da kururuwar ganin yadda kafafunta duk suka zama cingil-cingil kamar na tsuntsuwar ladin kogii.

Da sauri Rumaisa tace.
"Dan Allah Affan mu kaita gidan bokan ya karya sihirin".
Cikin tarin takaici da zubda hawaye Affan yace.
"Banza mahaukaciya gafalelliya ni nan Affan babu gidan wani mushirkin mugun kafurin bokan da zanje.
Anayi mata addu'o'in kina batun aje gidan boka".
Cikin ihu tace.
"Abba dan Allah mu kaita".
Da sauri Abba yace.
"In kika sake kirana kika haɗani da Allah dan inje inda zan tsaɓa mishi zan tsine miki shasha mara hankali".
Sheykh ne ya ɗan kalleta cikin sanyi yace.
"Aunty Rumaisa ki bari ki nitsu muyi mata addu'a in sha Allah zata samu lfy".
Da sauri tace.
"An ƙi ɗin sabida ba uwarka bace ai shiyasa zakace haka".
Sai kuma ta zaro wayarta ta kira bokan bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga cikin kurma ihu da kururuwa yace.
"Nima ƙonewa nakeyi, ita kuma a haka zataci gaba da rayuwa ita ba mutumba ita ba tsuntsuwar Boleru ba, zata zama aya ta yadda duk wanda ya ganta sai ya tambayi mai tayi. Domin dama shi mugunta ɗan aikene yakan iya dawowa wurin wanda ya aikeshi.
Sai kuma ya kurma ihu da ƙarfi.
A nan ya faɗi yana burburwa.
Ya shiga gudu yana kwaɓe kayansa yana cewa wuta na ƙonashi ya zama mahaukaci tubran.

Ita kuwa Rumaisa kamo Hannun Hajia Mama tayi suka tafi Part ɗin ta.
Lamiɗo kuwa kai ya jinnina tare da cewa.
"Ƙarshen mugu kena".

Sheykh kuwa da Mamey da sauri suka zauna gefen Affan dayake kuka kamar ya haɗiyi zuciya cikin sanyi Sheykh yace.
"Affan kayi haƙuri ka bar kuka in Sha Allah zamu dage da addu'a zata samu lfy".
Cikin shassheƙan kuka. Ya tashi yabi bayansu.
Sabida ita dai uwa duk yadda take uwace.


Abba kam juyawa yayi ya fita ko a jikinsa.
Domin shi tausayin Affan ne kawai ke cinsa a rai.
Lamiɗo da Gimbiya Aminatu da Galadima ma kwaffa kawai sukayi suka fita.

Umaymah kuwa cikin zafin zuciya tace.
"Wlh Ni dai ko duk zaku yafe mata ni ba yafewa zanyi ba".
Da sauri Sheykh ya kalleta idonshi cike da hawaye.
Sai kuma ya kalli Mamma da Aunty Rahma dasu Yah Jafar da suma suke cewa basu yafe mata ba.

Jin an kira sallan magriba ne yasa duk suka miƙe suka tafi masallaci.


Ana idar da sallan Isha'i Sheykh ya nufi Part ɗin Hajia Mama kuka sosai ya sameta tanayi Affan na gefenta shima kukan yakeyi

Addu'o'in ya rinƙa tofa mata.
Har saida yaga tayi bacci kana ya fita.
har yaje bakin ƙofar fita sai kuma ya juyo jin Affan ya ruggumeshi ta baya yana kuka tare da cewa.
"Ngd matuƙa Hamma Jabeer Allah ya bar zumunci da ƙauna".
Cikin rauni yace.
"Amin Amin Affan".
Daga nan suka fita kowa yayi Part ɗinsa.


Hira sosai sukayi ranar hirar yaushe gamo kusan sai gab da kiran sallan forko kana duk suka tashi sukayo al'wala sukayi ta nafila suna godewa Allah.

Washe gari da safe gaba ɗayansu suna falon Abba ya shigo.
Suna gaisawa yana kallon Umaymah dake mishi dariya ƙasa-ƙasa.

Hajia Mama kuwa da taimakon addu'o'in da Sheykh yake mata hankalinta ya ɗan dai-dai-ta yadda zata fi jin ciwo da zafin sauyawar halittarta, da gaba ɗaya yanzu kafafunta sun zama na tsuntsuwar ladin kogi, yatsun hannunta kuma sun zama fiffizgewa tsuntsuwar Boleru, idanunta kuwa kamar na tsuntsuwar Duji sunyi ƙuru-ƙuru tamkar an taka kwaɗo.

Wannan al'amarin yasa Lugga da saƙo mutanen masarartar Joɗa shigowa sunayi mata kallon sabuwar halitta masu dariya nayi.
Tsananin tsoron Allah ya wadaci zuƙatan mata da mazan Masarautar.

Bayan Aunty Juwairiyya ta dawone take suffantawa su Mamma yadda Allah ya maida Hajia Mama.
Sosai jikinsu yayi tsanyi.

Umaymah ce ta ɗan kalli Shatu da yanzu ta fito wonka cikin shirin baccinta.
"Naji kamar Jazlaan ke kiranki".
Umaymah ta faɗa cikin kulawa.
Da sauri tace to kana ta miƙe ta funi Side ɗinsa.
A falo ta sameshi gaban steps ɗin hawa wurin Dinning area.
Hannunshi na cikin zirin zirin igiyoyi dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Daimond.
Wanda a ciki yake liƙe da CCTV camera ta sama wanda da wuya mutun ya iya ganeshi.
Ruggume shi tayi ta baya tare da cewa.
"I miss you so much Sheykh Malam akarmakallu Dr Hamma Jabeer".
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi kana ya juyo ya ruggumeta.
A hankali tasa tafin sawunta saman rumfar sawunshi kana tasa hannun ta saƙalo wuyanshi.
Ya zama tana lafe a jikinsa.
A hankali ya fara taku a haka ya nufi Bedroom.
Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe.
Da cikin tsokana tace.
"Yah Sheykh Haroon".
Baki ya ɗan taɓe tare da cewa.
"Wannan jarabebben tun yaushe yaja Ƴar mutane suka shiga ɗakin nan suka rufe ko kunya babu".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Mutun da matarsa".
A hankali ya sunkuyo kan gadon ya kwantar da ita tare da yi mata rumfa da ƙirjinshi kana yace.
"Okay to ai nima gani da matata".
Da sauri tace.
"Yah Sheykh jego nakeyi, kwana Afreen goma kacal fa".
Hancinsa ya manna da wuyarta tare da cewa.
"Eh mu samo mata ƙanwa ko ƙani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login