Showing 315001 words to 318000 words out of 352722 words

Chapter 106 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30700

zuciyar Sheykh tayi da masifar ƙarfi wanda hakan ya haddasa wata iriyar fitinenneyar karkarwar zuciya da jiki, da ƙarfi ya sake rumtse idanunshi tare da sa yatsunshi cikin kunnuwanshi ya jijjiga sabida jin abin yakeyi kamar gizo.

Junainah kuwa wani irin masifeffen kuka tasa mai cike da rauni tare da yayyarfa hannunta murya a hargitse tace.
"Wayyo Adda Shatu! Adda Shatu zo kiga Ummeyn mu bata da lfy Adda Shatuuuu".
Tayi kiran da masifan ƙarfin.
Ganin yadda Ummeyn ta tureta tare da jujjuyawa a tsakiyar falon kamar irin wacce hajijiya ke juyawa haka take tafiya tangal-tangal.

Wani irin zabura Shatu tayi wanda yayi dai-dai da lokacin da Mamma da Umaymah da Ummi da suka fito yanzu suka haɗa baki wurin cewa.
"La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallam".
Sai kuma gaba ɗaya jikinsu ya saki wani irin masifeffen karkarwa da sakewa ya rufesu.
Suka kasa koda ɗaga sawunsu bare su matsa inda suke.
Sabida tsananin kaɗuwa.

Ita kuwa Shatu tsalle ɗaya tayi ana biyu sai gata a bakin ƙofar Bedroom ɗinsa.
Cikin gigita shima ya yunƙuro da ƙarfi ya mara mata baya, sabida yadda yake jiyo falon a hargitse.

Gudu ya farayi ganin yadda Shatu ta fice a guje sabida ihun Junainah da take jiyowa.


Da sauri Yah Al'ameen ya sako kansa cikin falon jin muryar Junainah da abinda take cewa.

Yah Jafar da Jalal da Aunty Juwairiyya na biye
dashi a baya.

Cikin matsanancin tashin hankali Shatu ke kallon Ummey dake tsaye acikin tsakiyar falon, tana me riƙe da kanta dake juya mata sosai, ko mai bibbiyu take ganinsa, hakan yasa numfashinta soma ƙoƙarin ɗaukewa, take kuma idanunta suka rufe rub, hakan yasa ta-ta-fi luuu zata faɗi.

Da wani irin sauri mai haɗe da gudu Shatu da hankalinta yakai ƙololuwa wajen tashi ta ƙarasa wajen da Ummeynta ke tsaye, hakanne kuma yasa Ummeyn ta faɗa jikinta.

Hannayenta duka biyu tasa ta rungume Ummeyn tare da fara jinjigata cikin kiɗima da gigita, cikin muryar kukan da yazo mata lokaci ɗaya ta shiga faɗin.

“Innalillahi Wa’inna ilahirraju’un.
Ummeyna Ummeyna maiya sameki? Ummey ki tashi dan Allah, ki buɗe idanunki!!!”.
Ta ƙare maganar nata cikin matsanancin kuka, tare kuma da sanya hannayenta ta shiga girgiza Ummeyn da ƙarfi.

Sheykh kuwa dake tsaye ganin fuskar matar da Shatu’n nasa ke kira da sunan Ummey ne yasa shi, jin wani irin abu ya daki zuciyarsa da ƙarfi, wanda hakan yasanya shi jin ƙafafunsa sunyi masa nauyi, lokaci ɗaya kuma wani irin rauni ya cika zuciyarsa, wanda har hakan yasa yaji wasu irin ƙwalla masu ƙuna suka bayyana acikin idanunsa.

Ahankali ya ɗan soma taka ƙafafunsa tare da ƙarasawa wajen da Shatu da kuma Ummey'n suke.

Durƙusa guiwowinsa yayi aƙasa a dai-dai lokacin daya iso wajen da suke, cikin wani irin yanayin dake fusgansa, ya shiga ambaton sunan Allah, a dai-dai lokacin daya sanya duka hannayensa biyu ya rungumo Shatu da kuma Ummey’n jikinsa.

Cikin wata irin sassanyar muryarsa wanda amo da kuma sautinta baya bayyana ya shiga faɗin.
“Subahanallah!. Alhamdulillah!! Hasbunallahu wani’imal wakil, innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, la haula wala k’uwwata illa billahil aliyil azim!!”
Sune tasbihan da yaketa mai-mai-tawa
Shatu dake kuka kuwa jin ya sakasu ajikinsa ne, yasa ta ɗago jajayen idanunta dake tsiyayar da hawaye, cikin matsanancin damuwa da kuma ruɗewa haɗi da tashin hankalin da ta samu kanta aciki tace.

“Hamma Jabeer Ummeyna bata numfashi.
Dan Allah kace ta-tashi, kace ta buɗe idanunta, banason wani abu ya samu Ummey na, ka taimakamin, wayyo Dedde na Umaymah kuzo Ummeyna ...”

Kasa ƙarasa maganar nata tayi, saboda sosai kuka yaci ƙarfinta, sai-dai kuma amma duk da haka bata daina jijjiga Ummeyn nata ba.

Su Yah Jafar Jalal Ummi Mamma Aunty Juwairiyya Aunty Rahma Khadiya Aunty Amina Ishma, Hafsi Yah Al'ameen kuwa gaba ɗayansu zobe sukayi musu, cike da tarin al'ajabi al'hini kaɗuwa da tarin farin ciki.

Junainah kuwa da ta ƙara ruɗewa saboda ganin kukan da Shatu keyi, ƙarasowa jikin Shatu’n tayi ta raɓa jikinta, cikin muryar kuka take cewa.
“Adda Shatu Ummeynmu.
Adda Shatu Ummyen kice ta tashu mukaita asibiti kada wani abu ya sameta!”.

Sauran jama'ar kuwa.
Kowannensu fuskarsa ɗauke da hawaye suka ƙaraso garisu sosai kusa dasu Shatu, Sheykh, da Ummey’n suke.

Sautin kukan Aunty Rahma ne mai nuna tsantsar farin ciki da na Umaymah da Mamma ne suka fito fili, a dai-dai lokacin da sukayiwa Ummey’n zobe, Kowannensu kuka yake, sai-dai kallo daya zakayiwa kukan nasu ka fahimci cewar ba kukan baƙin ciki bane kukane na tsantsar farin cikin da yiwa Allah godiya, domin kuwa acikin muryar kukan nasu suke ambaton sunan Allah, suna me faɗin.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah ya Allah!! Alhamdulillahil lazi bi ni’imati hi ala tatimussalihat!!!”

Umaymah kuwa da matsanancin farin cikin mara misaltuwa da take jin kanta aciki ya kasa ɓuya, durƙushewa tayi bisa guiwowinta tare da kifa goshinta aƙasa tayi Soujjadar nuna, matsanancin godia ga Allah daya dawo mata da ƴar uwarta.

Ummey kuwa wani irin Numfarfashi taja sai gata a sume.

Dai-dai lokacin kuma Jamil da jiyo hayaniyarsu ya sashi tahowa a guje, ganinsu cike a falon kowa fuska cike da hawaye kuma sai kalmar Alhamdulillah suke maimaitawa.
Duk sun kasa bin ta kan kalaman Shatu.
Ganin Jamil ne yasata mgn cikin rauni tace.
"Jamil dan Allah taimaka min Ummey na ta suma".
Jin hakane yasa ba tare da ya iso inda sukeba ya nufi kitchen da sauri mai kama da gudu ruwa ya ɗebo kana ya dawo.
Yana isowa gab dasu, ya zaro idonsa baki ɗaya murya can sama yace.
"Mammeyyyyy".
Sai ga ruwan ya kwaɓe a hannunshi shima ya faɗi bisa jikin Yah Jafar a sume.

Gaba ɗaya sun gaza cewa komai sai ambaton Allah.
Da gudu Affan da tun jiya daya dawo dasu Giɗi bai gana da Hamman nasu ba sai yanzu ya nufo Part ɗin.
Jin ƙaran muryar Jamil ne ya sashi shigowa falon da sauri yana cewa.
"Me haka Jamil lfyarka kuwa?".
Turus yayi a bakin ƙofar ganin duk suna cike a falon sun taru wuri ɗaya kowa da irin addu'ar da yakeyi.
Cikin tsaro da fargabar kardai wani abune ya samesu ya nufosu.

Cikin kaɗuwa yace.
"Mamey". Ya kira sunanta da ƙarfi lokacin da idanunshi suka sauƙa bisa fuskar Ummey.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli Sheykh dake mgn cikin rawan murya da rauni yake cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Yah Allah na gode maka bisa wannan rahama da kaimin ko yau ka ɗauki raina burina ya cika, yau gani ga Mameyna a cikin masarautar Joɗa a suffar mutun bani Adam ba tsuntsuwar Boleru ba".
Wani irin kuka ne mai rauni ya kwabce mishi.

Yah Jafar ma kuka yakeyi tare da cewa.
"Alhamdulillah al'ƙadarin Magauta ya karye".
Ummi kuwa da rarrafe ta rusuna gaban Ummey tare dayin ƙasa da kanta cikin rauni tace.
"Barka da dawowa Adalar Uwar gijiyata".
Umaymah kuwa da sauri ta jawo wayar da ta gani kusa da ita.
Saida ta danna sai taga ashema wayar Hibba ce da ta bawa Junainah nayi Game.
Jadda ta dannawa kira.
Yana ɗagawa tace.
"Assalamu alaikum Alhamdulillah Allahu Akbar Jadda! Jadda!! Jadda!!!".
Cike da kaɗuwa Jadda dake kishinƙiɗe ya miƙe zaune tare da kallon Sitti dake yanka mishi lemu wanda tana iya jiyo abinda Umaymah ke faɗa sabida yadda take mgn da ƙarfi.
Wani irin dogon numfashi suka sauƙe a tare jin Umaymah na cewa.
"Alhamdulillah Jadda Aunty Mamey ta dawo Jadda zatonmu da tsammanin mu ya zama gsky Aunty Mameyna ta dawo gata gabanbu Jadda kace Alhamdulillah".
A tare Jadda da Sitti suka fara maimaita kalmar hamdala.

Affan kuwa cikin wani irin sauri ya juya a guje tamkar ƙaramin yaro ya nufi Part ɗin Abbansu.
Yana shiga da gudu yana mai cewa.
"Abba Abbanmu Abbana Mamey Mamey".
Da sauri Gimbiya Samira amaryar Abban ta fito tare da cewa.
"Affan lfy kuwa Abbanku yana fada".
Ai bai kuma bin ta kanta ba ya fito.
Kiciɓis yayi da Hajia Mama tana cewa.
"Kai lfy kuwa kake gudu kamar yaro?".
Ba tare da ya tsaya ba yace.
"Abba nake nema ina yaje Mamye."
Daga nan ya nufi fada.

Ita kuwa Hajia Mama cikin wani irin masifeffen tsinkewar zuciya da fargaban jin sunan da bata ko son jin an kira ta juya ta nufi ɗakinta.

A can fada kuwa bayan sarkin ƙofa yayiwa su Bappa iso cikin ƙaton falon.
Abboi na gaba Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro suna biye dashi a baya kana sai masu tsaronshi da suka tsaya can bakin ƙofar shiga sabida dakatar dasu da yayi.

Suna shigowa Lamiɗo dake fuskantar Kofar shiga fuska cike da annuri da haiba yace.
"A a a Masha Allah lalle marhabin da Alhaji Abbo lale da zuwa masarautar Joɗa Fulle bandu fullo".
Da sauri Wambai, Dirankadi, Ɗan isa, Ɗan buram, Sarkin fada, Ɗan kade, Galadima Ɗan maliki Chiroma Durbi Ma'aji. Duk suka miƙe tsaye cikin tsananin sakin fuska da alamun sanayya na mutuntaka suka kalli Abboi tare da haɗa baki wurin cewa.
"Marhababika da zuwa masarautar Joɗa".
Sai kuma ɗan zagi ya fara baza rigarsa tare da cewa.
"Sarki ya gaisheka. Sarki yace ayi maka sannu da zuwa fullo Nbandu fullo manyan fada na farin ciki da zuwa ka".
Wani irin murmushi Abboi yakeyi mai cike da kamala ya nufi gaban Lamiɗo.
Har kusa dashi ya isa kana ya rusuna, yayinda Bappa da sauran ke biye dashi a baya.
A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da ture hularshi yayi baya da ita.
Cikin alamun shaƙuwa Lamiɗo yasa hannunsa tsakiyar kansa tare da cewa.
"Allah yayi muku al'barka".
Murmushi Abboi yayi tare da cewa.
"Amin ya Allah Baba".
Sabida Lamiɗo yasan Abboi a matsayin ɗansa yake zuwa gareshi yana jin daɗin abokin mahaifin nashi ya sanya mishi albarka".

A hankali ya koma ya zauna ya tanƙwashe sawunshi tare da cewa.
"Barka da hatsi".
"Barka dai".
Lamiɗo yace.
Abba dake gefenshi ne ya kalli Abboi tare da bashi hannu suka gaisa.

Sarkin fada kuwa da sauri ya fito ya umarci hadimai maza da su kawowa baƙin abin taɓawa ai kuwa nan da nan aka cika gabansu Abboi da abubuwan ci da na sha.

Cikin tarin kula Lamiɗo ya kalli Bappa tare da cewa.
"A a Malam liman tafe kuke tare da shine?".
Cikin nitsuwa Bappa yace.
"Na'am tare muke".
Kai Lamiɗo ya jinjina tare da kallon Abboi gyara zama Abboi yayi fahimtar tambayarsa Lamiɗo yayi a hankali yace.
"Ai mutumin ƙasar mu ne zamane da wani babban dalili ya dawo dashi nan ƙasar ku".
Cikin gamsuwa Lamiɗo yace.
"Makiyayinka ne shi?".
Cikin mutuntaka da kunya Abboi yayi shiru dan shi Bappa yafi ƙarfin makiyayinsa a wurinsa Bappa ɗan uwane".
Cikin yin murmushi Bappa yace.
"Eh ni ɗaya daga cikin makiyayansa ne".
Yayi mgnar sabida fahimtar Abboi bazaice hakanba.
Sai kuma suka sake wani sabon gaisuwa.
Nan Babba ke cewa.
"Tare muke da mai ɗauki shi da kuma ƙanwata sunzo ganin jikar tamu su sun isa can".
Cikin tarin jin daɗi Galadima yace.
"Masha Allah, Allah ya bada ladan ziyara".
Amin Amin duk suka amsa.
Dai-dai lokacin kuma Affan yasa hannunshi ya ture sarkin ƙofa dake tareshi yana cewa.
"Lamiɗo yana ganawa da manyan baƙi".
Cikin haki da ɗaga murya yace.
"Kai da Allah bani wuri. Abbana nake nema Abba! Lamiɗo!".
Yayi mgnar da ƙarfi tare da kutsa kai cikin falon.
A tare suka juyo suka zuba mishi ido Abba kuwa da sauri ya miƙa tare da cewa.
"Na'am Affan meya faru?".
Cikin haki yace.
"Abba Mamey Lamiɗo Mamey'nmu ta dawo wlh Mamey ta dawo gata can a Part ɗin Hamma Jabeer su Umaymah nata kuwa Mameynmu ta dawo a mutun ba tsuntsuwar Boleru ba".
Kusan a tare gaba ɗayansu suka miƙe banda Lamiɗo dasu Abboi tare da cewa.
"Kai Affan nitsu ka gaya mana".
Cikin kaɗuwa ya kamo hannun Abban nasu tare da cewa.
"Zo muje ka gani wlh Mamey na ta dawo a mutun ba tsuntsuwar Boleru ba".
Ai kafin ma ya rufe baki Abba ya juya da sauri yabi bayan Abbanshi.

Abboi kuwa da Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro kallon juna sukayi tare da yin murmushin zatonsu ya tabbata jinjinawa juna kai sukayi
Sai kuma Bappa yace.
"Ya ilahi meke faruwa?".
Cikin yin Murmushi Lamiɗo yace.
"An tashi taron fada sai gobe".
Nan take duk sauran suka miƙe suka fita kowa ya nufi muhalli sa cike da alhini.

Shi kuwa Lamiɗo Galadima ya kalla tare da cewa.
"Muje gidan Jabeer ɗin Kuma taso muje ƙofar surkin naku".
Yayi mgnar da yaƙini a ransa su Bappa ne ke tafe da abinda suka daɗe suna tsumayin wato dawowar Mamey (Ummey) kenen.

Ai kuwa da sauri su Bappa suka bi bayansu.
Fadawa na musu rakiya.
Ɗan zagi na baza riga da cewa.
"Gyara kimtsi, sarki ya gaisheku".

A haka suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Kusan a tare suka isa dasu Abba dan rawan da jikinsa keyi ya hana masa yin sauri.

Lokacin ɗaya kuma duk masararutar Joɗa ta cika da lbrin dawowar Mamey kamar yadda labarin juyewarta da bacewarta ya karaɗe ko ina na Masarautar Joɗa.

Suna shiga Affan yaja hannun Abbansu har gaban Shatu da Sheykh wanda ke ruggume da Ummey har yanzu a sume.
Sun kasa taɓuka komai, duk da shi dai Sheykh ya gane a sumen take.

Cikin haki Affan yace.
"Gata Abba ka gani ga Mameynmu".
Wani irin farin ciki ne mai masifar yawa dake shirin ɗauke masa numfashin sa ne ya sauƙo mishi, jin hakane yasa yayi sauri ya sunkuya a tsakiyar falon ya fuskanci al'ƙibla ya faɗi yayi sujjada gaban Ubangijin talikai sarki buwayi gagara misali.


Dai-dai lokacin su Lamiɗo suka shigo.
Ganin Bappa ne yasa kukan Shatu tsananta murya na rawa tace.
"Bappa Ummey na Bappa Ummey na".
Da sauri irin na sarakuna su Lamiɗo suka ƙara so wurin.
"La ha ila ha illalalhu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallam".
Suka faɗa a baki a haɗe tare da zama bisa kujera.

Cikin sanyi Bappa ya kalli Shatu kana a hankali ya juyo yankallesu gaba ɗaya hawayene cikin a fuskarsu.
Ga Jamil a sume.
Galadima kuwa da Lamiɗo murmushi sukeyi tare da maimaita ƙalmar hamdala".
Da sauri Junainah tazo ta faɗa jikin Bappa tare da sakin kuka tace.
"Bappa Ummey na ta rasu ne?".
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da juyowa ya kalli Khadijah ƙanwar Shatu cikin sanyi yace.
"Khadijah in akwai zam-zam a gidan kawo min in kuma babu bani ruwan sanyi".
Da sauri Ummi ta miƙe kitchen ta nufa tana mai cewa.
"Akwai zam-zam bari in kawo".
To kawai yace mata.
Abba kuwa a hankali ya ɗago kanshi kana ya jingina bayanshi da sawun Lamiɗo ya kife kanshi bisa guiwar Lamiɗo sai ga wani kuka mai rauni ya subce mishi.

Da sauri Bappa ya amshi goran zam-zam mai sanyin.
Matsowa yayi kusa da Shatu.
Da sauri ya buɗe goran zam-zam ɗin ya tsiyayi sassanyan ruwan a tafin hannunsa, kana ya saita fuskarta tare da cewa.
"BISMILLAHI".
Ya watsa mata shi a fuska da ƙarfi tare da sunan Allah.
Shiru babu motsi da sauri ya sake tsiyayo wani ya watsa mata tare da bismillah.
Stiil ba motsi da ƙarfi ya kuma watsa mata a karo na uku.
Da ƙarfi taja wani irin nannauyan numfashin mai tsawo tare da cewa.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Astagafirullaha wa'atubu illaik".
Kusan a tare gaba ɗayansu falon suke furta Alhamdulillah.

Cikin wani irin yanayi Jabeer, Jafar, Jalal, da Jamil wanda Bappa ya watsa mishi ruwan ya farfaɗo a firgice suka matso gabanta sukayi mata zobe.
Kana Umaymah da Mamma da Aunty Rahma suna kusa dasu.
Cikin wata iriyar murya mai raunin amo Sheykh ya kamo hannunta murya na rawa yace.
"M...mah..Mam.. Mameyyy".
Da sauri ta ɗago jajayen idanunta da tsananin ciwon kai ya rinasu ta watsa masa su cikin nashi ba tare da ta amsaba.
Cikin rauni ya kuma cewa.
"Mamey Mamey na Jabeer ɗinki ne! Mamey kin manceni ne, gani Ga Yah Jafar ɗina ga sakalallun tagwayenki ga Affan ɗinki ɗan lelenki ga Abba na Ga ƴan uwanki Umaymahna ga Mamma na ga autar Sitti Aunty Rahma Mamey Jabeer ɗinkin ne ga Ummi amintacciyar jakadiyarki mai riƙon amana".
Shiru sukayi baki ɗayansu suka zuba mata idanu.
Ita kuwa ido ta lumshe wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata cikin raunin murya tace.
"Alhamdulillah Jabeer na tunoku gaba ɗayanku".
Wani irin farin cikin ne mai tarin yawa ya cika musu zuƙatansu baki ɗayansu.

Da sauri suka juyo suka kalli Bappa da yake cewa.
"Alhamdulillah baiwar Allah ta tuno baya ta gane ƴaƴanta da ƴan uwanta".

Da sauri Sheykh ya juyo tare da kamo hannun Shatu wacce cikin kuka da rarrafe ta matso gaban Ummey da kyau murya na rawa hawaye na zuba tace.
"Innalillahi shike nan Ummey ta tuna baya kenan Bappa zata mantani kenan?".
Wani numfashin Ummey taja tare da zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu kamo hannun Junainah tayi cikin rawan murya hawaye na kwarya tace.
"Ummey ki kalleni Ummey nice Shatunki fa Ummey koda zaki tuna baya kada ki manceni Ummey kalleni fa nice Shatunki kalli Junainah'nki ƴar autarmu Ummey koda zaki manceni dan Allah kada ki mance Junainah ke kika haifeta a cikinku muka reneta bata san kowa ba sai nudake".
Wani irin kuka ta saki mai ƙarfi tare da jawo Junainah da itama kukan takeyi juyowa tayi ta kalli Yah Sheykh cikin rawan murya tace.
"Ummey nane fa da tun inada shekaru takwas a duniya na bar gaban Dedde na da Abboi na na dawo gabanta ita ta raineni kamar Uwa itace ta haifi Junainah itace ta bamu tarbiya sanadinta muka baro ƙasar Cameroon muka dawo Nigeria muka zauna Rugar Bani wayyoooooooo Allah na Ummeyna kada ki manceni".
Shirun da Ummey tayi yasa gaba ɗaya tausayin Shatu da Junainah yasa kowa zubda hawaye sabida fargabar kada fa ya zamo ta tuno baya can ta mance yanzu.
Kuka sukeyi baki ɗayansu hatta Afreeen dake hannun Aunty Amina kuka takeyi.

Cikin rawan murya Shatu ta kamo hannun Ummey ɗaya Junainah kuwa ta kwantar da kanta bisa cinyar Ummeynta a tare suka haɗa baki wurin cewa.
"Ummey kin mance mune?".
Da sauri Shatu ta saki wani irin kuka tare da faɗawa jikin Ummey jin tace.
"Ban mance kuba Boɗɗo na Autata".
Murmushi sukayi baki ɗayansu falon ita kuwa Shatu da Junainah kukan farin ciki sukeyi.

A hankali Bappa yasa tafin hannunshi ya share hawayensa dake gangarowa hakama Abboi sai suke tuno kamar yau suka samu ɓoleru'n nan.

A cikin masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya labarin dawowar Mamey ya riski kunnuwan mutanen cikinta da kewaye.

Cikin wani irin mamaki Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da kallon Babba Basiru daya kawo mata lbrin cike da kaɗuwa tace.
"Kai Basiru muje mu gani".
Ai kuwa da sauri suka juyo suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.

Yayinda Babban ɗan ta Yah Hashim da Laminu mai binshi suka mara mata baya.

Gimbiya Samira ma amaryar Abban da Mom mai bin Mamey da sauri suka nufi Part ɗin Sheykhhhh ɗin.

Gimbiya Aminatu da Matar Galadima ma jiki na rawa suka nufi can.

Hajia Mama kuwa wani irin ihu tayi tare da rugawa a guje ta nufi Part ɗin Sheykhhhh a gigice.

Baba Kamal da ɗansa Sulaiman da sauri suka nufi can.

Dr Aliyu ma da matarsa da ƴarsa Rahima da sauri suka nufi can.

A cikin falon kuwa da sauri Shatu ta amshi gorar zam-zam ɗin da Bappa ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login