Showing 63001 words to 66000 words out of 352722 words
tsaki cikin tsuke fuskarsa, da jin haushin yan uwan nashi yace.
"Ya Nasiru kufa, ji tsoron Allah, ku tuna, cikin Masallaci kuke, kuma ba kyau liman na huɗuba ana. Surutu."
Wani irin mugun kallo Baba Bashiru ya watsa mishi tare da cewa.
"To ɗan masu matacciyar zuciya, wa'azin da yakeyi ai tun kan a haifi uwarshi mun sani".
A kufule Barrister Kamal yace.
"Ƙaryane, da kun san abunda ya sani wala Allah da zuciyarku ta tsarkaka".
Shiru yayi tare da fuskantarta Inda limamin take jin yana cewa.
"Halaccin kallon matar da mutun yakeso ya aura.
Haƙiƙa munsan matarka abokiyar rayuwarka ce. Kuma gonarka ce da zakayi shuka a cikinta, sannan kuma gareta zaka samu konciyar hankali. Kuma shi manufar yin aure ya hana kallon wata ko wasu matan wanda ba nakaba da dai makamantansu Irin hakan.
IN KUWA HAKANE TO LALLAI AKWAI BUƘATAR SAI MUTUN YA ƊARJE! YA ZAƁA. Haka kuwa baya yiwuwa sai ka kalleta sosai da sosai. Saboda mahimmancin haka nema shariyar musulunci ta yardar maka da ka kalli wacce kakeso zaka aura da kyau. Don ka tabbatar da wancan abubuwan da aka ambata a sama.
Kuma wannan dama da Shari'a ta bada ta bada shine, a matsayin halasci na wurin mafi yawan malamai, kuma wannan Halascin da akace halasne ya haɗa da cewa. Shin ta yarda ka kalleta, ko bata yardaba, halasne in dai ka kalleta. Kuma wannan hukuncin haka yake a wojen mafiya yawan malamai, sai dai Malikiya, sunce shi hukuncin Halascin ya dogara ne, in ta bashi izinin amma in bata bashi izinin ba to bai halasta ba.
Haka kuma shi wannan hukuncin halascin an samo shine daga, hadisin Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) yace, wani mutun ya nemi auren wata mata, ƴar Madina, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: "Shin ka kalleta kuwa?". Sai mutumin yace, wa Manzon Allah (S.A.W) "A'a ban kalleta ba". Sai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Tafi ka kalleta, domin mutanen Madina sunada wata illa a idanunsu."
A wata ruwayar kuma da Abu Dauda ya ruwaito.
Daga Jabir Bin Abdullahi cewa: Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Idan ɗayanku zai nemi aure to idan ya sami ikon kallonta wato kallon abin da zai burgeshi zuwa ga aurenta, to ya aikata hakan, (ma'ana ya kalleta) Jabir yace sai na nemi wata mata, daga cikin ƙabilar Banu Salma na kasance ina bibiyanta har sai da naga abin da zai birgeni a aurenta.
Ɗan zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa.
"To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waɗannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci ɗanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, Gargaɗi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura.
Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keɓantaccen wuri wanda aka keɓe ko aka ce nanne kawai za'a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka:
1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta.
A Duba Fiƙhu wadi Juzu'i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ƙara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni'imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni'iman jiki.
Sheikh imamul Al-Auza'i yana cewa.
"Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura.
Duba cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa:
Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da ɗago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake ɗaure samfarin Gucci,
Ganin lokacin salla ya ƙara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace.
" A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurrazaƙ Umar Sa'idu ɗan Mansur yace,
(Amirul mu'minin) ya nemi auren ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ƙanƙantarta, sai yace.
Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ƙwaurinta.
Sai tace.
(Ba don kai Amirul mu'minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya inƙanta to ana iya yin hakan.
Anan kenan in har ka kalleta batayi maka ba, to ka kama bakinka kayi shiru. Kada ka faɗi wata magana wanda zata iya cutar da ita.
In kana ganin kai bata baka sha'awa ba, to tana iya bawa wani sha'awa ya aureta, domin ko wanne icce da ma tsincinsa, kuma abincin wani guban wani.
Allah yasa mu dace, lokacin salla yayi, bari muyi salla sai in Allah ya kaimu sati mai zuwa sai muyi bayani kan halaccin mace ta kalli mijin da zata aura.
Daga nan yayi addu'an kana, ya juya ya fuskanci gabas, tare da tada iƙama bayan yayi addu'an.
Bayan an idar da sallane, suka fito, a jere.
Ta ƙofarsun dai suka shiga, inda duk ahlin masarautar suke bin nan bayi da hadimai da sauran fadawa kusa, duk ta babbar ƙofar suke bi.
Kusan a jere a jere suke tafi.
Kasan cewar zasuyi tafiyar zuwa Rugar Bani ne yasa Mai martaba Lamiɗo ke sauri.
Hakama Sheykh Jabeer, wanda Jalal, Jamil, Jafar, Haroon, Imran, Hashim ke tare dashi,
A hankali ya tsaya jin muryar bappanshi ƙanin Abbanshi Baba Nasiru kenan na ce mishi.
"Kai! Jabeer tsaya".
Tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ba,
Suma sauran duk tsayuwa sukayi,
Kusan a tare Baba Nasiru da Baba Bashiru. Suka isosu.
Cikin haɗe fuska Baba Nasiri yace.
"Jabeer, in dai aure kake so ai gwara ka fito fili ka gaya mana, mu bazai gagara ba mu aurar maka koda yar baiwace, tunda shi ubanka zuciyarshi ta mace, baya iya tsinanawa kansa komai."
Da sauri ya rumtse idonshi,
Jalal kuwa wani irin kallo ya watsa bappanun nasu,
Shi kuwa Jabeer shiru yayi bai tanka musuba, Baba Basiru ne ya ne ya bugi kafaɗarshi tare da cewa.
"Kodai kafi ganewa yawon zinace- zinacen daka saba ɗin ne? Kafin burin a barka ba mata, kana zaune ka tsufe a gida ka fake da rigar malumta kana iskanci a cikin tsarkakekkiyar masarauta ko".
Ido ya zuba mishi babu ko kebtawa, ganin haka Baba Basirun ya ɗauke hannunshi dake kan kafaɗarshi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kamal da Dr Aliyu suka iso wurin.
Suna isa Ya Jafar yayi saurin kamo hannun Ƙanin shi Sheykh Jabeer, ya fara ja da sauri alamun su tafi su bar wurin gaba ɗaya, jikinshi rawa yakeyi.
Ganin hakane Haroon ya kalleshi cikin larabci yacewa Jabeer.
"Ɗan uwana mu tafi".
Barrister Kamal ne ya kalli Jabeer cikin sanyi yace.
"Jabeer jeka, ku tafi kada ka biye musu, tunda sun girma basu san sun girma ba."
Jin hakane yasa Jabeer ya juya ya fara tafiya.
Jalal kuwa wani harara ya watsa musu kana ya juya yabi bayan yayunshi.
Jafar kuwa Jan hannun Jabeer yakeyi a kiɗime gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Ganin haka yasa Jabeer ya jashi ya kaishi sashinsu, ya damƙa hannunshi wa Juwairiyya kana yace mata ta kula dashi, yanzu zai fita shida Lamiɗo.
Jiki a mace Juwairiyya ta mishi fatan a dawo 'lfy.
Ƙarfe biyu da rabi dai-dai suna cikin motoci, wanda a ƙalla sun kai su goma.
Motar forko Waziri ne wanda yake ɗane ga Yayar Lamiɗo.
Sai Galadima, da Wambai,
Ɗaya motar kuma Ɗan iyane da Sallama, da sarkin Dawaki, da sarkin fada,
Sai motar da Lamiɗo ke ciki, shida Garkuwa wato Jabeer sai Haroon sai kuma Hashim da Laminu, ƙanin Hashim wanda duk yaran Gimbiya Saudatu ne matar babban yayansu Habibullah wato Abbansu Jabeer, wanda da shine Galadima. Ɗaya rasune aka bawa Ya Jafar sarautar wanda kwananshi goma da sarautar, komai na rayuwarsu ya sauya.
Sai motar dake binsu wanda Jalal, Jamil, Imran Sulaiman ɗan Barrister Kamal, suke ciki.
Sai sauran motocin fadawa kamaru, Ɗan kazagi, mai yiwa sarki fadanci da kuna dogari mai riƙewa sarki laima, da sarki mota da dai sauransu.
A jere a jere motocin ke tafiya.
Gudu sukeyi mai ɗan yawa sabida ganin yamma ta ƙarato, gashi basu je bama bare su fara shirin dawowa.
Gudu sukeyi, kana fadawansu, rirtiƙe da bulalin dogaye.
Kai tsaye Rugar Bani suka nufa.
Koda suka iso cikin garin Shikan, sunga alamun garin babu lfy, har yanzu dan sai matasan ƙabilar ɓachama da hausawa suketa yawo a garin ko wanne na bawa yankinsu kariya.
Suna isa cikin Rugar Bani.
Gaba ɗaya mutanen Rugar duk inda suka gilma sai a bisu da ido,
Yara maza da mata sunata guduwa suna shiga cikin gidajensu.
Kai tsaye tsakiyar garin suka nufa wanda nanne fadar Arɗo Bani taken kuma lokacin duk manya da yara maza tsoffi da dattawan garin duk suna harabar wurin sabida yau jumma'a duk suna dawowa kiwo da wuri.
Kuma duk a tsakiyar garin suke taruwa sabida bawa garinsu kariya, domin har yanzu suna cike da taraddadin abinda akayi musu.
Kuma ya rigada yanzu an ƙure haƙurinsu sunata shirin ɗaukan fansar rayukan da aka kashe musune. Fiw-fiw haka motocin keta gilma mutane suna wucewa tara da tada ƙura sabida babu kolta a garin sai yashi. Sai sauti da ƙugin mitocin ne ya cika kunnuwan mutanen garin baki ɗayansu.
Motocin na isowa wurin. Gaba ɗaya mutanen Rugar dama baƙin mutanen maƙotansu sauran rugage duk suka miƙe tsaye.
Tare da gya tsayuwarsu, suka gyara riƙon da sukayiwa sanduna su.
Ba tsoro ba fargaba sukayiwa motoci goma nan zobe, suka sasu a tsakiya.
Cikin sauri Sarkin dogarai ya buɗe marfin motar da yake ciki, ya fito tare da zungureriyar bulalarashi. A take kuma Ɗan zagi ma ya fito.
Da sauri duk sauran fadawanma suka firfito kowa da zungureriyar bulalarashi.
Cikin ɗaga murya ɗanzagi yake cewa.
"Ta kawarka lfy Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, sarki ɗan sarki jikin Sarki,uban sarki kakan sarki. Jama'ar gari sun gaisheka,
Da sauri duk sauran fadawan suka, firfito cikin motar.
Sarƙin motane yazo ya buɗe wa Sarƙi ƙofar.
Dogari kuwa matsowa yayi da sauri ya buɗe wata ƙatuwar laima, gaba ɗaya sukayiwa ƙofar motar labule da mamyan jajayen rigunansu, yayin su duk sawunsu babu takalma, sannan kawu nansu naɗe cikin wasu ƙatti-ƙattin rawanunnuka masu girma babu kunne ko ɗaya a jiki.
Gaba ɗaya mutanen Rugar kuwa, sai ƙara tsuke fuskokinsu sukeyi, cikin jin haushin zuwa sun.
Can cikin motar kuwa Haroon ne saƙale da wayarshi a kunne cikin sanyi yake mgn sabida kada Lamiɗo ya jiyoshi, haka kuwa babu mai jinshi sai Jabeer.
Cikin sanyi ya ɗan kalli Jabeer kana yaci gaba da mgna a hankali yace.
"Umaymah ni dai hankali na ya tashi, da irin wasu mutane da wasu abubuwan da akeyiwa su Jabeer a masarautar su, Umaymah, meyasa bazasu bar musu sarautar da Masarautar tasu gaba ɗaya bane, sai kinga fa yadda Jazlaan dinki ke fuskanta ƙalubale fa."
Cikin wata iriyar murya Umaymah tace.
"Yanzu kuna inane?".
Kanshi ya ɗan jujjuya kana yace.
"Uhum ni ina zan san inda muke, na dai san munzo wata Rugar fulani ce, wai GARKUWAN FULANI nasu ya kawo musu ziyara dan ja-janta musu abinda ya faru, kuma gaba ɗaya mutanen rugar naga sai
Wani irin kallo suke mana kamar dai zasu huce a kanmu ne".
Cikin wani irin tattausan murmushi mai nuna jin daɗi tace.
"Bawa Jazlaan wayar".
A hankali ya miƙa Jabeer wayar tare da cewa.
"Umaymah ce".
Cikin sanyi yace.
"Kace tayi haƙuri sai mun koma zan kirata".
Da sauri ya like mishi wayar a kunne jin tana cewa.
"A a amshi wayar".
Ɗan haɗe fuska yayi kana ya amshi sallamar da tayi mishi.
Kana ya meda kai jikin kujerar murya can ƙasa yace.
"Umaymah, Na gaji tunda muka dawo ban hutaba, yau da sassafe wannan tsohon ya sani shara kamar wani bawanshi haka ya sani na share mishi wannan ɗakin nasu na gado wanda in dan ta nine rusashi za'ayi gashi yanzu kuma ya kwasoni zuwa wata rugar FULANI da duk makamaine a hannunsu, ko wa zasu daka".
Cikin wani irin jin daɗin daya bashi mamaki mai yawa tace.
"Ko kai zasu dakane Jazlaan, Sheykh Jabeer, yasha zana a hannun Fulani".
Cikin sanyi yace.
"Su kashe Ni dai Umaymah, ke kin sani tunda nake a duniya, ba'a taɓa dukana ba, sabida koda iba yaroma ban taɓa yiwa Mama da Ummi laifin da zai kaisu ga yimin dukaba, Abba na kuma baya dukanmu, Umaymah kema baki taɓa koda marina ba, to kuma wa kika ga zai dakeni a faɗin duniyar nan banda ruwan sama".
Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin cikin sanyi tace.
"Allah ya tabbatar da al'khairi cikin tafiyar naku, ka dai lura kaine GARKUWAR dole da duk abinda zai cutar da Lamiɗo ko masarautarku ko sunanta dole kai ne zaka zame musu Garkuwa, so dan Allah bana son kayiwa Lamiɗo musu bare gardama a cikin duk abinda zai umarceka".
Cikin sanyi yace.
"To Umaymah, in na koma zamuyi mgna".
Daga nan sukayi sallama, cikin mamaki ya kalli yadda gaba ɗaya manyan hakimai sun firfito, ga Lamiɗo ya fita amman yana tsaye bakin ƙofar motar.
Cikin sauri ya kalli Hashim tare da cewa.
"Hashim Lfy kuwa naga duk suna tsaye, garin basu da abin zamane daza'a karrama baƙi?".
Cikin nitsuwa Hashim yace.
"Uhum cewa sukeyi, wai sun yafe ziyara da ja-jantawar Lamiɗo".
A wojen kuwa, cikin ɗaga sauti Danzagi yace.
"Hattara dai fulani mai ƙasar ne gaba ɗaya, ke tsaye tsakiyar garinku, maza ku bada masauƙi".
Ya ƙarishe mgnar yana jujjuua bulalar hannunshi haka sauran fadawan.
Cikin fillanci ɗan aiken Arɗo Bani ya buɗe murya da ƙarfi cikin harshen fillanci tare da cewa.
"Maza ku bada hanya mai martaba ya iso fadar Arɗo Bani".
Jin haka gaba ɗaya taron al'ummar fulanin suka fara buɗa hanya,
Har gaban rumfar da Arɗo Bani ke ɗauke baƙi, inda aka shimfiɗe wurin da manyan taburmaii kana aka malale manyan kilisai irin namu na fulanin dawa.
Bappa Malam Liman Alhaji Haro Alhaji Umaru, Musu, da kuma Ardo Duno da Arɗo barwa maƙotansu, duk suka mimmiƙe tsaye sai dai gaba dayansu fuskokinsu babu wal-wala, asalima wasun cikinsu jikinsu har ɓari yakeyi, dan fushi da zafin zuciya.
A can cikin ƙauyen Bonon kuwa, Ba'ana da sauran ƙabilum ɓamawam duk suna gaban dodon tsafinsu Bonon ɗin,
Da gudu Maman Ba'ana ta iso wurin cikin Yaren ɓacamancin ta sanar dasu zuwan, sarki Lamiɗo da tawagarsa, jin hakane yasa, Ba'ana ya miƙe jiki na rawa ya nufi rugartasu.
Su kuwa sauran yace in yaje yaga da matsala zai kirasu.
Nan ya tafi su kuma sukaci gaba da dariyar mugunta.
A cikin Rugar Bani kuwa, Bukar Baban Ba'ana ne yayi wata iriyar fitinenneyar murmushi mai cike da mugunta dan son haddasa fitina, ta yadda zai samu masarauta Joɗo da kanta ta shiga matsala.
Kutsawa yayi tayi cikin mutane har ya samu ya shigo gaba-gaba.
Lamiɗo kuwa da tawagarsa taku sukeyi cikin al'farma da ƙasaita.
Su Waziri, Galadima, Wambai, Ɗan iya, ɗan buram, duk suna biye dashi a baya,
Dogari na rike mishi da laima, fadawa kuma na zazzaune a ƙasa, gefe da gefe, Ɗanzagi kuwa muryarsa ce cika wurin baki ɗaya duk da hayaniyar da wurin kedashi.
A hankali Jabeer ya sako sawunshi woje, yana taka ƙafarshi ta dama kan ƙasar garin, yaji zuciyarshi ta buga da azaban ƙarfi har saida ta kaishi da rumtse idonshi tare da ambaton.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
A saman red lips ɗinshi.
da ƙarfi yasa hannunshi ya dafe ƙahon zuciyarshi, tare da kuma maimata.
"Hasbunallahiwani'imanwakil".
Sabida ji yayi tamkar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ta faɗo ƙasa. Jalal, Jamil, kuwa ido suka zuba mishi, sabida ganin yadda ya rumtse idonshi, sabida suna bakin ƙofar motar, sune ma suka buɗe mishi marfin.
Haroon kuwa da Hashim da Laminu, jira suke ya fita kafin su fita.
Cikin mugun tsana Laminu ya kalli Jabeer ɗin da ya yunƙura ya fita,
zuwa yanzu, wani irin harbawa da tsalle zuciyarshi keyi, wani irin masifeffen fargaba, da kaɗuwa ne suka dirar masa lokaci ɗaya.
A hankali duk suma su Haroon suka fito, a tsakiya sukasa Jabeer kana bayinshi na biye dasu a baya.
A hankali ya gyara tattausan al'kyabbar jikinshi, tare gyara hiramin kanshi ya kange kekyawar fuskarshi.
Takun da yakeyi ne ya ƙarawa shigarsa ta al'farma daraja,
ya fito tamkar balarabe, gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ƙasar wannan wurin.
Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace.
"Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi".
Ga mamakinshi sai yaji Ɗanzagi na cewa.
"GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buɗuwa tana bajewa, sabida ɗaga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci.
Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'ƙur'ani, da kuma jin daɗin.
Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi.
A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin.
Inda Lamiɗo da sauran tawagarsa ke zaune.
Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna.
Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi.
Cikin nitsuwa Lamiɗo ya kallesu tare gyara zamanshi.
Muryar Ɗanzagi ce ta karaɗe wurin da cewa.
"Gyara kimtsi. A saurara dai Lamiɗo jikan ɗan Lami Bubayero jikan Lamiɗo Joɗa zaiyi mgna".
Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku tace.
"Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky."
Da ƙarfi Ɗanzagi yace.
"Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi.
Shi kuwa Lamiɗo a hankali yaci gaba da cewa.
"Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa."
Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa.
"Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu ɗaukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi".
Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar.
Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu.
Cikin tsauri Lamiɗo ya ɗagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa.
Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi,
Jabeer kuwa, a hankali