Showing 261001 words to 264000 words out of 352722 words

Chapter 88 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30747

su Umaymah'n a airport,

Shi kuwa Sheykh a hankali yabi bayan Ummi da ido ganin tashige ɗaki ne da sauri ya juyo.
Jin ta rungumeshi tabaya tasakalo hannun ta a kugun sa tasauke wuyan ta kan kafaɗarsa,
wani sassanyan numfashi yafesar a hankali yaɗaura hannunshi kan nata dake saƙale a gugunsa, tare da fara murza fatar hannun ta,
sai kuma yayi kasa da hannun ta ƙasa kaɗan dai-dai kan jikinsa yaɗaura hannun nata yahaɗa da jikinsa din ya matse wan da tuni yafara motsi Jin abin cinsa kusa da shi.

Sai Kuma yayi saurin ciro hannu nata yaɗan waiga gefe da gefen sa tuno ashefa a babban parlour suke,
Juyo da ita tagaban sa yayi yamannan mata kiss a goshi kana yayi ƙasa da bakin sa dai-dai saitin kunnen ta cikin yin ƙasa da murya yace
"Sheykh fa na fushi kinyi Mlmasa laifi tun shekaran jiya kike gudu nai".
Wani irin yarr taji sigar jikin ta yatashi, saboda kalar tsigar yadda yayi maganar cike da wani irin salo da sai da yasa ta lumshe ido,
Batare da tabuɗe idanunta ba tace
"Kabashi hakuri".
Iska yahura mata cikin kunne kana yace.
"Yaƙi hakura so yake kibashi da kanki".
Ware manyan idanunta tayi kan fuskarsa jin yasauke hannun sa Kan kirjin ta.

Da ɗan sauri tamatsa da baya langwaɓar da kai tayi tace.
"Ummi zata fitofa".
Tayi maganar tana kallon hanyar dakin ta,
Hular kansa yacire yashafa lallausan gashin kansa dake shinfiɗe sai tashi da sassanyan kamshi yake,
Sassayan iska ya ɗan furzar daga bakin sa cikin tsareta da idansa dasuka fara canza kala yace
"Kece ai".
Idon talumshe tare da kuma buɗesu tace
"Da nayi me?".
Hularsa yamaida ya dai-dai-ta zamanta, lumshe mata idanunsa yayi kana yace
"Dakika sokano shi mana".

Murmushi tayi kana tajuya tana faɗin.
"Nidai Babu ruwana".
Tattausan tafin hannunshi yasa ya shafa gefen fuskarsa ya shafa Yana binta da wani irin mayataccen kallo
Har tashige bedroom.
shikuwa ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙw kana ya juya yanufi hanyar fita zuciyar sa cike tab da farin ciki.

Tana shiga bedroom rage kayan jikin ta tafaɗa bathroom wanka tafesa mai rai da lfy kana taɗauro al'wala tafito, lokacin kuma masallacin Jod'a suka kira sallah.

Shin fiɗa sallaya tayi tazura babban hijab tafiskanci al'kebla ta tada sallah,
Tana idar wa tayi duk kanin addu'o'i.
Kana ta miƙe tazo gaban mirror nan tafara lailaye jikin ta da mayukan ta masu sanyin kamshi.

A ɓangaren Sheykh kuwa yana fita direct masallaci yanufa Jamil yarufa masa baya,
Kamar koda yaushe sahun gaba yashiga
Suka gabatar da sallar magriba,
Koda a ka idar a gogo yakalla ganin da ɗan sauran mintuna sai yacigaba da tasbihin sa har lokacin sallar Isha yayi.

Ana idarwa yafito da ɗan sauri,
acikin mota yasami Jamil zaune a mazaunin driver yana zaman jiransa,
Gefen mai zaman banza yabuɗe yashiga yana dai-dai ta zaman sa yakalli tsadadden a gogon dake ɗaure a tsinsiyar hannusa.

"Yisauri mutafi lokaci ya tafi".
Yafaɗa tare da maida idanunsa kan hanya,
"To". Jamil yace kana yywa motar key suka fice cikin masarautar,

Direct airport suka
nufa har acan ciki inda ake isa dan tarban manyan mutane Jamil yayi parking
ganin fasinjoji na fitowa suke hakanne
yatabbatarwa Sheykh jirgin yasauka kafin isowar su,
Dasauri ya buɗe
marfin motar hangosu Umaymah
da yayi sun fito suna gaba
(hadiman) masarautar Jod'a
wad'an da Lamid'o
ne da kansa yaturosu domin tararsu, suna biye
dasu riƙe da jakukkunan su.

Murmushi mai fad'i Umaymah tayi lokacin data hangoshi yana
tahowa garesu Jamil na biye dashi, a baya a haka suka iso garesu, ko wannen su zuciyoyin sa.
Cike da farin ciki fuskokin duk ɗaukeda yelwataccin murmushi
sannu da hanya su Sheykh suka yimusu.
Ishma dake rike hannun Aunty Rahama ne tajanye hannun ta taje ta rungume Sheykh tana faɗin.
"Oyoyo Hamma Jabeer".
Murmushi yayi yana masa hannu kan ta yace "Kunzo lfy ya gajiyar hanya".
Kai ta gyad'a tare da cewa.
"Lfy".,
sai Kuma tasakeshi takoma jikin Jamil tana masa Oyoyo.

Umaymah kuwa cikin tsananin kula ta zuba mishi ido mishi kallon kula duk da al'kyabbar dake jikinsa bai hanata gano ƴar ramar dayayiba


Fuska ɗaukeda murmushi haɗe da ƴar zolaya
Aunty Rahama tace.
"Sannu ɗan al'barka Ina ɗiyar tawa ko ba tare kuka zoba?".

Murmushi Momma tayi ganin yadda Sheykh ya tsare gira wai dan Aunty Rahama tace mishi ɗanta.

Cikin girmamawa ya juya ya kalli Umaymah tare da cewa.
"Mujen ko Umaymah".
Cikin sakin fuska tace to.
Kana suka raka'a suka nufi mota.

Aunty Rahama da Umaymah da Momma Ishma baya suka shiga Jamil na mazaunin driver shikuma yana mazau ninsa naɗazu.
Kayansu Kuma Yana can motar da Lamid'o yaturo domin tararsu,
nan suka nufi masarautar Jod'a.

Shatu tsaye gaban mirror tana feshe jikinta da turare sai wani kyalle da d'aukar Ido take
tsanye take da wani dogon rigar atamfa ɗinkin yazauna ajikin ta yayi ɗamas dashi,
Jin hayaniya cikin parlour yasa ta aje kwalbar turaren tanufi kofa da sauri, tana kutsa kanta cikin parlour'n tahangi su Umaymah da yanzu shigowar su Ummi nayi musu sannu da zuwa.
Cikeda farin ciki da murnar ganinsu takaraso cikin parlour'n da sassarfa ta rungume Umaymah data juyo tana mata murmushi.

Cikin farin ciki da kula Umaymah ta kalleta tare da cewa.
"Kai Masha Allah ɗiyata haka kika zama kincanza sosai, kodai abin da muka dad'e muna hasashen sa ne Allah ya ai komana shi".

Cikin sanani jin kunya tasaki Umaymah tarungume Momma da Aunty Rahama suma rungume ta sukayi suna mai jin sananin kaunarta cikin ransu,
Umaymah kam sosai tabita da kallo tana nazartar yanayin ta na sauyin data gani tattare da ita.

Sakesu tayi tariko hannun Ishma
Tana mai faɗin.
"Oyoyo my Ishma".

Dariya Ishma tayi wan da yasa Shatu zuba mata Ido, ji tayi zuciyar ta naɗan harbawa da sauri-sauri ya ilahi wannan kamar tayi yawa hatta dariyarta iri d'ayane da na Junaina sam ta kasa sabawa da ganin wannan kamacceniyar tasu dake sa ƙirjinta harbawa.
Rass takuma jin kirjinta yabuga jiyo muryar Aunty Rahama lumshe idanunta tayi.
"Yasalam".
Tafurta acikin zuciyar ta, muryar Aunty Rahama Babu banbanci data Ummey'n ta.

Kamshin turarensa ne yasata bud'e idanunta tazubasu kanshi,
Cikin yanayin zazzab'in daya fara rufeshi yakaraso cikin parlourn, al'kyabbar sa yaketa d'an bud'awa yana haɗeshi saboda wani masi faffen sanyin da yake ji,
Direct parlour'n sa yanufa cikin mawuyacin hali kai tsaye bedroom nasa yashiga yafaɗa kan gado.
Yaja blanket yarufe jikinsa duka har kansa, kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa.


Da ido Umaymah ta rakashi har yaɓacewa ganin ta, sosai tayi mamakin ƴarramar da yayi.
Taso ta binshi ɗakinshi to mutanen da suke ta shigowa suna yimusu barka da zuwane ya hanata bin bayanshi.

Bayan ƴan gaishe-gaishe sakanin su sai kuma sukayi salla kana.
Suka hau hira wane kamar waɗanda sukayi shekara cur rabonsu da juna.
Sosai Aunty Juwairiyya tasake cikin su ganin yanda Aysha tasaki jiki da ita, ganin hirar nasu bazata kare nan kusa ba yasa Ummi cewa
"Muje kuci abinci tukun a dawo aciga".
Nan suka mimmiƙe suka nufi dinning area Ishma na makale da Shatu,
Bayan sun gama cin abin cin ne suka kuma dawowa cikin parlour'n sai wajen karfe 12 da Rabi kowa yanufi
makwan cinsa.

Aunty Rahama da Ishma ɗakin Shatu suka shiga,
Anan zasu kwana,
Aunty Juwairiyya tatafi part in ita da Mamma,
Ummi da Umaymah Kuma ɗakin Ummi suka shiga in da nanne da ma masaukin Umaymah.

A hankali Shatu taɗauki Ishma wacce tayi bacci tuntuni tasaɓata a kafaɗa tayi tanufi ɗakin ta da ita a tsakiyar gado ta shimfi ɗata, yazamo tana gaban Aunty Rahama.
Ita Aunty Rahama tana can jikin bango ita kuwa Isham tana tsakiya.
Kyara mata kwanciya tayi taɗan sa pillow ta tokareta dashi tabaya,
Ido Aunty Rahma ta zuba mata ganin yadda taketa yimata komai a sannu kamar jaririyar goye,
Cikin jin sonta tace
"Aysha kenan sai wani lallaɓata kikeyi sai kace wata jaririya".
Murmushi tayi lokacin data gama gyara Mata pillow'n tamike tasauka kasa,
Gyara kwan ciya Aunty Rahama tayi
Kana tace.
"Ai kam saita tasaki ciwon baya tun d'azu tana jikinki tana bacci madadin kitasota da kafarta tazo Amma kika saɓota a kafaɗa.
Ishma kuwa uwar ƴan son jikine in kika bi ta nata kuwa sai ta saki ciwon jiki".

Murmushi takumayi kana tace
"Ai bako mai bazata sani ciwon jiki ba ai batada nauyi".
Tafaɗa tana shigewa bathroom rike da hijab a hannunta.

Tana shiga ta rataye hijab ɗin kana ta tuɓe kayan jikin ta ruwa ta cika cikin bath tashige cikinm
Kana ta ɗauki soso da sabulunta mai matukar kamshi tashiga wanke lungu da sako najikin ta.
Tana gamawa tajanyo towel taɗaura a kirjin ta
Kana taɗau hijab ɗin data tashigo dashi tazura sannan tafito,
Lokacin har bacci yafara ɗaukar Aunty Rahama sai dai tana ɗan jiyo motsin ta sama-sama kasan cewar baccin nata baiyi nisaba.

Gaban mirror tazauna batare da tacire hijab ɗin ba tashafa mai kana tamurza humra ta kowani lungu da sako najikin ta,
Tamike taje tabuɗe wardrobe wata rigar bacci mai santsi kalar pick mai siririn hannu da gidan bra taciro, taɗaki pant Shima kalar rigar,
Bathroom takoma tasaka kayan kana ta maida hijab ɗin ganin rigar da kaɗan ya shige guiwar ta.
A hankali ta fito,
Tazauna bakin gadon ta gaban Isham wacce tuni ta matso bakin gadon. pillow ta gyara tare da kwan ciya ta kasan kusa da Ishma.
Matsawa tayi taɗan daɗa gyara kwan ciyar ta dan tayi baki-bakin gadon da yawa taɗanyi baya da hannunta tana gyara hijabin jikinta, nan hannun ta yaɗan bigi ƙafar Aunty Rahma,
Ita kuwa Aunty Rahma da baccin nata baiyi wani nisaba, buɗe idanu tayi zatonta ma Ishma ce uwar birgimar yakawota kusa da isa da ɗan sauri tamike dan ta tarota kada tafaɗi.
Ido taware cike da mamakin ganin Shatu ce kwance a gun,mussuke Ido tayi cikin muryar bacci tace
"Ke Aysha me kike jira Anan da Baki tafi ɗakin mijin kiba jika kwanta Anan?".

Gyara kwanciya tayi kana tace
"Aunty Rahma anan zan kwana kusa da Ishma na".
Ido Rahma taɗa waro tace.
"A'a Aysha tashi maza kitafi ɗakin mijinki."
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba ganin haka yasa Aunty Rahma fahim tar kunyace ko rashin sabo da zuwa gareshin ke ɗawai niya da ita,
Muskutawa tayi cikin dabara tace
"To ai kinga nan ɗin ma gadon yakasa mana bazai ɗaukemu dukaba ga Ishma da birgima zamu kwana a takure ke kije can.
Kinga den bazamu takuraba maza tashi kinji, ki kula da mijinki kada kiyi yaji haushina yace nina riƙe masa mata, kinga dama ya rainani".
Ta ƙarashe mgnar cikin sigar raha.
"Toh". tace a hankali tamike tasauko daga Kan gadon,
Ita kuwa Aunty Rahma gyara kwanciyarta tayi tace.
"Yauwa in kin fita ki jamana kofar".
Namma to ɗin takuma cewa kana ta fita tare da ja musu kofar.
A hankali tanufi parlour'n shi.


A ɓangaren su Umaymah kuwa suna shiga ɗaki Ummi bathroom tashiga taɗan watsa ruwa dan taji daɗin jikinta, bayan ta fitone tayi shirin bacci Nan ta tadda Ummi harta kwanta Amma batayi bacci ba idonta biyu, Zama tayi bakin gado ta fuskanci Ummi da kyau cikin sauƙe numfashi tace.
"Niko Ummin Jabeer anya ɗiyarnan taki ba cikine gareta ba kuwa?".
Da sauri Ummi ta mike zaune tana cewa
"Kai Anya kuwa?".
Gyara zama da kyau Umaymah tayi tare dayin murmushi tace
"Nikam dai naga kamar akwai abu tattare da ita. Amma dai sai da safe in Allah yakaimu zan ƙara zuba ido in dubata da kyau in ƙoƙƙofo mana".
Ciki da jin daɗi da fatan Allah yasa akwai ɗin Ummi tace.
"Allah yakai mu".
Kana sukaa ta kwanta suna mai fatan hakan yazamo gaskiya.

Shatu kuwa a hankali ta kutsa kanta cikin parlour'n da sallama ɗauke a bakin ta,
Shiru parlour'n babu motsin komai sai karar A/C da wani sassanyan ƙamshin dake tashi.
A hankali tanufi kofar bedroom ɗin shi.
Tura ƙofar tayi a hankali tashiga da sallama kana ta ta mai da kofar tarufe, juyowa tayi cikin ɗan kin cikin nitsuwa da ɗan yanayin bacci.
Can ta hangoshi kan gado.
A dukunkune cikin blanket sai karkarwa yaka.
Cikin sauri haɗida sassarfa tanufi inda yake,
cikin tashin hankali ta hayo kan gadon.
Da sauri tasa hannu tayaye blanket ɗin,
Da sauri ta kuma matsoshi ganin yadda jikinsa yake wani irin karkarwa, cikin sananin tashin hankali da tausayi ganin halin da yake ciki takai hannu saman kafaɗar shi tana faɗin
"Innalillahi Yah Sheykh meya sameka! dama baka da lfy ne!?.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!".
Ta kuma haɗi da karfi lokacin da tasauke hannunta saman kafaɗarsa jin wani irin zafin da jikinsa yayi.
Shi kuwa Sheykh kanshi ya ɗago cikin mawuyacin hali yaɗaura kanshi bisa cinyar ta, cusa kanshi ya farayi cikin jikinta cikin sananin zazzafan zazzaɓin da yarufeshi yace
"Aish sanyi, sanyi nakeji".
Yayi maganar cikin mawuyacin hali yana daɗa cusa kansa cikin jikinta,
Wani irin sahihin runguma tayi mishi gam-gam tana ƙara mannashi da jikin nata.
Da sauri cire hijabin jikinta.
Tare ƙara tallafe kansa tamanna da ƙirjinta ganin Yadda yaketa manna jikinshi da nata yana bin ɗumin jikinta,
Wasu irin hawayene suka fara sassafo Mata
Murya narawa cike da tausaya mishi tace
"Yah Sheykh da ma haka zazzaɓin yake maka?".
Kai kawai ya iya gyaɗa mata alamar Eh
Hannunsa yaɗago da kyar yasauke kan ƙirjinta yacusa cikin bra'n rigar baccin dake jikinta yaciro Cab'b'ulenta duka biyu fuskarsa yacusa sakan kaninsu wani irin numfashi yasauke wanda yasanya Shatu rumtse idanunta jin ɗumin numfashin sa a kirjinta,
Hannunta ta ɗaura kansa a hankali tariƙa shafa sumar kanshi yayin da gudun hawayenta suka d karuwa,
wani irin masifaffen tausayin sane yarufeta,
lamo sukayi a jikin juna. Sun jima sosai a haka.
Kana ta ɗan ronƙofo suka kwanta manne da juna dan ta fahimci ɗumin jikinta yake bi.

Daren ranar dai Shatu taga tashin hankali Danko haka suka kwana basuyi bacci,
Sai can wajen kiran sallar farko zazzab'in yafara tafiya nanne yasamu bacci yaɗan ɗaukeshi.

Nan itama tasamu tad'an gyangyaɗa kaɗan.
Kiran sallar asuba kuwa a kunnen shi.
A hankali ya buɗe idanunshi tare da addu'a a bikinshi,
ido yatsurawa fuskarta ta kanainayeshi tayi lup a jikinsa tana fidda numfashi a hankali,
wani irin tausayinta ne yakamashi, tuno halin suka kwana jiya yadda baiyi bacci ba haka itama bata runtsaba.
Zame jikinsa yayi a hankali ya miƙe zaune.
Numfashin ya ɗan fesar kana ya sauƙo kan gadon.
Cikin lumshe ido ya nufi bathroom.
Yana mai mamakin yadda zazzaɓin nan yasakeshi watsai kamar ba shiba.
Wanka yayi tare da d'auro Al'awala kana yafito.
Farar jallabiya yazura tare da fesa turare mai sanyin ƙashi sannan ya murza hula bisa sumar kanshi.
Kana yaɗan maso bakin gadon da sauri jin ana kokarin tada ikama.
Ragowar ruwan hannunsa ya ɗan shafa nata a fuska tare da cewa.
"Aish tashi kije kiyi sallah".
A hankali tayi miƙa tare da buɗe idanunta kana tace.
"Toh, ya jikin naka?".
Murmushi yayi mai cike da jin daɗi cikin lumshe ido yace.
"Alhamdulillah da sauƙin tashi kiyi salla ko Boɗɗon Ummey".
Miƙewa zaune tayi.
Kana shikuma yafita.

Wayewar garin ranar kuma.
Shatu Ummi Sara suka shirya lafiyayyen breakfast suka jerashi kan dinning area dake cikin babban parlour.
Abinci kuwa takowani sashi yana fitowa zuwa wannan sashi.
Tuni Aunty Juwairiyya ta iso da nata lafiyayyen breakfast ɗin.
Bayan sunyi breakfast suka dawo cikin babban parlour nan suka buɗe sabon hira.

Shatu kuwa tun da sukayi breakfast ɗin takama hannun Ishma suka koma ɗakinta, wanka tayi sannan tayiwa Ishma.

Bayan tafiyar ta ba jimawa Sheykh yashigo parlour'n.
Cike da jin daɗin ganin ƙannen mahaifiyar tasu da aminta ciyar Jakadiyarsu mai kamar uwa.
Ya isa tsakiyar.
Suma cike da jin daɗi suke kallonshi.
A hankalu ya zauna kan kujerar dake fuskantar Umaymah.
Yayi wasai da shi kamar bashine jiya ya kwana da zazzafan zazzaɓi ba.

Hira sosai suka buɗe sunayi ana dariya da raha.
Shi kuwa Sheykh murmushi yake ɗanyi kanshi a sunkuye kan wayarsa da yake ɗan lasawa.
Umaymah kuwa gaba ɗaya ta maida hankalin ta kanshi, sosai hankalin ta yatashi dan yau tafi ganin ramar tasa da yawa fiye da jiya,
cike da kulawa ta tsare fuskarsa da ido tare da cewa.
"Jazlaan."
A hankali ya ɗago kwayar idanunshi ya kalleta cikin maida hankalinshi kanta yace.
"Na'am Umaymah".
Gyara zamanta tayi ta fuskanceshi da kyau cikin sanyi tace.
"Jazlaan meke damun ka baka da lfy ne wannan ramar duka ta mecece?".
Tajero mashi tambayoyin cikin alamun tashin hankalin.
Mamma da Ummi da Aunty Rahma da Juwairiyya kuwa shiru sukayi suna kallonsu.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya ɗan sa hannunshi ya shafi sajenshi.
Wayar hannun sa ya ajiye bisa hannun kujera da yake zaune.
Ɗan gyara zamanshi yayi tare da gyara zaman al'kebbar jikin sa,
kansa ya ɗan tankwasa gefe a hankali yace.
"Umaymah zazzaɓin dare ne yake damuna kullum , da rana kuma zan wuni lfy, da zaran yamma tayi sai zazzaɓin ya rufeni haka zan kwana da shi asuba nayi kuma zai tafi sai wani daren kuma".
Shiru sukayi baki ɗayansu.
Ita kuwa Umaymah hannunta tasa ta tallabe haɓarta.
Numfashi mai sanyi Umaymahn ta fesar tanamai nazartan kalaman sa wani irin yalwataccen murmushi mai faɗi Umaymah tayi.
Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito daga ɗakinta ta nufosu.
Suma su Mamma duk murmushi sukayi.
Murmushi Mai had'e da dariya Umaymah tayi cike da tsantsar jin daɗi
tace.
"Toh Jazlaan ina ga dai ka gaji Abba'n kune fa".

Da sauri ya kalleta tare da cewa.
"Kamar yaya Umaymah da me na ganeshi?".
Cikin sauri ya juyo ya kalli Ummi da Mamma dake cewa.
"Ai kuwa da ala kam tabbas".
Aunty Rahma da Juwairiyya kuwa dariyar jin daɗi sukayi.
Shi kuwa Umaymah ya zubawa ido tare da cewa.
"Ban ganeba?".
Cikin sakin fuska tace.
"Eh inaga kam tabbas kayi gado.
Domin tunda Mamey take Bata taɓa yin laulayin cikiba, a rayuwarta, ko su Jalal da suke tagwaye wlh Abbanku ne keyi mata laulayin, shiyasa kafin ma tasan tanada ciki shi yake rigata ganewa.
Toh inaga kaima hakan ne tabbas Shatu nada ciki ni dama na zargi hakan tun isewarmu".
Cikin tsananin jin kunya, Shatu tajuya da sauri ta koma dakinta cikin wani irin masifaffen jin kunya meda ƙofar ɗakin ta rufe.
Bayan ta sukabi da kallo.
cikin wani irin.

Shi kuwa Yah Sheykh wani irin yalwataccen murmushi mai cike da mashahurin farin ciki wan da yakasa ɓoyuwa bisa fuskarsa sai da ya bayyana kan fuskar shi cikin tsanani jin daɗi da tarin farin ciki, ya kuma faɗaɗa murmushin sa tare da cewa.
"Allah ko Umaymah tana da ciki ko".
Cikin jin daɗi tace.
"Tabbas kuwa Jazlaan".
Kanshi ya rausayar tare da lumshe ido cikin jin zallan farin ciki yace.
"Ai dama nafaɗa mata, amman sai taƙi yarda tace allanfie wai ita bata da ciki.
Toh kuma naga alama da idona ko jiya saida mukayi mgnar.
Cikin wasa
Aunty Rahama tace.
"To fa ikon Allah ah lallai jika yakusa zuwa".
Murmushi mai cike da yalwa yayi tare da cewa.
"A nan kusa ma kuwa ƙamar uwa zatayi jika."
Momma Kam bakinta ya kasa rufuwa dan sabar farin ciki,
Ummi kuwa hamdala tashiga yiwa ubangijin talikai.
Shima kuwa Sheykh sai.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Yaketa mai-mai-tawa
Tare da miƙewa ya koma falonshi yana shiga ya fuskanci al'ƙibila


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login