Showing 282001 words to 285000 words out of 352722 words
ɗinba".
Bappa ne ya amshi zancen da cewa.
"Ai kuwa itama Ummmeynkun da ta sani bazata fitaba".
A hankali Shatu tace.
"Ai magani taje amso min a Rugar Gebi, shine ita kuma Junainah tace sai ta bita.
Amman bazasu daɗe ba".
Jamil ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh ai sai mu ɗan jirasu ko?".
Da sauri Shatu tace.
"Yauwa ku jirasun".
Ta ƙare zancen tana turo tray'n tsakiyarsu kana ta kalli Jalal tare da cewa.
"Ga Kidar da gashi mai ɗumi".
Kai Jalal ya jinjina dan ya gamsu da tsabtan mutanen gidan".
Ganin hakane yasa Bappa ya miƙa ya basu wuri, yana mai cewa.
"Sheykh kusha tsala".
Kai Sheykh ya jinjina bayan Bappa ya fita ya ɗan kalli Jalal da Jamil da tuni suka jawo ƙoren bayan sun sauƙe akoshen gashin.
Ido ya zuwa Jamil ganin yadda ya lumshe idonshi lokacin da ya kai damun nan bakinshi, sai kuma ya kalli Jalal da ya matso gaban akoshin tare dasa hannunshi ya jawo ƴar ƙaramar butar Bappa dake wurin ya wonke hannunshi kana ya yago naman mai haɗe da robon man shanu, yasa a baki ido ya lumshe tare da taunawa kana ya haɗiye.
Cikin sauƙe dogon numfashi yace.
"Yah Sheykh kaci wlh yayi daɗi sosai.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
"Aish dubo waiji kisa musu kada su faɗi".
Dariya mai ɗan sauti tayi kana tace.
"Kaima in kaci sai kayi santi".
Idonshi ya ɗan zuba mata kana a hankali yace.
"A a aini abinci ɗaya nakeci inyi santi, kuma ba banishi zakiyi ba dan rowa".
Ya ƙarashe mgnar yana mata nuni da idonshi cewa.
"Kece".
Da sauri ta kauda kanta tare da cewa.
"To kaci dai".
Ƙoryar zallan nonon da zumar ya jawo kana yace.
"Toh kije ki shirya kafin mu gama sha ko".
Da sauri tace.
"Wai tare zamu tafine?".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.
"Ai babu wai, in sha Allah yau a masarautar Joɗa zaki kwana".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah dan Al...".
Da sauri yace.
"Please dan Allah kada ki haɗani da Allah ki cuceni ki sani yin abinda bana so, Please je kiyi shiri kinji ko Aish dan Allah".
Cikin sanyi tace.
"Toh zamu jira Ummey ta dawo ko".
Kanshi ya ɗan sunkuyar tare da cewa.
"Zuwa ƙarfe biyar da rabi zamu jira".
Cikin sanyi tace.
"In sha Allah ma kafin nan ma, zata dawo".
Kai ya gyaɗa mata kawai ta juya ta tafi.
Inna Amarya ta samu zaune da Ummi suna ɗan taɓa hira Ummi na shan nono.
Gefensu ta zauna, kana ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi kunzo Ummey na bata nan".
Cikin kula tace.
"Eh yanzu Inna Amarya ke gaya min, ai zamu ɗan jirata".
Da sauri tace yauwa.
Nan sukaci gaba da hira.
Bappa kuwa suna gama cin abinci yazo ya musu jagora cikin gida suka gaisa da Inna Amarya kana ya musu jagora har ƙofar gidan Arɗo Bani.
Nan suka zauna anata gaisawa.
Cikin kula Arɗo Bani yace.
"Mun gode sosai da ɗawainiya Sheykh Allah ya ƙara rufa asiri".
Amin Amin yace.
Kana Alhaji Haro da Umaru suma sukayi godiyar, dan Bappa dasu ya raba yadukan Getzner da Shatu ta kawo mishi, al'kyabbar kuwa ya barwa kansa.
Nan sukayi ta hira har biyar da minti ashirin.
Kana Bappa yace.
"Muje gida ko wata ƙil sun dawo".
To sukace kana suka miƙe sukabi bayanshi.
A gida kuwa, Ummi ce ta ɗan kalli Shatu tare da cewa.
"Shatu da kin kimtsa kayanki ai kinga magriba tana ƙara towa, kuma nasan bazamuyi salla a nanba".
Cikin yanayin sanyi tace.
"Ɗazu da safe Ummey tamin wonkin kayana duk suna cikin jaka ma."
Kai ta gyaɗa tare da cewa Inna Amarya.
"Anya kuwa ba kwana zasuyi a canba".
Da sauri tace.
"A a wlh da wuya su kwana sai dai garin da nisane."
Dai-dai lokacin Bappa ya shigo tare da cewa.
"Shatu fito ku tafi dare yanayi".
Jiki a mace tace.
"Bappa bazamu jira Ummeyna ba".
Kai ya jujjuya kana a hankali yace.
"A a kuje kawai ba komai Shatu nida kaina zan kawo miki mgnin naga kamar Sheykh ɗin hankalinsa yayi gida".
Kai Ummi ta gyaɗa cikin takaicin rashin ganin Ummey tace.
"Eh dole hankalinshi zai koma can da yake shike limancin masallacin. Kuma ina sha Allah ni da kaina zanzo amsar mata mgnin".
Da haka dai suka bawa Shatu ƙarfin guiwa suka taho.
Ita da Ummi a baya, Sheykh da Jamil a gaba Jalal a tsakiya.
Ana kiran sallan magriba suna isa bakin Part ɗin su.
Da sauri Sheykh ya fito ya buɗe gidan ya shiga, dan yin al'wala.
Kana suma suka shigo.
Jalal da Jamil kuwa sukayi side ɗin su.
Ummi na idar da salla ta miƙe da niyar shiga kitchen kenan Sara ta shigo da Foodflaks wanda Gimbiya Aminatu tasa aka shirya musu abinci.
Suna dawowa sallan isha'i sukaci kowa ya nufi makoncinsa.
Shi kuwa Sheykh yana shiga wonka yayi kana yayi shirin bacci.
Shiru-shiru baiga Shatu ta shigoba,
haka yasa ya miƙe ya fito falo, a hankali ya tsaya bayanta.
Ganin ta zaune da alamun waya takeyi da Ummeynta, cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummey na, baki dawoba har muka tafi hankalina ya tashi gashi dare yayi kuma baku dawo ba."
Murmushi mai kwantar da hankali Ummey tayi kana tace.
"Wlh kuwa Shatu na kuna fita, ina isowa, nama hango bayan motarku".
Sosai shima yaji abinda Ummeynta ta faɗa sabida kanshi da ya sunkuyar ya manna da wuyanta.
Cikin sanyi tace.
"Ayyah UMMEY NA ina Junainah".
"Gata nan tayi bacci, tun ɗazu wai yau gidan shiru ba daɗi tunda bakya nan".
Ummey ta bata amsa.
Da sauri tace.
"Ayyah ƴar uwata. To Ummey ya batun mgnin nawa kuma?".
"Bappanki yace zai kawo miki".
Ta bata amsa tana konciya.
Daga nan dai sukayi saida safe.
Hannunshi yasa ya juyota ya ruggumeta tsam a jikinshi a hankali yace.
"I miss u so much my dear".
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Miss u to".
Wuyanta ya ɗan sunsuna tare da jawota sukayi cikin bedroom.
A hankali ya kwanta kana ya jawota jikinshi,
hannunshi yasa ya zuge igiyoyin dake ƙasar gaban rigarta murya can ƙasa yace.
"Wai maganin menene Ummey ta haɗa mana".
Cikin fidda numfashi jin yadda ya kife tafin hannunshi kan Caɓɓulenta tace.
"Wai maganin zaƙine zan zubdashi".
Da sauri ya zaro ido tare da cewa.
"Na shiga aljanna da izinin ubangiji.
maganin zubda zaƙi kuma Boɗɗona bama na ƙara mana zaƙiba".
Cikin jujjuya ido tare da dariyar kalmar shi ta na Shiga aljanna da izinin ubangiji tace.
"A a zaƙifa na naƙuda, wai zai sauƙaƙawa mutun wahalar naƙuda".
Ajiyan zuciya yayi tare da jawota jikinshi,
ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, wani irin hott kiss mai cike da bege yake mata.
Daga nan suka narkewa juna.
Washe gari da safe Gimbiya Aminatu da kanta tazo har Side ɗinsu tai mata sannu da dawowa da tambayar mutanen gida.
Hakama Aunty Juwairiyya da Mom.
Yau kwananta uku da dawowa.
Junaidu da kanshi ya kawo maganin nata sai dai kai tsaye Valli Hospital ya kai mgnin ya bawa Sheykh.
Inda kuma nan ya bashi takardunshi ma na neman ci gaban karatun jami'a.
Sosai suke shan hira da Junaidun.
Shida kanshi ya ɗauke shi a motarsa zuwa tasha, inda zai shiga motar Shikan.
A cikin motar ne ya ɗan kalli Junaidun tare da cewa.
"Junaidu ai da kazo mana da Junainah".
Murmushi Junaidun yayi tare da cewa.
"Malam ai bata sanma zan zoba, sabida in ta sani zatace muzo tare, kuma yanzu nafi son ta meda hankali kan karatunta, kaga dama ta rasa shekara ɗaya tafiyarsu Cameroon".
Kai ya ɗan jinjina kana yace.
"Zan roƙi Bappa ya bamu ita ai, sai in sauya mata makaranta".
Cikin kwaɓe fuska Junaidu yace.
"Uhumm Yah Sheykh ai kuwa ni ina tsoro".
Da sauri yace.
"Tsoron me?".
Kai ya ɗan kauda ganin sun iso tashan, a hankali yace.
"Kada ka dawo da ita birni tai nesa dani ta manceni wani ɗan sarakuna yayi wuf da ita".
Murmushi mai yalwa Sheykh yayi kana a hankali yace.
"Astagafirullaha".
Sai kuma yace.
"A a in sha Allah zan ajiye maka ita, kuma ai kaima yanzu zaka dawo nan cikin birnin".
Murmushi yayi kana ya buɗe motar ya fita.
Kiranshi yayi ya zagayo ta inda yake, sannan ya bashi kuɗi.
Godiya yayi kana ya tafi, shima yaja mota ya tafi yana mai jin son Junaidun a ransa.
Dan shine ya sanar dashi komai kan Ba'ana da ɓatansu Yah Gaini. Da wulaƙancin da Ɓachamawa ke musu, sai dai iya abin ya sani kawai ya sanar masa.
Daga nan gidan Malam Abubakar ya wuce.
Bayan sun gaisa ne, yake ce mishi.
"Alhamdulillah Malam batun Sulaiman komai zaiyi sauƙi dan yanzu ina neman zama na musamman ne da shugaban SS da kuma shugabsn hukumar ƴan sanda na ƙasa.
In sha Allah gsky zatayi aikinta".
Cikin jin daɗi, Malam Abubakar yace.
"Kai Alhamdulillah Sheykh Allah yayi maka al'barka ya rufa maka asiri duniya da ƙiyama".
Amin Amin yace kana sukayi sallama da juna.
Shine bai shigo gidaba sai bayan sallan isha'i.
hannunshi riƙe da ledan magungunan da aka haɗawa Shatu wanda na zaƙine kuma yana sauƙaƙa naguɗa da izinin ubangiji.
(Ganyen bishiyar Ceɗiya, Dirim, Ganyen Barma Gada ban san sunanshi da Hausa ba, sai kuma zobo.
Sai cikinki ya kai wata bakwai zaki tafa sasu sai ki rinƙa shan ruwan, da zaran cikinki ya shiga wata takwas sai ki bari.
Sai randa duk kikaga alamun naƙuda sai kiyi maza ki tafa kiyi ta shansa da ɗuminsa, da izinin ubangiji wlh wani kafin ma mgnin ya tafasa da yardar ubangijin sammai da ƙassai zaki haihu lfy.
Yana sauƙaƙa nakuɗa sosai.
Ki haifo ɗanki lfy ƙato kuma jazir kamar ɗan larabawa da izinin ubangiji)
A hankali ya shigo cikin falon inda take zaune Ummi na gefenta.
Gefenta ya zauna tare da miƙa mata ledar.
Hannu tasa ta amsa tare da cewa.
"Ngd matuƙa Allah ya rufa asiri".
Cikin jin daɗi yawan addu'ar da take masa in ya bata abu koda bata san komai bane yace.
"Amin Amin".
"Na menene?." Ta tambayeshi a taƙaice.
cikinta ya ɗan kalla tare da cewa.
"Magungunan da Ummey ta amso miki ne".
Cikin sauri tace.
"Bappa yazo ne".
Kai ya jujjuya mata alamar a a.
"To kaine kaje".
Cikin wasa ya gyaɗa mata kai alamar eh.
Baki ta ɗan turo gaba tare da cewa.
"Shine ko kaje dani Hamma Jabeer".
Murmushi yayi yana miƙewa tsaye yace.
"To banine najeba Junaidu ne ya kawo minshi har Valli".
Cikin fidda numfashi Ummi tace.
"Niko da har ina cewa gobe Jamil zai kaini mu amso".
Yana mai nufar ɗakinsa yace.
"Ato Junaidu ya hutasshe mu".
Daga nan ya tafi, ita kuwa Ummi amsar mgnanin tayi taje kitchin rabashi biyu tayi ta tafasa mata rabi ta tace mata shi, ta tasa mata a ɗan madaidaicin bokatin roba mai marfi ta rufe, ta kawo mata.
Kana ta ƙulle saura kuma.
Daga ranar ta fara sha.
Alhamdulillah komai na tafiya dai-dai yanzu cikin Shatu yayi watanni takwas cib, duk bayan sati biyu zai ɗauketa suje Valli Hospital ayimata awu su dawo gida.
A hankali komai ke tafiya yanzu cikin ya shiga wata na tara.
Yau asabar ne ba aiki shiyasa yake hutu in banda zuwa Masallaci ba abinda ke fiddashi.
A hankali ta shigo riƙe da tray'n abincinsa.
Da sauri ya tashi tsaye, maƙale da waya a kunnenshi bisa alamu da Umaymah yake mgn. Ajiye tray'n yayi tare da jawo hannunta bisa kujera 3 str suka zauna.
Matsawa can ƙarshen kujerar yayi, kana ya sunkuyo ƙasa hannunshi yasa ya ɗago sawunta da yanzu sun fara ɗan kumbura, kan cinyarsa ya ɗora sawun nata.
A hankali yasa kafaɗarshi ya maƙale wayar da yakeyi kana a hankali yasa yatsunshi ya ɗan fara mammatse mata sawun.
Cikin nitsuwa ya ɗan kalleta kana a hankali yace.
"Uhum gata nan ma. Umaymah gashi naga yanzu ƙafafun nata sun kumbura sosai mafa, bataji saitayi ta zama bisa kuje ƙafar a ƙasa."
Cikin kula Umaymah tace.
"Amman dai ba wata matsalar ko?".
Da sauri yace.
"A a ba komai tana lfy baby ma na lfy".
hannunshi yasa ya gyara mata konciyarta, ganin ta mirgina ta konta.
"Yaushe ne EDD'nta?".
Umaymah ta tsmbayeshi
Cikin nitsuwa yace.
"Saura mako uku".
murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kaga kuwa su Mamma da Aunty Rahma ma suna gab da zuwa dan jikin Jadda dake yawan tashin masa yace, yana buƙatar ganinmu baki ɗayanmu to zasu zo nanda sati ukun, amman banda yaransu".
Cikin nitsuwa yace.
"Uhumm tsohonan da tsoroba so yake ya ruɗar mana daku yana komai kamar mai barin wasiyya, ni tun zuwanmu auren Haroon sai wani cewa yake ko bayan ransa kaza da kaza zaiyi kaza, to ni dai fatana Allah yasa Mamey na ta ƙara haɗa ido dashi kafin ya tafi".
Ya ƙarashe mgnar cike da rauni da kuma ƴar raha.
Cikin rauni Umaymah tace.
"Kaci gidanku ai kaima Abbanka zai tafi".
Numfashin ya ɗan sauƙe still ysnayiwa sawunta tausa.
Saida suka gama waya da Umaymah ya yunƙura zai ajiye wayar kenan.
Wani kiran ya shigo wayarshi yana ɗaga yaga DSS.
da sauri ya amsa tare da cewa.
"Hello sir barka da dare".
Yaƙi in sallama sabida sanin kafurune bisa lfyn.
"Barka dai Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa."
Murmushi yayi jin oganshi a fagen aiki ya kirasa da cikekken sunansa.
A hankali yace.
"Sir barka da dare".
Cikin hausar arnataku yace.
"Kai Sheykh, kai da yan uwan Sulaiman kun hanamu bacci da yawan Addu'o'in kuna gigitamu da addu'a dole mu fito da shiko".
Cikin dariya da kekyawar mu'amala yace.
"Sir ba dole muyi ta Addu'o'in ba, tunda bamu da kowa sai Allah da Manzonsa bamu da mai bi mana bayan gskyr masu gskyar da ake tozartawa.
Ya zamuyi sai mu haɗaka da Allah".
Cikin dariya shugaban hukumar binciken ƙasa na sirri yace.
"Gsky to ku barni inyi bacci, kuzo ayi mgnar belinshi, nayi mgn da wanda case ɗin yake hannunsa.
Yace shima duk sanda zai bacci sai yaga Sulaiman da wasu yara sunata kuka, suna salla da addu'a kuma da zai sa a duba hakan za'a samesu.
Ni kuwa kwarjin Sulaiman na min yawa ko naje da niyar bincikarsa sai inji ban gamsu cewa shi mai sayan kayan sata bane".
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah to yanzu wacce rana zamuzo ayi mgnar belin".
Cikin sauri yace.
"Next to weeks".
Da sauri yace.
"Allah ya kaimu".
Daga nan sukayi sallama.
Addu'a'u saifulmumini kenan
Gashi suda kansu sun nemesu.
Nan take ya kira malam Abubakar ya sanar mishi komai.
Bayan sati ɗaya, wanda ya kama saura kwanaki ne cikin Shatu ya cika wata tara.
Kuma Alhamdulillah komai na tafiya dai-dai.
A hankali suke tafiya lokacin da suka fito wurin awun.
A nitse suka miƙe ɗan corridor'n har cikin Office ɗin shi.
Bisa tattausar kujerar dake gefe ta zauna tare da sauƙe numfashi tace.
"Gsky Yah Sheykh yanzu kam fa na fara jin nauyin cikin nan, in zan ɗaga kafata sai inji ya tokareni".
Goron ruwan faro mara sanyin daya ɗauko ya miƙa mata, tare da cewa.
"Eh dole kiji haka yanzu tunda cikin yayi ƙasa. Alamun haihuwa yau ko gobe ake cewa ko?".
Rufe goran tayi bayan tasha mai yawa kana a hankali tace.
"Uhummm ni naƙuda kawai nake tsoro in badon shiba ni Ko yauma in haihu mana kawai in huta".
Sunkuyowa ya ɗanyi yayi kissing goshinta a hankali yace.
"La, la, la kada ki damu ke kam Aish na ƙudarma ni zan miki kinji"
Yayi mgnar cikin wasa da kwantar mata da hankali.
Da sauri tace.
"Allah yasa haka".
Amin Amin yace cikin murmushin.
Sai kuma ya fara tattare ƴan abubuwa shi dan zasu wuce gida.
Yana gamawa suka fita suka tafi.
Yau asabar Sheykh ne zaune gaban Malam Abubakar da Lamiɗo da Galadima dan Malam Abubakar ɗin ne yazo har gida a nitse Sheykh yace.
"Toh Alhamdulillah Malam in Allah ya kaimu gobe.
Ƙannen maman Sulaiman Ya Adam da Ashiru su shirya suje. Abuja su kai kuɗin beli kamar yadda suka faɗa. Naso inje to kuma abubuwa sun min yawa."
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai kana a hankali yace.
"Sai dai kuɗin belin ne wuyar 3 million da sukace".
Kai Sheykh ya ɗan ɗago tare da cewa.
"Eh ba damuwa na turawa Ashiru kuɗin a accutan ɗinsa in suje su cire suje musu da kash".
Cikin jin daɗi Malam Abubakar yace.
"Kai Alhamdulillah Muhammad Allah yayi maka al'barka Ngd matuƙa".
Amin Amin sukace kana sukaci gaba da wata hirarsun.
Alhamdulillah kuwa su Ashirun sunje lfya ranar Monday sun bada belin Sulaiman sun dawo lfy yan uwan shi mata kamar zasu mutu dan farin ciki.
Cikin Shatu kuwa gaba ɗaya ya sauƙo yayi ƙasa a hasashen likitoci sauran kwana takwas ta haihu.
Yau ta kasance ranar jumma'a ne.
Tunda safe Sheykh yayi shirin jumma'a'arsa.
Da sauri ya fito falonshi sai baza ƙamshi yakeyi.
Wani tattausan yadine a jikinsa lemon green mai masifar kyau yasha aiki da farin surfani.
Gariyar tayi cas da jikinsa.
farin hula mai ratsin lemon green ya kafa bisa tattausan gashin kansa.
sai takalminsa sau ciki shima lemon green.
Da sauri ya ɗan ja da baya ganin ya kusa yayi karo da Aish ɗinsa da cikinta da ya fito sosai yayi kuma ƙasa sosai in ka ganta har kamar ta ɗan rame.
Cikin kula tace.
"Hamma Jabeer fita zakayi ne?".
Motsota yayi a hankali ya ɗan ruggumota kana yasa hannunshi ya ɗan shafi cikin a hankali yace.
"Eh fita zanyi Aish ina son inje gidan Malam Abubakar dan mu gana da Sulaiman tunda ya dawo shekaran jiya ban samu mun naje na masa jajeba".
Cikin fidda sassanyan numfashi tace.
"To zaka dawone kafin azahar".
Kai ya jujjuya alamar a a.
Manna kanta tayi da ƙirjinsa kana a hankali tace.
"Toh kuma zanje makaranta fa, zan shiga aji daga ƙarfe sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya zamu gama takardun da suka rage mana".
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Wannan makaranta ni dai tana cimin rai".
Cikin sanyi tace.
"Toh ai ma mun kusa samun hutu yau last page ɗin ezam ɗin zamuyi".
Kai ya ɗan sunkuyar ya manna hancinsa a wuyanta a hankali yace.
"Toh yanzu muje in kaiki da kaina in na sauƙeki sai in wuce gidan malam kuna tashi inzo in ɗaukiki in dawo dake, nasan kafin nan kuma lokacin salla yayi."
To tace kana taje ta shirya.
Ta zurma ƙaton hijabi.
Haka kuwa akayi yana sauƙeta saida ya tabbatar ta shiga aji lfy kana, ya juya ya nufi gidan.
Malam Abubakar.
A falonshi ya sameshi zaune shida Sulaiman.
Da sauri Sulaiman ya tasa ya nufi inda yake.
Cikin yanayi sabo da shaƙuwa suka ruggume juna.
Murya na rawa Sulaiman yace.
"Sheykh ngd ngd Ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya rufa asiri duniya da ƙiyama ya ceceka da wahalar siraɗi kamar yadda ka zama sanadin cetoni daga azabar hukumar ƴan sanda da na faɗa ciki".
Amin Amin yace cike da tausayin ganin yadda Sulaiman ya rame yayi duhu farin shin nan duk ya tafi.
Ga alamun tashin hankali da firgicin da basu gama sakeshi ba.
A hankali suka zauna gaban Malam Abubakar da yaketa sanya musu al'baka a duniya bai taɓayin ɗaliban da yake so da ƙauna sama dasu ba.
Cikin kula Sheykh ya ɗan rusunar da kai tare da cewa.
"Barka da hantsi malam".
"Barka dai Muhammad, ya iyalin taka da ƴan tagwaye da Jafar".
"Alhamdulillah duk suna lfy sai dai Yah Jafar yanzu kusan wata uku kenan, yake yawan yin bacci dare da rana safe da yamma, salla da cin abinci kaɗai ke tada shi.
Ni kaina wasu lokutan sai inyi kusan kwana biyar ban ganshi ba, sai in nine naje Side ɗinsa".
Murmushi mai sanyi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
"Uhummm Alhamdulillah waraka na bisa hanya, ai bacci ga irin mai larurarsa alamun sauƙi ne".
Cikin jin daɗi