Showing 321001 words to 324000 words out of 352722 words
ayar tambaya a kanta.
itako ganin bawai magana Jafar ɗin keyiba sai bata damuba bata kuma fahimci cewa sun zargi meyafaru ba kuma basu gane me. Jafar ɗin yake cewa ba da hakan ba.
Hajia mama kuwa cikeda da karfin hali irin nata na makiran mugaye mata tafara tafa hannu tana masar kwalla tana faɗin
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Jafar me nake gani haka me yasami Mamey'n ku? kayi magana mana".
Sai kuma tasaki kuka mai haɗe da salati.
Lamiɗo ne yaɗanyi gyaran murya ganin Mamey'n tafara motsawa alamar tafarka daga nannauyan Baccin da take mikewa tayi zaune tare da zuba musu ido.
Da sauri suka ɗan matso gareta kana duk suka mai da hankalin su kanta.
Suna ce mata sannu Aisha, Amman shiru ba amsa.
Cikin tsananin sauri da tsoro Abba ya matso kusa da ita tare da zubawa yatsun kafarta ido mamaki cike da kiɗima yake kallon yatsun kafarta da suka fara sauya kamannin halitta suka koma kamar na tsuntsu.
Cike da alhini suma su Lamiɗo suke kallon yatsun kafar nata, hankali a tashe.
Cikin gigita Abba ya kamo hannunta tare da nunawa Lamiɗo murya a daburce yace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Lamiɗo kalli yatsunta".
wani matsanancin tashin hankalin ne yakuma dabaibayesu lokacin da suka ga yatsun hannunta yafara komawa irinna fiffiken tsuntsu.
Gaba ki ɗaya su haɗa baki sukayi wajan furta "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un hasbullahu wani'imalwakin". Sabida tsananin firgici da tashin hankali gaba ɗaya jikinsu rawa yakeyi.
Cikin matsanan cin tashin hankali Lamiɗo da cushewar tunani Lamiɗo ya juyo ya kalli Galadima murya a hargitse yace.
"Subahanallahi maza a kira Malam Musa yanzu nan".
Cikin hanzari Galadima ya amsa da. "To". Kana yajuya da sauri yafita.
Kan kace me labari yabaza masarautar Joɗo,
Batare da bata lokaci ba sakon kiran da Lamiɗo yayiwa Malam Musa ya isa gareshi.
Cikin ƴan daƙiƙu malam Musa ya iso cikin masarautar Joɗa Lamiɗo yabada umurnin a shigo dashi har cikin ɗakin Mamey.
Yana shiga kallonta malam Musa yayi cikin tashin hankali ya girgizata kai kana yakallesu Lamiɗo yace.
"Sihirine a kamata mai haɗe da tsafi kuma daga yanzu zuwa ko yaushe ko wanne lokacin zata iya juyewa daga mutun ta dawo tsunsuwa".
Salati suka ɗauka baki ɗayansu nan kuma ɗakin yakacame da koke-koke su Jamil da Jalal Affan Ummi Jafar yayin da duk muryar Hajia Mama yafi amo wajen kuka da shiga tashin hankali ziraran miraran.
(uhum makircin mugu kenan.)
(Sai daifa akwai kishiyoyi na gari da matsalar kishiya kan sasu kukan gaske wlh.)
Ranar kuwa wannan masarautar taga tashin hankali mara misaltuwa,
Jiƙe-jiƙe da hayaƙi da shafe-shafen magungun gargajiya babu wanda malam Musa baiba, kiɗima yasa sun mance da suyi amfanin da ayatul shifa.
Ganin anyi duk abinda za'ayi na gargaji abin yaci tura ne yasa hankalin.
Dr Aliyu yakasa ƙwanciya gani yake ko wata cutarce ta da ban haka yasa ya fitadaga ɗakin yatafi part ɗin sa,
kiran wasu manyan likitoci a bokansa.
Yasanar musu koda wani shawarin da zasu basu bayan sun gama wayar kuwa.
Kayan ai kinsa ya ɗauko yakomo ɗakin Mamey'n yayi iya gwaje-gwajen sa babu abinda ya gane na wani cuta ko wani abu.
Cikin takaici Malam Musa yace.
"Kama bar gwada ta babu wani cuta face sihiri".
Daga karshe dai dole ya hakura.
Ranar babu wanda ya rumtsa kusan a tsaye suka kwana nan cikin ɗakin Mamey'n ganin yadda gaba ɗaya kamannin halittarta ke juyewa, Gimbiya Aminatu tayi kuka iya kuka.
Lamiɗo ya kira Jadda ya sanar mishi halin da ake ciki tashin hankali iya tashin hankali Jadda da Sitti sun shigeshi nan suka fara shirin tahowa.
Can gabanin kiran sallar asuba lamari ya ƙara munana dan a lokacin suffar Mamey ta gama juyewa izuwa na tsunsuwar Boleru a gabana a gabansu Lamiɗo a gaban mafiya yawan al'ummar Masarautar Joɗa.
nan take kuwa Abba ya yanke jiki yafaɗi yasuma.
Cikin kiɗima Dr Aliyu yayi kansa yafara bashi taimakon gaggawa.
Mamey kuwa da yanzu takoma tsuntsuwa fara kaɗa fiffikenta tayi alamun son tashi take.
Ai kuwa tamkar al'mara sai gashi ta tashi firr ta fire tabi ta window dake a buɗe tayi tacikin Garden tashige cikin tawagarsa tsuntsayen dake wurin.
Innalillahi Jamil Jalal kuwa suma sumewa sukayi.
Cikin hanzari da kiɗima Lamiɗo da Galadima suka zo jikin window nan suka hango ta ta sauka cikin tsuntsayen kawai sai suka fashe da kukan tsoron al'amarin duniya.
Wani irin kuka Hajia Mama tasaka tana faɗin "wayyo Allah na waishin meke faruwa damune kam".
sai kawai ta yanke jiki tafaɗi ta kakkafe idanunta kamar wacce ta suma.
Ranar Hajia Mama haka tawuni tana kuka ta rungume Jamil da Jalal dasuke keta kuka kamar ransu zai fita.
Jadda da Sitti da Umaymah da Aunty Juwairiyya da babanta duk a ranar sukazo.
An kamo tsuntsuwar Boleru suna killaceta, yayinda aketa tururuwan zuwa ganin tsuntsuwar.
Ido da ido da Gimbiya Saudatu tazo da yake sokuwace.
Sai cewa tayi.
"Allah sarki wato al'haƙi kuikuyo ko sharrinta ya dawo kanta, ohoho larabawa an zama tsuntsuwar Boleru".
Toh fa daga nanne Magautan su Sheykh duk suka samu suka fake suka laɓe a bayanta.
Su kuwa haka sukaci gaba da kukan Hajia Mama ko uwartace ta mutu sai haka, duk wanda yaganta sai ta bashi tausayi akasin Lamiɗo da Galadima da suka sa zargi a kanta duk abin da take shirine da zallar iya tuggu munafurci da makirci.
Tun daga lokacin tsuntsuwar nan ko ince Mamey ko yaushe sai ana kamata ita kuwa tana firewa tana komawa cikin tsuntsaye ƴan uwanta.
Al'amarin ya magaga ya tada hankalin kowa.
Ana kamata zata zille ta fire ta koma cikin Garden ta zauna cikin tsuntsayen cikin masarautar Joɗa.
Duk wannan tashin hankali da ake ciki Sheykh Jabeer bashida labari dan lokacin yana karatu a jami'ar Madina sai dai kwata-kwata a lokacin hankalinsa yakasa ƙwanciya idan yakira wayar Mamey'n sai asa Aunty Rahma ta ɗauka tayi mishi mgn wanda ita kuma dama lokacin sun zo suna nan da Mamma.
Yadda Hajia Mama ke nuna tashin hankali tane yasa suka yarda da ita.
Wannan juyewar Mamey shine.
Sanadin da Jadda ya samu hawan jini kenan.
A ranar da dare Umaymah Mamma Aunty Rahma Aunty Juwairiyya Sitti duk sun gaza bacci, sun sa tsuntsuwar Boleru a gaba Magauta na musu dariya.
Sai da asubane sun kabbarta yin salla asuba, tsuntsuwar ta tashi ta fire, Bata tsaya cikin masararutar Joɗa bama ta fuskanci ƙasar Cameroon ta nausa tayi can yankin Yahunde.
Ɓacewar tsuntsuwar nan shi yafi tada musu hankali.
Anyi neman duniya har an gaji.
Ba ita ba dalilinta har dai aka ruggumi ƙaddara.
Sai dai Lamiɗo da Galadima da Jadda da Umaymah sunci gaba da bincikawa da neman mafita.
Lokacin da Sheykh ya kammala digirin sa na farko yazo.
Nigeria nan ne ake faɗa masa abin da ya faru a lokacin tashin hankalin da kiɗimar rayuwar daya faɗa ciki baya misaltuwa wani babban tashin hankalin kuwa shine daya iske ya Jafar baya magana sai addu'o'in da yin karatun al'ƙur'ani mai girma da kuka, dakuma ya buƙaci yaje yaga Mamey'n shi a yadda take ɗin a tsuntsuwar ta ɗin, nan ake faɗa masa ai tun lokacin da abun yafaru da kwana ɗaya rak ta fire tabar cikin masarautar Joɗa.
Ranar Sheykh kuka kamar karamin yaro ya rungume Jamil Jalal Yah Jafar da tun isowarsa Jafar ɗin ke ƙanƙame da hannun sa yana karatun yana kuka haka sukayi ta kuka Hajia Mama na tayasu.
Ranar tazamo musu tamkar sabuwa.
Tun daga wannan lokacin kuma sai yazamo kamar an cire hankalin Abba'n su a kansu madadin a lokacin ya janyosu jikinshi yazame musu Garkuwa dan suɗan sami sassaucin kunar dake cikin zuciyarsu sai yariƙa nisanta kanshi dasu.
Shi kansa bai san dalilin hakan ba,
duk wannan kuma acikin shirin Hajia Mama ce, kwana ɗayan da tsuntsuwar tayi tafire ma ita takoma gun bokanta tace tanaso tsuntsuwar tabar cikin masarautar gaba ɗaya dan taga sun dage da magungunan.
Dariya bokan nata yayi tare da cewa.
"Ke shar-shar banza da kika samu ma ba Addu'o'inku na musulmai sukeyiba ai da tuni sun karya sihirin".
Cikin jin daɗi tace.
"Aini gaba ta kaini da hankalin su baije ga canba".
Lamiɗo kuwa lokacin ya ƙara jan Sheykh a jiki sosai.
Sabida bayanin da Malam Musa yayi musu na cewar a sanadin aurensa da ba fulatanar daji mahaifiyarsu zata dawo.
Haka yasa part in da a ka bashi kusa da Garden inda tsuntsayen suke.
aka buɗe mishi wata kofa taciki in da daga cikin part ɗin direct zai sadashi da cikin Garden ɗin.
Bai wani jima sosai a Nigeria ba yakoma Madina sabida jin yakeyi ya tsani ƙasar Nigeria Especially Masarautar Joɗa.
Koda ya koma sosai ƴan uwan Sitti suka ga canji a rayuwarsa saida aka dage da addu'a kafin ya dawo hayyacinsa.
Daga nan suka ƙara kula ta musamman a kanshi suka zame mishi uwa uba ƙanne yayu sukeyi mishi komai.
Yakanyi shekara uku huɗu bai zoba.
Sai dai yana yawan sawa Jadda yazo mishi da Jamil Jalal Yah Jafar da Affan yawanci duk shekara zasu zo sau biyu hajji da umra wani shekaranma sau uku.
Ya maida hankali sa kan karatunsa da addu'a Allah ya baiya mishi Mameynshi a duk inda take ko a tsuntsuwar Boleru shi zaici gaba da rainonta da kula da ita iya rai da mutuwa.
Daga nan yayi master's madadin ya dawo ya haɗe. PHD ɗinsa. daga nan yadawo Nigeria'n bisa tirsasawar Lamiɗo da Jadda da Galadima da Umaymah dake matsayin Uwa.
Dole ya yarda ya dawo ya sanyawa ƙannensa ido wajen kula da su dakuma tarbiyyan su dakuma neman hamaifiyar su da kula da yayansa yakuma zame musu Garkuwa Da kuma bincikar Magautansu wanda dalilin haka ya samu matakin SS wanda dama shine burinsa to kuma Alhamdulillah ya gane komai Especially da ya samu damar aikin SS wanda dama burinshi kenan a dole Lamiɗo ya sashi karantan likitancin.
A kwai sabo ƙauna tausayi da shaƙuwa da tsama tsakaninshi da kakanun nashi sosai.
Hajia Mama kuwa da gayya ya barta da wayonta ita tanayi mishi kallon biri shi yana mata kallon ayaba.
Dama kuma malam Musa.
Ya faɗa musu cewa sanadin Sheykh ɗin ne Mamey'n zata dawo yabasu lbrin iya abinda Allah ya sanar mishi cewa bata rasuba tana raye kuma tajuye daga tsuntsuwar dasuke tunani tadawo mutum tuntuni tun bayan tafiyarta da watanni.
(Rayuwa kenan takan iya sauyawa a duk san da Allah yaso domin shi yake juya daƙuƙu i zuwa sa'a wuni zuwa dare kwana zuwa shekara ya fidda matacce a cikin rayayye ko ya fidda rayayye a cikin matacciya)
Ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe baki ɗayansu da suke cikin falon.
Bayan ya Jafar yagama basu labarin yadda akayi da abinda ya sani har Mamey'n su ta juye ta zama tsuntsuwa da kuma yadda akayi shima yakoma baya magana sai kuka da karatu.
Gabaki ɗaya parlour'n ya kaure da ambaton sunan Allah da yiwa uban giji tasbihi.
Ita kam Mamey sai murmushi takeyi tare da maimata.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah alakulli halin".
Affan kuwa kuka yakeyi tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.
Cike da rauni Sheykh ya jawoshi jikinshi ya ruggumeshi suna masu zubda hawaye baki ɗayansu.
Cikin rauni da tausayin irin kukan ƙuncin da Affan keyi Lamiɗo ya gyara zama tare da yin gyaran murya kana ya juyo ya kalli Bappa tare da cewa.
"Ka bamu labarin yadda akayi.
Aishatu tashigo hannun ku".
Ai kuwa kaf hankalin jamar parlour'n yadawo kan Bappa dan kowa nason jin yadda akayi Mamey'n tashigo hannunsa gaba ɗaya shi suka zuba ido.
A hankali yayi Bappa gyaran murya tare da gyara zamanshi kana ya ɗago hannunshi ya nuna Shatu da yatsarsa manuniya kana yace.
"Shatu itace sanadin.
Dan a lokacin da tashigo hannun mu mu muna mata kallon tsuntsuwar Boleru ne tsawon kusan wata bakwai muna tare da ita muna ganinta Giɗi yarona shike kula da ita saida ya zama tare suke cin abinci.
To Shatu itace ta fara ce mana ba tsuntsuwar Boleru bace mutunce ita a ranar wata jumma'a da tazo tare da mahaifin ta Alhaji Abboi wanda ni makiyayinsa ne.
Nan taga tsuntsuwar yara na son kamata su yaran damu manyan duk muna cewa tsuntsuwa ce.
Ita kuma tana cewa mutum ce.
Wanda haka yasa dole basu koma cikin birnin Yahunde a ranarba ita da mahaifinta suka kwana a gidana a Rugar Arɗo Babayo wanda nanne asalin mahaifata.
haka ta kwana tana gaɗin tsuntsuwar har dai Allah yanuna mana ikon sa da asuba tajuya ta dawo mutum a gaban idonmu,
Sai dai tana cikin larurar naƙuda.
Cikin ikon Allah ta haifu ta sauƙa lfy ta haifi ɗiyarta mace.
To lokacine mukaga sarƙar dake wuyanta.
Mai ɗauke da tambarin masarautar Joɗa kasan cewar masarautar fulɓe ce kuma mahaifin Alhaji Abboi abo kine ga Lamiɗo akan ɗan ziyarci juna kaɗan kaɗan to sanadin hakane Alhaji Abboi ya gane tambarin dake jin sarƙar na masarautar Joɗa ce.
Tofa anan muka gane cewa duk yadda akayi ita ahalin masarautar Joɗa ce.
Kuma Sarkin bakanmu ya tabbatar mana ita mutunce aikin sihirine to sai dai babu yadda za'ayi mu fuskanceku da mgnar kai tsaye tunda bamu san komai nakuba."
Ɗan tsakaita maganar yayi yaɗan ja numfashi kana yaci gaba da faɗin.
"Ni banine mahaifin Shatu ba Alh Abboi shine mahaifinta ga kuma mahaifiyarta.
Ni makiyayin mahaifinta ne.
inayi masa kiwone yana biyan.
Mafi akasari duk karshen wata suna zuwa tare da ita nan Rugar Arɗo Babayo.
To ita Shatu tanason yanayin daji rugarmu shiyasa duk sanda zaizo da ita zai zo, in zai koma kuma wasu lokutan yakan koma yabarta anan Rugarmu da yake ranar Jumma'a yake zuwa, to sai ranar lahadi da yamma Al'ameen ko wani daga cikin yayunta yazo ya ɗauke ta su koma.
Yawan zuwasu shi yasa tasaba da da yarana sosai da mai ɗakina.
To amman zuwansu da Allah ya ƙaddara lamarin Ummey ta juye a gabanta fir babu yadda ba'ayi da ita ta komaba taƙi bin mahaifinta fir taƙi tace ita zata zauna da Ummey ita ta zaɓa Junainah suna.
Wannan yasa dole mahaifinta ya koma ya barta.
To lokacin da Ummey'n Shatu'n ta faɗo hannunmu muka kuma ga wannan sarkar dake wuyanta na masarautar Joɗa shine Alh Abboi yace mu ƙaura mu dawo nan.
Nigeria kusa da masarautar Joɗa cikin Rugar Bani dan tasami kusan ci da masarautar.
to nan fa muka dawo Nigeria har da ita Shatu'n dan taƙi yar da a raba su da Ummey'n ta ashe rabo ke jawota nan.
dole iyayenta suka haƙura suka barta tare dani.
Muna dawowa nan muka sata a makarantar cikin Shikan".
Nan yaci gaba da basu labarin duk wani bayanin gwa-gwar mayar da
Shatu tayi a ka Ummey
duk sai da ya basu labari.
Ya ƙara da cewa.
"Lokacin da muka zo Nigeria da Ummey
wato (Mamey) Ba'ana naɗan shekaru sha takwas a duniya, lokacin (Parvina) wato Shatu kenan ita kuma du-du shekarun ta takwas ne,
to kafin mu dawo ma Mamey bata dawo daga haiyacin taba bata fara magana ba, lokacin da mukazo.
Nigeria Rugar Bani sai Ba'ana yace zai bata mgnin zata fara mgn kuma zata zama dai-dai sai dai zaiyi wuya ta tuna baya,
Amman zata dawo tayi mgn amman da sharadi. kasan cewar fatanmu ta tuna baya mu maidata ga ahlinta yasa mukace mun amince da sharaɗinsa wanda bamu san menene sharaɗin ba.
Shi saida ya fara bata mgnin kuma yace sai da sharaɗin in Ummey ta worke ta fara mgn muyi al'ƙawarin aura mishi Shatu.
To lokacin mu baƙine bamu san halinsa na ɓoyeba kuma burinmu da fatanmu ta worke mu maidata hannun ƴan uwanta sai muka amince mukayi mishi wannan al'ƙawarin bisa rashin sanin halin daga ranar Mata yake kiran Shatu.
Kullum Shatu ita ke zuwa gidansu Ba'ana da safe tana karɓawa Ummey magani a gunsa, dan shi tun tashin sa yake wannan cacube-cacuben nasa, so kullum.
Shike bawa Shatu magani ta kawo wa
Ummey tana sha har Ummey tadawo tafara magana sai dai bata iya tuna baya ba nan. Ba'ana'n ke ce mana duk randa taga wasu nata ko ƴan uwan ta ko wani abu nata zai yiwu tunanin ta
yadawo ta iya tuna baya."
Sai kuma ya ɗan tsagaita tare da sauƙe numfashi kana a hankali yaci gaba da cewa.
"Toh tun daga ranar ne muka fara neman hanya da dalilin da zai haɗamu daku mutanen masarautar Joɗa.
Sabida munsan aikin sihirine dole akwai Magauta sannan a gefen Ba'ana kuwa ya addabemu ya hana Shatu salama duk mai sonta sai yaga bayanshi.
To sai marigayi Cuɓaɗo ya bamu tabbacin bulalin Shaɗin masarautar Joɗa ne kawai zai karya duk wani sihirin jikin Ba'ana to kasan cewar yana sonta so na gsky bai cutar da ita in hankalinmu ya tashi kan muna tsoron ya aureta takan ce mana.
"Abinda in na gama karatuna zamu koma Yahunde sabida ita bamu sanar mata mun gano asalin Ummey ƴar ina bane gudun ita yarinyace kada tai ta gayawa wasu.
To munata son yadda alaƙa zata haɗamu sai kuma ga ƙabilar ɓachama su tasomu gaba.
Ran da muka zo nan na forko da muka ga Jamil sosai muka ƙara ƙarfafa guiwar ita ahlin masarautar Joɗa ce dan akwai kamar jini tare dashi da ita.
To da akayi faɗa kukaje mana jaje da gayya Arɗo Bani ya gaggayawa mai martaba Lamiɗo mgn dan ya tunzurashi ayi Shaɗi mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan.
Mun dawo da ita, mu kuma samu mgnin Ba'ana to kuma Alhamdulillah duk abin neman ya samu.
Sai kuma yayi ƙasa da kanshi murya na rawa yace.
"Sai dai sanadin faɗan ni na rasa kowa nawa".
Bappa ya ƙarashe mgnar cikin rauni da zubda hawayen tuno matarsa da zaratan yaranshi.
Cikin raunin tuno ahlinshi kuka mai rauni ya rufeshi yayinda Shatuma kuka mai ƙarfi ya kubce mata hakama Ummey sabida ita dai gata ta dawo ahlinta shi kuma garin dawo da ita cikin ƴaƴanta ya rasa nashi yaran.
Cikin tsananin jin daɗi
Sheykh ya ɗan muskuta cikin tsananin farin ciki da jin daɗin da godewa Allah daya bashi damar kuɓutar dasu ƴaƴan Bappa su Gaini shima zaisa Bappa farin ciki kwatankwacin yadda ya sashi.
Cikin sauri da bada umarni ya kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil tashi maza kaje kazo dasu".
"To". Jamil yace kana ya miƙe da sauri yafita batare da ɓata lokaciba sabida ya gano su waye Gaini.
Yana zuwa yace.
"Yah Gaini taso taso kuzo ga Bappanku da Shatu da Junainah".
Ai kafinma ya rufe baki duk sun muƙe cikin tsananin zaƙuwa suka biyo bayanshi.
Shi kuwa Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro da Alhaji Umaru rauninsu ya rigada ya dawo tuno irin kisan gillar da ƙabilar ɓachama sukayi musu.
Shi kuwa Sheykh dasu Lamiɗo shiru sukayi sabida son yi musu ba zata.
Da sauri Jamil yasa hannunshi ya tura ƙofar suka shigo tare da cewa.
"Assalamu alaikum Bappa share