Showing 159001 words to 162000 words out of 352722 words
Aysha".
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Shirme in banda sakarci da raki mutun ya bar kansa da yunwa da gajiyan aiki mutun har ya suma". Ya ƙarashe mgnar yana jinjina darajar sunanta a ranshi.
Cikin jin daɗin bai tsananta bincike ba tace.
"Akwai wani abune?".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Wannan mahaukaciyar Gimbiya Saudatunce tazo take cewa wai taji lbrin ta haukace".
Daga nan ya kauda zancen.
A hankali ya miƙe yana riƙe da wayar a kunne shi.
Dinning area ya nufa.
Murmushi yayi gano tabbas akwai abinda Umaymah ke ɓoye mishi.
Hannunshi yasa cikin zirin zirin igiyoyi masu duwatsu masu daraja sheƙin Daimond da sukayi Dinning area ɗinshi a madadin labule.
A hankali yasa hannunshin kan na'urar CCTV camera dake liƙe a gefen inda yake ajiye key, wanda duk abinda za'ayi a falon zai gani.
Cikin sanyi yace.
"Uhummm Umaymah kiyi mata faɗafa, ta dena hawan ƙawara kan mutanen masarautar Joɗa, ta kiyayi kanta da faɗa da magautana zasu ilatata.
Bata san komaiba a kaina ta tsaya matsayin baƙuwa Umaymah zafa suyi mata illa".
Ya ƙare mgnar a hankali.
System ɗinshi dake kan Dinning table ɗin ya jawo.
kana yaja kujera ya zauna ya fara haɗa na'urar.
Ita kuwa Umaymah a hankali tace.
"To ya zatayi tunda ƙaddara ta kasantar da ita matsayin matarka, ko ita kurmace dole sai sun nemi yi mata illa sun sabautata.
Dole kasata cikin jerin mutanen da ka zame musu GARKUWA a masarautar Joɗa, tunda ita dai matarka ce, amanarka kuma".
Shiru yayi yana jinta yana mai kallon fuskar System ɗinshi date ɗin shekaran jiya ya shiga.
ai kuwa Shatu ya fara cin karo da ita tana share falon da goge ko ina.
Sai kuma lokacin da suka shigo ita da Jamil da Hibba suka nufi bedroom ɗin sa.
A hankali yace.
"Uhmmm Umaymah sai anjima zan kiraki".
To tace kana ya katse kiran.
Ido ya zuwa System ɗinshi.
tsaki yaja karo na forko da yaji da ya haɗa na'urar da cikin ɗakinshi.
Gashi yanzu baya ganinsu sai dai ihun Hibba, da fitowa da tayi da gudu ta kira Ummi da yadda suka shigo da Aunty Juwairiyya.
Kanshi ya gyaɗa lokacin da yaga sun fito a hankali ya rufe System ɗinshi.
Dafe kanshi yayi yana nazari.
Ya dade a nan sosai kana ya koma ɗakin shi.
Da dare misalin karfe sha ɗaya na dare saura.
Shatu ta kalli Hibba dake konce tuni tayi bacci.
Yasa ta miƙa a hankali ta nufi ɗakin Ummi.
A bakin ƙofar ta tsaya a hankali tayi sallama.
Cikin mamaki Ummi dake zaune bisa sallaya ta idar da shafa'i da wutri kenan taji sallamarta.
Juyowa tayi tare da amsawa tace.
"Shatu".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Cikin mamaki tace.
"Lfy kuwa shigo mana".
A hankali ta shigo tare da cewa.
"Lfy lau Ummi, nazo wurinki ne."
"To".
tace tare da nuna mata wurin zama bakin gadonta.
A hankali ta ƙaraso kusa da ita,
Gabanta ta zauna kan sallayan cikin nitsuwa tace.
"Ummi kiyi haƙuri ko zakiyi bacci na hanaki".
Da sauri ta girgiza mata kai alamar a a.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"To Alhamdulillah".
Sai kuma tayi shiru.
A hankali Ummi tace.
"Kina buƙatar wani abune?".
Cikin nitsuwa tace.
"Uhum Ummi dama tambayarki nake son yi".
Gyara zama Ummi tayi kana tace.
"Ina jinki".
Itama zamanta ta gyara a hankali tace.
"Dan Allah Ummi in ba damuwa, dan Allah da Manzonsa ki sanar dani abinda Allah ya sanar dake a kan masarautar Joɗa mana.
Ummi kaina na kullewa da mutanen masarautar Joɗa, ban gane banbanci su da dankantakarsu da kuma. Alaƙarsu ba".
Wani irin dogon ajiyan zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
"To Shatu ai kin gama komai tunda kika haɗani da Allah da Manzonsa.
Kuma dama nace miki ki tambayeni duk abinda baki gane ba, zan gaya miki. To amman akwai wani abun sirrine garesu masarautar in na faɗa kamar cin amarsu ne, wani abun kuma nima kaina ban sanshi ba.
Hannun Ummi ta riƙe tare da zubda hawaye tace.
"Ummi gaya min yadda masarautar Joɗa take ko zan san irin zama da takun da zanyi da mutane da ɗaukar mataki kan abinda ke faruwa".
A hankali Ummi ta gyara zamanta.
Ta jingina da jikin gado.
Kana itama Shatu ta gyara zamanta ya zama suna fuskantar juna da kyau.
Cikin sanyi Ummi ta fara bata lbrin.
*Masarautar Joɗa*
tsohuwar masarautace.
wacce tun kafin zuwan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ƙasashen Afrika tana kafe da ƙafanta.
Kuma masarautar Fulɓe ce tun a wancan lokacin.
Lokacin da Shehu Usman Ɗanfodiyi ya iso nan ƙasashen hausa ya basu musulunci ya kafa tutocinsa tako ina tako wacce masarauta.
A lokacin Masarautar Joɗa sunanta masarautar Fulɓe.
Kuma lokacin Sarki Sule ne a kan karagar mulki. Baban Joɗa kenan wanda yake shi Joɗa shine kakan sarkinmu na yanzu wato Lamiɗo.
A lokacin sarki Sule yanada ƙarfin mulki yana da mata huɗu ƙwar-ƙwara biyar.
Allah ya azurtashi da arzikin yara a ƙalla sunfi hamsin a cikin matansa huɗu na aure.
Akwai wata ɗaya da ake kira Gimbiya sumaye ƴar sarkin kal'anace.
Gimbiya Sumaye inrin matannane da Allah ke jarabta da haihuwar wabi.
Bima'ana tana haihuwa kuma yaran na rasuwa.
A haka har ta haifi yara kusa goma kuma bata da rayeyye ko ɗaya.
Cikin ƙwar-ƙwaran sarki Sule ne ɗaya ta ɗauki ɗanta na miji ta bata halak malak kwanan yaron uku a hannunta ya rasu.
Wata cikinsu ta kuma bata still shima kwananshi uku ya rasu.
A haka duk ƙwar-ƙwaran sarki Sule saida suka bata yara suna rasuwa.
Daga nan uwar gidan Sarki Sule wacce take babarbariya ce.
Tasa mata suna cikin wasa na tsakanin Fulani da bare-bari amman a zahiri da gaske takeyi.
Gsky mai tafiya da wasa kenan.
Sai ta sawa Gimbiya Sumaye suna da fillanci wai
*Ɓadamaya* ma'ana wai duk wanda ya matso kusa da ita zai mutu, ko wanda ya bata riƙon ɗa kowa kwana uku ne mutuwa zaiyi.
Kamar da wasa sunanta ya zama Gimbiya Ɓadamaya.
Mutanen masarautar akayi ta mata izgili da habaici.
Takan zauna tayi ta kuka.
babu mai rarrashi dan ita masarautarsu nada nisa a lokacin kuma babu ko Radio bare waya.
Anan Allah ya bata wani ciki ta haifi ɗan ta namiji.
Akasa mishi suna Umar faruq.
Sai Gimbiya Sumaye take kiranshi da Joɗa ma'anar Joɗa shine zauna.
Da haka sai aka maida abun ba'a aka rinƙa kiran yaro da Joɗa.
Allah cikin ikonsa ta yaye yaro lfy lau.
Ta kuma haihuwa na goma sha biyu.
Yariyar watanta biyar ta rasu, sai aka rinƙa mata dariya ana cewa saura *Joɗa* shima ya *Dilli.*
Wato wai saura Joɗa shima ya *tafi.*
Cikin ikon Allah kuwa ya raya Joɗa ya girma.
Ya zama shine ƙarami cikin ƴaƴan sarki Sule kenan.
Bayan wasu shekaru, sai Sarki Sule yace to shi zaiyi murabus, a cikin yayanshi yace zai naɗa babban ɗanshi Madu.
Ɗan Gimbiya Falmata.
Sai ko sauran ƴan uba duk suka tashi akece to sai ayi zaɓen manyan.
To akwai ɗan Madu wanda yake mai ilimin addini dana zamani sunanshi Bala, sai ya shiga cikin masu neman mulkin ya kafa hujja da cewa.
"Babanshi Madu jahiline dan haka a bashi shine ya dace da mulkar garin.
Haka kuwa akayi aka ba Bala mulkin masarautar Fulɓe.
Dole babanshi Madu wanda shine Magajin gari ya ƙaura ya bar garin.
Tunda kinga bazai yiwuba ace yana mahaifinshi ya rinƙa serving ɗan shiba da baƙinsa ba.
Haka dai Bala yayi mulki tsawon shekaru arba'in inda Joɗa kuma yake matsayin Galadima tunda ɗan tsohon sarki ne.
To shi kuma Sarki Bala sai Allah ya azirtashi da tarin ya'ya mata ɗan shi na miji daya ne,
Sadik.
Ya bawa Sadik sarautan Sardaun.
Bayan wani lokacin sai tsoro ke rufe Sarki Bala kada fa abinda ya samu babanshi ya sameshi.
Wato kar ɗanshi bai gaji mulkiba kamar yadda sarautar ta tsallake babanshi ta dawo kanshi.
To shinefa ya tura ɗan shi Sadik wuraren sauran sarakunan ƙasar, cewa zaiyi murabus zai bawa Sadik mulkin.
To dama bisa ƙaida dole sai sarakunan sun yarda.
Cikin Sa'a kuwa duk sarakunan suka yarda sukasa hatimin amincewa a takardun.
To a kan hanyar dawowanshi ne kuma Allah yayi mishi rasuwa.
Wannan abu yayi masifar tada hankalin Sarki Bala.
Da mahaifiyarsa Gimbiya Salame, da kakarsa Gimbiya Falmata.
Saboda wannan pain ɗin mutuwar ɗan nasa, shene ya tattara yaranshi mata kab ya Aurar dasu.
Harda ƴar shekara takwas duk ya kwashesu ya aurar.
Sabida wai baya son ya mutu baiga aurensu ba.
Ya musu aure ya kuma basu sarauta.
Suka zama hakimai."
Cikin sanyi Shatu tace.
"Tirƙashi duk wannan don son mulki ne?".
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Uhum ai akan sarauta babu abinda ba'ayi sabida matsalar sai kowa yace shi ɗan sarkine zai gada.
Sabida in basu gadaba sarautar tabar hannunsu, Shatu Sarauta masiface a zuciyar masoyansa da zasu iya komai a kanta."
Kai Shatu ta gyaɗa tare da cewa.
"To Ummi ina jinki".
Gyara zama tayi tare daci gaba da cewa.
"To in takai ce miki a ƙarshe dai Joɗa shiya zama sarki wanda shine ɗan ƙaramin a ahlin Sule.
A lokacin ne kuma sunan jihar nan ya dawo Ɓadawaya sabida.
Nunawa duniya ba haka bane duniya Allah zai iya baka zai iya hanaka.
Masarautar Fulɓe kuma ta zama masarautar *JOƊA.*
Sabida sunan sarkin kenan.
Kuna ya zama adalin sarki mai son baƙi duk inda baƙo yazo zai wuce.
Sai Sarki Joɗa ya bashi wurin zama yace mushi Joɗa wato zauna ga wurin zama kayi kasuwanci kayi kiwo ki ciya ka ciyar kasha ka shayar."
Shiyasa Jihar Ɓadamaya tayi zarra da tarin ƙabilu sabida son baƙi da basu muhallin zama a wancan lokacin kawai fili za'a yanka a baka ka zauna in Kai baƙone
To babban ɗan Joɗa shine Bubayero wato kakan Lamiɗo.
Bayan Joɗa ya rasune Bubayero ya hau kan karagar mulki masarautar Joɗa.
Ahlin Gimbiya Falmata kuma suna yaɗuwa suma buri da kwaɗayin sarauta na jiƙa a ransu duk burinsu suga yadda sarauta zata dawo ɗakinsu.
To koda Bubayero zaiyi murabus ya bawa ɗansa Nuruddeen mulki sai ya aurawa ɗansa yar bappan shi jikar Madu ɗanshi.
Sukayi aure aka naɗa Sarki Nuruddeen da matarsa yakura.
Bayan anyi aurene da shekara biyu.
Ya auro wata ƴar masarautar su Gimbiya Sumaye.
To itace tazo ta haifi Lamiɗo.
Ita waccar bata taɓa haihuwa ba.
To shima Lamiɗo sai ya auro yar masarautarsun Gimbiya Sumaye, wato Gimbiya Aminatu a matsayin matarsa ta biyu.
To Galadima da kike gani yanzu bappan Lamiɗo ne ɗan autan su marigayi sarki Nuruddeen.
To shi kuma Lamiɗo da aka bashi mulki sai aka aura mishi yar zuriyar Gimbiya Falmata itace uwar gida.
Ta haifi Baba Basiru da Baba Nasiru da kuma Baba Kamal da kuma babban yayansu Marigayi Auwalu. Sai Dr Aliyu shi kuwa mamanshi daban itama ta rasu su biyu ta haifa da Gimbiya Surayyah.
To Mamansu Baba Nasiru.
Yanzu haka tana raye amman ta haukace babu mai shiga Side ɗinta, sai Lamiɗo da yaranta. Duk wanda yaje sai tace zatayi duka, ita da bakinta take bayanin Abbansu Sheykh da Gimbiya Aminatu da Gimbiya Aisha tayiwa asiri ya dawo kanta.
Galadima da yaga ya tsufane kuma baida ɗa namiji da zai gajeshi shine.
Yacewa Lamiɗo ya naɗan babban ɗan shi Auwalu mijin Gimbiya Saudatu a matsayin Galadima.
To bayan ya naɗa shi da shekara biyu ne, ya rasu.
To sai ya naɗa Ya Jafar ɗin nan da kike gani a matsayin Galadiman Masarautar Joɗa.
Lokacin lafiyarsa lau yadda kikaga Sheykh haka yake da ibada addini ilimi nitsuwa tausayi.
Kwananshi goma a kan mulkin washe gari za'a naɗa shi ne, ya dawo haka babu mgna sabida wani babban ibtila'i da tashin hankalin ɗaya samemu.
Kuma a lokacin an kusa amishi aure sabida sarautar da za'a bashi.
To wannan shine babban mafarin hargitsi da kitimurmurar dake masarautar Joɗa a yanzu.
Dan ranar da Jafar ya zama haka akwai babbar masifar data fi wannan muni daya faru a masarautar Joɗa.
Shine abunda yayi masifar girgiza mutane.
Lokacin Sheykh yana saudia yana karatu a jami'atul Madina.
Hankalin Hajia Mama yayi masifar tashi tayi ta suma tana sakewa Umaymah kuwa da Sitti mutuwace kawai da basuyi ba, dan baƙin ciki da tashin hankalin ɗaya samemu.
To kuma tun daga nan sai duk magautan suka dena kiyayyarsu kansu Jafar da ƙannensa.
Koda Jabeer yayi karatunshi a can yayi digirinsa na biyu da PHD dinsa duk a can.
Wani sabon tashin hankalin da Jabeer ya dawo Lamiɗo yabashi mulkin GARKUWAn FULANI, nanfa Magauta sukace zasu mutu.
Dan ma mulkin na gefen yaya mata aka bashi shine abin ya ɗanyi sanyi.
To kuma ingiza gabar sunga ɗawisun masarautar Joɗa tayiwa Jabeer abinda sai sarki takeyiwa.
To kinji lbrin a taƙaice sai a hankali zaki gane komai in kina bin komai a hankali."
Numfashi mai sanyi Shatu ta sauƙe tare da cewa.
"Ummi wacece Gimbiya Aisha?".
Da sauri Ummi tace.
"Baki santaba".
Da sauri Shatu tace.
"Toh ina take?".
"Bata nan". Ummi ta bata amsa a gajarce.
Da sauri Shatu tace.
"Ta rasu ne?".
Cikin zubda hawaye Ummi tace.
"Bamu san halin da take cikiba shine babban burin Sheykh a duniya, sanin inda take".
Cikin sanyi Shatu ta kauda waccar tambayar dan ko Ummi bata amsa mataba ita ta gane matsayin Gimbiya Aisha. Haka yasa a hankali tace.
"Allah ya baiyana ta. Ya cika mishi burinsa."
Amin Amin Ummi tace tana sharce hawaye.
Cikin nitsuwa Shatu tace.
"To Ummi mene kuma banbancin mulkin gefen yaya mata dana maza".
Cikin jin bacci tace.
"Da safe ki tambayi Hibba ko Jamil zasu gaya miki, yanzu jeki shiga dare yayi bacci nakeji".
Da haka tatashi taje ta shiga ta fahimci a duddunƙule Ummi ta bata lbrin Sarkin yanzu da matsalar dake faruwa.
Washe gari da safe, bayan sunci abinci.
Ummi ta miƙe dan taje tayi walaha, Hibba kuma ta tafi sashin Juwairiyya da tun jiya da safe bata sake shigowa ba.
Jamil ne ya shigo neman Jalal da sauri tace.
"Uhum yauwa Jamil zo mana".
To yace kana ya dawo ya zauna.
Cikin nitsuwa tace.
"Dan Allah in ɗan tambayeka mana".
Jingina yayi da jikin kujera tare da cewa.
"To ba matsala Allah yasa na sani".
Wayarta ta ajiye kana tace.
"In sha Allah ka sanima.
Wai menene banbanci sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata, dana gefen ƴaƴan ƴaƴa maza".
Dariya yayi mai sauti tare da cewa.
"Uhumm kema kin shiga Masarautar Joɗa cikin kitimurmuran yanayi ko kin ratso cikin ahlin da ba'a sonmu, kin fara fuskantar ƙalubale ko".
Tashi yayi yaje ya sha ruwa kana ya dawo ya zauna ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Banbancin tsakanin sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa maza da gefen ƴaƴan ƴaƴa mata.
Shine kamar haka.
1 Galadima (must be a prince )
2 Chiroma (crown prince)first born to the king
3 Tafida ( most be a prince )
4 Santuraki (must be a prince )
5 Sarkin dawaki ( prince)
6 Ɗan buram
7 Ɗan isa
8 Ɗan lawan
9 Durbi
10 Wambai
11 Turaki
12 Ɗan maje
13 Yarima
14 Ɗan iya
15 Majidadi.
Dan ɗagowa yayi ya kalleta tare da saƙe yatsunshi da yake naɗewa yana irga mata yace.
"Wannan duk royal family ne mostly biological sons din sarki ne wasu kuma jikokin sarki kuma kunne biyu sukeyi a rawunansu sabida su ƴaƴan sarki ne ko kuma iyayensu ƴaƴan sarki ne.
Kanta ta jinjina mishi alamun ta gamsu tana kuma ganewa.
Shi kuwa a nitse yaci ga da ce mata.
"Anan ake samin chief of staff da kuma senior councillor kamar galadima mostly shine senior councillor shine elders in royal bloodline ana samun galadima yapi sarki a shekaru kuma shi ake bama riqon gari in sarki bayanan.
Sannan duka anan sunayen dana irga miki da fari kowa zai iya yin sarki tunda daga ɗan sarki sai jikokinsa na gegen ƴaƴa maza, shiyasa su kunne biyu sukeyi a rawanunsu.
A hankali ya kalli Ummi data fito da Hijabi a jikinta ta zauna kusa da Shatu.
Tare da cewa.
"To kinji bayanin ƴaƴan ƴaƴa maza na sarki."
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Na gane kuwa Ummi, yanzu gaya min na ƴaƴan yaran sarki mata kuma inji".
Gyara zama Jamil yayi tare da cewa.
"To sukuma sarautar gefen yaya mata sune.
1 Madawaki
2 Garkuwa
3 Makama
4 Majidadi
4 Waziri
5 Matawalle
6 Sarkin yaki
7 Magayaki
8 Jarma
9 Talba
10 Shatima
11 Ubandoma
12 Ɗan kadai
13 Magajin gari
14 Ɗan masani
15 Barma.
Ɗan sauƙe numfashi yayi tare da ci gaba da cewa.
All of these hakimai ne wanda sukeyin kunne daya a rawunansu.
Kuma wasu a cikinsu jikokin sarki ne ta bangaren mamansu, mum dinsu ce yar sarki kamar dai mu a Masarautar su Sitti ko za'a bamu mulki iya waɗannan za'a bamu kinga baza suyi kunne biyu ba shiyasa suke kunne daya amma suma hakimai ne manya kuma yan majalissar sarki also akwai kin makers a cikinsu.
Sai dai su cikin jerinsu babu wanda zai gaji sarautar sarki kamar dai mu yanzu bazamu gaji Jadda ba da masarautar gargajiyace sai dai da yake nasu na musulcine, in Kuma a masarautar Joɗa ne sunayen da na ƙirga miki na forko cikinsu za'a iya bamu, domin yanzu GARKUWA da aka bawa Hamma Jabeer matsayinsa yafi ƙarfin hakan shiyasa Magauta basu damuba."
Ya ƙarishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu ɗan Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan ƴaƴan ɗakinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sauƙin abin ma ɗaya ne da suga sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata aka bashi duk da shi jikan ɗan ɗan ɗansa namiji ne".
Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaɓe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.
A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ƙasa da murya tace.
"Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana".
Kanta ta jujjuya a hankali ta buɗe baki tace.
"Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga ɗakin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?".
Ta ƙarishe mgnar wasu hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaɗa mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
"Ummi ɗakin Yan Sheykh ɗakine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al'wala wlh da badan wannan nagartar da Addu'o'in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
"Addu'a'u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar Joɗa.
Amman dan al'farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani".
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ƙasa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ƙasa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
"Ummi ku yarda dani, ku bani haɗin kai, zan tone duk abun cutarwa dake ɗakin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina buƙatar taimakon ku.
Amman