Showing 186001 words to 189000 words out of 352722 words
da azaba gaba ɗaya jikinta karkarwa yake.
Cikin bacci Umaymah da Ummi suka jiyo ihunta da rabka musu kiran da takeyi.
A guje suka fito cikin ɗakunan suka nufo inda suke jin ihunta.
A bakin ƙofar suka haɗu cikin karkarwa ta faɗa jikin Umaymah tare da Ruggume ta da hannu ɗaya.
Cikin kuka da fitan haiyaci take cewa.
"Umaymah wani, Ummi yau ma ya sake shigowa, zai saceni ya jani har bakin ƙofa, kunga can ƙofar a buɗe ko.
Wayyo Allah na, wayyo hannuna".
Da sauri Umaymah ta ruggumeta gab zamewa tayi suka zauna a nan.
Ummi kuwa hannunta mai ciwon da taga yana rawa tamkar mazari ne ta rinƙa hurawa iska tana cewa.
"Sannu Aysha innalillahi sannu".
Sai ta kuma fara kiran Sheykh.
"Sheykh! Sheykh!! Sheykh!!!".
A gigice ya buɗe ƙofarshi ya fito,
ya nufi inda suke yana cewa.
"Na'am! Na'am Ummi meya faru ne".
Cikin gigita tace kalli fa.
Dai-dai lokacin kuma numfashin ta ya tafi cak ta sume tana cewa.
"Jahan wai zai saceni".
Cikin gigita Umaymah tace.
"Jazlaan ta suma, ta sumafa.
Waye ne Jahan kagafa can ƙofar a buɗe".
Hannunshi yasa ya amsheta jikin Umaymah dan yaga itama jikinta karkarwa yakeyi.
Ruwan sanyin da Ummi ta miƙo mishi ya amsa, kana ya kurba a bakinshi ya fesa mata ruwan a fuska.
Cikin wani irin jan dogon numfashi ta sa hannunta mai lfyar ta saƙalo wuyanshi, tare da ɓoye fuskarta cikin jikinshi tana cewa.
"Zai saceni, ɗan iska ne shi".
Ummi ce ta miƙe taje ta rufe ƙofar.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya kalli Umaymah dake gigice yace.
"Umaymah ki kontar da hankalinki, babu abinda zai samemu da izinin ubangiji.
Kije ku kwanta. Ummi kuje,
kwana kima tayi haka cikin Ramadan inaga al'janunta ne ke rikitata.
Dan ranar da tace ta ganshi ya shiga Side na ba inda bamu dubaba ba kowa".
Cikin kiɗima Umaymah tace.
"Yau dai kam tabbas akwai abinda ta gani tunda harda suma kuma ga ƙofar a buɗe, Jazlaan na gaji wlh zaku bar Masarautar Joɗa ko zamu samu kwanciyar hankali a rayuwar mu".
Cikin son kontar mata da hankali ya ɗan dafe kanshi kana yace.
"To Umaymah zamu barta jeki kiyi al'wala kiyi addu'a Allah ya kare mu".
Ya ƙareshe mgnar yana miƙewa tsaye da ita a jikinshi.
Dan tayi mishi riƙon ɗaurin goro da hannunta mai lafiya.
A hankali Umaymah da Ummi suka juya suka tafi.
Shi kuwa Side ɗinsa ya nufa, kai tsaye.
Har cikin Bedroom, maida ƙofar yayi ya rufe.
Kana yazo kan gado ya sunkuyo ya kwantar da ita.
Jin yadda ta riƙe mishi wuya ƙam-ƙam ne ya sashi cewa.
"Zafa ki kasheni da shaƙa".
Shiru tayi tana ƙanƙame da wuyanshi, hannunta sai karkarwa yake amman bata kuka alamun zafin yayi zafi tsananin yayi tsanani domin wani zafin ya wuce inda hawaye suke.
Dole a hankali ya zame wuyanshi kana ya zauna gefenta.
Idonta suna buɗe amman sunyi masifar ja, goshinta sai zufa yake tsastsafowa.
Numfashin ta wani na korar wani.
A hankali ya gyara zamanshi ya fara yi mata tofi yana karanta duk surar da tazo bakinshi.
A hankali hannun ya fara rage karkarwan.
Tsawon miti talatin yana mata tofi yana jin tausayinta har cikin ransa ya dade yana mata tofin.
Sannan ta iya juyowa ta kalleshi cikin rauni da zubda hawaye tace.
"Yah Sheykh ka yanke min hannunan mana ko zan huta da azabar da nakeji in ya tashi".
Ido ya ɗan zuba mata tare da cewa.
"Kiyi bacci kinji ko?".
A hankali tace.
"Ina tsoronshi kar ya dawo".
Cikin sunkuyowa yana kallon hannun yace.
"Bazai shigo ɗakina ba. Ki dena tsoronshi babu abinda ya isa ya miki! Ki dena tsoronshi ko yaushe yana tare dake bai cutar da keba ki yarda dani".
Cikin zubda hawaye tace.
"Ɗan iska ne mugu ne".
Cike da mamaki ya yamutsa fuska tare da cewa.
"Ɗan iska kuma to me yayi miki na iskanci?".
yunƙura tayi ta konta kan gefenta na hagu ya zama fuskarta na kusa da cinyarshi a hankali tace.
"Tattaɓani yayi, yasa hannunshi har cikin".
Sai kuma tayi shiru, cikin rumtse idonshi yace.
"Cikin me?".
A hankali murya na rawa tace.
"Cikin rigata yana taɓa min".
Fuskarshi a murtuƙe kamar zaiyi ruwan jini yace.
"Meyasa kika tsaya har ya taɓa ki, kema iskancin kikeso ayi da keɗin inba iskanciba, ai hannunki ne ke ciwo ba ƙafarki ba, ki gudu mana".
Juyowa yayi ya fuskanceta tare da ciwa.
"Tukunma wanne iskancin ne ke fito dake da dare, in ba bikinku ba ɗaya ba, zakizo kina mana ihu da suman ƙarya ai so kike ayi ta taɓe-taɓe ko?.
In tattaɓakin kikeso anayi ki gaya min mana ba sai in tattaɓakin ba hankalinki ya kwanta in miki abin da kikeso duka har sai kince ya isheki".
Cikin zubda hawaye tace.
"Ina gudu ya kamoni kuma na fitone zanzo kamin tofi a hannuna na haɗu dashi.
Wlh ni dai ba yar iska bace.
Inata ihu har na fame hannuna Ina kafin kukaji kuka fito".
Wani irin kallo ya watsa mata ƙasa-ƙasa kana.
Ya juya ya kwanta, a haka sukayi bacci.
Washe gari da asuba kuwa.
Ta koma ɗakinta tayi baccinta.
Shi kuma yana dawowa masallaci, yayi Azkar ɗinsa.
Kana ya ɗauko gorar zam-zam.
sannan ya ɗauki ganyen magarya guda bakwai, cikin wanda ya amsa wurin Gimbiya Aminatu tun jiya da yamma.
Sa ganyen yayi a cikin gorar bayan ya ɗan sha ruwan ya rageshi.
Kasancewar bakin gorar nada ɗan faɗi.
Haka yasa ya zauna dashi bisa kan sallayarshi.
Ayatul shifa ya fara karantawa yana tofawa cikin ruwan zam-zam da ganyen magarya guda bakwan.
Kulhuwa
Falaƙi
Nasi
Ƙuluhiya
Ayatul-kursiy
Amanar-rasuulu
Attaba'u ma tatlush-shayaɗeenu ala mulki Sulayman.
Ita kuwa Aysha a hankali taje tayi wonka bayan Umaymah ta haɗa mata komai na wonka.
Koda ta fito kasa saka rigar tayi sai dogon wondon kawai ta saka.
Ganin hakane yasa Umaymah ta miƙo mata rigar dama da ɗan madaidacin hijabi a jikinta.
Da hannun hagu ta amshi rigar, ta tsaya tana kallon Umaymah.
Ita kuwa Umaymah cikin bada umarni tace.
"Kije Jazlaan ya saka miki rigar".
Cikin sanyi tace.
"Umaymah Hibba tazo ta saka min".
Fuska ta haɗe tace.
"Kije ya saka miki nace ko".
Cikin sanyi tace to.
Kana ta juya ta funi Side ɗinsa.
Ummi da Hibba da Saratu kuma suna Kitchen.
A hankali ta shiga falon.
Shiru tayi tana tunanin ta yaya zataje tace mishi ya saka mata riga.
Hakan yasa a hankali ta warware karin gugar rigar.
Sannan tasa hannunta na hagun ta riƙe wurin zip ɗin, sannan tasa bakinta kuma ta riƙo wuyan rigar.
Zut taja zip ɗin ta buɗe shi.
Hannunta na hagu ta zura cikin hannun rigar.
Sai kuma ta cireshi a hankali tasa hannun damanta mai ciwon a hankali.
Ya zama rigar na kan kafaɗar hannun damar Tata.
Shi kuwa Sheykh ya gama yin tofin, ya ɗauko goran ruwan ya nufi falon don zai maidashi cikin Fridge.
A hankali ya turo ƙofar.
Dai-dai lokacin ita kuma tasa hannun hagun nata mai lafiyar ta kamo hijabin jikinta ta ɗagoshi ta gaba zata cireshi.
Ya zama daga ita sai dogon wondon, daga ƙugunta zuwa shafeffen cikinta da ƙirjinta dake cike tab-tab da jajayen Caɓɓule duk suna fili.
Wani irin ƙara tayi a hankali jin hijabin ya riƙo ɗan kunnenta yaja da ƙarfi.
Da sauri tace.
"Wayyo Allah na ya zanyi hannu mai ciwo hijabi ya riƙe ɗan kunne, riga bata shigaba".
A hankali ta fara juyi tana kiran Ummi Ummi.
sabida duk yadda ta motsa hijabin sai taji ya ƙara jan hujin kunnenta.
Yadda take taku tana juyi ne yasa jikinta keyin wani irin kaɗawa.
Shi kuwa Sheykh, wani irin masifeffen numfashin ya fixga da azaban ƙarfi.
Rumtse idonshi yayi da sauri.
Tare da juyawa ya fuskanci Dinning area idonshi a rufe.
Yana jin tsikar jikinshi yana zubawa yana mummiƙewa.
Zuciyarshi na harbawa a dubu.
Yana isa ya ajiye goran kan Fridge ɗinsa.
Sannan ya juyo da sauri.
Juyowar da zaiyi kenan yaji yayi karo da ita.
Ta manna bayanta a ƙ....!
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta ƙara matsowa gabanshi.
A hankali tasa ƴar yatsarta ma nuniya dai-dai inda taga kan macijin.
Wurinda shi kuma yake masifar yimishi ƙaiƙayi.
Hannunta ɗayan kuma ta maidashi ta riƙe bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.
Ido ya zuba mata, cike da mamaki da kaɗuwa, da al'ajabi to me hakan me zatayi.
A hankali ta fara bin zanen kan macijiyar tana danna yatsarta, tanayi ƙasa da yatsar.
Wani irin yam-yam haka tsikar jikinshi ke tashi tana zubawa wani irin abu yakeji yana zir-zir-zirrrrr cikin jikinshi gaba ɗaya, abune da bai taɓa jin makamancinsa ba a rayuwarsa.
Cikin wani irin masifeffen da kasala daya diro mishi ya buɗi bakinshi a hankali yace.
"M.. me h hakan.".
Manna kanta tayi da ƙirjinshi ta kife kunnenta dai-dai kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa da sauri-sauri dib-dib dib-dib.
Cikin wata muryar data ganar dashi,
ba ita bace, bata haiyacinta mutanenta ne a kusa tace.
"Kayi shiru da Allah".
Kanshi ya sunkuyar a hankali.
Idonta a lumshe hawaye na zuba.
Cikin raunin muryar tace.
"Wurin yanayi maka ƙaiƙayi wasu lokutan ne?".
"Uhummmmmm". shine abinda kawai ya iya furtawa.
Ita kuwa ƙara shigewa jikinshi tayi.
tare da cewa.
"To kayi wa kanka jinyar wurin mana.
wannan zanen yana daga kan babbar yatsarka har zuwa nan.
Yana bin jikinka, kayi ma kanka aikin irin wanda kayi wa Aysha a ciwon hannunta.
Kana sha kana shafawa a wurin.
Zai bar jikinka zai ɓace duka.
Yanzu dai baya ci gaba da tafiya,
tunda Aysha ta tone aikin".
A hankali yace.
"Yau kuma zuwa kika sakeyi kenan? Bazaki bar jikinta ba kenan kike nufi? Sai ki biyota har ɗakina dan baki da tsoron Allah".
A hankali tace.
"Inada tsoron Allah wlh nima musulmace Kamarku.
Kafurun iska ko mugu bazai taɓa iya ratso cikin sashin kaba.
Sabida ka wadata wurin da ambaton Allah.
Ko yaushe madadin kallace- kallacen tv na banza da wofi karatun al'ƙur'ani kake sawa.
Duk sashin gidanka majigine na ƙura'an.
Ni ba muguwar iska bace.
Bana sata faɗuwa, ko kuka bare ihu.
Bana samata koda ciwon kai.
Ina kuma kareta ne ga wasu ababen cutarwa
wasu lokutan idonta kan iya ganin abinda ba kowa ke ganiba. Wanda wannan baiwar tace tun tana ƴar ƙaramarta"
Cikin dakekkiyar murya yace.
"Ki bar jikinta bana so.
Kina sata yin abinda in tana haiyacinta ba yinshi zatayi ba."
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Shike nan na tafi, amman in buƙatar zuwana yayi zaka gane nazo.
abinda ma babu wanda ya taɓa gane ina jikinta sai kai daga nayi mgn sai ka gane.
Zan tafi, amman tanada buƙatar daya kawota wurinka.
Zata roƙekasa yayunta a addu'o'in kane.
sabida sun ɓata tsawon lokaci har yau babu lbrinsu."
Cikin haɗe fuskarshi yace.
"Na sani ai, ba sai kin gaya minba, Ni nan nasan komai a kan matata, nasan abinda ya faru da yayunta jeki kawai".
Atishawa tayi a hankali.
Sai gashi ta narke a jikinshi tayi lib ido a lumshe alamun tayi bacci.
A hankali ya gyara tsayuwarshi.
Tallabeta yayi da kyau.
Hannunshi yasa ya cire hijabin jikinta.
A ranshi yake mgna.
"Na fahimta kenan iyayenta ma, basuma san tanada wata iska a jikinta ba.
Shiyasa basu sanarba kafin a ɗaura auren".
Ido ya lumshe yana goge wannan ayar tambayar da ya bugawa Bappa cikin ƙoƙolwarshi na ya aurar da yarshi ba tare daya sanar musu tanada al'matsutsaiba kamar yadda shariya tace.
A hankali ya zauna bakin gadon da ita.
Yana nazartan abubuwa da dama.
Ya fara fahimtar wasu ababen a kanta musamman da yake Junaidu ya labarta mishi komai abinda ya sani a kan Shatu da Ba'ana lokacin da suke asibitinshi Valli.
konciya yayi a gefen daya kwantar da ita.
Kana yasa hannunshi ya kashe wutan ɗakin.
Ido ya lumshe ba tare da yayi baccinba.
Ita kuwa Aysha a hankali ta farka daga baccin, ido ta ɗan buɗe.
tabbas kam tasan tazo ɗakin shi kuma tasan ta ganshi babu riga daga nan kuma bata kuma sanin meke wakana ba.
cikin sanyi take juya kwayar idonta.
A hankali ta kalleshi yana konce yayi rigingine, cikin sanyin murya alamun baccin tace.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh!".
A hankali ya ɗan juya kwayar idonshi ya kalleta.
cikin sanyi yasa hannunshi ya jawota jikinshi.
Kan ƙirjinshi ya kwantar da ita.
Yana mai jin wani irin baƙon yanayi yana game dukkanin sasan jikinsa gaba ɗaya.
Shiru tayi jikinta na wani irin sassanyan tsuma can ciki-ciki.
Cikin sanyi tace.
"Zan kwanta".
Cikin sanyi murya can ƙasa yace.
"Yanzu a tsaye kike ai".
Ya bata amsa a daƙile, shirun ta kumayi.
Shi kuwa gyara kwanciyar tasu yayi.
Tare da jawo blanket ya rufesu.
kana ya fara Addu'o'in yanayi yana tofawa a tafin hannunshi yana shafawa a fuskarta da sassan jikinta.
Idanunta ta lumshe yanaji sanyin tattausar fatar hannunshi.
A haka sukayi bacci, ɗaki ɗaya gado ɗaya borgo ɗaya pillow ɗaya a liƙe a jikin juna.
Karo na forko kenan da wannan kusancin ya samu tsakaninsu.
Washe gari kuwa.
Lamiɗo ya ƙara neman Sheykh akan batun tafiyar da dole zaiyita.
Shi kam yace zai tura wasu.
Dan yana son zuwa aikin haji,
Amman fir tsohon nan yaƙi.
Ya haɗashi da Abbanshi dole ya haƙura.
Washe gari da safe.
Mami matar Affan tazo, ita da Zahra'n Hamma Yusuf.
Bayan sun gaisane tace.
"Ga ƙanwata Zahra matar Yusuf".
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
"Ayyah ai kuna kama fa".
Da sauri Mami tace.
"A a na fita kyau duk gidanmu itace mummunar mu fa".
Dariya Zahra tayi tare da cewa.
"A daba".
Nan Aunty Juwairiyya ta shigo sukaci gaba da hira,
Ummi da Saratu suna kitchen.
To haka dai mafi akasarin lokuta Mami kanzo susha hira.
Tofa nan kewar ke ɗan raguwar mata, wani lokacin kuma ta kira Bappa susha hira ko ta kira Rafi'a ko Junaidu taji lbrin Rugar Bani.
Yau sallan layya saura sati biyu.
Kuma gobene Sheykh zai fita.
dole kuma tafiyar da motace bazai yiwu ta jirgiba.
Tunda rugogin manyan Arɗaɓe zai ziyarta wanda cikin dazuka suke.
Yana zaune a falon Lamiɗo shida Abbanshi da Galadima.
"Ka gama shiryawa ko Muhammad?".
Abba ya tambayeshi cikin kula.
Kanshi ya ɗan gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Lamiɗo ne ya ɗan shafi kan shi tare da cewa.
"Itama iyalin taka ta gama kimtsawa ko?".
Da sauri ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Ta kimtsa taje ina ɗin?".
Abba ne ya bashi amsa cikin bada umarni yace.
"Ta kimtsa ku tafi tare, dole tare zakuje".
A hankali yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
"Dan Allah Abba tafiyar da nima ba sonta nakeyi ba, a kuma sake haɗani da wani jidalin".
Fuska a haɗe Abba yace.
"A bayanka akace ka goyeta ku tafi ne?".
A hankali ya jujjuya kai.
Cikin yanke hukunci yace.
"To ku tafi tare Muhammad bana son musu a kan yarinyar nan duk abinda akace kayi dan Allah kayi tunda ba wanda ya saɓawa shariyar musulunci za'ace kayi ba.
Baka san abinda muke zaton samu ta sanadinta ba.
Muna ganin nasarori kan matsalarmu. Kaje da matarka kaji ko Muhammad na".
A hankali yace.
"To Abba ba komai in dai zakayi farin cikin hakan zanje da itan".
Kanshi ya shafa tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace cikin jin daɗi.
Kana ya sallamesu ya fita.
A falo ya samu Ummi ita ɗaya tana kallon wata tashar da aka saka wa'azin shi.
Cikin sanyi yace.
"Ummi gani gaki sai kin kalleni a tv".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ina ƙaruwa ne ai".
Kanshi ya jinjina tare da ɗan kallon gefe da gefe kana yace.
"Ummi ina take?".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Tana ɗakinta".
Kanshi ya gyaɗa kana yace.
"To Ummi Lamiɗo yace wai dole da ita zamuyi tafiyar zaga rugar Arɗabe.
A gaya mata ta shirya gobe sammako zamuyi inga ko zamu gama cikin kwana huɗun".
Cikin murmushin Ummi tace.
"To bari in gaya mata".
To yace shi ya nufi sashinsa.
Ita kuma ta nufi ɗakinta.
A gaban mirror ta sameta tanayiwa kanta kitson kalba manya-manya.
"Kitso kikeyi ne?".
Juyowa tayi tare da cewa.
"Har na gama ma!".
"Kuma yayi kyau sosai fa".
Dariya tayi tare da cewa.
"Allah ko Ummi".
Kai ta gyaɗa alamun eh.
Kana tace.
"Sheykh yace in gaya miki ki shirya gobe zaku tafi tare yawon ziyartan Arɗaɓen inda dama na gaya miki zaiyi tafi, duk an turawa Arɗaɓen saƙon zuwanshi ma".
Cikin jin daɗi tace.
"Kai naji daɗi na, zan fita in zagaya inga makiyayan in huta da zaman wuri ɗaya".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Wato zakije kiga fulani yan uwanki ko".
"Sosai ma kuwa Ummi yanzu tayani shiryawa".
Ta faɗa tana buɗe drower'n.
Nan kuwa Ummi ta tayata ta kimtsa ababen buƙatar ta.
Sannan suka fito falon inda suka samu Jamil ya dawo aiki Jalal kuma dama yana sashin Hajia Mama ne.
Sai yanzu ya dawo nan ɗin nan suka zauna sukaci gaba da hira.
Washe gari da safe suka fito cikin shirin tafiyar.
Motoci guda bakwai ne uku a gaban ta Sheykh uku a bayan tashi.
Biyu na gaba fadawa sai ta ukun Jalal ne da wasu mutane su biyu.
Sai motar Sheykh shida Aysha suna baya Ado na jan motar.
Sai wacce take binsu Affan ne da Ya Hashim sai Sulaiman kana Laminu ɗan jaridar, da zai ɗauki komai.
Sai biyu kuma na baya kuma Galadima ne.
Sai fadawa da godarai sai hadimai mata biyu da zasuyiwa Aysha hidima.
Tafiya mai ɗan nisa sukayi.
Kana suka ratsa wata babbar hanyar birji, suka fara tafiya suna kutsawa cikin daji.
A ƙalla awa ɗaya suna tafiya.
Sunata wuce ƙananan rugagen Fulani makiyaya, da dabbobinsu.
Kasan cewar manyan motocine masu inganci yasa.
Basu jin wannan gargada ta buwayesu.
Jalal da abokanshi sunata hira, sosai Jamil yayi mamakin sakin fuskar Jalal cikin abokanshi.
Sannan sukanyi mgna da wani salo na musamman.
Shi kuwa Jamil waya yakeyi da Khairat sabuwar budurwarshi.
A can baya kuwa Affan ne liƙe da waya a kunne yana mgna da Yusuf.
A motar Sheykh kuwa, shiru kakeji kowa da sabgar da yakeyi.
Shi zaune yake da kyau ya buɗe system ɗinshi yana wani aiki a ciki.
Hankalinshi duk yana kanta.
Ita kuwa Aysha wani irin farin ciki mai zaman kashi takeyi.
Shiyasa hankalinta kab yana kan rugagen Fulani da suke wucewa.
Murmushi mai baiyana shauƙinta da begen irin wuraren takeyi, yana tuno mata Rugar Bani, da sauran inda suka zauna.
Kana tana farin cikin bin wannan tafiyar ne ko zataga wani abin da ya shafi su Ya Gaini.
Ɗan juya kwayar idonshi yayi ya kalli inda take.
Hankalinta duk yana kan window.
Taɓe baki yayi kana ya maida idonshi kan fuskar na'urar tashi.
Wani babban rugar Jafun suka fara isa.
Rugar a cike take maƙil da maza da mata matasa da sofaffi
Bisa alumun sun san da wannan ziyar shiyasa basu fita kiwo ba.
Bayan sunyi parking ne.
Fadawan suka fara fitowa.
Sukazo sukayi buɗe wa sauran motocinsu.
Galadima ne ya fara fita kana gaba ɗaya su Jamil Jalal dasu Affan suka fito.
Ita kuwa Aysha da sauri ta yunƙura zata fita kasan cewar ta gefen da take aka buɗe.
Hannunshi yasa ya riƙo nata.
Da sauri ta juyo ta kalleshi cikin sanyi tace.
"Ba fita zamuyi ba?".
Ido ya zubawa fuskarta yana kallon yadda take mgn da alamun tsiwa da tura baki.
Uhum wato yanzu ta worke tsiwar zata dawo.
Ya raya a ransa,
a zahiri kuma kai ya jujjuya mata, tare da ronƙofowa, kan cinyoyinta.
Hannunshi ya miƙa ya jawo marfin ya rufe.
Su Galadima kuwa kan zuwa sukayi suka zagaye motar tashi, suna jiran fitowarshi.
A hankali ya buɗe marfin dake kusa dashi.
Kana yasa ƙafarshi ta dama, ya fita.
Meda ƙofar yayi ya rufe ganin tana shirin fitowa.
Buɗe al'kyabbar jikinshi yayi kana ya gyara zamanta.
Bayanshi Galadima ya koma.
Sannan Jalal da abokanshi suka koma gefe-gefenshi.
Sauran ayari kuma suka rufa mishi baya.
Su kuwa can cikin taron fulanin da sauri Arɗo Maru ya miƙe da sauran ƙananan Arɗo na gefenshi,
kasan cewar shine Arɗon araɗabe na yankin gaba ɗaya.
Da sauri suka nufosu cikin mutumtaka