Showing 123001 words to 126000 words out of 352722 words
inda take tare da cewa.
"Ɗauki markaɗen ki kai bari in ƙarisa wannan aikin".
Cikin mamaki tace.
"A a bar".
Da sauri ta katseta da cewa, jeki".
To tace cikin mamakin sauƙin halinta ta ɗauki robar jiƙeƙƙiyar shinkafar da ta kai mudu biyar har ta ɗaura a kai,
Ta kuma sauke jin Shatu na cewa.
"Yauwa naga akwai murjejjiyar gyaɗa, ɗebo, da wata shinkafar kizo ga dabino da kwakwa a nan ki haɗa ki jikasasu ki tafi dasu, na kunune kafin a markaɗa wannan na masan shinma ya jiƙa sai a markaɗa miki shi.
Da sauri ta juya tayi yadda tace ɗin tanayi tana nuna mata dai-dai yadda takeso, saida ta gama kana rufe babban roban da marfinshi sannan ta ɗaura ƙaramin a kai ta tafi.
Ita kuwa Shatu matsowa tayi taci gaba da tsinkan ganyen, ita kuma Ummi freezer'n ta buɗe tare da ɗebo kayan ciki mai yawa, tazo.
Ta wonƙeshi fes, kana ta watsa al'basa mai yawa a ciki, Sannan tasa citta,kanamfari, cory tare da sauran kayan ɗanɗanon.
Gas ta kunna ta ɗaura tukunyar, sannan ta dai-dai-ta wutar.
Wani babban roba ta ɗauko kana ta nufi Store Arish ta ɗebo mai ɗan yawa tazo tana fereshi cikin ɗan injin ɗin firar lokaci ɗaya tayi nisa a fitar.
Ita kuwa Shatu tana gana gyaran ganyen ta ɗebo kayan miya tazo ta jajjagasu yadda takeso.
Kusan a tare suka gama da Ummi.
Wankeshi Ummi tayi bayan ta yishi tsillk-tsillk kana ta sashi a tukunya, tare ɗan yaryaɗa gishiri, ta rufeshi.
Ta ajiye gefe.
Ita kuwa Shatu cikin kula ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me za'ayi da ganyen?".
"Miyan da za'aci masar dashi".
To bata amsa tana komawa cikin Freezer'n fruits ta ɗebo.
Tazo tana wonkesu tare da shiryasu cikin tray mai girma, kana ta shirya wasu kuma a wani ɗan madaidaicin tray mai masifar kyau.
rufesu tayi kana taje tasasu cikin Fridge.
It's kuwa Shatu can nama ta ɗebo dai-dai misali wonƙeshi tayi tasa a tukunya tare dasa kayan ƙamshi dana ɗanɗano.
ta ɗaura a wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta ɗaura a ɗaya murhun dake gas ɗin babbane.
Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al'basa,
ya soyu yana ƙamshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ƙara wonƙe ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haɗa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.
Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba.
Ita tayi miyar masan, ta kuma ƙarisa ferfesun kayan cikin da Ummi ta fara.
Ummi kuwa ta tafasa musu tea ta ɗuɗɗura a flaks,
Kana ta tafasa Arish ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Saratu ta dawo.
Ita Ummi ce ta ɗan amshi ƙullun masar tare da cewa.
"Gskya mun ɗan makara aikin Masar nan gashi ni hannuna baya tashi da wuri".
Da sauri Shatu ta matso tare da miƙawa Ummi roban markaɗen kunun.
Tace.
"Ba matsala Ummi ni hannuna na tashi da wuri.
Yanzu tace mana marƙaden kunun bari in kwaɓa mana Masar."
Haka kuwa akayi Ummi ta fara tacewa.
Ita kuwa kulun dafaffiyar ɗanyar shinkafar ta murmusa cikin marƙaden Masar,
Kana tasa fulawa tare da yis kaɗan sannan ta tarfa gishiri kaɗan.
Kana ta rufeshi a robar dan babbace, motso da robar tayi kusa da Gas ɗin yana ɗan jin ɗumin wuta.
Gefen Ummi ta dawo wacce ta gama tace markaɗen
A babbar tukunta ta zuba shi kana ta ɗaura kan wuta tare da dai-dai-ta wutar tanayi tana motsa kunun.
tare da ɗan tarfa wanda ta rage, da surkin lemun tsami.
Cikin Sa'a ɗaya ta dama kunun shinkafar fari ƙal tamkar madara.
Sugar tasa ta juye a a ƙatuwar kula kana tasa a maidaciyar kula, Sannan tasa a flaks ɗaya, sai kuma tasa a Mug mai marfi duk ta kimtsasu gefe.
Tuni Side ɗin ya ɗin ke da ƙamshi miyar masan da ferfesun nan.
Buɗewa tayi ganin miyar tayine ta sauƙe ta maida gefe.
Kana ta kalli Ummi tace.
"Ummi je kiyi salla la'asar tayi, in kin dawo sai inje inyi".
To Ummi tace ta fita tana mamakin saurin aikin Shatu.
Koda taje tayi sallan ta dawo ta sameta tana sauƙe tukunyar ferfesun.
ganin Ummi yasa tace. "Yauwa Ummi komai yayi dai-dai yanzu kaskon tuya zamu daura kinga kullun ya tashi".
Cikin mamaki Ummi ta kalli Robar da taga har kullun na shirin zubewa.
Ita kuma ɗiba tayi a wata roba kana duk tasa yankekken al'basane a ciki Sannan tasa sugar ta gauraya,
sannan ta matso da kasko biyu,
juyowa tayi ta kalli Saratu tace.
"Yauwa Sara matso. Ke ki rinƙa yi kina sawa a wannan babban kulan in ya cika kisa a wannan shima.
Ummi ke kuma kisa mana namu anan suyanki mukeson ci".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"To jekiyi salla".
To tace kana ta fita.
Ita kuma Ummi ta juya ta kalli Sara tare da cewa.
"Kema kije kiyi salla".
Cikin ci gaba da aikinta tace.
"Ai nima nayi".
"To shike nan". Ummi tace kana sukaci gaba da tuyan.
A falo ta haɗu da Hibba da Jamil, sai dariya yakeyi cikin dariyar yace.
"Yauwa Aunty Shatu dama idonki nazo in gani, dan ga Hibba kam ta kusa kasawa".
Murmushi tayi dan bata da sauran ƙarfin yin dariya.
Cikin ɗan fito da idanunta da suka ɗan faɗa tace.
"Gani ras dani".
Dariyar ƙeta mai cike da alamun yunwa da ƙishi yayi tare da cewa.
"Inafa ras kalli yadda idonki ya fito kamar kinyi azumi goma".
Murmushi tayi kana tace.
"Um bari inje inyi salla".
Sai ta kuma kalli Hibba dake lankwabe tace.
"Sannu Hibba kwanta ki huta".
Jalal da yanzu ya shigone ya ɗan taɓe baki tare da cewa.
"To me tayi da zata huta tunda fa gari ya waya in anga ta tashi dai yin salla ne, tun tuni birgima take a tayis wai sanyi take nema".
Dariya sukayi mata baki ɗayansu,
Ita dai Shatu ciki ta wuce.
Salla tayi kana ta fito. Koda tazo kitchen ta samu Hibba na suya musu Arish ɗin, tayi mamaki.
Cikin wasa tace.
"Kawo in karɓeki jeki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ai Hamma Jabeer ne yace min in ina aiki bazanji wuya ba, zanfi ganin lokaci ya gudu".
Dariya sukayi mata kana kowa yaci gaba da aikinshi.
Ita Shatu miyar sahur na asuba ta ɗaura musu.
Cikin ikon Allah shida dai-dai suka gam kan aikinsu.
Bayan Shatu'n ta taya Hibba suya kwai daban, ta jerasu a Foodflaks, in ta ajiye fefeyin soyayyan ƙwai da yaji haɗi da diddigin kifi, sai ta zuba soyayyan Arish a kai kana ta kuma rufeshi da fefeyin kwai haka ta rinƙa jerasu saida ta cika kulan.
Ummi kuwa ta sawa Saratu komai nata.
Sannan suka kimtsa wurin fes suka fito da komai suka jera a dinning table.
Nan duk suka wuce ɗauki.
Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu Imran, Jalal, Jamil, Sulaiman.
Cikin gajiya Ummi tace.
"Yauwa Jalal ku ɗauki manyan kulolin nan ku kai masallaci.
Sauran madaidaitan kuma ku ajiyewa sarkin bayi.
A bawa bayi da hadimai".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh lallai bana bayi sun samu uwar gijiyar data tuna dasu, bayan kuma anayi musu nasu na daban".
Cikin lumshe ido Shatu tace.
"Eh suma suci abinda muke dafawa da kanmu, ba sai na gandun nasuba".
Miƙewa sukayi suka ɗauki kulolin sun zo falon kenan Sheykh na shigowa, wani hadimi na biye dashi da manyan ledodi cike da ƴaƴan itatuwa.
Kusan a tare suke mishi sannu da dawowa.
Murya a bushe alamun ƙishi yake amsa musu kana ya nunawa Ummi leda ɗaya yace.
"Ummi a wonke wannan a haɗa da dabino mudu uku a basu su kai masallaci".
Ya ƙarishe mgnar yana wucewa.
Da sauri Ummi tace to.
Ta miƙe kenan Shatu tace.
"Ummi zauna bari in wanke sun".
To tace kana ta koma ta zauna.
Ita kuma taje ta wonke ta zubasu a tray kana ta ɗauko plates and cups masu yawa, tazo ta miƙawa Imran.
Da sauri suka amsa suka tafi.
Jim kaɗan suka dawo, cikin gajiya Jamil yace.
"Ummi ansha ruwafa mun samu Ladan na cin dabino".
Da sauri Hibba ta miƙa tare da cewa.
"Su ladanannan haka suke basa kiran salla sai sun sha ruwa."
Dariya sukayi mata kana suma suka miƙe sukabi bayanta.
Zama sukayi bisa kujerun kowa da abin yake hari.
Sai dai kab ɗibsu da dabino suka fara.
Ummi ce ta kalli Shatu tare da nuna mata babban tray'n da aka shirya komai na buɗa cikin Foodflaks guda 3 madaidata masu kyau, sai plate ɗin da aka shirya fruits masu ɗan karen sanyi, tupa, inabi ,kankana, abarba, gwanda, Lemu, ayaba, kana da dabino, da kwakwa,
Sai goran zam-zam madaidaci, kana sai cup da tea spoon a ciki, sai fork and knife a gefe da gefen plate ɗin dake cike da fruits ɗin komai biyu akasa.
Kulolin kuma ɗaya masane a ciki, ɗan namiyar kuma miyar Masar ne, sai ɗayan kuma, soyayyan ƙwai da dankalin, ɗayan kuma ferfesun kayan cikin ne.
Cikin nitsuwa Ummi ta ɗago tray ta miƙa mata tare da cewa.
"Yauwa gashi kai mishi lokacin shan ruwan na tafiya, yanzu zakiga ya fito".
Cikin sanyi da gajiya ta amshi tray'n kana ta nufi falon nashi, cikin nitsuwa take takun, a hankali tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon.
A can bisa Dinning area ta hangoshi yana zaune, kan kujera ɗaya, ya kuma jawo ɗaya kujerar ya ɗaura sawunshi a kai ya miƙesu, System ɗinshi na bisa cinyarshi.
A hankali take takowa saman steps ɗin tare da ratsa cikin jeren ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond sai sunkuyar da kanta tayi sabida ɗauke mata ido da suke.
A hankali ta isa kusa dashi, cikin tura baki tare da ɗan murguɗashi ta ajiye tray'n, a tsakiyar table ɗin.
ɗago kanta tayi da niyar ta ɗan juya, ta fita.
Wani irin buɗe idanin tayi gaba ɗaya tare da zubasu, bisa sharaban ƙafarsa ta dama, wanda sanaɗin zaman da ya ɗan yi ya miƙe ƙafafuwan nashi bisa ɗaya kujerar ne yasa suka ɗan baiyana, wani irin kallo mai cike da ɗimuwa takeyiwa zanen dake bisa ƙafarshi ta dama, da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannun hagun ta kama kanta sabida wani irin sarawa da ya farayi da ƙarfi.
Cikin sauri ta juyo tare da miƙa hannun damanta ta sauƙeshi kan...!
Akwai kayan gyara na amare da uwar gidaye da masu jego, ga mai buƙatar saya ga number ta 09097853276
By
*GARKUWAR FULANI*
[📝🍇🍇🍇🕊️🐩🌈🦚🐍🤴🏼💘
GARKUWA
PART TWO
PAGE 1
NA
AYSHA ALIYU GARKUWA
📝🍇🍇🍇🕊️🐩🌈🦚🐍🤴🏼💘
LITTAFINA NA KUDI NE TURO 300 DOMIN samun damar KARANTASHI.ko ki turo 1k damin shiga SP Group, inda zaku samu posting fiye da na 300.Ayyah yan SPG bana son katin ,turo dubu dayan ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha aliyu garkuwa,sai ki turo shaidar b iyanki ht a little bit and friends and I to come to Allah yakaemu to be t me know what time works a y me know what time works to get it to you as a ah ok to Allah Hafiz a ah well to the unique ladies I to the gym now and i me know when you're free and i
Ufdd me know what works for date to the store to get it to me by a few to get a hold to shikenan nagode Allah I to do that for you but you don't have my number so we get to Allah bless your family a ah well to get it out to shikenan nagode yasaka to Allah Hafiz to be a part to the unique ladies and gentlemen to get the unique to get it out to Allah bless and have a good weekend and i to be a ah well to get the unique to be in the office today so I will not have a chance and friends and i to the unique to be t me a call if you want a good laugh my family to be in a good mood to be t me a call at your family a Merry ba and i a ah ok to come by for date happy to help out to Allah yakaemu a good weekend and i me a call if Dan allah waye to get a ah well to the gym today and friends to Allah Hafiz me to get it out to shikenan nagode dakulawar to be t a good time to Allah Hafiz a ah ok well I'm going back in anan shine yace Yana dawowa xamuxo a few to get the gym today and tomorrow so the unique and special and I have to Allah yakaemu a good time to Allah Hafiz to be in a good mood to be a part to make a ah well to get it done by Friday and friends and I to be t a few to Allah Hafiz a few days ago a few to see the unique ladies and i a ah well to the unique and special to me too to get it done by Friday and I have been talking for date
[4/12, 8:34 PM] Maman Aslam: Tasa hannu tashafa taban macicin nan yaisauri yadauki kafassa ya miki afusa ce Ki kina haukani futarmun a daki Alhamdulillah. Allah ya kawomu watan Ramadan, wata mai tarin al'farma da al'barkatu da tarin ni'imomi. Mutane da dama Allah bai basu wannan damarba, da yawa sun rasu.
Wasu kuma basu da lfy, basu san me sukeyi ba ko a ina suke, bare su ribaci wannan dama da Allah ya bamu.
An ga wata wanda haka keda tabbacin gobe zamu tashi da azumi.
Duk kuyi niya, ɗaukar azumi talatin ko talatin ba ɗaya."
Sai ya kuma ya ɗan tsagaita tare da kallonsu Jalal da Jamil cikin sanyi yace.
"Dan Allah Jalal Jamil ku nitsu kunsan halin da muke ciki. Kun san matsalar rayuwarmu kunsan damuwarmu, wannan dama ce da zamu yi amfani da ita wurin tsananta addu'o'in ba dare ba rana.
In sha Allah, Wata rana komai zai dai-dai-ta domin Allahu sami'uddu'a ne.
Jamil kaji tsoron Allah ka ribaci wannan watar, ka raba kanka da zuwa club, ka yayewa kanka masifar nacin liƙewa mata da waya."
Juyowa yayi ya ɗan kalli Jalal kana yaci gaba da cewa.
"Jalal yawon bin yan iska da wani shegen shiga mara kan gado ba tsarine na Musulmin ƙwarai ba.
Aunty Juwairiyya Hibba Ummi Ke uwar bacci".
Ya ƙarishe mgnar da kallon gefenda Shatu da take zaune tana ɗan lullumshe ido,
da sauri ta waresu don a sama taji muryar tasa. Baki ta tura tare da sunkuyar da kanta, shi kuma jenye idonshi yayi daga gefen da take cikin ɗan ɗaga sauti yace.
"Watan Ramadan ya bambanta da sauran watanni.
Domin a cikin watanne daren laylatul Ƙadir yake, kuma a cikin watanne Allah ya sauƙe al'ƙur'ani mai girma.
Kana a cikin watar akwai ranakun da malamai sukeyi hasashen a daren laylatul Ƙadir yake, Daren 21, 23, 25, 27, 29. Sai dai ba'a tabbatar, da sahihin rana ɗaya tsayeyye ba ƙauli mafi rinjaye shine ranar 27.
Abi mafi kyau shine kada mutun ya sake koda dare ɗaya na Ramadan ya wuceshi.
Mu raya dararen da ibada da ambaton Allah, wajibine mutum ya tsare bakinsa, da munanan zantuka walau a baki walau a rubuce a social media,
Domin mu ribanci watar da ambaton Allah da samun ruɓanyar lada, wannan abubuwane da kullum nake gaya muku su, sai dai aiki dasu ya gagareku."
Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa.
"In Sha Allah zamuyi ƙoƙarin kiyayewa".
"Allah yasa yace, tare da sallanmansu duk suka fita sai Ya Jafar da Ummi.
Ganin yadda Hibba keta zuba hamma ne ya sashi cewa.
"Muhibbat tashi
Kije ki kwanta".
Kusan a tare ta mike ita da Shatu.
da sauri yace.
"Banda ke". Cikin bacci ta turo baki tare da cewa.
"Ayyah dan Allah fa".
Murmushi Ya Jafar yayi tare da zuba mata ido.
Wanda koda baya mgna ana iya gano yadda yake sonta a ranshi, so kuma irin son da yakeyiwa su Hibba.
Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"A barta tai bacci aiki mukeyi tun ɗazu".
Shiru bai kulasuba, ganin haka ita kuma tabi bayan Hibba.
A zatonta bai saniba, har sunje bakin ƙofar taji yace.
"Saura ki binƙire kiyi ta bacci, kada ki tashi ki raya daren. Sai gari ya waye ki buwayi mutane da ife-ife da rashin kunya".
Ya ƙarishe mgnar cikin jin haushinta tare da Binta da kallon fitinenneyar yarinya.
Ganin Ya Jafar ya miƙa ya juya zai fitane yasa yayi saurin.
Bin bayanshi ya rakashi kana ya dawo ya konta.
Ummi ma ta konta.
Ƙarfe ɗaya da rabi Sheykh ya tashi yayi ta nafilfilinshi tare da jere addu'o'in da neman warakar damuwar rayuwarshi data ahlinshin.
Ummi ma tuni ta tashi. Ƙarfe uku ta fito.
Falon hango haske a ɗakun Shatune ya tabbatar mata sun tashi.
Kitchen ta wuce. gas ta kunna ta ɗumama musu miyar, kana ta haɗa plate spoons and cups tazo ta jere bisa Dinning table.
Sannan ta koma kitchen ta ɗauko musu drinks and water masu sanyi tazo ta jere komai yadda ya dace.
Kana ta dawo falon ta zauna riƙe da carbinta.
Ƙarfe huɗu dai-dai su Jalal suka buga ƙofar sanin sune yasa, ta tashi ta buɗe musu.
Suna shiga ana buga bindigar sanarda mutanen masarautar Joɗa cewa lokacin sahur yayi.
Bayan mintuna talatin kuma za'a kuma sakin bindingar.
Cikin gudu Shatu ta fito falon jiki na rawa, kiciɓis tayi da Ummi da takeda niyar zuwa ta ta kirasu suzo suyi sahur.
Ruggume Ummi tayi ƙam-ƙam tare da neman inda zatasa ranta.
Allah ya sani tana tsoron ƙaran abu biyu, ƙaran aradu da walƙiya da kuma ƙaran harbin bindiga".
Cikin mamaki Ummi tace.
"Oho Aysha duk wannan tsoron na ƙaran harbin bindiga ne, lallai kuwa in baki sababa kafin Ramadan ya ƙare zakisha wuya."
Hibba ce ta fito tana dariya tace.
"Allah ko Ummi ana ɗaukan alhaƙin Aunty Aysha".
Babban Falon suka nufo yayinda duk jikinta ke karkarwar."
Dinning area Suka wuce.
Bayan duk sun zaunane Ummi tace Hibba tasa musu abinci.
Buɗe kulolin tayi.
Jolof ɗin taliya da kifi Aunty Juwairiyya tayi, sai kuma
Flaks ɗin kunun gyaɗa.
nasu kuma tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewan sai tea da sauran kayan sha.
Ta zubawa kowa abinda ranshi keso.
ita dai Shatu mamakin abincin Aunty Juwairiyya na yau takeyi sabida idonta bai gano mata wani mugun abu a cikiba.
Haka yasa itama shi taci. Da kunun.
duk sunyi nisa a yin sahur ɗin. Amman shi bai fitoba,
Sai ƙarfe huɗu da rabi ya fito.
A hankali ya iso Dinning area ɗin gaban washing hand Baby ya