Showing 213001 words to 216000 words out of 352722 words

Chapter 72 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30784

ƘADIIRA)
"Kusani Allah shine wanda ya halicci mutun daga ruwa kuma mai dangantaka surukuta kuma ka sani Allah mai iko ne akan haka".

Sassanyan numfashi ya fesar a hankali, kana yaci gaba da cewa.
"Shi Aure sunna ne mai samar da nitsuwa tsakanin ma'aurata. Ɗan Adam bazai samu cikekkiyar nitsuwa ba a gidansa ba, sai in har yanada mata wacce ya aura.
Domin zata ɗebe masa kewa ta sashi ya samu nitsuwar hankalinsa.
Saboda zamansu tare a inuwar aure zatayi masa maganin kaɗaici kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗi a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN AMFUSIKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA'ALA BAINAKUM MA'WADDATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN)
ma'ana.
Yana daga cikin ayoyin Allah mai girma da ya halitta mana mataye daga kawunan mu, mataye da muke aure da su.
Domin su samu nitsuwa da junansu, sannan kuma ya sama musu soyayya a tsakanin su, tare rahama da tausayawa juna lallai a cikin wannan al'amari akwai ayoyi abin lura ga jama'an da suke masu tunani.
Saboda haka idan muka dubi wannan ayar ga ma'aurata zamu gane girman kudirar Allah da hikimarsa mai girma da ya halicci maza da mata kuma ya sanya ko wanne sashi mai karkata ga junansu kuma ya sanya igiya ya ɗaure tsakaninsu, wannan igiyar kuwa itace soyayya da tausayin juna da jinƙai.
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce, cikin hadisin da Ibnu Majah ya ruwaito cewa.
(Babu wata fa'ida da mutun zai samu bayan ya. Takawar da Allah (tsoron Allah) wanda yafi masa al'khairi fiye da ya samu salihar mata ta kwarai wanda idan ya umarceta da tayi masa abu zata yi masa biyayya idan ya dubeta ta faranta masa ransa idan yayi rantsuwa game ita akan zatayi abu kaza ko bazata aikata abu kaza ba, zata kuɓutar dashi akan wannan rantsuwar da yayi, idan baya gida baya tare da ita, zata kiyaye mutuncinsa (Bazata yi fasiƙanci ba) kuma zata kula da dukiyarsa.
Ku duba cikin Fikihul Wadi littafin Dr Muhammad B Isma'il shafi na 9 zaku sami wannan hadisin.

A hankali Haroon ya ɗan juyo ya kalli fuskar amaryarshi Jannart, hannunshi yasa ta ƙasa table ɗin dake gabansu, tafin hannunta ya haɗe da nashi, tare da ɗan ronƙofowa kaɗan kana yace.
"Kina ji da kyau dai ko?".
Cikin lumshe ido tace.
"Sosai ma kuwa".
Aysha dake gefensu Haroon ya kalla tare da cewa.
"Al Sheƙiya matar Sheykh, ko zakije ki ja mishi baƙine?".
Ido ta ɗan sunkuyar tare da fidda nannauyan numfashi kana a hankali tace.
"Ba dan gefen can da tarin maza manya iyaye da kakanni da sarakuna ba, tabbas da naje na zauna gefenshi na ja mishi baƙi".
Safiyyah da Ibrahim dake bisa kujerun dake gefensu ne suka kalli juna tare da yin murmushi.

Abokan Haroon kuwa gaba ɗaya sun nitsu.
Abbansu Haroon da tawagarsa kuwa sai jinjina kai suke alamun gamsu ɗari bisa ɗari.

Ita kuwa Aysha a hankali ta ɗago kanta ta kalli inda yake, aikuwa karab idonsu ya haɗe cikin na juna,
taɓe laɓɓansa yayi tare dasa hannunshi ya shafi tattausan sajenshi kana a nitse yaci gaba da cewa.
"Aure kariya ce, kuma GARKUWA ce ga Musulmi saboda duk wanda yakeda mata, to ba zaka ganshi ya bar gida yana yawace-yawace ba ko ka ganshi yana leƙe-leƙe a woje ba, don yana da irinsa a gidansa, saboda haka mata ta zama GARKUWA a rayuwar ɗan Adam. Saboda haka ne ma Annabi (S.A.W). Ya kwaɗaitar da matasa samari da yin aure a cikin wani hadisin da muka samu a cikin Fiƙhul waɗi littafi na 2 na Dr Muhammad B Isma'il shafi na tara, Annabi (S.A.W) ya ce:-
Yaku samari wanda ya samu iko daga cikin ku to yayi aure.
Domin shi aure yana kare mutuncin farji da aukuwa cikin haram, (Yin zina) wanda bai sami iko ba to lallai ne ya juri yin azumi.
Domin assaumu junnatu, shi azumi GARKUWA ne.
Kuma shi aure cikon addini ne, saboda idan muka dubi aure sosai. Zamu fahimci aure yana taimakawa musulmi wajen tsare-tsaren addininsa kuma da wannan ne addininsa yake cika kamar yadda.
Dabarani da Hakim suka ruwaito daga Buhari da Muslim inda Manzon Allah (S.A.W) yake bamu labari a kan cewa aure tsari ne wanda yake taimakawa ga mutum ya cika addininsa a in da yake cewa:
Yana daga cikin arzikin Allah.
Allah ya azurtaka da mace salihan ko salihan mata, haƙiƙa zata taimaka ko wannan auren zai taimaka akan wani yanki na addini ka sai kuma kaji tsoron Allah akan sauran yankin.
Aure sunnace ta Annabawa da manzanni, saboda haka idan kayi aure ko yi ne da Annabawa da manzannin Allah. Allah maɗaukakin sarki ya faɗi:-
(WA LAKAD ARSALNA RUSULAN MIN ƘABLIKA WAJA'ALNA LAHUM AZWAJAN WA ZURRIYYAH)
Haƙiƙa mun aiko manzanni kafin kai, (Muhammad, S.A.W) kuma mun sanya matayen aure da zuriya a garesu.
Idan muka duba zamuga cewa yin aure koyi ne da aikin Annabinmu Muhammad (S.A.W) ne in da yace:-
(Kuyi aure ku yawaita domin ni zanyi alfahari da yawanku ranar lahira".

Juyowa yayi ya fuskanci gefen taron maza, kana yaci gaba da cewa.
"Kamar yadda muka sani cewa.
Mace abokiyar zama ce kuma shimfiɗa ce ga mijinta kuma mai rainon gidansa ce kuma abokiyar rayuwarsa ce, sannan kuma uwar ƴaƴansa ce sannan mai kula da dukiyarsa ce da mutuncinsa cikin amana saboda haka idan mata-ta zamo salihan ta gari to sai ta zamo kyakkyawan abu na duniya kuma ni'ima daga cikin manya-manyan ni'imomin da Allah ya azurtaka da ita".

Gyaran murya yayi tare da gyara zamanshi, kana ya fuskanci Haroon da Jannart da kyau, sannan ya ɗan kalli Aysha da wutsiyar idonshi.
Tura bakinta ta ɗanyi fahimtar ita yake kallo, kanshi ya jinjina kana ya buɗe muryarshi da ɗan ƙarfi dai-dai misali yadda amon mgnarsa zata ratsa kunnen kowa yace.

HAƘƘOƘIN MA'AURATA GA JUNANSU.

bari mu fara da haƙƙin macce akan mijinta.

HAƘƘIN MATA A KAN MIJINTA.

Haƙƙoƙin mata a kan mijinta suna da tarin yawa.
Kuma ya zamo wajibi a kan mai gida ya tsareshi dai-dai gwargwadon hali, kuma wannan haƙƙoƙin Allah da Manzonsa sun tabbatar dashi, ga faɗin Allah madaukakin sarki akan haka inda yayi mgna cikin Suratul Baƙara aya ta 228:-
(WALAHUNNA MISLULAZII ALAIHINNA BIL MA'ARUF WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAT)
Mata sunada haƙki a kan mazansu kamar yadda aka sani. Sannan maza suna da wata daraja akan mata.
Haƙƙokin mace a kan mijin ta, suna da yawa amman ga wasu daga cikinsu.

(1) Wurin zama ga matar aure wajibi ne a kan mijinta. Miji zai tanadi wurin zaman matarsa gwargwadon ikonsa da samunsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin Suratul Ɗalak aya ta 6:-
(ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJIDIKIM WALA. TUDAARUHUNNA LITUDHAYYIKUM ALAIHIN)
Ku zaunar da matanku inda kuke zaune wato gidajenku.
Ba mummunan wurin zamaba kada ku cutar dasu don ƙuntata musu.

(2) CIYARWA.
Ciyarwa yana daga cikin abubuwan dake wajabta kan miji wato wajibi ne miji ya ciyar da matarsa, kuma ciyarwar zai yishi ne gwargwadon ikonsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin Suratul ɗalak aya ta (7).
(LIYUN FIƘ ZUU SA'ATIH MIN SA'ATIH, WA MAN ƘUDIRA ALAIKU RIZKUHU FALYUNFIƘ MIMMA AATAHULLAH LAA YU KALLIFULLAHU NAFSAN ILLA MAA AATAHAA SAYAJA ALULLUHU BA'ADA USRIY YUSRAA).
Ma'ana.
Mawadaci sai ya ciyar da abinda Allah ya bashi na wadata, shi kuma wanda Allah ya ƙaranta masa arziƙinsa to sai ya ciyar daga abinda Allah ya bashi. Domin Allah baya ɗorawa bawa abinda bazai iyaba kuma ka sani Allah zai baka wadata bayan ƙuncin da ka shiga.
Dangane da hadisin Annabi (A.S.W) yace a hadisin da a ka ruwaito daga mu'awiyya Bin Haidatu Allah ya ƙara masa yarda yace:
Sai muka tambayi Manzon Allah (S.A.W) shin menene haƙƙin mata akan ɗaya daga cikinmu?. Annabi (S.A.W) ya ce.
"Idan kaci abinci to ka ciyar da ita, idan ka ɗinka sutura to itama ka ɗin ka mata, sannan kuma in tayi maka laifi zaka bugeta, to kada ka bugeta a fuskarta kada ka munanata, idan zaka ƙaurace mata to kada ka ƙaurace mata a woje sai dai a ɗaki."
(3) Kyakkyawan mu'amala.
Shi mu'amala mai kyau babban abune ga ma'aurata.
Especially shi miji, yana daga cikin haƙƙin mace akan mijinta, yayi mu'amala mai kyau da sakin fuska a tsakaninsu, raha da barkwanci ta yadda zasu shaƙu da junansu.
Lallai waɗannan muhimman abubuwane da miji zai kiyaye su, kuma wajibi ne miji ya yawaita nasihi da wa'azi ga matarsa a kan harkar addini da sauran al'amuran yau da kullum sai dai a kula wurin nasihar da wa'azin kada ka tsananta kuma kada ka sake kwarai sabida sani yadda mata suke murɗaɗɗune sai anyi da lura.
Duba da wani hadisin da Annabi (S.A.W) yana cewa a cikin hadisin da aka samo daga Abu Huraira inda yake cewa. Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Mafi cikar mumini a wajen imani shine wanda ya fiku kekkyawan ɗabi'a kuma zaɓaɓɓe a cikinsu shine wanda yafi Kyakkyawar mu'amala da iyalinsa.
A wani hadisin kuma yace.
Lallai ku sani cewa an halicci ƴa mace da ƙashin haƙarƙari ne bazata taɓa miƙewa gareka ba, wato ka sameta sak ba matsala, wannan kam bazai taɓa samuwaba in ka samu jin daɗinta to zaka samu jin daɗin ta ne a ƙarƙashin yadda take, (kuma ka sani in ka nemi miƙar da ita to tabbas zata karye.
Karyewarta kuwa shine SAKINTA saboda haka sai kuyi taka tsan-tsan acikin lamuran."

Gyara zamanshi yayi da kyau, kana yasa hannunshi ya gyara gilashin fuskarshi da kyau,
Sannan ya sa hannunshi zai ɗauki goran ruwan dake gabanshi.
Da sauri ɗan agajin dake bayanshi ya ɗauki gorar kana ya buɗe ya tsiyaya mishi sassayan ruwan cikin kofi,
kana ya miƙa mishi sannan ya koma inda yake ya tsaya.

Amsa yayi yasha ruwan sosai kana ya ajiye cup ɗin.
Sunkuyar da kanshi yayi sosai sannan yasa hannunshi ya gyara hiraminshi ya rufe gefe da gefen fuskarshi.

Al'ummar jama'ar dake wurin kuwa kan sun nitsu sunyi shiru maza da mata manya da yara.
Kab an zuba mishi idanu alamun ana dakonshi yaci gaba.
Domin sosai walimar tayi armishi sabida dace da tayi da fasihin malami.
Shiru kakeji sai sauti A\C dana numfarfashi.
Aysha kuwa haka nan take jin wani irin mashahurin daɗi.
Gaba ɗaya tsikar jikinta tashi takeyi, tana jin Allah yayi mata babban rahama da ni'imar duniya da bata Sheykh Jabeer a matsayin Garkuwan ta mijinta.

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi lokacin da yaji yace.

(4) SADUWA DA ITA.





Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300.
0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa. Ta nan zaki turo kuɗin, sai screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.


By
*GARKUWAR FULANI*


Littafin nan na kuɗine, akwai Normal group 300 a wata biyu za'a kare Part 1 and 2, kiyi transfer'n dari uku ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. In Kuma special Group kikeso wanda a wata ɗaya za'a gama Part one, two. 1k zaki turo ta ac no ɗin nan 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number da nake whatsapp dashi 09097853276.

Akwai kayan gyaɗa na amareni uwar gidaye sitin hawa-hawa ne, akwai na dedai talaka akwai na masu hannu da shuni, in kina buƙatar saya kimin mgn ta whatsapp 09097853276.


Idonshi ya ɗan lumshe kana ya ɗanyi ƙasa da kanshi cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
"Anan ana son miji ya dinga yin jima'i (Saduwa) da matarsa ko da sau ɗaya ne a cikin ko wanne tsarki ta, na Al'ada amman ƙaranci kada ya wuce wata huɗu ba tare da ya sadu da itaba kamar yadda wasu malamai suka faɗa, in bazai iya biya mata buƙatarta ba, kuma wannan za'a kauwacewa al'amarin jima'i kamar yadda al'ƙur'ani mai girma yace.
(Allah yayi mgna game da mazajen da suke barin matansu basu kula su har tsawon wata huɗu kai harma suna ƙarawa da rantsuwa bazasu tara (Sadu) da suba, to idan daga baya sun dawo ga iyalan nan to shike nan Allah mai gafara ne mai jinƙai.
Saboda haka idan muka dubi wannan ayar zamu fahimci cewa, idan miji ya bar matarsa tsawon wata huɗu bai sadu da itaba haka nan kawai ba tare da wani kyakkyawan dalili ba, to ya cuceta, kuma ana iya raba auren, Allah ya kiyaye.

Sai na (5) kiyaye mutuncinta kishi a kanta yana daga cikin mu'amala mai kyau tsakanin miji da mata ya zama miji ya kiyaye mutuncin matarsa da yin kishi a kanta, saboda haka wajibi ne ga miji yayi kishin matarsa ya kareta daga dukkan abinda zai taɓa mutuncinta da martabarta da dukkan abinda yayi kama da hakan domin mumini mai kishin gidansa ne, kamar yadda.
Dabarani ya ruwaito daga Ammar Ɗan Yasir Allah ya ƙara musu yarda, cewa Manzon Allah (S.A.W) yace.
Mutane uku bazasu shiga aljanna ba, 1 wanda baya kishin iyalansa 2 macen da take shigar maza, 3 wanda bai damuwa akan kowa da kowa ya shiga wajen iyalinsa.
Sai Sahabbai suka tambayi Annabi (S.A.W) suka ce,.
Ya manzon Allah shin dai bugegge sun san shi, to amman (Addayyus) wato mara kishi iyalinsa shine bamu sanshi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace musu.
Shine wanda bai damuwa kowa da kowa kare da doki su shiga gidansa wato mutumin banza da wofi idan sun shiga gidansa baya damuwa.
Shi wannan hadisin ya nuna mana cewa dole mu tsare mutuncin matanmu. Wannan kenan sune kaɗan daga haƙin mata akan mijinta.

Sai kuma haƙƙoƙin miji akan matarsa.
(1) yin ɗa'a ga mijinta domin Allah ya faɗi a Suratul Baƙara aya ta 228. ( WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAH) Su maza sunada wata daraja a kan matansu.
(2) Kula da dukiyarsa wajibi ne a kanki haƙƙine wanda ya zama dole mata su kiyayeshi
Dole mace ta kula da dukiyar mijinta fiye da yadda shi zai kula dashi. Kamar yadda Allah Mai girma da ɗaukaka ya faɗa a Suratul Nisa'i aya ta 34.
(FASSALIHATU ƘAANITAATUN HAAFIZAATUN LILGAIBI BIMA HAFIZALLAH) Allah ya ambaci salihai mata masu ɗa'a ga mazajensu masu tsoron Allah masu kiyaye abinda ke ɓoye na al'amuran mazan aurensu sobada Allah yace su kiyayeshi, kiyayewar kuma ta haɗa da tsare mutuncin kansu dana mijinsu ko yana nan ko baya nan.
(3) Yiwa miji hidimar cikin gida kamarsu girki shara kula da yara da dai sauransu duk aikin macene.
Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
(WALAHUNNA MISLULLAZZI ALAYHINNA BIL MA'ARUF) Mata suna da haƙƙi a kan mazansu kamar yadda suma maza sukeda haƙƙin a kan matansu.
(4) ikon canza mata wurin zama daga wannan garin zuwa wancan gari. Kamar yana aiki a jihar Ɓadamaya sai aka canza masa wurin aiki zuwa Tsinako to yana ikon ɗaukarta daga can zuwa nan.
Domin musulunci ya bashi dama kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
(ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJDIKUM WALA TU DARRUWHUNNA LITUDAYYIƘUN ALAIYHIN) ku zauna dasu inda kuke kada ku cucesu ku ƙuntata musu wajen zama.
Idan muka dubi wannan ayar tana gargaɗin mazaje ne akan cewa kada ka sauya mata garin zuwa wani garin ya zama cutarwa a gareta.
In taga cutarwa ne nan zata iya ƙin zuwa in ya matsa ta gayawa waliyansu.
(5) kada mace ta shigo da wani mutun gidansu sai da izinin mijinta, domin wannan haƙƙine kuma damarsa ce.
Numfashi ya sauƙe tare da kallon taron mazan kana yaci gaba da cewa.
"A gurguje.
(6) Neman izinin miji dan yin azumi.
Baya halasta ga mace tayi azumi in dai na nafila ne sai tare da izinin mijinta matukar mijinnan yana gida tare da ita. Duba haɗisin daya gabata na haƙƙin maigida saboda haka ya zama dole mace ta nemi izinin mijinta kafin tayi azumi nafila amman banda na farillah".
Haroon ne yayi wani irin murmushin jin daɗi kana ya kalli Jannart cikin raɗa yace.
"Kinaji kina ɗauka kina fahimta ko?".
Longoɓar da kai tayi.

Umaymah kuwa sai murmushi takeyi tana ƙara godewa Allah da samun Sheykh a ahlinsu.
Mamma ma sai murmushi takeyi.

Jamil Jalal Azeez da Sadiq da Imran ne suka ɗan haɗe kansu suna ƴar hira ƙasa-ƙasa.

Da sauri suka ɗago kansu jin muryar Sheykh yana cewa.
"Jamil ku fita waje kuna toshewa jama'a kunne".
Cike da mamaki suka miƙe suna kallonshi suna al'ajabin ya akayi ya gane su kuma har yaji muryarsu.
"Ku fita". Suka sake jin muryarsa, cikin tuttura baki suka fita.
Aysha kuwa tafin hannunta tasa ta tallabe haɓarta, tare da zuba mishi ido cikin wani abinda bata san sahihancinsa ba, take kallon tattausan lips ɗinshi suna motsawa yana mai ci gaba da cewa.

Kanshi ya sunkuyar sosai, babu mai iya ganin kwayar idanunshi cikin tarin al'kunya yace.

"Haƙƙin jima'i haƙƙine wanda yake tsakanin miji da mata.
Amman ƙarfin haƙƙin yafine gashi mijin, shi yake da haƙƙi mafi girma. Kuma shi wannan jima'in yana daga cikin manufofin aure, domin shi aure shi yake tabbatar da mutane su wanzu, su tabbata akan ma'aunin mutane su ba nau'in dabbobi ba.
Domin shi dabba duk lokacin daya buƙaci biyan buƙata yin jima'i zai tare dabba mace ƴar uwarsa ne a hanya nan take ya biya buƙatarsa ya rabu da ita, kamar yadda muke gani a tsakaninsu yana faruwa.
Shiyasa duk mazinaci bashi da banbanci da Dabba!.
Jima'i babban al'amari ne cikin auratayya, domin biyawa kowa buƙatar sa, kana jima'i wata iriyar sutura ce wadda ma'aurata suke suturce junansu, kamar dai yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin suratul baƙara aya ta 187:-
(UHILLA LAKUM LAILATASSIYAMIRRAFASA ILAA NISA'A IKUM HUNNA LIBAASULLAKUM WA'ANTUM LIBAASULLAKUM) A halasta muku matanyenku kuyi jima'i dasu a dararen Azumi, domin su mata sutura ne a gareku, kuma suturce a garesu."
Ɗan ɗago kwayar idanunshi yayi ya fuskanceta Aysha, kollon kwayar idanunta data zuba mishi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login