Showing 258001 words to 261000 words out of 352722 words
a ƙiyayyar da dalilin zaɓin tambarine".
Cike da kaɗuwa Aysha tace.
"Menene zaɓin tambarin?".
Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace.
"Bisa al'adar masarautun gargajiya na Hausa Fulani, dole har kwanan gobe suna da al'adu ko wacce masarauta da al'adarta, sai dai mafiya yawan masarautun al'adar tambarin ɗaya ce.
In kinji ance tambari wani kayan kiɗane da babu shi a ko ina sai gijen manyan masarautu. A bisa al'adar masarautar Joɗa bawai sarkine ke ko mutanen gari kance wane ne zai gaji sarauta ko wanene zaiyi mikinba. Duk ranar bikin salla ana fito da kakaki da al'gaita mabusar masarauta da kuma tambari a ajiye a tsakiyar faɗa, gaban sarki. Kana duk ƴaƴan sarki da jikokinsa da makusantasa maza, zasu hallara a fada, inda kowa zaije gaban sarki ya gaishesa, to muddin akwai nasibin gadar sarauta, a jikin mutun kana isa gaban sarki, kakaki da al'gaita nan zasu fara bisa kansu da kansu.
In kuma kaine zaka gaji mulki daga hannun shi wannan sarkin na wannan lokaci to tambarin masarautar zaiyi ta kaɗa kanshi da kashi,. Duk sanda ka isa kusa dashi, in ka wuce zai bari in ka dawo zaici gaba da yi.
Wannan al'adace tun ta zamanin jahiliya, kuma har yanzu wasu masarautun sunayi, to Amman masarautar Joɗa tun a kan Sheykh aka bar wannan al'adar tun yanada shekara uku a duniya, da akaje fada gaisuwar salla da yazo gaban Lamiɗo sai tambari yayi ta kaɗa kanshi kana kakaki da al'gaita sukayi ta busa kansu.
Tofa wannan shine musabbabin ƙiyayyar da yake fuskanta har ya shafi mahaifiyarshi mahaifinshi yayanshi da ƙannenshi, sabida duk mutanen masarauta sun gani a gabansu abin ya faru".
Ɗan tsagaitawa tayi kana a hankali tace.
"Kinji amsar tambayoyinka duka".
Da sauri Ummi ta kalli Aysha jin ta jefo mata tammayar.
"Ummi Waye Mamansu Yah Sheykh ina Mamansu Yah Sheykh meya sameta".
Jikin sauri Ummi ta miƙe tare da cewa.
"Hajia Mama ce".
Da sauri Aysha tace.
"Kiyi haƙuri Ummi ki gaya min gsky".
Juyawa Ummi tayi ta nufi falonsu tare da cewa.
"Je ki tambayi mijinki shi yafi cancanta ki tambaya bani ba".
Tana faɗin haka ta wuce ɗakinta.
Jiki a mace Aysha ta miƙa ta nufi ɗakinta cikin tsananin gaskata tunaninta na ba Hajia Mamace mahaifiyarsu Yah Sheykh ba.
Kai tsaye Bathroom ta shige,
Brosh tayi sannan tayi wonka da ruwan ɗumi sosai, kana tayi al'wala.
Tana fitowa ta shafa mai tare da shefe jikinta da humranta mai ɗan karen sanyi da daɗin shaƙa.
Wata tattausar rigar bacci wacce iya karta cinya ta saka tare da pant ɗinta da hularta, rigar pink guava color cr mak taushi.
A hankali tayi hamma tare da salati, ba tare daya kashe wutan ɗakinba ta juya ta hau kan gadonta ta kwanta ta bawa kofar shigowa tasa hannunta zata jawo blanket kenan taji wayarta na ringing da sauri tasa hannu ta ɗauka ganin Rafi'a ce, haka yasa bata rufe jikin nataba.
Murmushi Rafi'a tayi tare da cewa.
"Ina son kiranki Ina jin tsoro kada oga yana kusa".
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
"To baya kusa, muyi hirarmu".
Cikin shaƙuwarsu Rafi'a tace.
"A a kai ba wata hira zamuyi ba, zan dai gaya miki cewa, gwamnatin tarayya ta nemi malaman jami'o'i da su zauna wata ƙil zasu sasanta mu koma makaranta".
Cikin jin daɗi tace.
"Kai Alhamdulillah Allah yasa a sasanta nima gobe zan kira Umaymah in gaya mata".
Cikin sauri Rafi'a tace.
"Allah ya kaimu, Ni saida safe tashi ki tafi wurin mijinki".
Da sauri tace.
"Ke da Allah baya nanne tsaya muyi hirarmu".
Cikin wasa Rafi'a tace.
"To da sauƙi tsoro nake kar in shiga lokacin sa ai".
Dariya tayi kana sukaci gaba da hira.
Shi kuwa Yah Sheykh ya kasa zaune ya kasa tsaye, yanzu karo na biyu kenan ya shiga Bathroom ya watsa ruwan sanyi.
Sabida a zatonshi ko har yanzu suna falo da Ummi sabida ya leƙa ɗazu ya gansu duk da baijin me suke cewaba.
Yana watsa ruwan ya fito jikinsa ya ɗan tsane kana ya shafa OudKareem dake cikin saman dreesing mirror'n.
Wasu riga da wondo masu taushi red color and white
yasa wondon iya guiwa ne rigar kuma mai guntun hannune sai dai tana da hula rigar.
sa hular yayi a kanshi, kana ya feffesa turaren.
A hankali ya ya kuma fitowa ganin sun hada ido da Ummi wacce lokacin ne ta miƙa zata tafi.
da sauri ya ɗan wayance ya koma falo yana jin kasala, da sha'awa, zama ya yi kan kujera, ya jingina da ita tare da lumshe ido, hancinsa na zuko masa ƙamshin ƙasa mai daɗi, kunnensa na jiyo sautin kukan tsuntsaye mai daɗi, yanayin ya ƙara sakar masa da jiki kasala mai ƙarfi ta rufeshi wannen yasa bai sake leƙawaba, har suka watse, har yaje tai wonka.
Ido a lumsh miƙe da sauri.
Ƙarfe ɗaya na dare dai-dai agogon wayarshi ta nuna mishi.
Hannunshi na hagu yasa ya damƙi kan Jabeer ɗin sa daketa harbawa, da miƙewa tsaye.
"Hehyyyyyy". Ya fidda wani wani dogon sauti tare da komawa zaune yana taune lips ɗinsa ido ya zubawa Jabeer ɗin nasa data miƙe tayi sama ba alamun sassauci.
Don izuwa yanzu ya fara jin mararsa ta yi nauyi, cikin tafiya da sassarfa, ya fito falon wani dogon ajiyan zuciya ya sauƙe ganin basa nan kuma ko ina shiru alamun sunayi bacci.
Da sauri yaje ya rufe kofar babban falon tare da addu'a, kana ya kashe duk kayan wutan falon, ya wuce falon Aysha.
A hankali yake taku wai sabida kada Ummi ta jishi.
Saɗab-saɗab yake ɗaya ƙafafushi.
Har ya isa kofar bedroom ɗin Aysha, hannunshi yasa a hankali ya murɗa handil ɗin, ajiyan zuciya ya kuma sauƙewa jin ɗakin a buɗe ne.
Ga kuma wani masifeffen ƙamshi daya shaƙa.
Ƙamshin turaren da take amfani da shi idan zata kwanta, ƙamshin ya kara hautsuna masa tunani.
Can ya hangota bisa gadon, tana riƙe da waya ta bawa kofar shigowa baya,
sai dariya takeyi, sam bataji motsin buɗe ƙofar ba bare shigowarsa.
Cibiyoyin ta ya zubawa ido sabida a bayyane suke a fili.
Dogon numfashi yana tare da ƙarasawa kusa da ita a hankali, ya hau bisa gadon tare dasa hannun sa ya rug......
By
*GARKUWAR FULANI*
: Cikin wani irin tarin farin ciki mai wuyar misaltuwa jiki na kermam farin ciki da annashuwa ya jawota ta faɗa jikinshi.
Ture system ɗinshi dake gabanshi yayi ya ruggumeta tsam cikin jikinshi wasu irin hawayen farin ciki ne suka zubo mishi tamkar ƙaramin yaro.
Sai ya kuma ɗago kanta cikin tsoro da mamakin ganin hawaye na kwaranyo mishi murya na rawa tace.
"Innalillahi Yah Sheykh me nayi maka".
Da sauri ya kuma ruggumeta gam-gam cikin wani irin tsantsar farin ciki murya na rawa yace.
"Alhamdulillah Aish, Alhamdulillah meyasa baki gaya minba, kina da cikiba, meyasa zaki ɓoye min wannan abin farin cikin?".
Cikin wani irin yanayi ta faɗa jikinshi ta rungume gam a jikinta murya can ƙasa tace.
"Ciki kuma Yah Sheykh?".
Da sauri yace.
"Yes ciki mana Aish".
Da sauri tace.
"A a ni kam bani da wani ciki bayan na cin abinci".
Da sauri ya ɗagota har lau hawayen farin ciki na zubo mishi babu ƙaƙƙautawa cikin ruɗani yace.
"No kada kice min haka. Kada ki cemin baki da ciki ga nan alamomi duk sun baiyana.
Kina da cikina mana Aish, ya zaki cemin baki da ciki".
Cikin tura baki da son ɓoye mishi batun tana da cikin tace.
"Ni dai bani da ciki".
A kiɗime ya miƙe tsaye, tare da cewa.
"Ok tashi, tashi mu tafi Valli muje in duba".
Da sauri ta maƙe kafaɗarta tare da cewa.
"Ni dai bani da ciki".
Ta ƙarashe mgnar tana sa hannunta cikin boxes ɗin sa.
da sauri yace.
"Ni kada ki cemin haka muje in gwada in ga Zahiri".
Da sauri ya dawo ya zauna jin yadda take mishi wani salo.
Murya a mace tace.
"Sai dai in yanzu zaka bani cikin".
Ta ƙarashe mgnar da sigar yaudara da mantar dashi batun cikin da tasan yanzu watanninsa biyu harda kwanaki, a jikinta.
Ruggume ta yayi da ƙarfi tare da cewa.
"Tun tuni ai na baki ciki Aish, wlh kina da ciki.
Ya za'ayi ina Dr ki musa min".
Bakinsu ta haɗe wuri ɗaya tare da fara mishi wasu abubuwan da dole ya haɗiye regowar mgnarshi.
Yayinda zuciyarshi ke cike fal da farin ciki.
Kiran sallan la'asar ne yasa suka sahirtawa juna.
Ganin lokacin sallan yayine yasashi yin wanka a gaggauce ya tafi masallaci.
Ita kuwa Shatu.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da sa hannunta ta shafa ɗan lafeffen cikinta.
Lokacin da take wonka.
murmushi tayi tare da cewa.
"Abbanka yana cikin tarin farin cikin gano alamun kana jikina, duk da ɓoye mishi da nakeyi.
sabida ina gudun kada ya gaza ɓoye farin cikin sa har magautansa su gano da kai su rabani da kai."
Sai kuma ta lumshe idonta.
Tana ganin yadda jikin Sheykh yayita rawa yana fidda hawayen dake bayyana tsantsar jin daɗinsa ziryan.
A hankali tace.
"Abbanka yana sonka so mai tarin yawa, wanda har ya kaishi da zubda hawaye.
Ina sonka so mai yawa wanda ya zame min dole in sirrantaka, dan ɗanyen mamlngoro buya yake sai ya nuna ya baiyana. Ina soron magautan Abbanka su dawo gareka".
A haka tana surutai taje tayi salla.
Tana idarwa tajoshi a falo yana cewa Ummi.
"Ummi ina Aish?".
"Tana ɗakinta, tana salla".
Ta bashi amsa,
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
"In ta idar tazo".
Yana faɗin haka yayi cikin falonshi.
Ita kuma Ummi to tace kana ta shigo ta gayawa A'isha.
Ita kuwa to kawai tace tana fita.
Ta nufi sashin Aunty Juwairiyya sabida tasan in taje mgnar su tafi asibiti zai mata.
A falo ta samu Aunty Juwairiyya gefenta ta zauna.
Hannun tasa ta kamo hannun Mimi ɗiyar Aunty Juwairiyya kana a hankali tace.
"Yah Jafar fa".
Cike da mamakin sauyawar da Aishan tayi mata a ya kwanakin nan tace.
"Bai dawo masallaci ba".
Kai ta jinjina kana a hankali ta juyo ta kalli Aunty Juwairiyya cikin sanyi tace.
"Dan Allah Aunty Juwairiyya kiyi haƙuri da wasu abubuwan dake faruwa a wasu ma banbanta lokuta.
Abune da dole ya faru tunda ban san gaibuba bare in banbane abunda ke ɓoye, sai iya abinda Allah yaso in sani ya sanar dani ya nuna min cikin hikimarsa".
Cikin sanyi da rauni Aunty Juwairiyya tace.
"Uhummm Shatu kenan ba komai.".
Tayi mgnar hawaye na zubo mata.
Da sauri Shatu tace.
"Dan Allah kiyi haƙuri".
Kai ta jinjina hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Nayi kuka a lokuta da dama, na rasa wa zan gayawa damuwata ya fahimceni, kin nuna kina zargin zan cutar dake da kuma ƴan uwana.
Mahayarfiyarsu Yah Jafar da mahaifina uwa ɗaya uba daya suke.
Bani da kowa sama dasu a Masarautar Joɗa, sune ƴan uwana sune farin cikina rana ɗaya na fahimci kina zargin zan cutar dasu nayi kuka mai ƙuna a raina naji tsoron in gayawa Umaymah kada itama ta zargeni.
Ta yaya zanyi haka, ƴan uwana na jinina.
Ta ya zan cutar dasu.
Bayan tarin son da nakewa Yah Jafar wanda yasa duk da halin da yake ciki a haka na dage akayi mana aure wanda a lokacin su Sitti sun so a fasa aurena dashi.
Ina son Sheykh a raina tamkar yadda nake son Ibrahim ɗin mu".
Sosai take kuka alamun ƙuna a ranta.
Cikin sanyi da zubda hawaye Shatu ta riƙo hannunta a hankali tace.
"Aunty Juwairiyya, akwai dalilin nuna rashin yardarta.
Amman yanzu na gano ta ina matsalar take.
Ina neman al'farmar ki sallami Huwaila mai tayaki aiki.
tana cutar dake da yaranki da ingiza cutar Yah Jafar ita ke ƙara sa mishi abinda ke hanashi mgn, nanma Allah yayi yana yawan zama da al'wala da yawan karatu.
Ba dan hakaba da tuni sun kaudashi a masarautar Joɗa sun medashi kan juji.
Ki kuma kula kisa lura.
In babu halin ki sallameta kuma to ki cireta a masu tayaki aikin girki".
Cike da mamaki da tsoro Aunty Juwairiyya tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Cikin nitsuwa.
"Tace no kada ki tada anhlalinki ki lura zaki gane abinda nake nufi.
Kiyi kwana bakwai kacal ba tare da kin bawa Yah Jafar abinci da Huwaila ke dafawa ba, zakisha mamaki".
Cikin gamsuwa da shawarar Shatu tace.
"In sha Allah kuwa zan gwada da izinin ubangiji".
Daga nan sukaci gaba da hirarsu.
Yah Sheykh kuwa jin shiru-shiru bata zo bane.
Yasa ya fito.
Ya tambayi Ummi da ita kuma a zatonta suna can tare.
Ganin bata ɗakinta ne Ummi ta kirata a waya.
Cikin murmushi tace.
"Ummi ina wurin Aunty Juwairiyya ne".
Jin hakane yasa Sheykh yace.
Ba matsala a barta.
Daga nan ya juya ya fita, kai tsaye gidan Malam Abubakar ya nufa.
Inda suka ƙara tattauna batun Sulaiman.
Ita kuwa Shatu tun jiyan gudunshi takeyi.
Wayewar garin yau kuma sun tashi da aiyukan tarban su Umaymah.
Shi kuwa Sheykh wunin yau duk yana tare da Lamiɗo da Galadima suna tattauna wa.
A ɓangaren su
Aysha ƙarfe 3 suka shiga kitchen
girki na musamman suka fara ƙoƙarin shiryawa baƙin nasu,
Cikin kula Ummi ta kalli Sara da yanzu shigowar ta tace
"Yauwa Sara ƙaraso ki yankamin waɗan nan".
Tafaɗi tana nuna Mata Karas da green beans da kabejin data rigada ta wankesu ta tsane cikin kwando
"To". Sara tace tare da karasowa tad'au wuka ta fara yankan kamar yadda aka umurceta.
Shatu kuwa gaban tukunyar data ɗaura.
Kan gas taje tabuɗe tuni shin kafar da tazuba ciki yatafasu yadda take so irin tafsaa ɗaya zuwa uku'nna,
sauƙewa tayi kana tatsaneshi cikin kwando,
Wata tukunyar ta ɗaura tasulala Mai a ciki tare da wasa yankakken al'basa a ciki
Al'basar tana soyuwa Ummi tamiƙo mata jajjagegen kayan miyar da ta jajjaga bawani mai yawa bane tazuba cikin man,
shin kafar data tsane ta ɗauko tarika zubawa cikin man tana mosawa sai da tajuyeshi Kaf, kana takalli Ummi tace
"Ummi karasa wanna". Tafaɗa tare da Mika Mata ludayin dake hannunta wanda take motsa shinkafar dashi,
amsa Ummi tayi ita kuma tamatsa can gefe.
Ɗan ma dai-dai-cin roba taɗauka ta nufi in da fridge yake tabuɗe taɗebi hanta mai yawa sai jan nama ɗan dai-dai.
Wanke hantar da naman da taɗebo cikin roban tayi tazubashi cikin tukunya kana ta kunna wuta,
Citta da kanumfari da tafarnuwa tazuba a ciki sannan tazuba thym da curry da Maggi sai ɗan gishiri ɗan dai-dai, kana ta ɗauki al'basa ta yankashi mai ɗan yawa
ta wasa a ciki kana ta rufe tukunyar.
Attaruhu da al'basa ta ɗiba tawanke ta jajjagasu.
Tuni Naman ya dahu har ruwan cikin sa ya kafe yayi dai-dai yadda takeso
Sai wani tashin daddaɗan kamshi na namusamman yake,
A nitse tasauke tukunyar taɗan barshi yahuce,
Sannan taraba hantar da Jan namar ko wanne tacire shi daban,
hantar tajuye cikin madaki ta dakeshi yaɗanyi laushi, kana tazuba cikin wani roba Mai d'an faɗi.
Attahuru da albasan da ta jajjaga tazuba cikin dakekkeyer hantarna, sannan tafasa kwai guda15 takaɗa tajuye ciki,
tazuba curry da Maggi da gishiri daɗan garin citta kad'an tayanka al'basa tazuba ta ɗibi Karas acikin wan da Sara ta yanka ta haɗa da ɗan
Ƴaƴan green beans tazuba ciki,
kana ta ɗan zuba mai me ɗan yawa ba sosai ba
sokokim naman nan ta yayyanka shi kanana tatajuye ciki, motsashi tayi sosai, kana taɗaki laida tafara ƙullawa.
Matsowa kusa da ita Sara tayi kasan cewar tagama aikin da Ummi tasa ta,
idan Shatu tazuba haɗin cikin laida saita amsa ta ƙulla, a haka har suka gama ƙullashi kamar ƙullin alale,
A tukunya tajuye
Tazuba ruwa taɗaura kan wuta.
Ummi kuwa tuni tagama shirya lafiyayyen Friend Rice wan da yaji wadataccen nama da sauran kayan haɗi.
Wani haɗɗen foodflaks mai kyan gaske mai ɗan girma Ummi ta ɗauka tazuba a bincin, kana taɗau wata karamar kula tazuba ragowar abincin a ciki.
Shatu kuwa matsowa tayi jikin tukunyar ganin yanda yataso, har yana ɗaga murfin tukunyar murmushi tayi lokacin data buɗe murfin ganin Yadda yahaɗa jikin sa yayi wani tip-tip dashi gwanin sha'awa,
Laida ɗaya taciro taɗaki plate tasa a ciki kana ta yaga laidar da fork sabo da tirriin da yake bazata iya sa hannunta cikiba,
Wani hamshakin kamshine yabigi hancinta nan take kamshin yagauraye ilahirin cikin kitchen ɗin, kamshin ta zuko tare da lumshe idanunta kana
tayan koshi takai baki Kai ta gyad'a alamar gamsuwa,
Murmushi Ummi tayi kana tamasota ganin yanda take gyaɗa kai har tana wani lumshe idanu,
Murmushi tayi tare da cewa.
"To zauna kici Mana Aysha da ma ai bakici wani abun kirkiba tun safiya".
Idanunta tabuɗe tare da faɗin
"Mugama tukun zamuci da su Umaymah nasan ma yanzu haka suna can suna shiri ".
Ta ƙarshe mgnar tana sauƙe tukunyar.
Wata haɗeɗɗiyar kula Ummi tamiko mata nan suka fara cire haɗin hanta da nama da kwan nan wanda yajuye yadawo alale suka rinƙa cireshi cikin laidar suna sakawa cikin kula,
Sara kuwa in da suka ɓata tafara tsaftacewa, suna gama cirewa Shatu tamaida kular gefe batare da ta rufe kular ba,sotake yaɗan huce kafin ta rufeshi dan kada zufa ya ɓatashi.
Karfe shida da Rabi suka gama shirya komai kan dinning area.
Jamil ne yashigo cikin parlour'n daɗan sauri kallon Shatu dake tsaye saman dinning area tana gyara zaman kayakin dasuke kai yayi.
Tare da cewa.
"Aunty Shatu wanna kamshin fa yau kuma me a kayi mana wata ƙil dai yau da naman ɗawisu a ka haɗa girkin nan ko?".
Murmushi Ummi dake tsaye cikin parlour'n tayi
Kana tace,
"Kai Jamil tun bakaci ba har kafara sanni".
Cikin yin kasa da murya yace
"Allah dai yasa yau bason kai za akuma nuna mana ba, shi kibashi mai daɗi mu a barmu da na tsakar gida, nidai ko kaɗan ne a ɗibamin a cikin na Hamma Jabeer in dan..."
Saurin haɗeye sauran ragowar maganar yayi, ganin Sheykh yafito daga parlour'n sa, yanufo parlour'n cikin shigarsa ta Kamala kamar na yau da kullum sai baza kamshi yake.
Aysha ko murmushi tabi Jamil da shi ganin yanda ya rusunar da kai kamar bashinr yayi maganar ba,
Karasowa yayi inda Jamil ke tsaye a hankali yaɗan talli ƙeyarsa kana yace
"Wuce muje magananne kawai".
Hannu yakai bayan keyar nasa in da Sheykh yaɗan talleshi ya ɗan sosa wurin yace.
"Afwan Hamma Sheykh".
Shiko kuwa Yah Shekara wani irin juya kwayar idanunsa yayi yanayiwa Shatun sa kallon kasa-kasa wani irin mayataccen kallo yake binta dashi takasan ido.
Da sauri ya janye idonshi ya juyo jin Ummi nacewa
"Am Sheykh fita zakuyi ne?".
Kai ya gyaɗa kana yace
"Eh Ummi zamuje ɗauko su Umaymah ne".
Kai Ummi ta jinjina cike da farin ciki tace.
"Masha Allah Allah ya iso dasu lfy".
"Amin Amin". yace.
Shatu kuwa da sauri ta
sauko daga saman dinning area da farin cikin jin sa sun kusa su iso.
Ita kuwa Ummi cikin yanayi gajiya tajuya tashige ɗaki.
Dan so taje taɗan watsa ruwa kafin su iso,
Jamil kuwa tuni yafita Yana can waje yana jiran Hamman nashi dan tare zasu tafi tarar