Showing 225001 words to 228000 words out of 352722 words
By
*GARKUWAR FULANI*
: Luuuh ida nunta suka limshe ta sume.
Da sauri yasa hannunsa ya tallabo ta faɗa jikinsa, cike da tsoro Ummi ta matsoshi tare da cewa.
"Sheykh lfy kuwa meke faruwa?".
Cicciɓota yayi ya ruggumeta tsam a jikinshi kana, ya juya ya fara taku, yana ratsawa gefe.
Cikin tsananin tsoro Umaymah, Ummi, Mamma. Suka rufa mishi baya.
Yayinda Aunty Rahma kuwa da sauran tawagar ƙawayen Umaymah suke zaton, kawai wani salone hakan sabida abu da Ustazu sai kallo.
Hajia Mama kuwa da ido ta bisu tare da yin wani ɓoyeyyen murmushi mai cike da manufofi masu ƙarfi.
MC kuwa wani sassanyan ƙiɗan da DJ ya saki yake takawa rawa.
Yanayi musu kirari, Affan da Jamil kuwa tafi sukeyi tare da alamun, jinjina dan babu wanda ya gano Aysha a tsume take ko Haroon da Ibrahim da Jannart basu ganeba.
Da sauri Jalal ya miƙe shima ya rufa musu baya.
Da sauri Ummi ke biye dashi a baya tare da cewa.
"Sheykh lfy kuwa".
A hankali ya jujjuya kanshi tare da cewa.
"Ummi a sume take fa".
"Subahanallahi!". Suka faɗa a tare.
Da sauri Umaymah tayi gabansu tare da cewa.
"Zo nan zo muje part ɗin Abban Haroon."
Binta a baya yayi sabida yasan canne kaɗai zasu samu babu taron mutane.
Suna shiga part ɗin ta juya gefen da.
Wani ɗan madaidaicin Side ne mai kyau.
Wanda yake da ƴar tazara tsakaninsa da Side ɗin Abbansu Haroon.
Hannu tasa ta tura ƙofar.
Cikin wani ƙawataccen falo suka shiga,
da sauri ya kontar da ita bisa kujera.
Kana ya miƙe tsaye tare da sauƙe numfashi yana ɗan miƙar da hannunsa,
cikin ruɗani Mamma tace.
"Umaymah ya haka, bata da lfy tana sume kuma mu zauna da ita a gida mu tafi asibiti mana".
Ta ƙare zancen a firgice sabida bata san matsalar Aysha ba.
Ummi ce ta ɗan sauƙe numfashi tare da cewa.
"To meya tayar da jikinta kuma lokaci ɗaya haka".
Cikin takaici ya ɗan tauni lip ɗin shi na ƙasa tare da cewa.
"Uhummm to Ummi kuma kun sani mutun tana na nan matsala, sannan anzo ansa ƙiɗe-ƙiɗe ga ƙarin al'gaita, sannan kuma aka ƙara da sarewa.
Ko wanda baida komai a kan shi sai yaji tsikar jikinai na tashi.
To ga irinta nan, in kuma ba'a katse sarewar nanba duk zasuyi ta sumewa masu makaran".
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Wlh duk tsiyar Rahma ce, yanzu kayi wani abu ta farfaɗo yafi".
Kanshi ya gyaɗa kana yace.
"Da fari aje ace subar wannan bushe-bushen sarewa da kiɗan tambarin, a ma tashi kawai a taron haka ya isa haka kowa yaje yayi al'wala magriba ta gabato."
Jalal dake tsaye bakin ƙofar ne yace.
"To bari inje in gaya musu".
Da sauri Ya juya ya fita.
Ita kuwa Ummi a hankali ta matso kusa da Umaymah kana tace.
"Muje kawai, ba komai zai kula da komai".
To Umaymah tace jiki a mace, hankali a tashe, Mamma tace.
"Haka za'a barta".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Mamma kana a hankali ya ce.
"Ba komai Mamma kada ki damu zata dawo dai-dai, kije kuyi salla".
Bisa dole dai tabi bayansu suka fita.
A can wurin kuwa kai tsaye wurin MC Jalal yaje yace.
A tashi taron haka lokacin salla yayi.
Dole aka tashi kowa ya kama gabansa, bayan ƙannnen ango su Hibba sunyi liƙinsu.
Su Umaymah kuwa wurin suka koma taje ta jagoranci ƙawayenta suka koma cikin Part ɗinta.
Ƴan cikin garin Tsinako duk suka koma gidajensu sai ƴan nesa-nesa wanda duk gobe zasu tattafi.
Su Ya Hisham da Affan kuwa tare da Haroon da Ibrahim suka koma part ɗin da aka sauƙesu,
nan kowa ya fara shirin al'wala dan lokacin ya ƙara to.
Sheykh kuwa a can Side ɗin.
Su Umaymah na fita, ya maida ƙofar ya rufe, kana ya dawo gaban kujerar da ya kwantar da ita.
Tayi lib kamar gawa.
A hankali ya sunkuyo hannunshi yasa ya dafe hannun kujerar da kanta yake kai.
A hankali ya sunkuyo kanta sosai,
yatsunsa yasa tsakiyar goshinta ya ɗan buga da ƙarfi tare da cewa.
"BISMILLAH". Kana yaci gaba da ɗan buge goshin nata, a hankali tayi wani irin sassanyan miƙa tamkar wahainiya, fatan idonta ta fara motsawa shi kuwa Sheykh ci gaba yayi da buge goshin nata tare da cewa.
"Aeeyshah! Aeeyshah!!."
Cikin fizgar numfashin da mgn tace.
"Na'am".
Haɗe fuska yayi tare da cewa.
"Ba ke na kiraba,".
Da sauri tace.
"Ni ka kira mana kanata dukana a goshin da amton sunan Allah".
Fuskarshi ya tsuke tare da cewa.
"Goshinki ko goshin matata! sanina dake kince kin tafi, meya kuma kawoki me kike nema?".
Kwaɓe fuska tayi murya na rawa hawaye na zuba tace.
"Kirana ankayi tunda anka kunna Sarewa da al'gaita dole du inda nake zan taho".
Cikin faɗa yace.
"Ke tafi daga nan maƙaryaciyar banza".
A hankali ta buɗe baki alamun zatayi atishawa cikin tsawa yace.
"Tsaya ban gama mgn da keba in kika kuskura kika tafi, to tabbas zan jawoki in kuma ɗaureki in ƙonaki".
Cikin rawar murya tace.
"Na tsaya, kayi haƙuri".
"Maza tashi ki zauna". Yace a faɗace.
Da sauri ta tashi ta zauna,
Gefenta ya zauna kana ya kamo hannunta ya riƙe gam saida tayi ƙara sannan yace.
"Baki san gidan da take bane".
Da sauri tace.
"Na sani".
"To ina take?". Ya kuma tambayarta.
"Masarautar Joɗa take".
Kanshi ya gyaɗa sannan yace.
"Na'am kin san kuma dole duk wanda ke cikin masarautar Joɗa sai yaji kakaki da al'gaita da tambura da sarewa tunda mabusar masarauta ne, ko kina nufin duk sanda taji sai kinzo kin fiddata cikin haiyacinta kin tozarta min aurena a bainal jama'a, in bana kusa ta faɗi har ƙasa a sume ko me kike nufi ace matata tana sume a kwance ƙasa".
Da sauri tace.
"A a baza'ayi hakaba in sha Allah bazan zoba, in dai dan kiɗane da sarewa nayima al'ƙawarin bazan zoba, na dena zuwa har abadan dan Allah sake min hannuna".
Kanshi ya jinjina kana yaci gaba da matse hannun da kuma karantar Baƙara da yakeyi a hankali.
Cikin kuka tace.
"Dan Allah kada ka cutar dani wlh nima ban taɓa cutar da Shatu ba, Ni makariyace a wurinta, dan Allah kada ka ƙonani, zan tafi dama ko iyayenta basu san in jikinta ba, sai dai sukayi zaton akwai wani abu jikinta tunda sa'i zuwa lokacin takan ga abinda bani adam basa iya gani da yardar ubangiji".
Cikin sanyi yace.
"Wato dan raini baki taɓa baiyana a jikinta iyayenta suka saniba sai Ni Muhammad kikewa hakan ko?".
Da sauri tace.
"Wallahi Allah kenan na baiyana a jikinta ne bisa dole da kuma ceton lafiyarta da kuma bata kariya dama kai kanka".
Cikin hatsala yace.
"Ubangijina shine mai bani kariya, in kika kuskura na ƙara ji ko ganinki to tabbas zan babbakaki, fice min daga jikin mata dan kan babarki".
Ai kuwa a take Aysha ta fesa wasu tagwayen atishawa guda uku.
Sai gashi ta koma ta konta lib a jikinshi tayi bacci.
Kanta dake bisa kafaɗarshi ya dungure tare da cewa.
"Jiki duk al'janu sai son bidi'a da sakalcin yin addu'a ma wai kin gajiya, gaba barinsu zanyi su mummurƙusheki zaki gane kurenki, wai Yah Sheykh na gaji kayi min addu'ar".
Sai kuma yayi murmushi tuno jiya-jiya nan taketa mitar ya dena ce mata mai al'janu, wai harda cewa yana bazata a gari.
Zareta daga jikinshi yayi kana ya miƙe yana cewa.
"Zaki bazu yarinya bari ki shiga tarkon Muhammad zaki bazu iya bazuwa".
Ya ƙarashe mgnar yana wuce bedroom ɗin yana shiga bathroom ya wuce al'wala yayi kana ya fito.
Wayarshi ya zaro a al'jihunsa, kirar arshi mai sauti yasa mata kana ya ajiye mata gefen kanta, sannan ya fita ya tafi masalacin.
Bayan sunyi sallan mangriba basu fitoba saida sukayi isha'i, kana suka dawo gida.
A falon ya samu Umaymah, Ummi, Mamma, Aunty Rahma, Safiyyah Jannart.
Itama Aysha tana zaune,
yana ganinsu a cike ya ɗan tsaya kana ya kalli Umaymah dake cewa.
"Jazlaan ya jikin nata dai".
Matsowa yayi yasa hannunsa ya ɗauki wayarshi dake kusa da ita kana yace.
"Uhumm ta worke ai".
"Alhamdulillah Allah ya ƙara lfy".
sukace a tare,
A hankali Aysha tace. "Amin".
Safiyya, Jannart, Aunty Rahma, ne suka fita.
Hakane yasa ya rage Umaymah, Ummi Mamma.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli Ummi dake cewa.
"Wannan abun fa sai an tsaya mata zata rabu dashi Sheykh".
Yana lallatsa wayarshi yace.
"Dama ai Ni na sani tun jiya data fara cewa, taga Jahan a a Jahan yazo nasan ba wani Jahan ababaɗenta ne kawai ke mata gizo. Amman ba komai zan juyo kansu ya faɗa yana ɗan guntun murmushi, domin yasan Umaymah dai tasan waye Jahan".
Ita kuwa Aysha.
Tura baki tayi tana kallonshi kamar tayi kuka. Allah ya sani bata son yana cewa tana da al'jani".
Murmushi Umaymah tayi ganin yadda tayi kana a hankali tace.
"Kada ki damu, yana raba wasuma da nasu bare ke, in sha Allah zasu bar jikinki juyowa ɗaya zaiyi kansu bazasu sake waiwayarki ba ɗiyata. Kirkiji komai mu mun sani matsalar a masarautarsu ce, da Juwairiyya ma lfya lau muka kaita gidan Jafar bata shekaraba makarai suka shige ta".
Da sauri yace.
"Amman dai ita wannan da abunta tazo Umaymah ba a masarautarmu ta sameshi ba".
Mamma ce tace.
"Kada ka kare wancan masarautar taku, mu tayi mana illa mafi muni a rayuwa."
Kanshi ya jinjina tare da lumshe idonsa kana yace.
"To ya zanyi Mamma tunda jigo nane asalinane, kuma ba kowa na ciki keda mugun dafiba, kada kuyi mana kuɗin goro, Nima inai musu uzuri duk da dai nasan duk duniya babu wanda sukayiwa illa sama dani, sai dai nasan zanen ƙaddaratace suka bi".
Kai Ummi ta jinjina kana suka miƙe tsaye.
Umaymah ce ta nuna mishi Foodflaks dake tsakiyar falon tace.
"Kuci abinci ka kula da ita,sai da safe".
Ta ƙare mgnar suna fita.
Cikin jin kunya yace.
"Allah ya bamu al'khairi".
Amin sukace kana suka tafi.
Washe gari da asuba, a hankali ta buɗe idonta jin muryarshi yana karatu.
Ganin ya bata baya baya ganinta ne, yasa ta yunƙura a hankali, ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa.
Kana ta miƙe ta nufi Bathroom, ruwan ɗumi ta haɗa cikin bathtub ɗin sabida alamun hadari da sassayan iskan dake busowa.
Wonka sabulu tayi, kana tayi na tsarki sabida al'adarta ta ɗauke.
Towel ɗin dake bisa masaƙalin ta ɗauka ta tsane jikinta, kana ta meda kayan jikin nata.sannan ta fito.
Gefenshi ta ɗan ratsa sannan tace.
"Zanyi salla kuma ba hijabi".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta,
kana yaci gaba da karatun.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ni ban san ina mukeba, kuma ba hijabi".
Miƙewa tsaye yayi jin masallacin Masarautar suna ƙoƙarin tada kabbara.
Al'kyabbar ajikinshi ya zare, kana ya dawo ta bayanta.
Hannunshi yasa ya ɗago hannunta ya zura mata hannun al'kyabbar, kana ya ɗago ɗayan ma ya zura mata.
Sannan ya saketa.
Har ƙasa ta zo mata,
kasan cewar irin al'kyabba mai duhu da kaurin nanne yasa tayiwa jikinta ƙawanya.
Gabanta ya dawo, jallabiyace a jikinshi fara ƙal.
Hiramin kanshi ya cire, kana ya ɗaura mata shi a kanta tare da dai-dai-ta zamanshi ya rufe komai na kanta sai fuskarta kawai.
Ido kawai ta zuba mishi tana mai shaƙar ƙamshin jikinshi.
"Ni dai ba ɗan aikenki bane, kuma bani nace kisa suturar da bai inƙanta ayi salla da itaba, dan haka babu ruwana. Al'barkacin salla zakiyi ne yasa na baki aron rigata, kina idar da salla ki cire min abuna".
Ya gaya mata yana tsareta da ido.
Cikin yin mui-mui da baki tace.
"Uhummm".
Shi kuwa juyawa yayi ya fita.
Daga nan Side ɗin da kayansu yake shida Ibrahim yaje.
Wata al'kyabbar yasa kana suka nufi masallacin.
Bayan an idar da salla sune suka dawo gida.
Tuni Umaymah kuma tasa Safiyyah da Aunty Rahma sun shiga kitchen da kansu sun haɗa breakfast.
Nan aka kaiwa su Affan da Ya Hashim, Imran Sulaiman.
Sukaci abinci kana suka kama hanyar komawa Ɓadamaya.
Sheykh, Ummi, Aysha, Hajia Mama da Batool da Jamil, Jalal ya Jafar kuwa su sai bayan sallan isha'i jirginsu zai tashi.
Haka kuwa akayi. Bayan sallan isha'i.
Su Umaymah Haroon, Ibrahim, Safiyyah, Sadiq, Azeex, Hibba Azima Aunty Rahma Ishma sukayi musu rakiya har Airport.
Sunata kewar juna,
A cikin mota ne, Aysha ta kalli Safiyyah dake gefen Umaymah da Mamma tace.
"Safiyyah ai zaku zo mana kafin ku tafi ko".
Aunty Rahma dake jen motarce tace.
"In sha Allah kuwa, ai muma duk zamuzo, sabida zamu ɗan kwana biyu kafin mu koma".
Cikin jin daɗi tace.
"To Aunty Rahma a bamu Ishma mana mu koma da ita sai kunzo ku taho da ita".
Cikin dariya Hibba dake can baya ita da Hajia Mama da Ummi tace.
"Aunty Aysha wayo ko".
Da sauri Aunty Rahma tace.
"Kada ki damu in sha Allah zasu dawo tare da Juwairiyya, kinga mu zamuyi ko kwana uku ne nan gaba kafin mu koma wurin Sittinmu, in mun koma kuwa bazai dadeba Juwairiyya zata komo to sai ta taho miki da Ishma'n".
Cikin gamsuwa tace.
"To Allah ya kaimu Lokacin".
Amin Amin sukace, kana dai-dai lokacin suka isa, harabar airport ɗin.
Nan suka samu su Aunty Juwairiyya da Azeema da Jazrah ma sun iso.
Gefensu Sheykh suka isa.
Nan sukayi sallama da juna, cikin bege da kewar juna.
Suka rabu.
Jin ana cekiyar matafiya.
Nan suka nufi cikin jirgi su kuma suka koma baya.
Basu dai tafiba saida jirgin ya tashi, kana suka juya suka koma gida.
Tsakanin Tsinako da Ɓadamaya tafiyar 40 minutes ne a jirgi.
A mota kuwa awa goma sha biyar ne.
So takwas dai-dai jirginsu ya tashi.
Su Affan kuwa dai-dai lokacin suka isa. Kasan cewar a gajiye suka isa, kowa wonka yayi kawai dama sunyi salollinsu a hanya sun kuma ci abinci sai bacci kawa.
8:40 dai-dai na dare jirginsu ya sauƙa a Airport ɗin Ɓadamaya.
Dr Aliyu, da Baba Kamal mahaifin Sulaiman kenan, sai Sarkin fada da Galadima ne sukaje tarbosu tun kafin su iso.
Tafiyar 24 minutes ne tsakanin Airport ɗin da masarautar Joɗa.
Tara da minti goma dai-dai motar Dr Aliyu ta iso har farfajiyar Side ɗin Sheykh, wanda Sheykh yake gaba kusa dashi, Ummi da Aysha suke baya.
Motar Baba Kamal kuwa Hajia Mama ce da Batool,
Sai,
Motar da Galadima ke ciki kuwa, Nan Ya Jafar da Jalal da Jamil suke ciki.
Kai tsaye kuma Side ɗinsu Jalal ɗin aka wuce dasu.
Itama Hajia Mama har bakin Part ɗin ta aka sauƙeta.
Da sauri Ummi ta buɗe marfin motar gefenta ta fita.
Nan Aysha ma tabi ta fita.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli Dr Aliyu cikin nitsuwa yace.
"Baba Aliyu ngd matuƙa".
Kai Dr Aliyu ya gyaɗa tare da cewa.
"To sai da safe".
Allah ya bamu al'khairi yace.
Amin Amin yace kana yaja motar ya tafi.
A bakin ƙofar shiga falon suka tsaye.
Suna rike da jakukkunansu.
Gefen Aysha ya ratsa ya wuce, ya isa gaban ƙofar, hannunshi yasa ya ɗan zuge zip ɗin jakar dake hannunshi key ya zaro.
Kana ya zuge zip ɗin ya rufe.
Cusa key ɗin yayi a ramin kana yayi bismillah tare da murza key ɗin, kat-kat yayi sau uku kana yasa hannunshi ya tura ƙofar sannan ya wuce ciki tare dasa hannunshi ta sama jikin ginin ya kunna wutan falon kana ya juyo ya kallesu tare da cewa.
"Bismillah Ummi shigo".
"To". tace kana ta nuna Aysha hanya alamun tayi gaba.
Kafar dama tasa tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Ba tare da ya juyoba yace.
"Wa laikissalam". Ya amsa sallamar a hankali batama jishi ba.
Ummi na biye da ita a baya suka shigo cikin kekkyawan falonsu da sukayi kewarsa.
Ajiyan zuciya Aysha ta sauƙe tare da cewa.
"Masha Allah komai tsab, Allah sarki HIBBA AZEEMA ina kewarku Safiyyah ina begenki kusa Ayyah my Ishma fuskarki ta tuna min Junainah na, Aunty Rahma ganinki ya tada min begen ganin Ummey na.
Ayyah 40 minutes kawai ya nesantamu Umaymah, Mamma Ina kewarku Ina jinku kamar yadda nake jin Ummey na".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Kinga gama Umaymah na kira".
Ta ƙare mgnar tana amsa kiran.
"Eh Alhamdulillah mun isa lfy gamu nan a tsakiyar falo, ɗiyarki nata kewarsu Hibba da Safiyyah naga harda ƙwalla a idonta".
Ummi ta faɗawa Umaymah cikin kewarta.
Ita kuwa Aysha da sauri tasa hannunta ta shafi haɓarta sai ma lokacin ta gane ashe harda hawaye take zubdawa.
Ita kuwa Umaymah cikin murmushin tace.
"Wallahi gamu muma yau duk sai mukaji babu daɗi Safiyyah tace ita fa da Aysha ta tafi gidan ba daɗi".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Sabo kenan".
"To ku huta gajiya". Umaymah tace kana ta katse kiran.
Ita kuwa Aysha haka nan yau take jin bege da kewar ahlinta ta kasa tsaida hawayenta Especially Ahlin Abboi.
Tana tuno Didenta su Yah Al'ameen da Innayinta.
Bappa'nta Ummeynta, Ya Giɗi, Ya Seyo, Ya Gaini, da Ya Lado.
Shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata ganin yadda hawaye keta shatata a fuskarta babu ƙaƙƙautawa.
Remote ɗin A/C'n dake hannunshi ya meda a masaƙalinshi kana, bakin ƙofar ya koma ya rufe ƙofar kana yazo ya wuce.
Side ɗinsa.
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
"To nan dai Side dinmu Sara ta gyara mana komai amman nasan Side ɗin Sheykh ba a share yakeba, tunda tare muka dawo da Jamil, dan haka tashi kije ki ɗan kimtsa mishi bedroom ɗin".
Miƙewa tayi itama tare da share hawayenta kana a hankali tace.
"Naji kafin jirginmu ya tashi yayi mgn da Affan yana ce mishi ya share mishi ɗakin ya amshi key a wurin Gimbiya Aminatu".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh hakafa ni na mance ai Affan na nan".
Falon Aysha suka nufa, suna shiga kowa ta nufi ɗaukinta.
Ummi Al'wala tayi kana tazo ta kwanta.
Ita kuwa Aysha tana shiga, ta ajiye jakarta gefe kana ta faɗa kan gado ta kwanta a kife, ta kifa kanta bisa pillow kuka mai ƙarfine ya kwabce mata, sabida suya da zafin da zuciyarta keyi na tuno ƴan uwanta da suka ɓace.
Duk da kuma kontar mata hankali da Bappa keyi na cewa anji lbrinsu har an gansu.
Kuka tayi tayi sosai wanda ita kanta bata san tsawon lokacin da tayi tana kukanba.
Sai ƙarfe uku dai-dai ta samu bacci ya saceta.
Shi kuwa Sheykh yana shiga,
yayi ajiyan numfashin sabida ya samu komai tsab-tsab a gyare a killace ko ina na ƙamshi.
Kasan cewar ana zabga zafin da rashin ruwan sama da akayi kwanaki ba'ayi bane yasa, garin ɗinkewa da zafi.
Gudun A/C'n ya ƙara kana ya ajiye jakarshi cikin drower'nshi.
Rage kayan jikinshi yayi kana ya shiga bathroom wonka yayi tare da al'wala sannan ya kimsa cikin tattausan rigan bacci riga da dogon wondo ne.
Yana fitowa ya rage hasken ɗakin kana yazo ya zauna bakin gadon.
Ya buɗe hannunshi ya ɗagasu sama alamun zaiyi addu'o'in kwanciya baccine, kiran Haroon ya shiga wayarsa.
Yasan idan ba ɗagawa yayiba Haroon ba barinshi zaiba, hakane yasa ya amsa kiran da sauri.
"Alhamdulillah mun iso lfy yanzuma bacci zan kwanta".
Ya faɗa da sauri. Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"Ya haka dai malam kamar korata kakeyi, nima sabon ango banma hakaba sai kai tsohon ango, to a huta gajiyar hanya, ni yanzu zan kama hanyar fatauci ne".
Wani gajeren tsaki yaja tare da katse kiran.
Dariya Haroon yayi kana ya jawo hannun Jannart ɗinshi suka nufi ɗauki shi.
Shi kuwa Sheykh addu'a yayi