Showing 285001 words to 288000 words out of 352722 words
yace
"Allah yasa haka".
Amin Amin sukace.
Kana ya kalli Sulaiman cikin kula yace.
"Sannu Sulaiman Allah ya kiyaye gaba ya taƙaita, ya sauƙaƙa mana ƙadda rorinmu, dani da kai dama sauran al'ummar musulmi baki ɗaya."
Cikin rauni murya na rawa hawaye na kwaranya, Sulaiman ya ɗago kanshi tare da son danne shessheƙan kukan da yake taso masa yace.
"Tabbas wannan yana ɗaya daga cikin manyan ƙaddarorina masu zafi a rayuwata, na kuma samu tsira da kuɓuta cikin sauƙi, kasan cewar inda masu damar yin mgn aji.
Amman tunda na dawo Jabeer ban bar yin kukan bayin Allah'n da na bari a tsare a can magarƙamar.
Ina kuka har inji numfarfashi na yana fizga, tunda na fito na barsu ban sake samun nayi bacciba.
Inajin tausayin kaina, inji tausayinsu, nayi ta kuka dana dawo da naga halin ƙunci da iyayena da yan uwana suka shiga.
Ina tuno su kuma wanne hali iyayensu da ƴan uwansu suke ciki."
Sosai kukansa ya tsananta cikin tsananin kukan da yasa.
Malam Abubakar zubda hawaye Sheykh kuwa sai taune lip ɗinsa na ƙasa yayi cikin tausayin waɗanda Sulaiman yake mgn a kansu koda bai sansuba.
Shi kuwa Sulaiman murya na rawa yace.
"Yara ƙanana sun sadaukar da rayuwarsu domin tawa sun amsa laifin da ba nasuba domin ni in tsira.
Ko wani hali iyayensu ke ciki, kuma dukansu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya".
Cikin rauni Sheykh yace.
"Me sukayi ne Sulaiman?".
Cikin wani irin shessheƙan kuka mai ciwo da rauni da tausayawa yace.
"Wanna itace tambayar da kullum sukeyiwa haukumar dake tsare damu kullum in sun shigo suna dukansu suna azabtar dasu tammaya ɗaya sukeyi mushi nee.
"Wai me mukayi ne aka kawowu nan kuke ta dukanmu ku gaya mana laifinmu".
Zuwa yanzu hawaye sosai Malam Abubakar yake zubdawa.
Sheykh kuwa tausayi da rauni sun adaddabi zuciyarshi hawaye musu masifar zafi ke tsastsafo mishi.
Cikin rauni yace.
"To Sulaiman sun gaya maka ya kayi aka kaisu can ne?".
Kai ya fara jujjuyawa yana kuka murya a disashe kamar mace yace.
"Sunce suma basu san me sukayi ba, kawai suna kiwo sun shiga suyi al'wala akazo akayi ta kamasu ɗaya bayan ɗaya, daga nan aka rufe musu ido, su dai sunji an kwana tafiya dasu a wannan ranar da asuba aka iso dasu wannan magarƙamar. Ƙaramin cikinsu kullum yakanyi ta kuka yana kiran iyayensu".
Da sauri Sheykh yace.
"To amman meyasa aka tsaresu kuma su kansu basu san laifinsu ba anya ba karya sukeyi ba ko dai criminals ne, kasan suna da taurin zuciya".
Da sauri Sulaiman yace.
"Wlh wlh su ba criminals bane, tunda na gani a gaban idona akayi musu sharri kuma akasa suka yarda dashi dole, amman sun yarda dashi ne dan su tseretar dani".
Da sauri Sheykh yace.
"Kamar yaya akayi musu sharri?".
Hannu yasa ya share hawayensa murya na rawa yaci gaba da cewa.
"Tun randa aka kaini wannan magarƙamar nayi matuƙar mamkin ganin waɗannan yaran, yarane ƴaƴan Fulani masu tarin kyau da farin fata, saidai yanayin wahalar da ake gana musu kullum tasa sun rame sunyi baƙi.
Mafi akasarin kwanaki sai an daukesu hotuna ana tirsasu amsa laifinsu.
Ni da yake ko muntsilina ba'ayi wlh ana dukan yaran nan ina kuka, da fari na fahimci ko isasshiyar Hausa basaji tabbacin fulanine kamar dai yadda duniya takewa Fulani kuɗin goro ga duk wanda aka ji ya iya fillanci ko yana kiwo to ya zama ba fulatani, so nima kai tsaye nai zaton fulanine kuma sai akayi dace hakan ne.
Kullum ana dukansu ina kuka.
Idan an tafi sai manya biyun su taru kan karamin cikinsu, suyita mishi tofi dan shi irin mutanen nan ne da basa jurar wahala lokuta da dama yana sumewa in an dakeshi sai daga baya ya farfaɗo, sukanyi ta kuka ina tayasu.
Daga nan muka fara sabawa, ina mamakin rauninsu kan iyaye da yar uwarsu mace da kullum suke tunota nakan ruggume karamin inyi ta kuka dan yana tuna min yarana.
A haka dai har ranar wata jumma'a nace musu dan Allah zan tambayesu me sukayi aka kawosu nan.
To anane sukayi ta rantse min da Allah suna cewa wlh tallahi su basu san me sukayi ba, kawai an kamosu daga wurin kiwone aka kawosu nan,
Babban cikinsu ya ƙara da cemin.
"Yanzu shekararmu ɗaya a nan harda watanni, kullum in an zo an dakemu da dare akan dawo ace mana mu amsa cewa mu yan kinnafin ne, sukance mu yarda kawai cewa mu yan kinnafin ne za'a dena dukanmu, mu kuwa bamu ma san menene hakan ba sai daga baya muka fahimci masu sace mutane suce a basu kuɗine ƴan kinnafin ɗin.
Yace min wlh tallahi summa tallahi mu ko gyadar gonon wani bamu taɓa sacewa mu bawa dabbobin bama, bare mu sace mutane ta yaya zamu yarda da laifin da bamuyi ba.
Har ace muyi bayani a saka a gidajen tv da Radio, to nima a ranar na basu lbrin abinda ya kawoni nan ga mamakina sai sukayi ta kuka wai sun tausaya min gwara su basa da yara sai iyaye."
Cikin rauni Sulaiman ya ɗan tsagaita kana ya ɗago kanshi ya kalli Sheykh da sai yanzu hawayenshi suka samu zubowa.
Cikin kukan yaci gaba da cewa.
"Inda na tabbatar da cewa,
sharri akeyi musu basu san komaiba.
Saida aka fara batun belina.
Randa aka kai kuɗin sukazo sukace an kawo belina amman ba kuɗinane zai fiddani ba.
Dole sai an samu wanda za'a liƙa sharrin sune suke kawo min kayan satan ina saya ta hakane za'a nunawa duniya an kama ainihin masu satan shiyasa ni za'a sakeni.
Hankalina ya tashi ina zan samo wasu ayi musu sharri a banza tunda asalin waɗanda suka saida min saraƙunan can dai sun gudu su kansu hukuma sun kasa kamosu.
Cikin tashin hankali nace.
"Musu ni kam babu wanda zan nuna ince shike kawo min kayan sata ina saya.
Sai suka cemin to asheko zanci gaba da tabbata a cikin magarƙamar babu belin.
Ga mamaki na, sai yaran nan sukace.
To su sun amince in nunasu su, da dai ace su masu satan mutanene gwara satan sarƙa kuma zasu samu a dena dukansu dan haka gwara su yarda su ɓarayin sarƙane, sabida su dai basu san darajar gold ba, basu kuma san saraƙunan matar gwamna bane.
Haka yasa nace musu a a ni kam bazan iyaba bazan bari a ɓata musu sunanba."
Hawayensa ya share tare da cewa.
"Sai babban cikinsu ya matsoni cikin rauni yace.
Kada mu zauna damu da kai duk mu ƙare rayuwarmu a nan.
Mu dai bamu da gatan kowa a duniya sai Allah da iyayenmu, kuma mu yanzu iyayenmu su sadakar dan zasuyi tunanin kashemu akayi.
Kuma mu bamu da yara, kai kuma kana da mata da yara da ƙanne da yayu waɗanda kaine gatansu.
Mun amince zamuce duk abinda sukeso a fidda kai.
In ka fita in ka samu dama ka nunawa duniya halin da muke ciki, kasa makusantanka su samu a Addu'o'insu tabbas munsan watan wata rana gsky zatayi aikinta, mu mun ɗaukeka matsayin ɗan uwanmu."
Sai kuma ya kife kansa a jikin kujera yaci gaba da kuka yana mai cewa.
"Yana gaya min haka ƙanne shi ma suka matsoni sukace su sun san tasu ta ƙare a ciki amma zasu tsaretar dani.
A haka a gabana inaji ina gani aka fitar dasu woje, aka jera bindigogi da makamai da kuɗaɗen a gabansu, kana aka dasa musu camera bayan an gaya musu abinda zasuce.
Anan ake tambayarsu ku su wayene.
Cikin bushewar zuciya ganin sharrin da akeyi musu ido na ganin ido sukace.
"Mu ƴan kinnafin ne".
Kana aka sake cewa.
"Ku wanne yarene?".
Sukace.
"Mu fulanine".
Wlh sai gashi wanda suke ciki kusa dani suna dariya suna cewa.
"Shegu fulanin dole sai mun koreku a kasar nan mun hanaku jin daɗi mun ɓata muku sunan ƙabilar shugaban ƙasar namu hegen bafullatani".
Hankalina ya tashi dana gane wai ashe duk anayin hakane dan a ɓata sunan fulanin a dozarta ƙabilar shugaban ƙasar to amma. Alhamdulillah tun daga ranar aka dena dukansu da wahal dusu".
Wani nannauyan numfashi suka sauƙe gaba ɗayansu suna masu zubda hawaye.
Cikin rauni Sulaiman yace.
"To tashin hankali na yaune za'a haska video da kayiwa yaran a nuna duniya cewa sune ɓarayin mutane".
Tofa wannan al'amari yayi masifar tada hankalin Sheykh yayi kukan da shi kanshi bai san yaushe rabonsa da yinsa ba.
Ganin ƙarfe ɗaya ta wuce ne yasa ya sharce hawayensa, murya a disashe yace.
"Zan tafi Malam, amman in sha Allah zan meda hankali na kan batun yaran nan, in Allah ya yarda zan sasu cikin addu'o'i na.
Zan kuma roƙi duk limamen masallacin jumma'a su sasu a addu'a."
Cikin tsananin jin daɗi Sulaiman da Malam sukace.
"Allah ya yarda ya bamu sa'a, ya tsaresu al'farmar Annabi da al'ƙur'ani ya fito dasu lfy".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya tafi.
Daga nan kai tsaye makarantar su Shatu ya wuce ya ɗaukota.
Ta lura yana cikin tashin hankali kuma duk jikinsa a mace.
To amma ganin lokacin salla yayi ne yasa batayi mishi mgn ba.
Suna dawowa ta shiga ɗakin ta, shi kuwa al'wala yayi ya fita.
Bayan an idar da salla kuma wurin Lamiɗo ya shiga ya mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi.
Wannan ne yasa baiyi baccin tsakanin azahar da la'asar ba.
Kiran salla ne ya medasu masallaci.
Ita kuwa Shatu koda ta shiga wonka tayi kana tayi salla, akan sallayar ta miƙe, dan ta gaji.
Ummi kuwa jin motsinta ne yasa taje ta kai mata abinci.
To nanma da kyar taci kaɗan kana ta koma ta konta.
Itama Ummi ta koma ɗakinta.
Saida tayi sallan la'asar ne ta fito ta nufi kitchen ita da Sara.
Ita kuwa Shatu cikin ɗan jin sauƙin gajiyar ta miƙe doguwar riga ta zura kana ta fito, falonta.
Har kamar zata wuce babban falonsu kuma sai taji ƙafarta ta riƙe wanda yafi wata da fara mata hakan.
A hankali ta ja ƙafar ta isa gaban kayan kallon, hannu tasa ta kunna TV inda ta samu tashar BTV a kunne anayin zabi sonka.
A hankali ta koma baya ta zauna bisa kujera 3 str, tana fuskantar tv murmushi tayi tare da cewa.
"Oh ikon Allah ashe har yanzu anayin zaɓi sonka".
Zama tayi tanajin ana gaishe-gaishe bayan minti biyar asa waƙa tayi minti biyar a cireta.
Ƙarfe biyar dai-dai aka gama shirin.
Shi kuwa Sheykh ana idar da sallan la'asar ya nufi gida,
tafiya yakeyi cikin yanayin tsantsar dauriya da danne tsananin halin da yake ciki.
Sabida wani irin masifeffen sarawa da ƙugunsa yake har sai yaji ƙahon zuciyarshi ya bada sautin ras-ras wata iriyar fitinenneyar zuface mai azabar zafi ce ta keto mishi tana tsastsafo mishi tako wani hudan gashin jikinsa.
Da sauri ya tura ƙofar falon ya shiga.
Ba kowa sai wulgawar Ummi daya hango ta shiga kitchen.
Yah Jafar kuwa gidanshi ya nufa.
Jalal kuwa yau kwana ukuma kenan baya gida.
Jamil kuwa tun safe daya tafi wurin aiki bai dawoba.
Wani irin azabebben karkarwa jikin shi ya farayi da tsuma sabida azabar ciwon da bai taɓa jin makamancinsa ba.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama".
Haka yake maimaita kalmar shahadar sabida jin tamkar ciwon zai ɗauke ransa.
So yake ya zaro wayarshi ya kira, Shatu ko Umaymah ko Abbanshi ko Lamiɗo ya gaza wani irin raunine ya rufeshi wanda yasa hawaye fara kwaranyo mishi, cikin zuciyarsa yake tunanin shike nan zai rasu ba tare da burinshi ya cikaba zai tafi matarsa bata haifuba zai bar ɗansa maraya.
Zai bar su Jalal cikin makirin masarauta.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da taune lip ɗinsa na ƙasa.
Kar-kar haka jikinsa ke karkarwar.
Babu abinda yake cewa sai maimaita kalmar shahada, wani irin jujjuya kai yayi ya tafi luuu ya...!
Ita kuwa Shatu, a hankali ta sunkuyar da kanta ta ɗaura hannunta bisa cikinta.
Tana jin yadda ɗan cikin ke jujjuyawa.
Da sauri ta ɗago kanta ta zubawa tv Ido, jin ɗan jaridar na cewa.
To masu kallo barkanmu da war haka yau dai gamu tare da SP Daniel tare da rahoton ƴan kinnafin ƴan bindiga daɗi, daga babbar het kotansu na babban birnin tarayya, zaku kalli video ƴan kinnafin ɗin kana muji ƙarin bayani daga SP Daniel
Ido ta zubawa allon tv lokacin da aka fara haske makaman dake jere gabansu Yah Giɗi Seyo Gaini da wasu matasan fulani waɗanda aka kamo kamar yadda aka kamosu.
Ana cikin nuna makaman, ana jefa musu tambaya.
"Wato wannan shine makaman da kuke amfani dasu a matsayin ku na masu GARKUWA da mutane?".
Dai-dai lokacin kuma ake haska camerar kan fuskar Yah Gaini wanda duk sauyin da zai samu a duniya bazata gaza ganeshi ba.
Ana ƙarasa haska fuskarshi da fuskar Yah Seyo da Giɗi.
Tayi wani irin yunƙura da azaban ƙarfi zuciyarta kuwa tayi wani irin azabebben tsinkewa da masifan karfi.
Wani irin azabebben juyi ɗan cikinta, yayi gaba ɗaya jikinta karkarwa ya farayi kamar wacce aka jonawa wutar lantarki.
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi tare damke cikinta, ta buɗe bakinta da azabar firgita da karfi ta kurma wani irin azabebben kuka mai haɗe da ihu da kiran sunan.
"Yah Giɗi Seyo Gaini wlh ƙaryane. Sherri akeyi maku innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil wayyoooooooo Bappa wayyoooooooo Ummey na Yah Sheykhhhhhhhhhhhhh...!
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 zaku tura ta Account 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na Debit alert ɗin ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276 ƴan 300 ku in baki da damar biya ta Account ku sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ku copy numbers ɗin ku turo min ta whatsApp 09097853276. Banbancin special Group da Normal group q yawan posting ne.
Special Group su yanzu muna gab da ƙare littafin da izinin ubangiji.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ina masoya na 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ina masoyan littafin GARKUWA ?
To ku marmatso kusa don ina da babban albishir a gare ku. Hazikar marubuciyar nan Mai suna RUKAIYA IBRAHIM GAWATA marubuciyar littafin " *Cikar buri na* " ta zo muku da wani littafin mai suna "ZURI'A BIYU".
Zuri'a biyu ya zo da sabon salo mai ban mamaki da daukan hankalin Mai karatu, littafi ne da yake kunshe da fadakarwa, tunatarwa ilmantarwa, tare da nishadantarwa. "ZURI'A BIYU" sunan littafin na GAWATAN GARKUWA
Kada Ku bari a baku labari....🤝🏻🥰😘
"Yah Sheykhhhh". Ta ƙira sunansa da ƙarfi da kuma karaji.
Wani irin juyowa Ummi dake kitchin tayi da sauri cike da tsaro ta nufi falon nasu cikin ruɗani da gudu.
Shi kuwa Sheykh jin muryarta da yadda ta zurma ihu da rakaji, yayi dai-dai da lokacin da yaji wani irin masifeffen azaban sarawa da ƙugunsa yayi, tare da harabar jijiyar bayanshi.
Dai-dai lokacin Ummi kuma ta isa falon Shatu, da gudu ta ƙara sa gabanta, ita kuwa Shatu dai-dai lokacin ta kuma yin wani irin ƙara tare da sa hannunta duka biyu ta dafe bayanta,
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam". Ta faɗa cikin wani irin masifeffen azaban sarawar da gugunta ya fara da ƙarfi naƙudar ta baro jikin Sheykh ta dawo gareta gadan-gadan.
Cikin tsananin tashin hankali Ummi ta iso gareta,
Ruggume ta tayi a jikinta ganin yadda take karkarwa, wani irin masifeffen zufa mai tsananin zafi ya keto mata tako wani hudan gashin jikinta.
Cikin tsananin kiɗima Ummi ta fara kiciniyar zaunar da ita, jin yadda ta ƙaƙƙandare ne, yasa Ummi cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Sheykh! Sheykh!! Sheykh!!!".
Ta ƙarashe kiran sunansa murya a hargitse.
Shi kuwa Sheykh wani irin ajiyan zuciya mai azaɓan ƙarfin da nauyi ya sake.
"Bismillah". Ya furta da ƙarfi tare da yunƙura ya miƙe tsaye jin lokacin ɗaya gaba ɗaya ciwon da yakeji ya sakeshi, tamkar a zare zirin gashi cikin man shanu.
Cikin tsananin tsuma da tashin hankali ya nufi, falon sabida jin yadda Ummi ke auna mishi kira babu ƙaƙƙautawa.
Yana shiga falon.
Kuma dai-dai lokacin faya ta fashe a jikin Shatu.
"Fushhhi".
Cikin gigita Ummi tace.
"Sheykh kayi sauri haihuwace.
Wani irin saurin isowa garesu yayi.
Yana isa yasa hannunshi ya tallabo ya mannata da jikinshi.
Cikin tsananin tausayawa yanayin da take cike yace.
"Aish! Aishhhhhhhh".
Ina bata amsa mishi sai karkarwar da jikin ta, keyi kana hannunta na dama tasa tana nuna musu tv da har yanzu ake nuna fuskokin yayun nata, cikin tsananin wahala da azabar naƙuda da gigi da kiɗimar ganin ƴan uwanta tace.
"Yah Sheykh kalli wlh ƙarya akeyi musu, wlh yan uwana ba ƴan ta'adda bane, su kam ba ƴan kinnafin bane, wlh ƙarya akeyi musu ƙazafine".
Ta ƙarashe mgnar da ƙarfi tare da fara wani irin gigitaccen nishi wanda yasa jikin Ummi karkarwa ta kasa koda motsa ƙafarta, bata taɓa haihuwa bata san cewa azabar haihuwa ta kai hakaba.
Shi kuwa Sheykh idonshi ya zubawa, tv inda take nuna mishi.
Yanayi yana zaunar da ita kan kujerar yana cewa.
"Aishhhhhhhh ki zauna ki nitsu".
Cikin ƙarfi ta cakumo wuyan rigarshi sabida azabar da taji ta tsargun mata, cikin gigin wahala tace.
"Ina nuna maka su Yah Giɗi Seyo Gaini kana cemin in zauna wlh ƙarya akeyi musu".
Da sauri yace.
"Eh A'ish na sani ƙarya akeyi musu, ki kwantar da hankalinki zan fito dasu, ki nitsu kinga haihuwa zakiyi."
Da sauri ta rumtse idanunta wasu hawaye masu ɗumi suka kwaranyo mata ga cutar naƙuda ga fargar abinda ta gani murya na rawa tace.
"Kayi min al'ƙawarin zaka taimakawa ƴan uwana Yah Sheykh wlh basu da laifi".
Cikin tashin hankali ganin yadda idonta suke juyewa yace.
"Nayi miki al'kawari Aysha zanyi duk iya iyawata zan fito dasu, kotu zata wonkesu fiye da yadda gurɓatattun jami'an tsaron kasar nan suka ɓatasu.
Ido ta lumshe a hankali, kana ta sake wuyanshi.
Sai kuma ta kamo hannun Ummi dake gifenta.
Cikin rawan jiki ta zamo ƙasa bisa carpet,
kanta ta jingina jikin Ummi ta riƙe ta gam-gam tare da karkarwa murya a fizge tace.
"Yah ilahi ya mujibadda'awati Yah Sheykh riƙe min ƙafata".
Da sauri ya zamo yayi ƙasa,
hannunshi yasa yayi sama da rigarta, robar ƙugun gajeren wondon jikinta, ya kamo, da sauri yayi ƙasa dashi, ya zare shi.
Kana ya gyara mata zamanta sannan ya meda doguwar rigar tata ya rufe mata jikinta.
Hannunshi ɗaya yasa ya share mata zufar dake tsastsafo mata bisa goshinta tare da hura mata sassanyan iskan bakinshi a wuyanta.
Cikin zubda hawaye tausaya mata yace.
"Kiyi nishi Aish kiyi nishi".
Cikin tattaro sauran kuzarinta tayi nishi mai karfi.
Ai kuwa cikin ikon Allah da sahalewarsa sai ga yarinya mace fara ƙal ta faɗo kan hannunshi da yasa ya tare.
Ita kuwa Shatu wani irin numfarfashi masifeffen wahala ta sauƙe tare da komawa ta jingina da jikin kujera.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin murmushi mai tafe da hawaye da rawan jiki yakeyi tare da kallon agogon Daimond dake ɗaure a hannunshi murya na rawa cike da rauni da tsananin farin