Showing 318001 words to 321000 words out of 352722 words

Chapter 107 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30745

miƙa mata, ta sawa Ummey ita a baki.
Sosai tasha kana ta janye goran.

Da sauri ta miƙowa Aunty Amina hannu alamun ta bata Afreen miƙo mata ita tayi.
Ita kuwa amsa tayi kana ta miƙa wa Ummey ita tare da cewa.
"Ummey sa mata al'barka tunda kece kaka mahaifiyar uba da mai renon Uwa sai ki bawa Dedde na ita tasa mata al'barka itama".
Murmushi Ummey tayi tare da amsarta sai kuma ta kalli Sheykh tare da cewa.
"Jabeer na ya girma".
Murmushi dake baiyana tsantsar jin daɗi sukayi.
Nan suka ɗanyi shiru jin Lamiɗo yayi gyaran murya tare da cewa.
"To Alhamdulillah wannan shi ake cewa ƙudurar Ubangiji babu bawan daya isa kaudashi.
Sai kuma ya kalli Bappa da tare da cewa.
"Dan Allah malam Liman bani lbrin yadda akayi Aisha ta kasance tare daku da kuma sanadin haɗuwarku da samun lfyarta?".

Cikin sanyi Bappa yace.
"Bazamu bari ta hutaba tukun?".
Da sauri Ummey ta jujjuya kai tare da cewa.
"A a Bappa gaya musu kawai domin nasan gaba ɗayansu wannan tambayarce a ransu.
Duk da zanso inji ya lbrin Jaddana da Sittina naga kowa sune ban ganiba".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Aunty Mamey Jaddanmu da Sittinmu suna lfy suna gab da tasowa zuwa nan suma".
Cikin tarin farin ciki tace.
"Alhamdulillah to Bappa gaya musu ko ince gaya mana meya faru?."
Shiru Bappa yayi sai kuma ya kalli Umaymah dake cewa.
"Dan Allah gaya mana a wacce suppar ka samu yar uwata a wani yankin".
Cikin nitsuwa Bappa ya gyara zamanshi kana ya ɗan yi gyaran murya a hankali yace.
"Ranar wata jumma'a data gabata tsawon shekaru goma sha uku a can ƙasar Cameroon a yanki dake gefen babban birnin Yahunde cikin Rugar Arɗo Babayo...!
Da sauri suka juyo suna kallon bakin ƙofar shigowa sabida jiyo muryar Hajia Mama daga nesa tana cewa.
"Zancen banza zancen wofi kenan ta yayama za'ayi ta dawo mutun har ta dawo nan cikin masarautar Joɗa".
Ta ƙarashe mgnar da ƙarfi tare da banko ƙofar ta shigo a fijajan.

Yayinda duk sauran tawagar masarautar Joɗa ke biye da ita a baya.
Tana shigowa tayi wani irin zabura tare da zaro idanunta gaba ɗaya sai kuma tayi kan Ummey da gudu.
Da sauri Shatu ta miƙe ta tsaya gaban Ummey tare da cewa.
"Da dakuka cutar da ita kuka fitar da ita haiyacinta da halittar ta a zatonku a haka zata tabbatane?".
Da sauri Sheykh yasa hannunshi ya kamo na Shatu yajata ya zaunar da ita.
Ita kuwa Ummey idanu ta zubawa Hajia Mama tamkar zata manna matasu a jikinta sai jujjuya kai takeyi.

Ita kuwa Hajia Mama ganin idon Ummey cikin natane yasa duk wani sihirinta ya dawowa jikinta kamar yadda Ba'ana yace musu zai bawa Ummey mgnin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya duk randa tayi Ido biyu da wacce tai mata sihirin zai dawo jikinta.
Bayan kwanaki biyar zata koma tsuntsuwar Boleru kamar yadda sukayi mata.
A lokacin Bappa yaƙi shi dai yace ta samu lfy ta fara mgn amman da gaiya Ba'ana ya bata wannan mgnin sabida zalumcin da akayi mata ya tsananta.

Cikin wani irin gigita Hajia Mama ta kai hannunta ta taɓa fuskar Ummey tare da cewa.
"Kika dawo mutum kenan bokana yamin ƙarya yace min har abadan yadda matacce bazai dawo duniyaba haka bazaki dawo mutunba bazaki taɓa dawowa Masarautar Joɗa ba."
Sai kuma ta kai hannu ta bugi gefen bayanta ta sosa tare da karkata baki kana tasa hannun ta ɗaya ta cire ɗan kwalin kanta ta cillashi gefe tare da cewa.
"Shigayar balarabiya mai nacin tsiya ki aure min miji ki haife mishi zaratan maza harda tagwaye kana ace cikin ƴaƴan ki za'a samu mai gadar mulkin Masarautar Joɗa ai wlh bazata saɓuba".
Sai kuma ta fara yatsuma gashin kanta tare da kurma ihu.

Cikin wani irin yanayi mai cike da rauni kunya tashin hankali kiɗima gigita.
Affan ya kife kansa da jikin sawun Sheykh ya saki wani irin kunyataccen kuka mai cin rai tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Hamma Jabeer wanne yanayi ne wannan Hajia Mama take ciki wannan wanne ranane mai cike da kunya Allah ya zai nuna min".
Da sauri suka juyo suna kallon Baba Kamal da yake fifita da hularshi tare da kecewa da dariya yace.
"Hahaha ta haukace ta haukace na haukace, zasu haukace duk zamu haukace.
Shegiya muguwar babarbariya ba ke kikayi mata sihiri ta zama tsuntsuwar Boleru ba kika haukata Jafar ba kika sawa Jamil bin mata Jalal bin mutanen banza bw".
Da sauri ta juyo cikin wani irin rawa-rawan haka na sakayyar mugun aikinta tace.
"Tafi daga nan mugun bafulatanin kai kuma ai kai ne kayi mishi ashirin kashe mishi lfyarsa dan kada yayi aure bare ya haihu kana zaton bansan duk abinda kakeyi bane".
Sai kuma duk suka kece da dariyar hauka tare da faɗi ƙasa sunayi harda tafa hannunsu.

Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil waɗannan sune kalaman da gaba ɗaya mutanen falon sukeyi sabida fahimtar sakayyace ta riskesu tun a duniya.
Baba Basiru ne ya matso kusa da Baba Kamal tare da cewa.
"Mugu bashi da kama Kamal kaida Hajia Mama tabbas kun cika mugaye masu cikekkiyar manufa wanda har kuka iya ɓoye muguntarku."
Su dai su Sheykh Umaymah Shatu Lamiɗo Abba Bappa gaba ɗaya zuba sarautar Allah ido sukayi.
Affan kuwa kukane mai cin rai yakeyi cike da kunyar abinda mahaifiyarshi ta aikata.

Shi kuwa Baba Basiru a hankali ya matso gaban Gimbiya Saudatu daketa zazzare idanunta cike da mamakin jin tsantsar muguntar mutanen da kullum take faɗa dasu a zatonta masoyan Sheykh ne.
A hankali ya kalleta kana yace.
"Jabeer yau dai ka yarda ka gamsu da abinda nake ce maka ko".
Cikin yanayi gamsuwa Jabeer ya kalli Baba Basiru wanda mutane ke zato maƙiyinshine har Gimbiya Saudatu ta haɗe dashi bata san cewa ƙididdigarta yakeyi ba.
Shi kuwa Baba Basiru a nitse yace.
"Dama na gaya maka Gimbiya Saudatu sha giri girbauce wautace kawai ke damunta da ƴar hasada, sannan kuma da zugan wannan maƙiyin nata".
Yayi mgnar yana nuna Baba Nasiru wanda ita a zatonta masoyi ta ne.
Cikin gyara tsayuwarshi ya kalleta kana ya kalli shi Baba Nasiru daketa karkarwa cikin zubda hawaye yace.
"Ke Gimbiya Saudatu kullum Nasiru na ingizaki da zugaki da cewa Gimbiya Aisha da ɗan ta Jafar ne suka kashe miki mijinki babban yayanmu Yah Aumalu mahaifinsu Hashim da Laminu wan dan Jafar ya gaji sarautar Galadima ko?".
Da sauri ta gyaɗa kanta.
Yayinda suma duk saura suka zuba mishi ido.
Cikin zubda hawaye yace.
"Toh kinga Yah Nasiru ɗan uwanmu uwa ɗaya uba ɗaya shine ya kashe miki mijinki uban ƴaƴanki sannan yanke ingizaki kan su Sheykh da mahaifiyarsu yasa miki tsanarsu kiketa haushi a kansu kamar karya.
Ita wannan muguwar kuwa Hajia Mama da Kamal da Hashim ɗanki da kuke gani kamar yana son Jabeer alhalin ya tsaneshi shi kuwa wai dan Lamiɗo yafi janshi a jikinshi.
Duk sai suka fake a bayanki sunayiwa Sheykh da ahlinsa mugunta yayinda kowani sai yayi zargin kece kinga kin zama bushiya kamar yadda Shatu ta faɗa a zahiri in anganki jiki duk ƙaya amman cikin bushiya namansa ma maganine su kuma suka kasance belbela siffarsa fara cikinta baƙiƙƙirin".
Cikin rauni Gimbiya Saudatu tace.
"Innalillahi wallahi ni dai Allah ya sani ko garin marke ban taɓa nemowa da niyar cutar dasuba..
Yanzu ashe Hashim kaima muguwar zuciya gareka ban saniba har zaka iya cutar da ɗan uwanka."
Ina Affan kam tuni yake kuka tamkar zai shiɗe dan baƙin ciki da takaicin abinda uwarsa ta aikata.

Yah Jafar ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Tabbas kuwa Hajia Mama da Baba Kamal da Baba Nasiru da Hashim sune manyan Magautan mu".

Da sauri Sheykh ya miƙa tare da kamo hannun Hajia Mama da taketa son kwaɓe kayanta.
Da sauri ya nufi Side ɗinsa.
A wannan ɗaya ɗakin yasata ya rufeta bayan yayi mata allurar bacci.
Kana ya fito.
Nan ya samu Lamiɗo yasa Fadawan shi sun fita da Baba Kamal dake ta ihun hauka.
Sannan Jalal kuma ya miƙa ya damƙi Baba Nasiru dake son guduwa.
Ya miƙashi hannun abokanshi sojojin daya kira bisa laifin kisan kai.

Shi kuwa Yah Sheykh a hankali ya kalli Yah Hashim a hankali yace.
"Ashe harda kai a cikin magautana Yah Hashim. Kai lallai ɗan Adam darene babu mai saninsa sai Allah".
Lamiɗo ne ya kamo hannunshi ya zaunar dashi kana yace.
"Kai Hashim fice mana daga nan bama buƙatar mai muguwar zuciya ko ɗaya a nan".
Ai kuwa da gudu ya fice cike da kunya.

Shi kuwa Lamiɗo gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Jafar bamu lbrin meya faru da kai da mahaifiyarku a dare ɗaya ta sauya halitta daga mutun zuwa tsuntsuwar Boleru kai kuma ka dena mgn".

Gyara zamansu sukayi baki ɗayansu dan wannan itace tambayar da take cinsu a rai tsawon shekaru goma sha uku kenan gaba ɗayansu.

Cikin gyara zamanshi ya ya fuskancesu kana a hankali yace.
"A ranar...!






Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a posting ne 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Ta wannan ac no zaku tura kuɗin sai kiyi screenshort na Debit Alert ɗin ki turo min shaidar biyan ki ta whatsApp 09097853276 ku yan 300 in baku da damar biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku kacal sai ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.

By
*GARKUWAR FULANI*



"Aranar wata jumma da da wanna Zazzafar ƙaddara ta rufta damu shekaru goma sha uku baya."
Sai kuma ya ɗan tsakaita
tare da jan
sassayan numfashi ya gyara
zamansa tare dasa tafin hannunshi ya share hawayensa.
Yayin da gaba
ɗayansu kacokam
suka mai da hankalin su kansa,
Duk sun ƙagu suji yadda a kayi a wannan ranar da basu manceba.
Shi kuwa Yah Jafar wani numfashin yakuma.
Saukewa kana yaci gaba da cewa.
"Ranar da dare bayan anyi sallan isha'i duk muna falon Mamey dani dasu Jalal Jamil Affan da Ummi da Imran yana ɗan sheksru takwas lokacin.
Anan mukaci abinci kana muka zauna muna hira.
Kasan cewar akwai shaƙuwa mai tarin yawa tsakanin Mamey da Affan da yake tana da son yara.
Amman son Affan da banne a wurinta har su Jamil kance wa Affan na hannun daman Mamey.
Takanyi Dariya tace.
"Eh ɗin ai ya fiku nitsuwa".
Muna zaune sai hamma Mamey keyi tare da miƙa da lumshe idonta hakane yasa tace mana.
Duk ta sallamemu saida safe tanajin bacci.
Ummi tace.
To.
Still Kuma sai mukaci gaba da hira.
Da ido muka bita ganin ta miƙa cikin sanyi tace.
"Kai zanje inyi bacci wlh wani irin bacci mai nauyi nakeji yana fuzgata tamkar zan faɗi.
Ni na shiga saida safenku".
Allah ya bamu al'khairi mukace dukanmu kana ta shiga.
Tana shiga kwanta ko second uku batayi da kwanciya ba tayi bacci.
Mu kuwa muna gama hira muka watse.
To su Jalal ne ƙarshen fita ashe basu tasheta ta rufe ƙofarta ba a famintata kenan fa?".
Ya ƙare mgnar yana kallon su Jamil.
Da sauri Jamil yace.
Eh.
Cikin sanyi ya kalli su Lamiɗo kana yaci gaba da cewa.
"Ina komawa ɗaki na kira Juwairiyya muka fara hira a waya kamar kullum.
To bayan mun gama
waya da Juwairiyya
har na kwanta sai na mike na nufi
ɗakin Mamey dan
inaso nayi mata magana a kan Juwairiyya fa tasanar wa mahaifin su maganar auren mu da ita, tun da lokacin takammala
karatun ta dan haka itama ta gayawa Abba na ayi batun aurenmu dan nima tuni lokacin na gama karatuna har na fara aiki.
Kuma a kwanakin ne aka bani sarautar Galadima wanda da mijin Gimbiya Saudatu ce mai matsayin to daya rasune Lamiɗo ya maida mulkin kaina.
A zatonshi ta hakane zaisa yaranshi bazasuyi faɗa da junaba tunda bazasuce ya baiwa wane ya hana waneba.
Ni a lokacin dagani har Mamey da Jabeer da baya ƙasar ma ba son wannan mulkin mukayiba bisa dole aka bani ita.
Sai kuma ya jingina bayanshi da kujera kana yaci gaba da cewa.

Ina isa bakin kofar
Mamey natura kofar da sallama nashiga ɗakinta.

Da sauri naja natsaya nan bakin kofar.
Can na hangi Mamey na kwance.
Bisa gado tana bacci da alamun baccin mai nauyi ne.
Hajiya mama kuwa na tsaye a kanta da wata iriyar shiga da tafi kama data bokaye ko ince matsafa.
Da mamaki nake kallon
Hajia Mama dake tsaye bakin gadon sanye da wasu irin jajayen kaya tun daga samanta har ƙasa,
kanta babu ko ɗan kwali
hannunta rike da wani ƙwarya.
Tana yayyafawa Mamey
wani ruwa dake cikin ƙwaryar tare da yin wasu surutai da sukafi kama da surkullen matsafa.

"Innalillahi wa'inanna ilaihirraji'un, nafurta da karfi.
Da sauri nanufo in da Hajia Mama'n ke tsaye cikin ruɗani da kiɗima ina faɗin.
Meye hakan Hajia Mama? me kike mata? me kike zuba mata a jiki haka?.
Dasauri tajuyo kaina tasaka hannunta cikin ƙwaryar taɗibo ruwan tashiga watsamin tana ƙara matsoni,
kaucewa nashiga yi ina matsowa in da Mamey take kwance kamar gawa ko matsi batayi,
itako Hajia Mama masoni tarikayi tana watsamin ruwan,
Baki na buɗe da karfi sabida wani irin masifeffen suka da naji duk inda ruwan ya taɓa a jikina yanayi.
Ƙara watsomin tayi wanda yasa na ƙara kaucewa da sauri tare da buɗe baki da nufin yin ihun zafin da nakeji da kuma fargabar halin da Mamey na ke ciki.
Sai kawai naji harshena yafurta Innalillahi wa'inanna ilaihirraji'un,wannan kalmar narika nanawata da karfi madadin inyi ihu."

Ita kuwa Hajia Mama da sauri tajuya cikin alamun tsoron tonuwar asirinta.
dan lokacin dare baiyi nisa sosai ba misalin ƙarfe goma ne,
da gudu tafita a ɗaki dan jin yadda na kara sautin salatin da nake.


Ita kuwa Hajia Mama tana fita part ɗinta ta nufa direct bathroom ɗinta ta shiga gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi number'n bokan ta takira yana ɗagawa cikin haki da fargabar a bin da zaije ya da wo tace.
"Boka yanzu nafito daga ɗakin matarnan na samu tayi bacci kamar yadda kace, kuma na watsa mata ruwan bata farka a sai daifa wani yaganni lokacin danake yayyafa mata ruwan maganin nan babban ɗanta Galadiman Masarautar Joɗa kenan ya ganni".
Wani irin dariya irin nasu na hatsabibai bokan yayi kana yace.
"Toh daya ganki me yakeyi? me kuma yake cewa?".
cikin rawar baki da soron da ya ziyarce ta gudun kada ai kin ya ɓaci tace.
"Sunan Allah yaketa ambata salati yaketayi babu ko kakkautawa da wasu addu'o'i".
Cikin ɗan tsagaita dariyar mugayen bokan yace
"To aiki kam zaici amma dai akwai nakasu aciki, amma kada kidamu yanzu shi yaron zamu rufemasa baki zai dauwama kurma ba mgna a bakinsa bazai iya yin maganaba bazai iya furta komai ba haka zai dauwama ba mgn saidai yayi ta mai-mai-ta abinda yake cewa.
Sannan daga nan tagwayen kuma zamu haɗa ɗaya da bin mata ɗaya shaye-shaye shi kuma babban kinga zai zama kamar Mahaukaci, shi kuma wancan Jabeer ɗin na gaya miki tun yana ƙaramin akwai sihirin da wani yayi mishi kada ki damu dashi bazai taɓa yin aureba har gaban abadan ko an mishi bazai zauna da matarba, kinga kenan duk sun zama suna da matsalar da dole baza'a basu mulkiba sai dai a bawa ɗanki Affan tunda kinga shi Imran ɗan ɗaya kishiyar taki shine ƙarami kan Affan."
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Yauwa boka na gode ni dama fatana ɗana yayi mulki dan bana son mulkin ya bar ɗakina tunda dai kace min tabbas cikin yaran Habibullah ne mijin wani zai gaji kakansa sarauta.
Dariya yayi tare da cewa.
"Kada ki damu mulki na gareki da ɗanki".
Wa iyazubillah kaɗan kenan daga sharrin tsinannun shaiɗanu maƙiya Allah da Manzonsa bokaye taɓaɓɓu masu sa mai binsu ya taɓe ya gaza sauri a ranar da muminai ke sauri a bisa siraɗi.

Acan cikin ɗakin Mamey kuwa.
Sosai sautin addu'a da karatun da Jafar keyi yatsanan ta yana kankame da Mamey, wacce ke ƙwance ida nunta a rufe, har lokacin bata farka daga.
Baccin sihirin da akasa takeyi ba saboda nauyin. Baccin da suka je fata ciki.
Sheko bakinsa baya iya furta komai sai addu'o'in sai kuma hawaye da keta tsatstsafowa daga cikin ida nunsa sabida fargarba da kuma zafin da yakeji,
Abba kuwa dake can part ɗinsa da yake Part ɗin shi na natsakanin na matan nashi ne.
Yana cikin ɗakinsa dake sama.
Haka yasa yarinƙa jiyo muryar Jafar da irin addu'o'in dayake cikin kiɗima, da kajin addu'ar kasan acikin tsananin firgici da tashin hankali yake yinsa,
Wuf yamike yanufo part in Mamey kasan cewar babu wata tazara sakaninsu.
Gudu-gudu sauri-sauri ya isa.
Cikin hanzari yatura kofar bedroom ɗin Mamey cikin sananin tashin hankali da kaɗuwa ganin yadda Yah Jafar ke rungume da Mamey sai innalillahi yake da karfi hawaye yagama wanke fuskarsa idanunsa sun yi jazir saboda kuka da zafin da yakeji da fargabar ganin tamkar Mamey a mace take a kiɗime yanufo in da suke yana faɗin.
"Subahanallahi kai Jafar meya farune me ya sameta?".
Yayi tambayar hankali a tashe, tare da miƙa hannu ya ɗago kan Mamey dake kan kafar Ya Jafar yashiga girgizata yana kiran sunan ta.
"Aisha! Aisha!! Ummu Jabeer!.
Gani shiru bata ko matsi sai dai tana numfashi ya tsananta firgicinsa.

Hankali a tashe yakuma kallon ya Jafar wanda keta addu'o'in babu ko kakkautawa.
Mai da kan Mamey'n yayi ya kwantar kan cinyar kafar Jafar.
Kana ya juya a kiɗime ya fita a ɗakin da sauri ya nufi sashin mahaifinsa Lamiɗo.

Shi ko ya Jafar cigaba da maimata innalillahi yakeyi yana zubda hawayen.

A can ɓangaren Hajia Mama kuwa.
fitowar ta daga ɗakinta kenan cike da jin daɗin yadda bokan ya karfafa mata guiwa tanajin daɗi a ranta yanzu komai zai tafi mata yadda take bukata zata rabu da zugar yayan Mamey da ita duk kowa ya huta, tana fita ta hangi Abba ta window yafita daga cikin part ɗinsa hankali a tashe.

Fuska ta ɗan yamusa tazauna saman ɗaya daga cikin kujerun parlour'n, can kuma tamike kamar an tsikareta tabi bayansa da sauri.

Acan shashin Lamiɗo kuwa.
Da sauri Lamiɗo da Galadima suka mike, bayan Abba yagama sanar musu abin da ke faruwa.
A tare suka fito suka nufi part ɗin Mamey'n.

Lamiɗo na gaba Galadima da Abba na biye dashi suka shiga ɗakin, in da Abba yabar Yah Jafar a haka suka iske shi yana ganinsu ya miƙe da sauri Mamey yashiga nuna wasu Lamiɗo da hannu yana kuka yana nuna musu ita da kwatanta musu yadda Hajia Mama tayi mata.

Da sauri Hajia Mama ta turo kofar dan taga shigowar su Lamiɗo'n.
Jafar kuwa yana ganinta yashiga nunata da hannu sai kuma ya nuna Mamey'n yana cigaba da ƙwatanta yadda tayi matan shidai baki kam babu shi sai dai addu'o'in da kuma kukan dayake tayi.

Gaba ɗaya su suka maida kallonsu kan Hajia Mama nan take Lamiɗo da Galadima da Abba suka ɗiga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login