Showing 297001 words to 300000 words out of 352722 words

Chapter 100 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30719

mahaifiyarta".
Da sauri tace.
"Ummey na tana gida, bata zoba".
Cikin son fahimtar manufar Abba Sheykh yace.
"Kuma kuna irin zaton da nakeyi ne?".
Da sauri Lamiɗo yace.
"Aimu namu ma yafi naka ƙarfi".
A hankali yace.
"Toko dole mubi komai a hankali".

Kai suka jinjina kana Sheykh ya nuna mata hanya tare da cewa.
"Koma ciki ina zuwa".
To tace kana ta juya ta tafi.
Su kuwa zama sukayi.
A nan Sheykh yake basu lbrin batun ƙarar da ya shigar kan case ɗinsu Gaini.
Tuni Affan kuwa ya tattara dukkan hujjoji da shaida a matsayinsa na lawyer mai cikar ƙwarewa.
So yama tafi shida Sulaiman da Malam Abubakar.

Gobe za'a zauna a kotun.


Alhamdulillah yau kwana biyar da haihuwar Shatu.
Anata shirye-shirye bikin suna.
Su Umaymah ma yau tunda safe suka iso, ita da Hibba da Aunty Rahma da Mamma da Ishma.
Sai Haroon da Jannart ɗinsa.
Gaba ɗaya gidan ya cika da ɓakin.

Junainah kuwa tun kafin su iso take Part ɗin Mami matar Affan da yaransu Zahra'n Hamma Yusuf ce da tazo take zana musu lalle.

Gaba ɗayansu cike suke a falon.
Sai hadimai dake can kitchen sunata faman aiki.

Umaymah ce riƙe da jaririyar cikin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah yau gani riƙe da Yar Jazlaan.
Alhamdulillah ƴarinya kuwa sak Mamey.
Cikin sauri Aunty Rahma ta ajiye cup ɗin da take shan ruwan da shi tare da leƙo fuskar ƴar tace.
"Alhamdulillah kuce dani take kama".
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa".
Jamil ne ya ɗan jujjuya kanshi tare da cewa.
"Yoh ai ke masu kama dake sunada yawa Adda Shatu ina Junainah ne".
Khadija ce ta ɗan kalleshi tare da cewa.
"Uhumm Junainah kuwa Sarkin yawo tun da sassafe ta tafi gidan Affan har yanzu bata dawoba".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Tanada saurin sabone ba ruwanta kowa natane".
Kai Sheykh ya jingina jikin kujera yana kallon Shatu dake lumshe idonta alamun bacci takeji.

A hankali Jalal ke tafiya tana riƙe da yatsarsa manuniya tana ɗigirgire da sawunta.
Wanda takalmanta ke hannun Jalal ɗaya cikin yawan surutunta tace.
"Yah Jalal lallena zai ɓaci fa.
Ni mu zauna a nan sai ya bushe mu tafi".
Sunkuyowa yayi ya ɗan kalleta fuska ɗauke da murmushi yace.
"Mun isofa Junnu saura kaɗan".
Tura baki tayi dai-dai lokacin da yasa hannunshi ya tura ƙofar tare da sallama a bakinshi.
"Ni dai bana son Junnu Hamma Jabeer yace ba kyau ace Junainah yafi daɗi".
Tayi mgnar tana ƙara riƙo hannunshi.
Da sauri Umaymah ta kalleta ta kuma juyo ta kalli Ishma dake lafe jikin Shatu.
Ita kuwa Junainah da sauri ta saki hannun Jalal tare da rugowa a guje tare da cewa.
"Lah oyoyo Ummey na".
Tayi mgnar tana nufo gaban Aunty Rahma data hango tamkar Ummey'nta.
Da sauri ta tsaya tare da cewa.
"Laah".
Sai kuma ta juyo ta kalli Ishma kana ta kalli Aunty Rahma.
A hankali ta ɗan matsa kusa da Shatu cikin yanayin jin kunya tace.
"Ina kwana".
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Rahma da suma duk ita suke kallo.
Da sauri Mamma tasa hannunta ta kamo hannun ta jawota kusa da ita kusan a tare sukace.
"Ikon Allah kenan dan Allah kalli kama".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ai natama dana Ishma wasane na Ummey na da Aunty Rahma shine gaske".
Cikin sauri Jalal yace.
"Dan Allah yaushe Ummeynki zata zo mana ne kam".
Murmushi Aunty Amina tayi tare da cewa.
"Ai kam zata zo wata rana amman ba yanzuba".
Da sauri Aunty Rahma tace.
"Ai kuwa in sha Allah mu kam zamuje mu ganta".
Junainah ce ta ɗan lafe jikin Mamma tana kallon Umaymah a hankali tace.
"Itama ai zata zo taga Baby".
Murmushi Umaymah tayi tare da shafa fuskarta.

Hibba kuwa Jawo Ishma tayi ta ajiyeta kusa da Junainah hota ta fara ɗaukansu tana cewa.
"Masha Allah tagwayen kamanni".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Wlh kuwa".

Ranar dai haka suka wuni.
Anata hira da raha.


Ranar suna bayan sallan asuba, aka raba goro da dabino.
Kana akayi yanka yarinya taci sunan Ummey kuma Mamey Aisha.
Jamil na shigowa ya faɗawa Umaymah dasu Mamma dake cike a falon.
Da sauri Hibba tace.
"To da wanne sunan za'a kirata?."
Shiru Shatu dake cikin shiga ta al'farma tayi tana kallonsu.

Khadija ce ta ɗan gyara zama tare da cewa.
"Afreen yayi".
Da sauri Jamil yace.
"Sosai ma kuwa kin iya zaɓi mai kyau kamar yadda kike mai kyau".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunya, sai kuma ta tashi da sauri tayi falon Shatu jin Jamil ɗin na cewa.
"Umaymah tayi ko surkaki ce".
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Murmushi sukayi tare da cewa.
"A tayi sosai ma kuwa".
Sai kuma yace.
"Ko dai baza'a bani ita bane Adda Shatu?".
Da sauri tace.
"A a ni kam banceba ba ruwana, ai ina ganinku bini-bini kuna tare".
Sheykh da yanzu shigowarsa ne yace.
"In ka nitsu mu baka ita in Kuma baka bar ƙelle-ƙellen idoba da kallon mata mu habaka its".
Ƙeyarshi ya sosa tare da cewa.
"A ai yanzu na girma na bari ko Yah Haroon."
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Haroon dake bayan Sheykh.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa Haroon zama yayi gefen Mamma tare da cewa.
"Ai kam yanzu ka girma".

Ummi ce ta fito daga kitchen da akoshin cike da hanta gashin tukunyar da akayiwa Shatu.
Sai Jannart kuma riƙe da gashin da tayi musu nasu daban.
Sara da Larai kuwa da sauran duk riƙe da manyan Foodflaks suka shigo dasu a hannunsu.
Kana suka koma suka dauko plates da cups da spoons.
A tsakiyar falon suka ajiyesu.

Nan suka taru gaba ɗayansu suka zauna a falon.
Harda Junainah.

Aunty Amina kuma da Khadijah da Shatu falonta suka tafi.
Shi kanshi Sheykh a nan kusa da Umaymah ya zauna a plate ɗaya sukeci shida Haroon.
Ishma da Junainah.
Jannart da Hibba da Aunty Juwairiyya.
Rahma Kuma ita da Mamma Umaymah kuwa ita da Ummi.
Jalal da Jamil.

Affan kuwa yana can Abuja bai dawoba shida Sulaiman da Malam Abubakar sai dai Alhamdulillah shariya tayi kyau babu jeka ka dawo kasan cewar akwai manyan shaidu kuma ga yawan Addu'o'in iyaye da yan uwa kan su Gaini da Addu'o'in masallatan jumma'a kana ga taimakon gskya. Da samun ƙwararren lawyer da kuma sa bakin babban mutum Lamiɗo da Jadda da kuma shi kansa Sheykh.
A ranar kotu ta wonkesu tsab.
Kana akayi ram da Dineal dama sauran ɓata garin jami'an tsaron kasar da suke da hannu cikin irin wannan kitimurmurar.

Shi kuwa Sheykh Affan ya gaya mishi komai amman yaƙi ya yardama suyi mgnar da Shatu da zaran ta fara mishi mgnar sai ya zille yafi son yayi mata ba zata.

Bayan duk sun gama cin abinci ne, kowa wacce ta fesa wonka da kolliya
Sosai sukayi kyau cikin shiga ta al'farma, Hajia Kubra ma tazo.
Dama sauran abokan arziki.


A hankali Sheykh ya meda ƙofar ɗakinshi ya rufe, tare da amsa kiran Hajia Mama.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
"Hahaha shegu zanyi mgninsu yau.
Tuni fatar ragon sunan ya shiga hannuna na gama yin shirina har na meyar musu da ita.
Da sauri cikin tsoro yace.
"Toh me kikasa a cikinta".

Dai-dai lokacin kuma sairkin al'adun Sunan masarautar Joɗa ya shigo falon wurinsu Umaymah tare da Gimbiya Aminatu da
Yana riƙe da fatar ragon sunan.

Bayan sun zauna ne ya sun gaisa ya shimfiɗa fatar ragon sunan.
Tare da miƙowa Ummi dake riƙe da Afreen yace.
"Masha Allah kawo Aisha ƴar Aysha jikar Aisha mu cika mata masakinta".
Da sauri Ummi ta miƙa mishi Afreen dake naɗe cikin shawul fari ƙal mai taushi da ɗaukan, ido.

Hannunshi yasa ya fara zare Shawul ɗin yayi kana ya fara cire mata kayan jikinta ya rage daga ita sai Pampers.
Aunty Rahma ce ta ɗanyi ajiyar zuciya tare da cewa.
"Kai wannan masarautar Joɗa taku tanada tsarabe-,tsaraben al'adu masu masifar tsauri.
Allah ya baku cikekken ahlul sunna ya mulki masarautar shine kaɗai zai kauda al'adun ya wanzar da sunna, ina dalili a ninke yarinya cikin ɗanyen fata ayi ta garata a tsakiyar ɗakin mahaifiyarta ai ko ba'ayi hakaba dole zata san ɗakin uwartace".

Umaymah ce ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
"Toh ya zamuyi tunda abu nasune".
Gimbiya Aminatu ce tayi murmushi tare da cewa.
"Watan wata rana dai tabbas al'adun zasu kau sunna ta wanzu in wanda muke zaton ya yarda ya amshi masarautar".

Allah ya sa haka.
Umaymah tace.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Suna masu kauda kansu kan fatar dan wani irin warin da basu gane kamsaba da fatar keyi wanda dole in kaji zakayi zaton ƙarnin ɗanyar fatarne.
Wanda fiyafiyen ya gauraye dashi sai dai shi kanshi sarkin al'adun sunan kauda kanshi yakeyi dan azabar warin fiyafiyar da Hajia Mama ta turbuɗa cikin fatar.
Kansu suka ɗan kakkauda tare da cewa.
"Dan Allah kayi maza ka gama ka fito da baiwar Allah".
Cewar Umaymah da Mamma.
Shi kuwa Sarkin al'adun suna murmushi yayi tare da naɗa Afreen cikin fatar ragon sunan,
da Hajia Mama ta gama zazzaga mata madarar fiyafiya mai masifar ƙarfi.
Sai dai da yake fatar a ninke take yana kuma warewa ya naɗe da sauri to sai ya zama kamar a rufe yake, shiyasa basu ji wari sosai ba.
Dan duk wari shi ai in a rufe yake bakajin warin sosai.
Cikin murmushi mugunta ya haɗe yarinyar ya ninke ciki ya matse da ƙarfi kana ya ɗagata ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Zaune ya sameta bisa bakin gado.
Tayi masifar kyau cikin wata dakekkiyar Getzner Orange color mai masifar kyau da sheƙi.
Khadija na tsaye gefenta tana ninke ɗan kwalin zatayi mata ɗauri.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Sairkin al'adun Suna cikin mamaki tace.
"A bawan Allah ya da kawo fatan rago kuma har cikin ɗaki".
Cikin yin ƙasa da kai yace.
"Al'adar ranar suna zamuyi".
Hannunta tasa ta dafe kanta kana ɗaya hannun ta ɗaurashi kan ƙirjinta dake harbawa da azaban ƙarfi da sauri-sauri kuma.

Aunty Amina ce tace.
"Kai gsky yana wani irin wari fa".
Ummi dake biye dashi a baya da ita da Umaymah da Gimbiya Aminatu ne suka haɗa baki wurin cewa.
"Toh ka fara mana".
Juyowa Khadijah kam tayi ta zauna tana kallon ikon Allah.
Itama Aunty Amina hannu tasa ta dafe haɓarta tana kallon ikon Allah.

Dan dagasu har Shatu basuma gane cewa.
Afreen ce a naɗe a cikiba.

Shi kuwa a hankali yake komai yana mai jin yadda yarinyar take mutsu-mutsun neman ceton rai sai ƙara danneta yakeyi.
Ƙarshen ginin ɗakin yaje kana ya sunkuya ya ajiyeta tare da garata ta gangaro har gaban gadon.
Tuni zuwa yanzu numfashin yariyar in ya fita baya komawa.
Gaba ɗaya fatan jikinta yayi jazir idanunta sun ƙaƙƙafe.

A can ɗakin Sheykh kuwa cikin tsananin hatsala da gajiya da dariyar muguntar da Hajia Mama ke kerketa mishi cikin kunnensa tsawon lokaci a tsale yaja tsaki tare da cewa.
"In kin san bazaki gaya minba meyasa kika kirani ina tambayarki me kikasa cikin fatar ragon sunan kina tamin dariya".
Cikin dariyar mugunta tace.
"Hahahahahhh madarar fiyafiyar mai surke da garin sukudaye na turbuɗa cikin fatar da nasan yanzu ana can an naɗe musu ƴar tasu a ciki, kafin miti biyar da za'ayi ana garata ta zama gaw..."
Cikin wani irin tashin hankali ruɗani da firgici da gigita ya cilla wayar ya liƙata da jikin gini a take ta buɗe batir ɗin ya rabu da wayar.
ba tare daya bari ya ida jin me zata ceba.
Cikin tsananin tashin hankali ya fito da gudu.
Gaba ɗaya jikinsa tsuma da karkarwa yakeyi tamkar mazari namfashinsa tamkar zai bar gangar jikinsa.
Daga falonshi yake rabkawa Shatu da Umaymah kira da ƙarfi yana cewa.
"Aysha! Aysha!! Umaymah! Umaymah!!! Ummi! Kada ku bari asa Ƴarinyar nan cikin fatar nan".
Da sauri Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Haroon da Jannart suka miƙe tsaye.
Da sauri Haroon ya nufi falonshi su Jamil ma kan tashi tsaye sukayi jin yadda yake mgn da azaban ƙarfi.
Kiciɓis sukayi da harun.
Da ƙarfi yace.
"Haroon ina Aysha ina Baby Ina Umaymah?".
Cikin tsoro Aunty Rahma tace.
"Suna ɗakin Shatu ana al'adar fata".
Da ƙarfi ya ture Haroon dake gabanshi.
Cikin tsananin masifar tashin hankali da ruɗani ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Wanda haka yasa suka kab suka bishi a baya.

Da sauri Shatu ta miƙe tsaye tare da cewa.
"Na'am Yah Sheykh".
Sabida jin yadda yake abka mata kira tare da cewa.
"Aysha Aish Ina kike ina ƴata?".

Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar shigowa ita zata fita shi zai shiga.
Da sauri tasa hannun shi ya tureta har saida ta faɗa jikin Umaymah sabida hango Sarkin Al'adun suna yana gara Afreen dake cikin fatar a ƙasa a tsakiyar ɗakin.
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali yasa hannunshin da ƙarfi ya ture sarkin al'adun sunan
Ya faɗi ƙasa tib.

Cikin rawan jiki da tashin hankali Umaymah da Ummi sukayi kanshi.
Aunty Amina da Khadijah kuwa cikin mamaki suka zuba mishi idanu.

Su Aunty Juwairiyya kusa duk shigowa sukayi cike da mamaki.
Ita kuwa Shatu da sauri ta gyara tsayuwarta tare da nufoshi.
Ganin yadda gaba ɗaya jikinshi ke karkarwar tamkar mazari.
A gigice ya sunkuyo ya zaro Afreen dake naɗe cikin fatar da sauri ya fara worwore fatar.
Gani yakeyi ma tamkar baya sauri murya na rawa hankali a tashe yake cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil Aish zasu kashe mana ita."
Dai-dai lokacin kuma ya gama woreta.
Cikin wani irin tashin hankali Ya juyo a gigice yace.
"Innalillahi Umaymah sun kashe min ita".
Jiki na rawa hankali a tashe Umaymah ta iso gabanshi da sauri tasa hannunta ta amshi yarinyar ganin yadda jikinsa ke karkarwar.
Da Sauri ta juyo gaban Gimbiya Aminatu tare da cewa.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam.
Ta rasu."
Da ƙarfi Shatu tace.
"Innalillahi Umaymah me kikace kada kice haka dan Allah ku duba da kyau".
Cikin tsananin tashin hankali Gimbiya Aminatu ta amshi Afreen jujjuya yaya tayi da sauri tace.
"Ta...!

By
*GARKUWAR FULANI*


Ta Suma ne!". Da sauri Sheykh ɗin ya taso, tare da sa hannunshi ya amsheta, da sauri ya juya.
Itama Umaymah da sauri tabi bayanshi.
Side ɗinsa ya koma da sauri key ɗin motarsa ya ɗauka Umaymah na biye dashi a baya kana Haroon ma na biye dasu a baya.

Shatu kuwa cikin wani irin kuka mai rauni daya kubce mata ta koma bakin gado ta zauna gaba ɗaya jikinta kerma yakeyi.

Shi kuwa Sarkin al'adun suna, da rarrafe ya fita ya bar ɗakin yana fita falon ya miƙe a guje ya bar Part ɗin da sauri Jalal ya mara mishi baya, kafinma ya bar Part ɗin ya damƙeshi Part ɗinsu ya wuce dashi.

Mamma kuwa da Gimbiya Aminatu gefen Shatu suka zauna.
Hannunta tasa bisa kafaɗarta a hankali tace.
"Kiyi haƙuri Aysha in sha Allah babu abinda zai samu ƴarki da izinin ubangiji, zata samu lfy".
Cikin rauni murya na rawa ta juyo ta kalli Mamma ido cike da hawaye tace.
"Mamma me tayi musu, da zasu cutar da ita ba tare da haƙƙinta ba, shike nan yanzu duk magautan Yah Sheykh sai su dawo kanta, kawai dan ta kasance ƴarsa, Mamma ya zamuyi".
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
"Babu komai Shatu da izin Ubangiji baza suci nasara a kankuba".

Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Jannart kuwa jiki a mace suka koma falon Shatu suka zauna.
Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi.

Khadija da Aunty Amin kuwa tsoron al'amarin masarautar Joɗa ne ya rufesu.

Da sauri Mamma ta miƙa ganin Shatu ta zabura ta miƙe tsaye da sauri tare da tallabe breast ɗinta.
"Aysha zauna".
Murya na rawa tace.
"Mamma maman Afreen na tsastsafo da ruwa,
Ina Yah Sheykh ya tafi da ita? Ni kam zanje inga halin da take ciki".
Ajiyan zuciya mai nauyi Hajia Kubra dake tsaye gefen Mamma tace.
"Asibiti suka tafi, kuma insha Allah zataji sauƙi".
Kai Gimbiya Aminatu ta gyaɗa tare da cewa.
"Sosai ma kuwa tunda har kikaji haka to ta farfaɗo ne".

Dai-dai lokacin kuma Umaymah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin da Sheykh da wasu manyan likitocin su na Valli Hospital Suka shiga da Afreen a sume.
Ta sauƙe wata ƙaƙkarfan ajiyan zuciya jin kukan da Afreen ta cillara da ƙarfi.

A cikin ɗakin kuwa.
Kusan a tare sauran likitocin suka sauƙe ajiyan zuciya tare da ɗagowa suna kallon Sheykh daya ruggumeta jikinshi tare da cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!".
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Dr Lukman Ibrahim babban likitan yara kenan na asibitin na cewa.
"Ina Maman baby a yi maza a bata mama tasha shi zai taimaka wurin ƙara ƙarya ƙarfin gubar".
Da sauri Sheykh yace.
"To".
Kana ya juya.
Yana fitowa Umaymah tabi bayanshi.
Tana tambayarshi.
"Ta farfaɗo ko?".
Cikin ƙara saurin tafiyarsa yace.
"Eh Umaymah".
Suna shiga motar yaja da sauri ya nufi masarautar Joɗa a guje.

A can part ɗinsu Jalal kuwa.
Wani irin gigitaccen mari Jalal ya yarfawa Sarkin al'adun suna.
Wanda yasa shi jin fitsari ya kubce mishi.
Ba tare daya gama dawowa hayyacisa ba ya kuma jin saukan wasu tagwayen maruka a gigice ya kurma ihu tare da cewa.
"Wayyoooooooo Allah na na shiga uku ni ilu Jalaluddin kayi haƙuri".
A fusace Jalal yasa ƙafarshi ya taɗe sawunshi har saida ya faɗi tib! A ƙasa hannunshi yasa ya tallabe ƙeyarsa tare da sakin wani gigitaccen ihu.
Da sauri Jalal yasa ƙafarshi ya taƙa yatsun hannunshi tare da cewa.
"Sheeeyyt rufe min baki, uban me kuka sa a cikin fatar ragon sunan?".
Cikin kerma da zare ido yace.
"Wlh bani ne na sakaba".
Ƙara taka yatsun yayi tare da murjesu da ƙarfi yace.
"Me akasa a cikin fatar ragon? kuma waya saka? Nawa kuma aka biyaka?".
Cikin sakin fitsarin azaba yace.
"Madarar fiyafiya ce aka saka cikin fatar. Hajia Mama ce ta saka! Dubu ɗari bakwai ta biyani".
Wani irin murza yasun yayi da ƙarfi tare da cewa.
"Okay bari in daddage yatsun hannun da zaiyi kisan kai da amsar kuɗin yin kisan kai ɗin".
Zuwa yanzu ya gigice ihu kawai yakeyi, shi kuwa Jalal rufe Windows ɗinsa yayi ya mishi ɗan karen duka.
Kana ya kira ɗaya daga cikin ma'akatansu na jami'an sirri na soja yazo ya tafi dashi.

A nan falon Shatu kuwa, a hankali Jamil da Yah Jafar Suka koma suka zauna.

Yana gaba Umaymah na binshi a baya a haka suka shigo.
"Aish Aish Aysha!". Ya ɗan ƙare kiran da ƙarfi.
Da sauri Shatu ta miƙe da sauri ta nufo falon.
Ummi da sauran na biye da ita a baya.
Aunty Amina da Khadijah kuma suna zaune.
Da sauri ya kamo hannunta bisa kujera ya ajiyeta gefen Aunty Rahma da sauri yace.
"Bata nono yi sauri".
Da sauri tace to tare da fara kiciniyar ɗago rigarta.
Ina gani yake bata sauri shiyasa cikin sauri ya ɗaura mata ita kan cinyarta.
Kana yasa hannunshi ta baya ya zuge zip ɗin rigar yayi ƙasa da ita.
Hannunshi yasa ya fito da breast ɗinta na dama.
Tare da ɗago kan Afreen daketa fidda wani irin numfarfashi alamun har yanzu numfashin bai dai-dai taba.

Da sauri kuwa ta damƙi nonon tare da fara zuƙa.

Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe a tare shi da ita.
Lokaci ɗaya kuma hawayensu ya kwaranyo bisa fuskokinsu.
Cikin sanyin murya yace.
"Alhamdulillah Aish kada kiyi kuka kiyi mata addu'o'in samun lfy ke wuce addu'aki gareta bata da hijabi".
Hannunta tasa tana ƙara tallaɓe kan Babyn murya na rawa tace.
"Yah Allah ka bawa wannan baiwa taka lfy ka yaye mata wahalar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login