Showing 129001 words to 132000 words out of 352722 words
wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta ɗaura a ɗaya murhun dake gas ɗin babbane.
Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al'basa,
ya soyu yana ƙamshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ƙara wonƙe ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haɗa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.
Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba.
Ita tayi miyar masan, ta kuma ƙarisa ferfesun kayan cikin da Ummi ta fara.
Ummi kuwa ta tafasa musu tea ta ɗuɗɗura a flaks,
Kana ta tafasa Arish ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Saratu ta dawo.
Ita Ummi ce ta ɗan amshi ƙullun masar tare da cewa.
"Gskya mun ɗan makara aikin Masar nan gashi ni hannuna baya tashi da wuri".
Da sauri Shatu ta matso tare da miƙawa Ummi roban markaɗen kunun.
Tace.
"Ba matsala Ummi ni hannuna na tashi da wuri.
Yanzu tace mana marƙaden kunun bari in kwaɓa mana Masar."
Haka kuwa akayi Ummi ta fara tacewa.
Ita kuwa kulun dafaffiyar ɗanyar shinkafar ta murmusa cikin marƙaden Masar,
Kana tasa fulawa tare da yis kaɗan sannan ta tarfa gishiri kaɗan.
Kana ta rufeshi a robar dan babbace, motso da robar tayi kusa da Gas ɗin yana ɗan jin ɗumin wuta.
Gefen Ummi ta dawo wacce ta gama tace markaɗen
A babbar tukunta ta zuba shi kana ta ɗaura kan wuta tare da dai-dai-ta wutar tanayi tana motsa kunun.
tare da ɗan tarfa wanda ta rage, da surkin lemun tsami.
Cikin Sa'a ɗaya ta dama kunun shinkafar fari ƙal tamkar madara.
Sugar tasa ta juye a a ƙatuwar kula kana tasa a maidaciyar kula, Sannan tasa a flaks ɗaya, sai kuma tasa a Mug mai marfi duk ta kimtsasu gefe.
Tuni Side ɗin ya ɗin ke da ƙamshi miyar masan da ferfesun nan.
Buɗewa tayi ganin miyar tayine ta sauƙe ta maida gefe.
Kana ta kalli Ummi tace.
"Ummi je kiyi salla la'asar tayi, in kin dawo sai inje inyi".
To Ummi tace ta fita tana mamakin saurin aikin Shatu.
Koda taje tayi sallan ta dawo ta sameta tana sauƙe tukunyar ferfesun.
ganin Ummi yasa tace. "Yauwa Ummi komai yayi dai-dai yanzu kaskon tuya zamu daura kinga kullun ya tashi".
Cikin mamaki Ummi ta kalli Robar da taga har kullun na shirin zubewa.
Ita kuma ɗiba tayi a wata roba kana duk tasa yankekken al'basane a ciki Sannan tasa sugar ta gauraya,
sannan ta matso da kasko biyu,
juyowa tayi ta kalli Saratu tace.
"Yauwa Sara matso. Ke ki rinƙa yi kina sawa a wannan babban kulan in ya cika kisa a wannan shima.
Ummi ke kuma kisa mana namu anan suyanki mukeson ci".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"To jekiyi salla".
To tace kana ta fita.
Ita kuma Ummi ta juya ta kalli Sara tare da cewa.
"Kema kije kiyi salla".
Cikin ci gaba da aikinta tace.
"Ai nima nayi".
"To shike nan". Ummi tace kana sukaci gaba da tuyan.
A falo ta haɗu da Hibba da Jamil, sai dariya yakeyi cikin dariyar yace.
"Yauwa Aunty Shatu dama idonki nazo in gani, dan ga Hibba kam ta kusa kasawa".
Murmushi tayi dan bata da sauran ƙarfin yin dariya.
Cikin ɗan fito da idanunta da suka ɗan faɗa tace.
"Gani ras dani".
Dariyar ƙeta mai cike da alamun yunwa da ƙishi yayi tare da cewa.
"Inafa ras kalli yadda idonki ya fito kamar kinyi azumi goma".
Murmushi tayi kana tace.
"Um bari inje inyi salla".
Sai ta kuma kalli Hibba dake lankwabe tace.
"Sannu Hibba kwanta ki huta".
Jalal da yanzu ya shigone ya ɗan taɓe baki tare da cewa.
"To me tayi da zata huta tunda fa gari ya waya in anga ta tashi dai yin salla ne, tun tuni birgima take a tayis wai sanyi take nema".
Dariya sukayi mata baki ɗayansu,
Ita dai Shatu ciki ta wuce.
Salla tayi kana ta fito. Koda tazo kitchen ta samu Hibba na suya musu Arish ɗin, tayi mamaki.
Cikin wasa tace.
"Kawo in karɓeki jeki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ai Hamma Jabeer ne yace min in ina aiki bazanji wuya ba, zanfi ganin lokaci ya gudu".
Dariya sukayi mata kana kowa yaci gaba da aikinshi.
Ita Shatu miyar sahur na asuba ta ɗaura musu.
Cikin ikon Allah shida dai-dai suka gam kan aikinsu.
Bayan Shatu'n ta taya Hibba suya kwai daban, ta jerasu a Foodflaks, in ta ajiye fefeyin soyayyan ƙwai da yaji haɗi da diddigin kifi, sai ta zuba soyayyan Arish a kai kana ta kuma rufeshi da fefeyin kwai haka ta rinƙa jerasu saida ta cika kulan.
Ummi kuwa ta sawa Saratu komai nata.
Sannan suka kimtsa wurin fes suka fito da komai suka jera a dinning table.
Nan duk suka wuce ɗauki.
Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu Imran, Jalal, Jamil, Sulaiman.
Cikin gajiya Ummi tace.
"Yauwa Jalal ku ɗauki manyan kulolin nan ku kai masallaci.
Sauran madaidaitan kuma ku ajiyewa sarkin bayi.
A bawa bayi da hadimai".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh lallai bana bayi sun samu uwar gijiyar data tuna dasu, bayan kuma anayi musu nasu na daban".
Cikin lumshe ido Shatu tace.
"Eh suma suci abinda muke dafawa da kanmu, ba sai na gandun nasuba".
Miƙewa sukayi suka ɗauki kulolin sun zo falon kenan Sheykh na shigowa, wani hadimi na biye dashi da manyan ledodi cike da ƴaƴan itatuwa.
Kusan a tare suke mishi sannu da dawowa.
Murya a bushe alamun ƙishi yake amsa musu kana ya nunawa Ummi leda ɗaya yace.
"Ummi a wonke wannan a haɗa da dabino mudu uku a basu su kai masallaci".
Ya ƙarishe mgnar yana wucewa.
Da sauri Ummi tace to.
Ta miƙe kenan Shatu tace.
"Ummi zauna bari in wanke sun".
To tace kana ta koma ta zauna.
Ita kuma taje ta wonke ta zubasu a tray kana ta ɗauko plates and cups masu yawa, tazo ta miƙawa Imran.
Da sauri suka amsa suka tafi.
Jim kaɗan suka dawo, cikin gajiya Jamil yace.
"Ummi ansha ruwafa mun samu Ladan na cin dabino".
Da sauri Hibba ta miƙa tare da cewa.
"Su ladanannan haka suke basa kiran salla sai sun sha ruwa."
Dariya sukayi mata kana suma suka miƙe sukabi bayanta.
Zama sukayi bisa kujerun kowa da abin yake hari.
Sai dai kab ɗibsu da dabino suka fara.
Ummi ce ta kalli Shatu tare da nuna mata babban tray'n da aka shirya komai na buɗa cikin Foodflaks guda 3 madaidata masu kyau, sai plate ɗin da aka shirya fruits masu ɗan karen sanyi, tupa, inabi ,kankana, abarba, gwanda, Lemu, ayaba, kana da dabino, da kwakwa,
Sai goran zam-zam madaidaci, kana sai cup da tea spoon a ciki, sai fork and knife a gefe da gefen plate ɗin dake cike da fruits ɗin komai biyu akasa.
Kulolin kuma ɗaya masane a ciki, ɗan namiyar kuma miyar Masar ne, sai ɗayan kuma, soyayyan ƙwai da dankalin, ɗayan kuma ferfesun kayan cikin ne.
Cikin nitsuwa Ummi ta ɗago tray ta miƙa mata tare da cewa.
"Yauwa gashi kai mishi lokacin shan ruwan na tafiya, yanzu zakiga ya fito".
Cikin sanyi da gajiya ta amshi tray'n kana ta nufi falon nashi, cikin nitsuwa take takun, a hankali tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon.
A can bisa Dinning area ta hangoshi yana zaune, kan kujera ɗaya, ya kuma jawo ɗaya kujerar ya ɗaura sawunshi a kai ya miƙesu, System ɗinshi na bisa cinyarshi.
A hankali take takowa saman steps ɗin tare da ratsa cikin jeren ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond sai sunkuyar da kanta tayi sabida ɗauke mata ido da suke.
A hankali ta isa kusa dashi, cikin tura baki tare da ɗan murguɗashi ta ajiye tray'n, a tsakiyar table ɗin.
ɗago kanta tayi da niyar ta ɗan juya, ta fita.
Wani irin buɗe idanin tayi gaba ɗaya tare da zubasu, bisa sharaban ƙafarsa ta dama, wanda sanaɗin zaman da ya ɗan yi ya miƙe ƙafafuwan nashi bisa ɗaya kujerar ne yasa suka ɗan baiyana, wani irin kallo mai cike da ɗimuwa takeyiwa zanen dake bisa ƙafarshi ta dama, da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannun hagun ta kama kanta sabida wani irin sarawa da ya farayi da ƙarfi.
Cikin sauri ta juyo tare da miƙa hannun damanta ta sauƙeshi kan...!
Akwai kayan gyara na amare da uwar gidaye da masu jego, ga mai buƙatar saya ga number ta 09097853276
By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kerman jiki, ta juyo ta fuskanci inda yake tsaye tare da abkawa jikinshi.
Cikin abinda bai gaza one second ba tamkar gilmawar walƙiya ya janye jikinshi ya kauce gefe.
Hakan yasa ta faɗa jikin show glass ta ruggumeshi gam-gam cikin tsuma da karkarwa tare da sa hannunta duka biyu ta riƙe kanta, tana mai cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil, Auzubikalimatillahi ta'ammati minsherri makalaƙa."
Tanayi cikin ɗan ɗaga murya mai baiyana firgicin da take ciki.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga ƙasan zuciyarshi har zuwa kan lips ɗinshi dole ya taune lip ɗin shi na ƙasa.
Kana sai ya gimtse ya murtuƙe fuska cikin tsare gida yace.
"Karki fasamin abuna!".
Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta.
Janye jikinta tayi daga jikin show glass ɗin da abkawar da tayi kanshi marfinshi ya ɗan tsage.
Nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe da ƙarfi.
Kana ta tura baki sannan ta juya ta fara tafiya tana ƙunƙunin.
"Allah ya isana banzan al'ada a rinƙa razana mutun anasa hanjin cikina na hautsunewa".
Baki ya taɓe kana ya zauna bisa kujerar ya jawo tray'n ya ɗibi abincin tuƙeƙen tuwo ne da miyar kase.
Tana fitowa sukayi sahur ɗin a gaggauce sabida lokacin ya ɗan ƙara to.
Washe garin da rana bayan anyi sallan azahar.
Ya shigo kamar ko yaushe.
A falo ya samu Ummi da Hibba ita kuwa Shatu tana ɗakinta tana karatu so take ta samu izu uku a wunin yau ɗin.
Gefen su ya ratsa kana ya zauna bisa kujerar zamanshi.
Bayan sun mishi sannu da zuwa ne, ya kalli Hibba cikin kula yace.
"Muhibbat ya azumin".
Cikin langwaɓe kai tace.
"Da wuya".
Kanshi ya jinjina kana yace.
"Jeki kira Aunty Juwairiyya".
To tace tare da miƙewa da sauri ta fita.
Shi kuwa wayarshi ya ciro ya kira Jalal dasu Imaran yace suzo su sameshi a falo.
Jim kaɗan duk suka shigo.
Key ya zaro daga al'jihun tattausan jallabiyar dake ƙasan al'kyabbar jikinshi ya miƙa wa Jamil tare da cewa.
"Ɗauko min briefcase a kan Bedside drower'n."
To yace kana ya juya ya tafi.
Shi kuwa Ummi ya kalla tare da cewa.
"Ummi me dame kuke buƙata ne?".
Cikin kulawa tace.
"Akwai komai, sai zam-zam ɗin kane ya ƙare saura baifi gora biyarba".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ba matsala zai isa".
Lokacin Jamil ya iso. Miƙa mishi jakar yayi, tare da zaunawa gefenshi.
Shi kuwa buɗe jakar yayi.
Murmushi Jamil yayi ganin tana ciƙe maƙil da rafan dubu-dubu sabbi dal-dal.
Rafa huɗu ya miƙawa Jamil hakama Jalal da Imran da Sulaiman.
Sannan ya kallesu tare da cewa.
"Kuje KMC plaza ku zabi kayan sallan.
Sai ya kuma kalli Aunty Juwairiyya yace.
"Aunty Juwairiyya, kuje tare dasu, da Ya Jafar ayi yadda aka saba.
Sannan ku zaɓi abin buƙatar ku."
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
"To mu gode, kuma za'ayi yadda kace."
Sai kuma ya kalli Ummi yace.
"Ummi kada ki manta da su Saratu".
Murmushi tayi tare da cewa.
"In Sha Allah babu abinda za'a mance".
Kai ya jinjina kana ya zaro rafan guda biyar ya miƙa mata, sannan ya miƙa wa Aunty Juwairiyya wasu rafofin kana ya bawa Hibba biyu.
Daga nan sukaci gaba da tattaunawarsu.
Washe gari kuwa da safe, suka shirya tsab zasu fita.
Aunty Juwairiyya ta Ummi cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ko zan kirawo Shatu mu tafi tare da ita ne?".
Da sauri Ummi tace.
"A a mijinta baice muje da itaba mujata mu tafi. Muje dai mu zaɓo mata duk abinda takeso".
Cikin gamsuwa da hakan tace to.
Hibba kuwa cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi muje da ita".
Fitowar Shatu ne ta samesu a tsaye cikin shirin tafi yasa ta kalli Ummi cikin sauri tace.
"Ummi ina zakuje?".
"KMC plaza".
Ta Bata amsa a taƙaice cikin sanyi tace.
"Nima inzo muje, in samu in fita insha iskan woje".
Jalal ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
"Boss ya hana". Ido ta zuba mishi kana ta juya ta kalli Ummi cikin sanyi tace.
"Shike nan Ummi kuje, Allah kiyaye hanya."
Amin Amin sukace har sun juya zasu tafi sai kuma tace.
"Ayyah Ummi dan Allah karku daɗe".
To sukace kana suka fita.
Shiru ta zauna a falon ba kowa hakane yasa ta kunna TV tashar Zee world.
Wani film mai daɗi ta samu sukeyi, sai dai bata san forkonshiba, bisa alamu duk sabone.
Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta.
Tana mgna da Rafi'a.
A haka bacci yayi awon gaba da ita.
Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta.
Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace.
"Ba salla sai kallo da bacci".
Jin haka yasa ta miƙe zaune tana gyara mayafin kanta.
Shi kuwa tuni ya wuce Side ɗinsa.
Tana idar da salla ta fito. Nan ta samu Saratu tazo, kitchen Suka shiga suka fara aikin yamman.
Sai gab da la'asar su. Ummi suka dawo da kaya niƙi-niƙi. Nan suka ajiye sukayi salla kana suka shiga kitchen ɗin.
Hibba kuwa yashuwa tayi a ƙasa tana birgima kamar bazata kai magriba.
Sai bayan sallan isha'i sun gama aikin sahur ɗin ne.
Suka dawo falo, nan Ummi ta nuna mata ɗinkunanta da aka bada tun Umaymah bata tafiba.
Sosai taji daɗin kayan da ɗinkunan, lallai tana son dogayen riguna Amman tana son surkawa da Shadda, atampa, leshi, musamman Waɗan nan ɗinkunan sunyi masifar kyau. Ko wanne dai-dai jikinta kamar an gwada ta.
Daga nan kuma suka nuna mata gellulluka da hibai da takalma da saraƙunan da suka zaɓo mata bayan sun zaɓawa kansu.
Sun nuna mata nasun ma.
Ummi ta ƙara da cewa.
"Duk zannuwan da abun ɗinkawan kuma an bawa Kabir telen suma duk cikin KMC suke.
Nanda salla dai komai zaizo dai-dai.
Cikin jin daɗi tace.
"Ngd matuƙa Ummi Allah ya saka da al'khairi".
Amin Amin tace. Kana tace.
"Sheykh zakiyiwa godiya".
Shiru tayi kamar bataji ba.
Hibba kuwa cikin jin daɗi tace.
Aunty Shatu na zaɓa mana wani Shadda lace mai masifar kyau iri ɗaya na ɗauka mana Royal blue and white Golding color. Nace a tsantsara mana dogayen riguna".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kai kinko kyauta mana".
Daga nan suka tattara tarkacen suka nufi makoncin baccin su.
Zaune take gefen Ummi tana riƙe da waya cikin murmushi tace.
"Allah ko Umaymah munyi kewarki".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"To ko zaku zomin Barka da sallane".
Da sauri tace.
"Eh Umaymah Allah in ya yarda zamuzo ki tambayan mana shi".
Cikin dariya Umaymah tace.
"Yoh mace da mijinta sai wani ne zai tambayar miki".
Cikin sanyi tace.
"Uhummm".
Ita kuwa Umaymah cewa tayi.
"Ina Umminku?".
Da sauri tace.
"Gata ta ƙarishe mgnar da miƙawa Ummi wayar.
Cikin fara'a suka gaisa kana Umaymah ta tambayeta ya yaran nata, tace duk suna lfy.
Nan take ce musu ta cewa Shatu ai a saudia zasuyi salla.
Sosai Shatu ta tayasu Murna.
Suna cikin hirar Hadimai guda uku suka shigo da jakukkunan guda uku.
Rusunawa sukayi bayan sun gaidasu ne,
suka ajiye jakukkunan tare da cewa.
"Gashi biyun inji Lamiɗo ɗaya kuma Gimbiya Aminatu ce tace mu kawo miki".
Sukarishe mgnar suna kallon Shatu.
Godiya tayi musu kana ta kalli Hibba data miƙo mata kuɗi sun kai dubu biyar.
Ta gane manufar Hibba shiyasa ta amsa ta basu.
Godiya sukayi kana suka tafi.
Jim kaɗan Hadiman Hajia Mama sukazo da saƙon Hajia Maman.
Sosai Shatu tayi godiya ta mashi kuɗi a hannun Hibba ta basu.
Nan Hibba ta tattara kayan ta shigar dasu, zata shigar dana HAJIA MAMA tace
"A Hibba barsu zan shiga dasu."
Gefe ta nuna mata tace ajiyesu anan.
Bayan sunyi sallan azahar sun fito zasu Fara aiki ne ta kalli Ummi tace.
"Ummi bari inje inyi godiya wurin Hajia Mama".
Cikin tsareta da ido tace.
"Ki bari mana sai ansha ruwa sai in rakaki daga nan kiyiwa Lamiɗo ma godiya.
Duk dai wannan kyauta da yakeyiwa duk ahlin masarautar Joɗa in lokacin salla ya gabato amman muje kiyi godiyar."
Da sauri tace.
"No Ummi ba sai an rakani ba, zanje ni ɗaya ma, kinga nasa al'kyabba".
Daga nan ta fice, cike da mamaki suka bita da ido.
Bayan kamar 37 minute ta dawo cike da fara'a sukaci gaba da aikinsu.
Can da suka fito dan yin sallan la'asar,
Ba kayan ba dalilinshi. Da sauri Hibba tace.
"Aunty Shatu kin shigar da kayan ne?".
Ci gaba da tafiya tayi tare da cewa.
"Maisu ta aiko an kwashe mata abunta dai".
cikin mamaki sukabi bayanta.
Yau azumi goma sha huɗu gobe 15 in Allah ya kaimu.
Bayan yaci abinci ne ya kira Umaymah nan yake ce mata.
"In Allah ya kaimu gobe iwar haka ƙarfe goma na dare zuwa sha ɗaya jirginmu zai tashi Umaymah".
"Kai da waye zaku tafi ne?".
"Nida Dr Aliyu, da Barrister Kamal, sai kuma Ya Hashim da Galadima, da Wambai da Abba na da cimgan ɗin shi".
Da sauri tace.
"To wai kana nufin kai bazaka je da taka cingam ɗin bane?".
Cikin sanyi yace.
"Kiyi haƙuri Umaymah dan Allah na roƙeki kada kice inje da kowa, dan Allah a barni mana in huta in na bar ƙasar kam".
Shiru Umaymah tayi saida taji ya kai ayane tace.
"Shi kenan Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, kuma muna nan tafe".
Amin Amin yace kana sukayi sallama.
Washe gari kab mutanen masarautar Joɗa masu zuwa Umrah sun gama shirin su.
Bayan ansha ruwa anyi sallan isha'i ne suka shiga kitchen dan aikin sahur, koda ta ɗauko Foodflaks ɗin da akasa mishi abin buɗa baki ko buɗe su baiba.
Hakane yasa Ummi tace to maza ta dafa mishi wani abun.
To tace kana ta juya ta ɗauko, kaza, kwai, dankalin turawa kaɗan, maggi, gishiri, tattasai, attaruhu al'basa mai Curry,
Duk ta matso dasu kusa.
Sai kuma ta ɗebo Kabeji karas.
Ta miƙawa Saratu tace.
"Yauwa Sara goga min su ƙananan, kada ki haɗasu wuri ɗaya, kana ki yayyaka min al'basa sannan ki jajjaga min wata."
Ta faɗin tana tura mata Attaruhu da al'basan.
Cikin nitsuwa Saratu tace.
"To Aunty ba matsala".
Ita kuwa Ummi meda hankali tayi kan girkin sahur ɗin.
Wanke rabin kazar tayi, tare da sata a tukunya ta watsa al'basa da maggi da tafarnuwa da citta da kanamfari kaɗan.
Sannan ta rufeshi. Tasa wuta yadda ya kamata.
Kana ta jawo robar dankalin ta fara ferewa tare da cewa.
"Allah aikin nan yana yawa Ummi, kusan wuni muke a kitchen mu kuma kusan kwana shima