Showing 279001 words to 282000 words out of 352722 words
3 nasi 3 ƙulhuwa 3 ya ƙara da azubikalmatillahi har ƙarshe.
Ya tofe a cikin sannan ya taso. Ya ruggumeta tare da cewa.
"Allah ya kaiku lfy yasa ku samesu lfy ki gaida min Ummey da Bappa da kyau.
Akwai tsarabar Junainah tana cikin motar kice ina gaisheta".
Cikin sanyi tace.
"Zasuji Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya rufe asiri".
Fuskarta ya shafa tare da cewa.
"Amin My dear bey'.
Yana faɗin haka ya juya ya fita.
Itama ta binshi a baya.
Da sauri Ummi ta miƙa jin yana ce mata.
"Toh Ummi mu tafi".
Da sauri Ummi tace.
"Toh Shatu sai mun dawo".
A hankali tace.
"Ummi nina yanzu zan tafi Baba Ado zai kaini".
Dai-dai lokacin Baba Ado da Jamil suka shigo da sallama.
Ita kuwa Ummi cikin ƙarfin hali dason zuwa gidansu Shatu ta ƙiddigi zarginsu tace.
"A a Sheykh ba tare zamu jeba".
Kanshi ya ɗan juyo kana a hankali yace.
"No Ummi kada ki damu zamuje ɗaukota yanzu dai Baba Ado zai kaita".
Sai kuma ya juyo ya kalli Baba Ado a hankali yace.
"Baba Ado na yarda da tuƙinka amman a ƙara kulawa kuje a hankali, tafiyar kuma ta zama ta siiri kada kowa yasan da ita kuka fita kaji ko".
Cikin mutunta juna Baba Ado yace.
"In sha Allah ba matsala".
Daga nan yace.
"Jamil fito mata da kayanta, mu mun tafi".
Nan suka fita shida Ummi.
Ita kuwa Jamil ya kai mata kayanta cikin motar da Baba Ado ya kawo har bakin Part ɗin su.
Tana fita Jalal na binta a baya, ya rage Sarace kadai ke musu aikin abincin dare.
Tana shiga motar Baba Ado yaja a bakin Part ɗin Lamiɗo suka tsaya nan ta shiga tai musu sallama kana suka fito suka tafi.
Ƙarfe uku dai-dai suka isa Rugar Bani.
Motar nayin parking tayi sauri ta fito.
Junaidu dake fitowa gidan ne, yayi maza ya nufi inda take fuska cike da murmushi yace.
"Oyoyo Adda Shatu masha".
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Oyoyo Junaidu.
Yauwa isa ka shigo min da kayana".
Da sauri yace to, kana ya nufi.
Wurin motar inda Baba Ado ya fito mata da jakarta da kuma ɗaya jakar wacce Sheykh yayiwa Junainah tsaraba.
Amsar jakukkunan yayi ya ajiye a bakin zauren kana ya dawo kusa da Baba Ado ya bashi hannun suka gaisa tare da cewa.
"Ka iso mana Baba".
Cikin nitsuwa Baba Ado yace.
"A a ba komai yaro sauri nake zan juya so nake kafin a kira la'asar na isa gida."
"Bazaka tsaya ku gaisa da Bappanmu Baba".
Junaidu ya Kuma faɗa.
A a ba matsala sai in munzo ɗaukarta.
Dole Junaidu ya barshi yaja mota ya tafi.
Shatu kuwa cikin wani irin masifeffen jin daɗi da begensu ta kutsa kanta cikin gidan tare da cewa.
"Assalamu alaikum Ummey ina kike Junanaih Ina Inna Amarya".
Wani irin zabura Ummey dake cikin ɗaukita tayi tare da miƙewa ta nufi waje da sauri.
Junainah kuwa da fitowarta daga ban ɗaki kenan.
Wani irin ihu mai cike da tsalle da jin daɗi tayi ta cilla butar hannunta can gefe.
Tare da nufo Shatu a guje tana cewa.
"Wayyoooooooo Allah na Adda Shatu na Ummey ga Adda Shatu na Oyoyo".
Ta ƙare zancen cikin tsananin jin daɗi tare da nufo Shatu haiƙan ƙadaran.
Zaro ido Ummey tayi tare da cewa.
"A a fa a a Junainah kada ki faɗa jikinta zakiji mata ciwo".
Sai kuma tayi shiru tare da zuba musu ido ganin itama Shatu gudun takeyi cikin ƴar sassarfa kamar ba mai cikiba.
ta nufo Junainah.
Wani irin ruggume juna sukayi da ƙarfi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ta ɗago Junainah data makaleta tafara jujjuyawa da ita.
Da sauri Ummey ta nufosu tana cewa.
"Na shiga uku Shatu ki sauƙeta zakiji ciwofa.
Inna Amarya ma da sauri ta nufosu tana.
"La hailahalillah Shatu zaku faɗifa".
Junaidun da shima yanzu ya shigo da jakukkunan sai kallonsu yake yana murmushi.
Ita kuwa Shatu Ummey na isosu ta sauƙe Junainah kana ta faɗa jikin Ummey ta ruggume ta gam-gam tana maida numfashi da haki take cewa.
"Oyoyo Ummey na yau kam daɗi zai kasheni".
Itama Ummey wani irin ruggume ta tayi cikin tsantsar jin daɗi da tsananin so.
Tace.
"Oyoyo Shatuna Boɗɗona mangana yar al'barka."
Sai kuma tayi saurin janye jikinta jin yadda ɗan cikin yake wutsul-wutsul da sauri ta kamo hannun ta.
Ita kuwa Shatu hawayen farin ciki take zubdawa.
Inna Amarya kuwa taburma ta shimfiɗa musu a tsakiyar gidan.
A ƙarƙashin inuwar bishiyar mango da bishiyoyin ayaba suka zagayeshi hakan ya bada daddaɗan inuwa mai sanyi.
Da sauri Ummey ta ajiyeta.
Ruwan sanyin da Inna Amarya ke miƙa mata ta amsa ta bata.
Ba musu ta amsa ta kafa kai dan hakin da takeyi yasata jin ƙishi.
Gefenta Junainah ta zauna.
Ummey kuwa gabanta ta zauna Inna Amarya kuma gefenta.
Junaidu kuma shigar da kayanta ɗakin Ummey yayi kana ya fito ya gaisheta sannan ya tafi.
Ita kuwa Shatu a hankali ta zame ta kwanta ta ɗaura kanta bisa cinyar Ummeynta cikin sanyi tace.
"Alhamdulillah yau gani ga Ummey na".
Murmushi Ummey tayi kana ta shafa cikinta tare da cewa.
"Shatu ki dena wasa da jikinkifa, kada kije ki tadawa kanki naƙuda lokacin ta baiba".
Cikin jin ɗan kunya tace.
"Toh Ummey itama ai yau tana farin cikin ganinki".
Sai kuma tayi maza ta miƙa zaune.
Jin muryar Bappa na cewa.
"A a a masha ALLAH yau gani ga Shatu na".
Cikin sauri ya iso inda suke gefenta ya zauna ita kuwa hijabinta ta gyara tana ɗan rufe cikinta alamun kunya tace.
"Oyoyo Bappa na".
Cike da jin daɗi yace.
"Sannu Shatu na.
Nanfa suka fara gaggaisawa da hirar yaushe gamo, ɗaya Bayan ɗaya haka take tambayar ahlinta wato ahlin Abboi.
Su iro ma suna dawowa aka zauna ana hira.
Inna Amarya kuwa da Ummey gidin murhu suka koma sunata haɗa miyar jumma'a.
Junainah kuwa na liƙe da ita.
Sai salla ne kawai yake ɗagasu a wurin.
Sai bayan sallan isha'i kuma duk suka zauna bisa taburma suna hira suna cin abinci.
Cikin nitsuwa Shatu ta juyo ta kalli Bappa dake gefe dashi dasu Iro yayinda farin wata ya haskasu ras, numfashin ta ɗan fesar tare da cewa.
"Bappa na ya lbrin su Yah Giɗi na".
Tayi mgnar hawaye na ciko mata ido".
Cikin sanyi yace.
"Wlh Shatu jikina na gaya min su Giɗi suna gab da baiyana.
Dan wayewar asuban yau nayi mafarkinsu wai Mijinki ya dawo min dasu da hannunshi.
In sha Allah kuwa suna kan hanya da izinin ubangiji tabbas suna hanya, muci gaba da Addu'o'in da muka sabayi".
Cikin gamsuwa da jin sanyi tace.
"In sha Allah kuwa."
Nan sukayi ta hira maƙota nata zuwa Binto budurwar Ya Gaini tazo haka Hari.
Sune basu shiga sai kusan ƙarfe sha biyu na dare.
Yau ko Junainah batayi bacci ba.
Suna shiga suka kwanta, Ummey na kan ɗaya gadon ita kuwa Shatu ita da Junainah suna kan ɗaya gadon.
Cikin sanyi Ummey tace.
"Uhumm Shatu ya mai gidan naki da mutanen gidan naku?".
Dogon numfashi ta sauƙe tare da cewa.
"Uhumm Alhamdulillah Ummey yana lfy yace in gaidaki shima zaizo da tarema zamuzo to sai aka kai wasu asibitinsa sunyi hatsiri".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Allah ya basu lfy".
Amin tace kana a hankali ta gyara kwanciyarta tare da jawo hand bang ɗin ta hannun tasa ta fito da cakuleti masu daɗi ta miƙa Junainah da sauri ta amsa ta ɓare tasa a baki.
Ita kuwa Ummey ta kalla tare da cewa.
"Uhmmm mutanen gidansu kuwa masu cike da sarƙaƙiya da mugunta suna can sunata fama da muguntarsu.
Kai Ummey gidajen sarauta akwai wuyan zama".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Ke dai ki dage da addu'a in sha Allah babu abinda zai sameki".
Cikin gamsuwa tace.
"In sha Allah kuwa, shima Yah Sheykh yana yawan mana addu'o'in".
Kai Ummey ta jinjina cikin gamsuwa.
Dai-dai lokacin kuma.
Sheykh ne tsaye tsakiyar falonshi gaba ɗaya ya rasa me ke mishi daɗi.
Tsaki ya ɗan ja, tare da cewa.
"Gidan ba daɗi".
Sai kuma ya zauna bisa kujera, a karo na biyar ya kuma kiranta stiil bata ɗagaba.
Sabida wayar na sailent kuma tana cikin hand bang ɗin ta.
Allah ya sani ta mance da batun wani suyi waya dashi.
Dogon tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"Yayi kyau Aish wato kin samu su Ummeynki ni kin mance da nima".
Haka dai ya kwanta yanata jan tsaki a haka yayi bacci.
Ita kuwa da Ummey kusan kwanan zaune sukayi ranar.
Koda asuba sukayi salla wani hirar suka kuma buɗe wa.
Harda Bappa daya shigo.
Nan ta jawo jakar da Sheykh yace tsarabar Junainah ne.
Tana buɗe wa daga sama ta samu wata leda cike da kayayyakin kwalam na makwaɗaita irin Junainah.
Sai kuma wasu irin tsala-tsalan turame atamfa da Shadda da lashi da hijabai guda biyar-biyar iri ɗaya alamun na Ummey da Inna Amarya.
Sai kuma wasu dogayen riguna masu kyau guda biyar irin na larabawa da alamun na Junainah ne sai dai zasu ɗan mata tsawo kaɗan.
kana sai takalma na manya da kamar na Junainah.
Sai kuma wasu irin yadin Getzner masu kyau kala biyar sai manyan al'kyabba guda biyu da alamun na Bappa ne.
Sai kuma kuɗi a cikin ko wanne kaso alamun kuɗin ɗinkin ne, sai can ƙasar jakar kuma turaruka ne masu tsadar gaske da sabulai da mayukan shafawa.
Ido kawai suke zuba mata.
Ita kuwa cikin jin daɗi tace.
"Gashi inji Yah Sheykh".
Cikin jin daɗi Junainah ta fara tsalle da ribibi kan kayan zaƙin sam batama kula kayan suturun ba.
Bappa da Ummey da Inna Amarya data shigo musu da karin kumallo kuwa cikin fulaku da kawaicin fulanin kwarai sukace.
"Kai Shatu ya zakiyi ki barshi yayi mana irin wannan hidimar haka".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummey kawai kusa mana al'baka".
Cikin sanyi suka haɗa bakin cewa.
"Allah ya muku al'baka ya sauƙeki lfy".
Amin Amin tace tana jawon akoshin ɗumamen gashesshen naman.
Nan Bappa ya fita su kuma suka zauna suka fara cin abinci.
Ranar ma dai haka suka wuni hira, sam ko ta kan wayarta bata biba.
Yauma kamar daren jiya haka sunata hira.
A ɗaki duk da kusan sha ɗaya ne.
Sheykh kuwa a hankali ya fito falo inda Ummi da Juwairiyya suke zaune dan Juwairiyya ta shigo dubata Ummi da jiki a haka nan a hankali yace.
"Ummi gidan shiru ba daɗi".
Da sauri Juwairiyya ta kalleshi tare da son gimtse dariyarta.
Kana a hankali tace.
"Ai fa kam gidan ba daɗi fa Sheykh".
Kanshi ya ɗan jinjina kana yace.
"Ummi ki shirya gobe zamuje Rugar Bani".
Cikin jin daɗi Ummi tace.
"To Allah ya kaimu".
Amin Amin yace yana mai juyawa ya koma falonshi yana maici gaba da kiran Shatu.
Dai-dai lokacin kuwa Shatu kwance take gefen Ummey cikin kula Ummey ta kalli cikin nata tare da cewa.
"Ya kai wata nawa Shatu?".
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
"Bakwai".
Kai ta gyaɗa cikin gamsuwa tare da cewa.
"Masha Allah, zan haɗa miki mgnin zaƙi ki fara sha yana sauƙaƙa naƙuda".
Cikin gamsuwa tace.
"Toh Ummey na".
Sai kuma tasa hannunta ta jawo hand bang ɗin ta ganin haske da sauri ta fito da wayarta.
Cikin juya ƙwayar idanunta ta amsa kiran tare da karawa a kunne a hankali tace.
"Assalamu alaikum".
Wani irin sassanyan numfashi ya fesar tare da cewa.
"Wa alaikassalam yah Aishhhhhhhh".
A hankali ta ɗan juya ta kalli Ummey tare da yin ƙasa da murya tace.
"Ina wuni".
Cikin narke fuska yace.
"Aish nayi fushi dake".
Da sauri tace.
"Na tuba".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Wato kin samu su Junainah kin mance dani ko? Kin barni da kewa gaba ɗaya gidan ba daɗi".
"Murmushi tayi tare da cewa.
"Junainah ce take shagaltar dani".
Da sauri yace.
"Okay to ki shirya gobe da wuri zamu zo ɗaukari".
A hankali tace.
"A a dai kam Hamma".
Kauda zancen yayi da cewa.
"Ya Baby na tana Lfy ko".
"Alhamdulillah tana lfy".
"Masha Allah".
Yace kana sukaci gaba da hira
Daga bisani sukayi sallama.
Ita harda Allah gani take zai barta tayi koda mako ɗaya ne.
Koda ta juyo taga tuni Ummey da Junainah sunyi bacci.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi Bedroom yana mmkin tsawon lokacin da sukayi suna hira.
Allah ya sani bai taɓa zato da tunanin shaƙuwarsu ta kai hakaba saida bata kusa dashi.
Washe gari bayan anyi sallan la'asar.
Suna fitowa suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Suna shiga abincin rana sukaci kana suka fito cikin shiri suka shiga mota.
Jalal ke tuƙi Sheykh na gefensa.
Jamil kuwa na baya kusa dasu.
Ummey kuwa tana can baya sit ɗin ƙarshe.
Waya takeyi da Umaymah tana sanarmata cewa gasu nan kan hanya.
Ƙarfe huɗu da kwata dai-dai suna bakin ƙofar gidan Bappa.
A hankali sukayi parking cikin nitsuwa Sheykh ya buɗe marfin gefensa kana ya zira ƙafarsa ta dama ya fito.
Da sauri Bappa ya miƙe tsaye ganin Sheykh.
Hakama Junaidu.
Shima Sheykh da sauri ya nufi Bappa Jamil da Jalal na biye dashi a baya.
Ummi kuwa yanzu ta buɗe marfin motar ta fito.
Ciken girmamawa Sheykh ya miƙawa Bappa hannu tare da ɗan rusunawa.
Cike da mutumtaka Bappa ya bashi hannun fuska cike da fara yace.
"A a a a masha ALLAH maraba lale marhabin da baƙin kirki kai sannunku da zuwa".
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gasheshi yayinda Junaidu kuwa ya rusuna yana gaida Sheykh.
Cikin tsananin karramawa Bappa ya juya yace.
"Maraba lale kushi go ku shigo daga ciki."
Cikin sanyi Sheykh yace.
"Bappa nanma yayi ai".
Da sauri ya jujjuya kai tare da cewa.
"A a Muhammadu kada muyi haka da kai maza ku shigo ciki, ai nanma gidane".
Yana faɗin haka ya juya yayi cikin gida.
Dole tasa Sheykh ya bisa a baya.
Kana Jalal da Jamil na biye dashi.
Ummi kuwa na biye da bayansu.
Haka nan sukeji suna mararin shiga cikin gida.
Yayinda gaba ɗaya zuciyarsu ke bugawa da sauri-sauri.
A hankali Sheykh ya sako ƙafarsa ta dama cikin gidan dai-dai lokacin kuma ya yayi ido biyu da....!
By
*GARKUWAR FULANI*
Ya hango Shatu tsaye a gaban randunansu.
Tana cikin shigar asalin fulani, riga da zanin, rigar guntuwa sai dai tasa wata a cikin red color mai dogon hannun yayinda yadin rigar da zanin kuma fari ne an ƙawatasu da kolliyar zanen ɗawosu, da zaren ulu red, blue and yellow, sosai cikinta ya baiyana.
Ya fito ras
Cikin da mamaki take kallonshi.
Shi kuwa Sheykh ido ya lumshe tare da sauƙe sassayan numfashi, sabida tayi masifar mishi kyau Especially kitson kumbo bobini da akayi mata asalin kitsonmu na Fulani kenen.
Murmushi tayi ganin wani irin mayataccen kallo mai cike da bege, shauƙi, kewa, so, kauna, tare da zallan fileeng mai kashe sasasan jiki.
Ita kuwa kai ta ɗan ɗago ta kalli bayanshi hango Jalal da Jamil ne yasata.
Faɗaɗa murmushin ta tare da cewa.
"Lale marhaɓin da Hassan da Hussaini."
Bappa kuwa bai kula da ita bama sai yanzu da tayi mgn,
Dan sauri ya nufi ƙogar ɗakinshi yana ce musu.
"Kai kunsha hanya kam, masha ALLAH ku iso ku iso."
Haka yasa suke biye dashi a baya.
Ita kuwa Shatu da sauri ta nufo bakin ƙofar zauren nasu sabida hango Ummi da tayi cikin tsanani jin daɗi tace.
"Lah oyoyo Ummina,"
Ta ƙarashe mgnar cikin jin daɗi da isowa gaban Ummi ta ruggume ta.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da kwaɓe fuskarsa ya tura baki ya mata alamun.
"Wato ni baki ganni bako".
Harshenta ta ɗan zaro mishi ta gefe.
Kanshi ya juyo da sauri ya kalli gabanshi jin ya ɗan bugi kanshi jikin rumfar Bappa.
Cikin kula Bappa ya shimfiɗa musu babbar taburma, kana ya ware wani ɗan carpet a kam taburmar cike da kulawa yace.
"Bismillah ku zauna".
To sukace kana duk suka zauna.
Ita kuwa Ummi cikin jin daɗi tace.
"Oyoyo Shatu na, munyi kewarki".
Cikin dariya ta ɗan janye jikinta, kana tace.
"Ummi mu isa ciki".
Sai kuma ta juyo da sauri tana cewa.
"Inna Amarya! Inna Amarya gasu Ummi na sun zo".
Da sauri Inna Amarya dake Kitchen tana gasa musu yan shilan tattabarun. Ta fito tare da cewa.
"A maraba lale marhabin".
Sai kuma tayi maza ta nufi ɗakin Ummi inda suma Shatu nan suka nufa.
Cikin sakin fuska tace
"Ummi shigo ɗakin Ummeyna".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Toh Shatun Ummey da Ummi".
Dariya Inna Amarya tayi tare da cewa.
"A lallai kam Shatun Ummey da Ummi fa".
"Sannu da zuwa Ummi". Inna Amarya ta faɗa tare da juyawa har taje bakin ƙofar kuma sai ta juyo tace.
"Shatu taho ki kai musu ruwa".
Da sauri itama Shatu ta miƙa tabi bayanta.
Shiru Ummi tayi bayan sun fita, tana mai bin ɗakin da kallo komai a kimtse yake ras.
Babu hargitsi ko ƙura duk da jeren kayan dake da yawa.
Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi tare da cewa.
"Toh ina Ummeynta ɗin, naji wannan dai Inna Amarya ta kirata".
Su kuwa Shatu kai tsaye kitchin ɗin suka koma,
Da sauri Inna Amarya ta jawo kwaryan kindar tare dasa maburgi a ciki, ta fara burgashi tana cewa.
"Yauwa Shatu miƙo min ƙwaryar zumar nan".
Da sauri tace to, kana ta miƙa mata.
Tsulala zumar tayi a ciki, ta burgeshi da kyau.
Kana ta rabashi biyu, sannan ta jawo akoshin data saka furar data gama kirɓawa yanzu.
Ta ɗauki ludayin damu ta fara damawa da sauri.
Sai kuma ta kalli Shatu data jera ƴan ƙananan ƙore guda huɗu bisa tray'n fefeyin saƙa,
damun ta fara zubawa cikin ƙoren kana tace.
"Yauwa Shatu dauki akoshin nan ki haɗa musu da gashin tattabarun naki.
To tace kana ta jawo ƙaramin akoshin tasa na Ummi kana nasun kuma ta barshi a ciki, ta rufe da fefeyin sai tururin da ƙamshin gashin tukunyar ƙasa yake da ƙamshin man shanu.
Bayan sun gama kimtsa komai ne.
Inna Amarya ta ɗauki na Ummi ƙaramar kwarya da damun kidar dai mai binshi zallan nonon da zuma, kana sai akoshin mai ɗauke da gasassun tattabarun.
Ita kuwa Shatu akan fefeyin ta jera ƙoro Ukun ta rufe da fefeyin ɗaya babba kama ta jera kananan ƙoren uku masu zallar nono da zuma suma ta rufesu da fefeyi ɗaya,
Kana ta ɗauka akoshin gashin a sama ta rufe sannan ta jera ludayeyin suma masu kyau da kwalli a saman fefeyin.
Ta ɗauka ta nufi bakin ƙofar ɗakin Bappa inda suke gaisawa.
A hankali tace.
"Assalamu alaikum".
Da sauri Sheykh ya juyo ya kalleta, ido ya zuba mata cike da bege.
Bappa da Jamil ne suka amsa mata.
A hankali ta zare takalmanta kana ta hau bisa taburmar, gefenshi ta ɗan tsuguna ta ajiye tray'n.
Tare da kallon Jalal daketa kallon tsakiyar gidan yana murmushi da yanayin tsarin gidajen gargajin suna burgeshi.
Jamil ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
"Ina wuni Adda Shatu".
Cikin kula tace.
"Lfy lau Alhamdulillah Jamil ya gida ya Gimbiya Aminatu da Abba da Lamiɗo da Galadima da Aunty Juwairiyya suna lfy ko".
Jalal ne ya ɗan juyi cikin ɗan sakin fuska yace.
"Alhamdulillah suna lfy, Lamiɗo yace mu gaidaka".
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Bappa.
"Ina amsawa kuwa ngd matuƙa".
Bappa ya bashi amsa.
Ita kuwa juyawa tayi ta ɗan kalli Yah Sheykh a hankali tace.
"Barka da yamma".
Cikin sassauƙar murya yace.
"Barka dai ya gida, ina Junainah?".
Cikin jin daɗin kular da yake kan Junainah tace.
"Yanzu nan ba jimawa suka fita unguwa ita da Ummey na".
Fuska ya ɗan tsuke tare da cewa.
"To amma meyasa baki cewa Junainah ina zuwaba nasan da zata bar zuwa unguwar".
Cikin tura baki tace.
"Toh ai ni banyi zaton zakuzo