Showing 21001 words to 24000 words out of 352722 words

Chapter 8 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30707

Shatu tayi tare da karasowa gabansu cikin ladabi ba biyayya tace.
"Inna ina wuni".
Fuska a sake tace.
"Lfy lau Alhamdulillah ya karatu".

"Alhamdulillah karatu dai mun samu ɗan hutu."

"Masha ALLAH yayi kyau".
cewar Ummey
hannun Ummeyn ta kamo tare da cewa.
"Ummey ina wuni".
Murmushi tayi tare da shafa kekyawar fuskarta tace.
"Lfy lau Shatu muje muyi salla ko?".
Kanta ta ɗan sosa tare da cewa.
"Ummey ni nayi sallana a mota".
Dariya Ummey tayi domin ta gano cewa Shatu na fashin salla,
Ita kuwa Junainah baki ta tura tare da cewa.
"To ba gashi ba, ba yanzu muka gama musuba ya Giɗi ba nace mishi nafi Addana son salla, tunda ni kullum sai nayi ita kuma wata rana sai tace a a ita tayi a makka ko kuma tace wai ai tayi kuma babu wanda zai ganta tanayin sallan".
Ummey ce ta.
Buge bakinta tare da cewa.
"To Aku uwar mgna maza wuce kiyi salla, babu wanda ke son jawabin ki".
Tura baki tayi kana ta wuce cikin ɗakin nasu, tana cewa.
"Ai dama nasan kunfi sonta".
Ita kuwa Ummey harara ta watsawa Shatu tare da cewa.
"Ke kuma kada dai ki rinƙa kiyaye bakin wannan magananniyar".
Murmushi tayi ta bita kana ta ɗauki buta ta shiga bayan gida dan gyara jikinta, sannan ta dawo.

Tana shiga ta samu Junainah ta idar da sallan,
Gefenta ta zauna, tare da jawo jakarta, sweet ɗinta data seyo mata, ta kwaso ta fitar mata.
Ai kuwa tuni fushi ya ƙare, tazo ta raɓa jikin yayartata.

Ummey kuwa da Inna saida sukayi sallan isha, kafin suka, fito tsakar gida dan tuni hadarin nan ya watse sai iska mai sanyi daketa kaɗawa.

Bappa da su Ya Ladoma saida aka idar da sallan isha kafin suka dawo gida.

Gaba ɗayansu a tsakiyar gidan suka zauna bisa manyan taburmaii guda biyu mazan na kan ɗaya matan na kan ɗaya.

Abinci sukeci mai rai da lfy, tuwon faran ɗanyar shinkafa, da miyar ɗanyar kuɓewa data sha man shanu da tantakwashi, sai kifin banda sabi kifi na araha a wurinsu.

Sai kuma zazzafan kunun nono da yaji nono da zuma.

Sunaci suna ira ga hasken farin wata daya fito yayi ral ya haska ko ina na gidan.

Cikin jin daɗi, Giɗi yace.
"Shatu hutun mai tsawone ko gajere?".
Kunun nonon data kurɓa ta haɗiye kafin tace.
"Eh to Yaya Giɗi hutun sati uku ne muka samu".
Seyo ne ya amshi zancen da cewa.
"A hutun da ɗan yawa".
Shi kuwa Giɗi dariyar mugunta yayi tare da cewa.
"Ai kuwa naji daɗi wlh sai kinyi kiwo kema kiji hazar da muke ji".
Bappa ne ya amshi zancen da cewa.
"Giɗi mugunta ba kyaufa, Wato kai wuya kakeso tasha".
dariyar ƙeta ya kumayi tare da cewa.
"Ai naga duk anfi kashe mata kuɗi kuma muke wahalar kiwo, makarantar da takeyi kawai duk shekara kusan million 1 takeci muko sai wuyar tsiya da muke ci".
Gaini ne yace.
"To ai kuma ita bata da shanu ko ɗaya kaikuma garke biyu kakeda naka na kanka haka kuma muma".
Ladone ya ɗanyi murmushi bayan ya haɗiye lomar da yasa a baki yace.
"Ato gaya mishi kam".
Ummey ce ta ɗan kalli Shatu tare da cewa.
"Kici abinci ki dena shan ruwan kunu ba rike miki ciki zaiyiba".
Da sauri Junainah tace..
"A a Ummey ai Inna tana tasa an yanka zabbi zata gasa mana Adda karkici tuwo".
Dariya sukayi baki ɗayansu dan duk kowa yasan Junainah tsakaninta da.
Nama akwai ƙauna.

Haka dai sukaci gaba da hira da dariya,
Hatta makiyayan gidan nasu wanda ba yan gidan bane saida suka shigo akayi ta hira da dariya dasu.
Suna cikin hirar ne yaro yayi sallama cewa Ba'ana yana kiran Aysha, cikin sauri Aysha ta konta tare da lumshe idonta, ganin hakane yasa Ummey cewa yaron.
"Ayyah kaje kace mishi yayi hakuri AYSHA har tayi bacci, in ba matsala yaje sai gobe, in kuma da matsala a tada ita".
To yaron yace ya juya ya tafi.
Fitarshi bada daɗewa ba ya dawo,
Yace,.
"Yace a barta tayi baccinta gobe da safe zaizo".
To sukace kana yaron ya fita ya tafi. Sukuwa sukaci gaba da hira.

Gashin zabbi mai kyau Inna tayi musu gashin da yaji haɗi, nan ta ware na maza ta basu kana ta ware nata da Ummey sannan ta bawa Aysha da Junainah, nan fa sukaci gaba da ci, suna hirarsu ta zumunci wanda ko yaushe haka suke duk daren kuma anan Bappa ke karantar dasu.

Bayan duk sun fara miƙewa da dare ya fara nisa, a hankali Bappa yace.
"Aysha kinyi baccine?".
Cikin sauri ta miƙe zaune daga konciyar da tayi kanta na bisa cinyar Ummey, a hankali tace.
"A a Bappa idona biyu".

Tashi zaune yayi tare da fuskantar ta, ganin haka yasa ta rarrafa a hankali ta iso gabanshi, cikin kulawa yace.
"Ya karatun naki?".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah Bappa karatu na tafiya yadda ya kamata".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Baki da matsalar komai dai ko?".
Da sauri tace.
"Babu matsalar komai Bappa na".

"Masha ALLAH haka nake son ji, Allah ya miki al'barka dake da sauran ƴan uwanki baki ɗaya. Allah ya miki zaɓi da miji na gari".
A hankali suka amsa da Amin Amin gaba ɗayansu.

Daga nan kuma yayi ta mata nasihar ta kama kanta,
Jin sanyi ya fara yawane yasa sukayi saida safe kowa ya nufi makoncinsa.

Yayinda a can cikin garima masu hira a dandali duk sun watse.

Al'walan konciya bacci sukayi kana suka shiga, ɗakin Ummey da yake mai girma da faɗi an laileyeshi da siminti da leda carpet, kana ga jere da gadajenta biyu masu kyau,
Ita da Junainah suna kan babban gadon ita kuwa Ummey tana kan ƙaramin gadon.
Hira sukaci gaba da yi irin hira ta tsakanin uwa da ƴarta, cikin sanyi tace.
"Aysha, kinji Hashimu ɗan Arɗo ya rasu ko?".
Da sauri cikin razana AYSHA ta tashi zaune tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Ummey banjiba yaushe ya rasu meya sameshi?".
Ta jero tambayoyin a tare kana ga hawaye na kwaranya cikin sanyi Ummey tace.
"Kwanan ya rasu, yankan rago akayi mishi sai tsintar gawanshi akayi a burtali ana zaton Ɓachamawa ne suka kasheshi".
Cikin shessheƙan kuka tace.
"Allah sarki Ya Hashimu Allah ya jiƙanka da rahama yasa ka huta, Allah ya saka maka duk wanda ya kasheka Allah ya toni asirinshi."
Sai kuma ta konta tana kuka sosai saida tayi kamar 3 minute tana kuka kafin tace.
"Yanzu shike nan Ummey duk wanda zai soni ƙarshensa yankan rago?".
Cikin yin ƙasa da murya Ummey tace.
"Ba dukaba in sha Allah akwai wanda zai soki ya kuma rayu dake bisa lfy".
A hankali tace.
"Ummey wa zai soni a irin yadda kullum ya Ba'ana yake kara zama masafi mugu, wa zai tsira da tarkonshi?".
Da sauri Ummey tace.
"Wanda yake mai ƙare rayuwarsa a amɓaton Allah da kekyawar zuciya."
Kai kawai ta kife tana mai kukan rasuwar Yaya Hashimun ta, a haka dai sukayi ta hira har bacci ya sacesu.



A can cikin masarautar Joɗa kuwa.
Bayan anyi sallan ishane, Sheykh ya fito cikin shirinsa na tafiya, riga da wondon yaɗin wagambarine a jikinsa sai bakar alkyebbarsa dayasa kana sai hiraminshi fari da kuma bakin tarden dake saman kanshi.
Sai takalman sarautar da ya saka, suma farare kalar hiraminshi.
Jamil ne ke biye dashi a baya yana riƙe da ƴar madai-daiciyar jakar Hamman nasu, kana hannunshi ɗaya na riƙe da jakar System ɗinshi, shi kuwa Sheykh woyoyinsh ya zura a al'jihunshi.

Tare suka fito, a mashigar ƙofarshi nan sukayi kiciɓis da Jalal, da Jakadiyarsu, cikin muryar da bata cika fara'aba Jalal yace.
"Please Hamma Jabeer, dan Allah karka daɗe".
Kafaɗanshi ya dafa tare da cewa.
"In sha Allah bazan daɗeba Jalaluddin, ka kula da kanka da Yah Jafar".
Kanshi ya gyaɗa alamar to, Jakadiya kuwa, ido ta zuma musu tana jin so da ƙaunar yaran kamar itace ta haifesu a cikinta.
Cikin girmamawa Sheykh yace.
"Ummi bari inje in sallami Yaya Jafar".
To tace kana ta juya ta nufi sashin, Hajia Fatima, tsakar gidan Maigirma Habibullah.

Su kuwa suna shiga a falo suka samu Yayan nasu da iyalanshi, a hankali Sheykh ya ƙaraso gaban ɗan uwan nashi, cikin sanyi yace.
"Ya Jafar zan tafi Leddi julɓe Sitti ta nemi muje gidansu, can ƙasar saudia, Abba ne da kanshi yace inje badon hakaba babu inda zanje in barka a haka, zanje ƙasa mai tsarki tushen mahaifiyarmu da kakarmu da take jininsu, in sha Allah zan nemi al'farman a buɗe min ka'aba zan shiga har ciki inyi maka addu'o'in samun lfy, kuma bazan daɗe ba zan dawo kajiko Ya Jafar?".
Bai kulashiba kana kuma bai bar karatun da yakeyiba, sai dai hawaye daya fara zubdawa a jere-a jere. Jamil kam juyawa yayi ya fita da jakar ɗan uwan nashi dan yasan zaiyi kuka.

Ita kuwa Juwairiyya cikin sanyi tace.
"Babu komai Sheykh Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy in sha Allah zanyi ta kula dashi yadda ya kamata".
Jalal kuwa tattauna laɓɓa shi kawai yake tamkar zai hudasu, tabbas sunada ciwo a cikin zuƙatansu musamman Sheykh da yasan shike ɗaukan damuwarsu kab harda ta mahaifiyarsu".

Shi kuwa Sheykh hannu yasa yana sharewa Yayan nashi hawayen, a hankali suka juyo suka kalli ƙofar ɗakin Hajia Mama ce, ta shigo hadimanta na biye da ita a baya.
Gefen Juwairiyya ta zauna ta zubawa su Sheykh ido, lokacin ɗaya hawaye ya fara kwaranyowa da idanunta, cikin rawan murya tace.
"Sheykh lokacin na tafiya, Maimartaba ya aika a kirawo ka a zatonsa kana sashina, tashi kaje, Allah ya kiyaye hanya karka damu yayanku na ƙarƙashin kulawata musamman".
A hankali ya miƙe ga mamakinsu sai gashi shima Jafar ya mike hannunshi yasa ya kamo ƙanin nashi,
cikin rauni Sheykh yace,
"Hajia Mama kodai in tafi dashine, kingafa baya son in tafi in barshine".
Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace.
"Bazai yiwu ka tafi da shiba, karka damu Jabeer komai zai wuce".
Kai ya gyaɗa mata, sannan ya juya, ya nufi hanyar fita yana riƙe da hannun yayan nashi, Jalal na biye dasu a baya,
Hajia Mama da Juwairiyya da yaranta na biye dasu.
Koda suka zo tsakiyar farfajiyar gidan cikin bada umarni Hajia Mama ta kalli Sheykh tare da cewa.
"Jabeer kuje sashin Hajia Fatima ka sallamarta".
Ɗan jim yayi, a hankali ya kalleta, ita kuwa da sauri tace.
"Umarnine ba shawaraba".
Kanshi ya gyaɗa alamun to.

Daga nan suka shiga sashin nata, bayan Jakadiya tayi musu iso.

A folon forko suka Sameta, tana hakimce hadimanta na zagaye da ita.
Tana ganinsu ta tashi ta zauna, cikin sanyi tace.
"A a Sheykh da kanka".
Ɗan rusunawa yayi tare da cewa.
"Zanyi tafiya Hajia mamace tace inzo in sallameki".
Da sauri tace.
"Ayyah, to Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy". Amin yace a takaice kana ya kama hannun Ya Jafar ɗinshi suka fito.

Nan suka raka'a zuwa sashin Gimbiya Aminatu nan suka sameta a falon, sukayi sallama da ita.
Daga nan ya wuce fada, Hajia Mama kuwa ta koma sashinta da hadimanta bayan ta mishi addu'o'in insa lfy.

Juwairiyya kuwa parking lot ɗin su inda ta hango an jera motoci. Ta nufa inda Jamil ke tsaye da alamun waya yakeyi da Malika sahibarsa sabuwar budurwar da yayi.

Shi kuwa Sheykh yana shiga fada ya samu Waziri ne kaɗai da Maimartaba da alamun zaman jiransa sukeyi.
A gaban Maimartaba ya rusuna, tare dasa hannu ya tura hularshi ya maidashi baya,
Cikin kulawa Sarki Nuruddeen yasa hannu kan tsakiyar kanshi ya dafa tare da cewa.
"Allah ya kaika lfy, ya dawo da kai lfy, ya baka sa'an tafiya, ya kareka a duk inda kake".
Amin Amin suka amsa baki dayansu, kana Waziri ma ya mishi addu'o'in sannan suka miƙe gaba ɗayansu sukayi woje dan mishi rakiya,
Sarki Nuruddeen da bayinshi wazirinsa da bayinshi, shina Sheykh da bayinshi, sai ya zama rakiyar ta samu taron mutane,
kana ga bayin Ya Jafar, nan suka shishshiga tsala-tsalan motoci a ƙalla motoci goma sha biyar ne sukayi mishi rakiya zuwa Airport.

A wurin rabuwarsa da Ya Jafar ne yasa zuciyar kowa raunata domin Jafar kuka sosai yayi tayi da kyar dai suka dawo gida bayan jirgin su Sheykh ya tashi zuwa birnin Jalaluddin.


Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba sai gasu a birnin Jalaluddin.

Kafin jirginsu ya sauƙama a ƙalla motoci goma ne suka zo tarbansa, a ciki kuwa harda mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Koda yaga jikan nasa mota ɗaya suka shiga,
suna isa fadar musulunci,
suka fito daga cikin motocin da sauri Sarki Jalaluddin ya zagayo ya kamo hannun jikan nashi, suka nufi sashin Amaryarshi Gimbiya Kulsum, jikanshi Kabir na biye dasu a baya, suna isa falonta gaba ɗaya ma'aikatanta suka fita ganin mai alfarma da kanshi, shi kuwa Jalaluddin cikin ɗan ɗaga murya yake cewa.
"UmmuKulsum! UmmuKulsum!! Ga Jazlaan ya iso, gashi na kawo mikishi har ɗauki".
Wata kekyawar tsohuwar balarabiyace ta fito da sauri, cikin tsananin soyayyanshi ta ruggumeshi,
shima ruggumeta yayi cikin harshen larabci Sheykh yace .
"Ana uhubbiki hubban axeeman ya Sitti".
Kanshi ta shafa cikin tsananin son jikan nata tace.
"Laisa li misluka abadan ya habibee".
Murmushi mai faɗi yayi tare da bin bayanta, kai tsaye dinning area ta nufa dashi Kabir da Sarki Jalaluddin na biye dasu, da kallon sha'awa.
Kujera taja ta ajiyeshi, kana ta jawa Jalaluddin tasa kujerar nan kabirma ya zauna,
Suna zama sai ga wasu dattijan mata su uku sun shigo a jere a jere, suna zuwa duk kanshi suke shafawa shi kuwa sai murmushi yayi tare da kallon Mai alfarma Sarki Jalaluddin yace.
"Malam kace su dena shafa min kai haka na gaji".
Murmushi sukayi baki ɗayansu kana suka zauna, cikin kulawa babbar cikinsu tace.
"Kazo lfy, ya jikin Jafar?".
A hankali ya ɗan kalleta tare da cewa.
"To Alhamdulillah jiki da sauƙi zance".
Allah ya ƙara sauƙi cewar Jalaluddin Amin Amin suka amsa baki ɗayan su, ƙaramar cikinsun ce ta ɗan kalleshi cikin tsokana tace.
"Ina mai gidanmu Sarki muminai".
Taɓe baki Sheykh yayi tare da cewa .
"Uhumm Jalal ne Sarkin Musulmai ko? Baki sanshi bane".
Dariya sukayi duka kana suk gaggaisa sannan suka fita gaba ɗayansu, ita kuwa Sitti abinci tayi ta bashi har saida ya kwaɓe fuska tare da cewa.
"Na tuba ki barni haka na ƙoshi".
Kai ta gyaɗa kana suka dawo falo zata fara hira, yace shi dai ya gaji bacci yakeji hakanne yasa, Jalaluddin da kanshi ya kaishi makwancinsa.

Asuba ta gari al'ummar Sokotawa

A nan Ɓadamaya kuma cikin Rugar Bani
Washe gari da hantsi, bayan duk sun karya, kowa makiyaya duk sun tafiya kiwo, manoma kuma duk sun tafi noma, kana mata masu shiga tallan nono cikin gari sun tafi, garin yayi tsit kamar yadda aka saba

Ba'ana kuwa da Shatu suna zaune a ginɗin bishiyar mangoro dake bakin zauren su, ita tanata.
Ciki shi kuma yanata woje, cikin sakin fuska ya kalli Junainah dake gefensu yace.
"Junainah je cikin gida kice a baki ɗanyen kwai ki kawo mana in dafa mana".
Da mmki Shatu tace.
"Ka dafa mana kuma?". Kai ya gyaɗa mata, ita kuwa Junainah uwar kwaɗayi tuni ta tafi cikin gida Inna na tambayarta me zatayima Bata kulataba, sai ɗan kwano data ɗauko a konɗonsu kwan zabbi ta ɗebo a kalla sun kai goma, kana da gudu ta dawo wurinsu.

Da sauri yasa hannunshin ya amshi robar, ita dai Shatu Ido ta zuba mishi taga ta ina zai dafa kwan,
shi kuwa Ba'ana hannunshi yasa ya fara tona ɗan ma dai-dai cin rami, da mmki Shatu tace.
"Ya Ba'ana me zakayi da tona rami kuma?".
Cikin murmushi yace.
"A ciki zan dafa mana kwan".
Junainah kam gabanshi tazo ta zauna, tana kallonshi har ya gama tona ramin.
Kana ya zuba kwayayen a ciki ya maida ƙasar ya binnesu.
Sannan ya juyo ya kalli Shatu yace.
"To musha hirarmu kafin kwan ya nuna".
Junainah ce tace.
"Ya Ba'ana ta yaya zai nuna kuma babu wuta?". Kamo hannunta yayi tare da cewa.
"Ke dai zauna ki jira ki gani ƙaƙara".
Kai ta gyaɗa tare da gyara zama, shi kuwa Ba'ana murmushi yake a baiyane a ranshi kuma cewa yakeyi.
"Uhummm shi Bappa dan ina son yarsa bazai hanani yashe Garkensa ba, kuma da koyayen gidanshi kawai zan iya karya kafin da yayiwa garkenshi".
A zahiri kuwa kallon Shatu a yayi tare da cewa.
"Zakiji girkina mai daɗi". Kai ta jinjina tare da cewa.
"Uhumm girki ko al'mara."
Kanshi kawai ya gyaɗa alamun zaki gani daga nan sukaci gaba da hira.

Bayan kamar 42 minutes ya fara tono wannan ramin daya tona a gabansu babu wuta ko ɗigo ya binne ɗanyen koyaye, sai gashi ramin yana tururi tamkar an bude tukunyar dake tafasa, da sauri Aysha ta waro idonta.
Junainah kuwa sai tsalle take,
shiko Ba'ana saida ya kwatso ƙoyayen kab kana ya sasu a robar da aka kawosu a ciki,
Ɗaya daga ciki yasa a gefen dutsen da yake zaune ya konkotsashi kaɗan kana ya ɗagoshi, yatsunshi biyu yasa yafara ɓarewa.

Cikin mamaki Shatu ta zazzaro idanunta woje tare da cewa.
"Hehhhhh...!



Ga masu buƙatar biyan kudi littafin mutanen Niger ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 in kun biya ta wurinta ita zata turo min number ku in saku cikin group.
By
*GARKUWAR FULANI*


📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 7

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘



*Littafina na kuɗine, turo 1k domin karanta part 1 cikin mako biyu, ko ki turo 300 domin karanta part 1 a kwanaki talatin, da izinin ubangiji. Turosu ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank, Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta number da nake whatsapp dashi. 09097853276, in da hali bana son kati, amman in babu dama turo katin ba matsala, domin wani baida damar turowa ta bank ac.*

*Ayyah masuyi mun voice note Dan Allah ku rinƙa ɗaga murya, baku saniba ko inada matsalar kunne bayan na idon. In kinga kinyi min mgn ban amsaba wata ƙl fahimceki bane, ko kuma mgnarki bata da amsa a wurina, kana abubuwa suna min yawa, irin asha hira a chart ɗin nan bazai yiwuba, kuyi haƙuri masoya, yawan maimata min slm ince wslm ayi sama da sau goma yana sa in share mutun tsakani da Allah sabida kamar bashi da abin faɗane so Please na tuba,🙏🏻


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login