Showing 222001 words to 225000 words out of 352722 words

Chapter 75 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30737

yayi duhu yayi dim sai azabar zafi da ake tsulawa zafi irin na tsakiyar damuna irin wanda in an kwana biyu ba'ayi ruwan samaba, bisa alamu hadari ke diddigowa daga ƙasa shiyasa garin yayi dim babu alamun iska.

Suna shiga Boka Tsitaka ya kwashe da dariya tare da cewa.
"Lbri mara daɗin gashi can konce da matarsa bisa gado ɗaya, sai dai kun san ɗan naku ba'a iya ganin sirrinshi, ko matar tashi bana gani sai wani haske daya rufesu.
Kuma yana gab da ɗirkawa ƴar fulani ciki hegen yaro dan yanada ƙoyayen haihuwa da ƙenƙesa".
Cikin tashin hankali ɗayan yace.
"Kusantar mata harda haihuwa, anya kuwa bazan sa a dandatse min wannan yaron ba, shin wai shi wanne irin mutum ne da baya jin sihiri da tuggu da makirci".
Ɗayan ne yace.
"Ai kuwa koda ya haihu yarane dai bazasu rayuba".
Dariyar mugunta Boka Tsitaka yayi tare da cewa.
"Ku dai kun iya kawo aiki kun kuma iya faɗin mugunta sai dai tabbas akwai wani wanda yake gefenku, da yake aikata musu fiye da shirinku, kullum in kun tuna yimasa wani abun kafinma kuyi abun zakuga fiye da hakan ya faru tun shekarun baya.
To bare kuma yanzu an sake samun wani taƙadirin ma yasa mishi ido".
Dariyar jin daɗi sukayi kana sukaci gaba da muhawarar mugunta.

Washe gari azahar Gimbiya Aminatu ce zaune gefen Lamiɗo da ya kira Sheykh suna gaisawa, tare da cewa.
"Muhammadu Akwai babban uzurin dake buƙatar ka dawo gobe".
Gyara zamanshi yayi tare da kallon Aysha dake gefenshi ita da Hibba da Jalal da sune suka kawo musu abinci a hotel ɗin da suke. Maida kanshi yayi ya jingina da kujera kana ya lumshe idonshi tare da cewa.
"Eh dama gobe zamu taho, amman sai dare jirginmu zai tashi.
Su Ya Hisham da Affan kuwa sunce sammako zasuyi wai tafiyar mota zasuyi".
Cikin sauƙe numfashin Lamiɗo yace.
"To Allah ya kaimu ya kuma dawo daku lfy, itafa Juwairiyya sai yaushe zata dawo".
Kanshi ya ɗan mirgina kana yace.
"Zan dai taho da Ya Jafar da Jalal, in bata gama uzurorinta ba, sai ta koma masarautar Jadda ta dawo daga baya."
Cikin gamsuwa da hakan Lamiɗo yace.
"To hakan yayi Allah ya kawoku lfy".
Amin Amin yace kana ya katse kiran.

Jalal ne da Hibba suka miƙa tare da cewa.
"Mu zamu tafi."
Bai kulasu ba, Jalal ne ya ɗan matsoshi tare da cewa.
"Umaymah tace ka kai mata Ɗiyarta taga ya ta kwana da jikin".
Kai ya gyaɗa alamar to.
kana Hibba ta kalleta tare da cewa.
"Aunty Aysha sai kin dawo, Allah ya ƙara sauƙin".
Amin tace tana gyara zamanta tare da jawo ƴar jakar kayan da Hibba ta kawo mata. Wai na anko ɗin fansan idon da za'ayi.

Su kuma nan suka fita.

Suna fita, ya miƙe ya rufe ƙofar, kana ya dawo ya hau kan gado ya kwanta.
Da ido ta bishi tare da cewa.
"Yah Sheykh gado kuma to yaushe zamu tafi ko inbi su Hibba kawai ne?".
Lumshe idonshi yayi alamun bacci zaiyi, a hankali tace.
"Dole ne kullum sai kayi baccin tsakanin azahar da la'asar ɗin nan". Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh.
kana ya juya mata baya.

Dole itama ɗin ta hau ta kwanta, tana konciya ya jawota jikinshi nan take sukayi bacci.


Ƙarfe uku da minti arba'in da biyar ya farka, da sauri ya zareta daga jikinshi kana ya shiga bathroom, wonka yayi fes kana yayi al'wala ya fito.
zaune ya sameta bakin gado.
"Tashi kiyi wonka mu tafi tunda ke bakya cikin masuyin salla".
Cikin sanyi tace.
"Ah ina cikin masuyin salla mana".
Kai ya gyaɗa yana zura tattausan al'kyabbar shi. Yace.
"Eh amman ni dai tun jiya banga kinyi salla ba".
Cikin rashin fahimtar wayon da yake mata tace.
"In Sha Allah gobe dai da safe ai zan fara".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To tashi kiyi wonka kafin inyi sallan".
To tace kana ta miƙe ta shiga Bathroom da ƴar jakar kayanta.
Shi kuwa ya kabbarta sallan la'asar.

A cikin bathroom ɗin ta canza kayanta bayan ta kimtsa jikinta.
Kana ta ninke wanda ta cire ta saka a ciki ta feshe jikinta da turarenta mai sanyin ƙamshi, sannan ta fito.

Zaune ta sameshi bisa sallayar yasa System ɗinshi a gaba ya maida hankalinshi kab kanta. Bisa alamun wani abu mai tarin mahimmanci yakeyi.
Dan gaba ɗaya yatsun hannunshi aiki sukeyi sai kwayar idanunshi da yake jujjuyawa kan screen ɗin na'ura. Yanayi kuma yana motsa lips ɗinshi alamun still kuma tasbihi yakeyi bincikar number da ake tura masa text a rufe yakeyi yadda zai samu ya buɗe layin yabi diddiginshi.
A hankali ta kalleshi da kyau, kana ta kalli kayanshi da ya cire ɗauka tayi ta ninninkesu ninkewa mai kyau, tasa a ƴar jakar ta zuge zip ta rufe.
Sannan ta koma gefenshi can ta zauna bayanshi.
Cikin sanyi tace.
"Ni dai banga wayata ba".
Bai kulata ba, domin aikin da yakeyi ya tunzura mishi nitsuwa.
Cikin sanyi tace.
"Ayyah to dan Allah. Sammin wayarka in yi kira".
Tura mata wayarshi dake gefenshi yayi sabida ya samu ta rabu dashi dan tana raba mishi hankali".
Ɗaukar wayar tayi sai kuma taga akwai security code a jiki.
Matsoshi tayi da mamaki dan tasan akwai woyoyin shi biyu data taɓa riƙewa basa da security, jujjuya yar wayar tayi ganin yar micilace kuma harda liƙa mata matakan tsaro, taɓe baki tayi tare da cewa.
"Me code ɗin buɗe shi".
"Mamey". Yace mata ba tare da ya kalleta ba.
jujjuya yar mitsitsiyar wayar tayi a tafin hannunta, contacts ta danna da nufin ta ɗan duba ko da number sai ta samu nanma a garƙame yake.
Ikon Allah tace a hankali kana ta danna. Phone na ma kirib yake, cike da mamaki tace.
"Wayarfa tako ina ansa mata kan tsaro".
Da sauri ya juyo ya kalli wayar da ke hannunta. Hannunshi yasa ya amshi wayar da sauri tare da zurata a al'jihunsa kana ya yasa kan yatsunshi ya ɗan bugi goshinsa tare da kwaɓe fuska kana ya kalleta cike da alamun damuwa yace.
"Kai Alhamdulillah, Allah na gode maka daka jarabceni da wannan fitinenneyar yarinya Aish mata, kinzo kin tasani gaba da surutu, kuma kina gani aiki nakeyi, ko so kike na ki rikitamin tunani ne".
Kanta ta langoɓar tare da kwaɓe fuska tace.
"A a, Ni kawai wayata zan kira".
Cikin zubawa lips ɗinta ido yace.
"Ba kin barta a motaba".
Da sauri tace.
"Laah hakafa ni na manta ma".
Kanshi ya gyaɗa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci System ɗin nasa.
Gefenshi ta ɗan kalla tare da cewa.
"Yah Sheykh!".
Shiru bai amsa ba yaci gaba da aikinshi.
a hankali ta kuma cewa.
"Yah Sheykh!!".
Bai amsaba bai kalleta ba.
A karo na huɗu ta kuma kiranshi.
"Yah Sheykhhhh". Ta ƙarashe kiran murya can ƙasa da alamun bacci ya fara kamata, a hankali ya ɗan juyo kwayar idanunshi ya kalli inda take.
Cikin lumshe ido tace.
"Mu tafi mana, za'ayi fansan ido da bamu jeba".
Kanshi ya gyaɗa alamun to, daga nan ya meda kai yaci gaba da aiki.

A can gida kuwa, tuni anyi fansan idon amarya da ango gaba ɗaya an gama komi da komai.

Har an fara shirya farfajiyar Side ɗin Umaymah wanda anan za'ayi shagalin mother's day ɗin.
An gyara wurin an kimtsa an shirya komai yadda ya kamata.

Ƙarfe biyar dai-dai duk an gama shirya amarya cikin shiga ta al'farma, hakama ango Haroon ɗan ayi.
Aunty Rahma kuwa tasa mabusan masarauta da makaɗa yan kakaki da tambura da al'gaita duk sun shiryawa shagalin tunda abu na jinin sarauta ai dole a gwada iyawar.

Safiyyah ce ta shigo bedroom ɗin Umaymah inda ta wuce zugan ƙawayen ta duk suna falo cikin kwalliyar ƙasaitattun mata, matsowa kusa da Umaymah tayi tare da cewa.
"Umaymah Aysha fa har yanzu fa Hamma Jabeer bai kawota ba,".
Cikin sauri Aunty Juwairiyya tace.
"Dan Allah Umaymah kirashi ya kawota Mamma tace su Haroon ma bazasu fitoba sai sun iso".
Murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
"Uhummm Jazlaan fa ba son waɗannan abubuwan yake ba. Bana son tirsasa masa yin abinda baya so ku kuma kun dage, ala dole tunda bikinsa ba shiri ba'a zoba yanzu sai kunyi shagalin".
Ummi ce ta ɗanyi murmushi tare da cewa.
"To bari ni in kirashi".
Cikin sauri Umaymah tace.
"Yauwa yama fi min".
Ita kuwa Ummi wayarta ta kara a kunne bayan ta danna mishi kira.
Bugu biyu ana uku taji ya katse kiran.
Jim kaɗan kuwa sai ga kiranshi.
Bayan sun gaisane sai kuma ta ɗan yi shiru.
Jin hakane ya sashi cewa.
"Na'am Ummi meke faruwa ne?".
Cikin tausasa murya tace.
"Eh dama duk an gama shirine ku kaɗai ake jira".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Haroon dake ta murmushi kana a hankali yace.
"Ummi ai mun dawo, yanzu muka shigo, bata iso wurinku bane?".
Da sauri Ummi ta juyo ta kalli bakin ƙofar jin muryar, Aysha tana sallama.
"Yauwa gata ta iso". Ta faɗa mishi tare da katse kiran".
Safiyyah ce tayi sauri kamo hannun Aysha tare da cewa.
"Yauwa zo muje ɗakin Hibba ki shirya".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Safiyyah barni mu gaisa dasu Umaymah mana".
Murmushi Mamma da yanzu ta shigo tayi tare da cewa.
"Uhumm Safiyyah kuwa da gaggawa".
Cikin ladab da biyayya ta rusuna ta gaidasu kana, Safiyyah ta jata suka tafi ɗakin Hibba.

A can Side ɗin dasu Haroon suke kuwa, Ibrahim ne ya ɗauko wasu tattausan kaya masu masifar kyau da taushi, yadin Getzner ne mai ɗan karen kyau kalar pink guava mai masifar kyau, riga da wonɗone da babbar riga gariya an watsawa mats aiki da surfani mint green color irin mai sheƙin nan, sai baƙin hula mai ɗan karen kyau shima da ratsin mint green da fari,
amsa yayi tare da kallon Haroon da Ibrahim ɗin sosai kayan sukayi masifar musu kyau, kanshi ya ɗan juya ya kalli takalman da Ibrahim ke nuna mishi baƙaƙene irin masu sheƙin fatar nanne.
Fita sukayi, dan bashi wuri yasa kayan.

Sosai kayan sukayi masifar amsar fatar jikinshi da surarshi ya fito ras balaraben asali. Komai.
Hular ta zauna ras a kanshi, gefe da gefen kan nashi duk tattausan sumanshi ya ɗan fito, Especially ƙeyarshi da sumar ta kwanta lib kana farar fatarshi tayi ras ciki sajenshi da girarshi komai tubar kalla masha ALLAH.

A hankali ya taƙo ya fito falo.
Nan take su Haroon Suka miƙe, kasan cewar duk abokansu sun tafi sun watse tunda bikin maza ya ƙare, sai su uku suka rage sai kuma su Ya Hisham, Affan, Jamil, Jalal, Azeez, Sadiq, imran, Kabir, Kamal, Sulaiman, da dai sauran ƴan uwa da wasu makusanta.
Haka suka fito a tare,
Tuni harabar wurin ta cika tayi maƙil manyan matane tako ina matan sarakuna da manyan yan kasuwa da siyasa, aminan Umaymah da matan abokon Abbansu Haroon, sabida ranar tasuce ko wacce tasan Umaymah da Jazlaan ɗin ta sun san soyayyarsa a ranta fiye data Haroon ce sun kuwa san biyayyarsa gareta.

Shiru wurin babu hayaniya, hakane yasa Sheykh bai damuba dan baiga abun kiɗe-kiɗen da ya tsana ba.
Kuma gashi babu wasu taron maza, duk ƙannenshi ne.
Sai kuma iyayenshi, duk da har ga Allah har ransa baiso wannan tsarin ba sai dai bisa dole Umaymah'nshi da Abba Hajia Mama da Ummi suka tirsasashi.
Kuma suma basu san Aunty Rahma ta tsara kayan kiɗa da bushe-bushen sarewa da al'gaitanba.

"To ma in banda su Umaymah ya za'ayi ayi abu salam".
inji Aunty Rahma da take tare da mabusan. Hibba ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Ai kuwa Hamma Jabeer zaiyi faɗa".
Dariya tayi tare da cewa.
"Me ruwana".
Sai kuma ta juyo ta kallesu tare da cewa.
"Kuna ganin amaren sun fito ku fara buga tambura da kakaki ayi bikin gidajen sarakuna haka Salam".
Ai kuwa bata ida rufe baki ba.
Aunty Juwairiyya ta buɗe ƙofar babban falon Umaymah ta fito ita da Jazrah.
Jannart na bayanta Aysha na bayanta.
Sai kuma Safiyyah ta biyosu.


Wani irin murmushi da gyaɗa kai Aunty Rahma tayi lokacin da taji an saki sautin tamburan.
"Uhum yauwa haka mana asan ana biki kam".
Ta ƙarashe mgnar tana tahowo kusa dasu Umaymah cike da mamaki suke kallonta ita kuwa tana musu murmushi Yar autar Sitti kenan.

A hankali Aysha ta lumshe idonta sabida wani irin yam da taji tsikar jikinta na badawa.
Hannun Safiyyah dake riƙe da nata ta ɗan juya itama ta riƙe.

A hankali sukaci gaba da taku cikin irin wasu masifaffun kaya masu masifar kyau, irin dai kayyakin nan da yan gayu ke sawa mai shara-sharan tattausan yadin cikin pink guava ne, kana net ɗin saman kuwa mint green ne. Anyi ɗinkunan dogayen riguna masu kyau cib cib da jikinsu.
Sai wasu takalma masu ɗan karen tsini kalar azurfa da yar karamar fosa sai a goggoronsu shina kolon takalman. Sosai sukayi kyau,

A hankali suke shigowa cikin taron ana mc ɗin yana mai bin waƙar da ya saki ta.
"Ku-martsa-ku-martsa ga amarya ta iso".
Wani irin murmushi mai cike da jin daɗi Umaymah tayi kana ta kalli Hajia Mama dake gefenta tace.
"Kinga surkanki masha Allah".
Uhummmm tace tare da kaɗa ƙafarta.

Sheykh kuwa wani irin rumtse idanunshi yayi lokacin da yaji an saki kuɗin badujalan injishi da faɗin.
Tsayawa yayi cak ba tare da ya ƙara koda taku ɗaya ba.
Haroon da sauran tawagar ma tsayuwa sukayi, Ibrahim ne ya ƙara matsoshi tare da cewa.
"Dan Allah kayi haƙuri mu ƙarasa koda 5 minute ne kayi sai ka tashi. Dan Allah muje Umaymah zataji daɗin hakan".
Cikin takaici yace.
"Bazan jeb..".
Bai rufe bakinshi ba yaji an riƙe hannunshi na dama da sauri ya juyo, Aunty Hafsat Mamma kenan
Cikin sanyin murya tace.
"Dan Allah Muhammad muje na roƙi wannan al'farmar kayiwa Allah da Manzonsa muje, koda zaman daƙiƙu ukune kayi. Kada mu kunyata wurin aminan Umaymah".
Ya zaiyi sun gama ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa,
Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi kana ya gyaɗa kanshi yaci gaba da tafiya.
Still Mamma na rike da hannunshi a haka har suka iso, farfajiyar wurin.

Har gaban kujeru inda aka shirya wurin zamansu taje ta ajiyeshi kusa da Aysha, tuni shi Haroon ya zauna kusa da amaryarsa.
Shi kuwa Ibrahim shima ya zauna gefen Safiyyarshi.

Kana su Affan kuwa duk suka zauna tare dasu Jazrah da Azeema da Hibba da sauran cousin sisters ɗin su.

Mc ne ya fara shelan Amare su fito, surkansu su nuna musu gata.
A hankali Jannart ta miƙe tsaye sabida ita duk yan uwanta ne, ita kuwa Aysha gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi Allah ya sani ita dai tana tsoron idon mutane, ganin bata miƙe tsayeba ne, yasa Aunty Rahma yin sauri ta iso garesu sunkuyowa tayi ta kamo hannun Aysha tana miƙar da ita tsaye.
Ɗan juyowa tayi ta kalli Sheykh.
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Zabiya kiyi a hankali dai dan dujal da ganga yake baiyana tsoro nake jiye miki kada ki zama cikin mabiyansa".
Murmushi tayi kana taja hannun Aysha suka shiga cikin taron tare da Jannart.
Wani sassanyan waƙa aka saki.
Kana su Hibba suka taso da sauri suna feffesa turare mai ƙamshi kana da bada wani kala na musamman.

Cikin tsananin jin daɗi Umaymah, Mamma Aunty Rahma, Hajia Mama. Suka fito bisa dandamali buɗe bakin jakukkunansu sukayi, wani irin liƙi na musamman sukeyiwa amarenta tamkar babu talauci.
Gaba ɗayansu da 1-1k suke liƙi cikin ƙasaita.

Kusan 5 minute sukayi suna liƙi kana MC yace su koma su zauna su huta.

Wani irin banbaraƙwai Sheykh yake ganin abun sabida shi dai a iya tsawon tarihin rayuwarsa bai taɓa zuwa ba, kuma shi bai taɓa ganin tsarin wannan bidi'o'inba.
Ina dalili wannan abun, ai ko basuyi hakaba tabbas an san dai suna cikin farin cikin.

Baya zamansu kamar da mintuna 3 MC ya kuma kiran amare dasu fito tsakiyar taron.
A hankali suka miƙe tsaye,
kana suka fara tafiya a hankali,
wani irin masifeffen zubawa tsikar jikin Aysha yayi tare da bugawan ƙirji da ƙarfi.
Sabida sarewa da al'gaita da tamburan da kakakin da aka sake gaba ɗaya a lokaci ɗaya.
A hankali dai suke takowa, suna nufo tsakiyar taron.

Nan MC ya kuma cewa yana buƙatar uwar angwayen Gimbiya Khadijah Umaymah kenan da tawagar ƙawayenta.
A nitse Umaymah ta miƙe kana Su Hajia Kubra, Hajia Rakiya, Gimbiya Ruƙayya Hajia Maimunatu sai kuma Ummi da dai sauransu.

Suna shigowa Umaymah taci gaba da yin liƙin 1-1k duk sauran kuma 5-500 suka fara miƙa wa.

Yadda ake busan sarewa ne yake ta'azzara tashin tsikar jikinta da kuma bugawan zuciya.
Busar sarewan yakeyi mai busar cike da iyawa da ƙwarewa da bajinta,.

Kana ga tamburan da aketa dokawa, a hankali Aysha ta sunkuyar da kanta tare da rumtse idanunta jin naman jikinta ya fara tsuma da karkarwa.

Cikin haka MC ya buɗe muryarshi da azaban ƙarfi tare da cewa.
"In kaji tambura sai Babbar fada kakaki da al'gaita mabusar masarauta ne.
ai duk daren daɗewar tsuntsu a sararin samani bai kai tala-talaba kaga jefa garma a caɓe sai ɗan gada kiɗan shantu sai mata.
Ina angwayen Gimbiya Aysha da Gimbiya Jannart fili dominku ku shigo gaban iyayenku".
Wani irin haɗe fuska Sheykh yayi to waima ta yaya ta ina zai fara.
Haroon kuwa tuni ya miƙe dan gaba ɗaya tsikar jikinshi tashi yakeyi sabida kirarin da akayi musu.
Hannunshi yasa ya kamo hannun Sheykh kana yaja,
Ƙin miƙewa yayi. Sai dai kuma ya ɗago kanshi ya kalli can tsakiyar taron tsakanin kafaɗun Ummi da Hajia Kubra ya hango Aysha, Ido ya zuwa fuskarta da kyau, kasan cewar shi a zaune yake ita kuma a tsaye take ta kuma rusunar da kanta yasa yana kallon fuskarta ras.
Cike da mamaki Haroon ya kalleshi ganin ya miƙe ya kuma nufi wurin.
juyawa yayi kana yabi bayanshi suka fara taku a tare.
MC ne ya ɗan dakada daga kirarin da yakeyi kana ya buɗe murya tare da cewa.
"Gimbiya Khadijah Umaymah ga yaranki angwayen a bayanki a basu wuri su ƙarasa kusa da amaren.
Da sauri Umaymah da Ummi suka ɗan ja da baya suka basu hanya.
A hankali Haroon ya matso kusa da Jannart.
wani sabon liƙi Umaymah da ƙawayenta suka fara, shi kuwa Sheykh a hankali yake ƙara matso inda Aysha take tsaye.
Ita kuwa Aysha wani irin tsuma da karkarwa jikin ta yakeyi tuni numfashinta ya fara fizga.
Ido Sheykh ya zubawa goshinta ganin yadda zufa ta tsastsafo mata, har tana kwaranya ta gefen kunnenta.
A hankali ya ƙara matsota wanda hakan yasa mutane zaton wani salone kawai nashi.
Haka yasa Mamma da Aunty Rahma da Hajia Mama suka shigo suma aka ci gaba da liƙin dasu.

Affan, da Jamil kuwa murmushi sukeyi, Jalal kuwa ido ya zuba musu.
Hajia Mama kuwa sai wani irin sihirtaccen Murmushi takeyi wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa.
Shi kuwa Sheykh ƙara matsota yayi da kyau har kamar zai ruggumeta, hannunshi na dama yasa ƙasan haɓarta ya tallaɓeshi tare da cewa.
"Aish! Ais.. da sauri ya ida ƙarasowa gareta lokacin da ya ɗago kanta yayi dai-dai da ƙaƙƙafewar da idanunta sukayi, kana numfashinta ya tafi cak ya ɗauke ta sum...!





Kiyi haƙuri da typing errors banyi editing ba, abubuwa sunmin yawa.



Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login