Showing 108001 words to 111000 words out of 352722 words

Chapter 37 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30767

zuciyarshi ta koma ta nitsu tabar wannan tsinkewar da bugawar da tsalle tayi lib a cikin ƙirjinsa.
Jin muryar Jakadiya ne yasa, Sheykh Jabeer, yin ƙarfin halin ɗaga ƙafarshi ta dama.
Jin ya ɗan yi gabane yasa itama, ta ɗaga ƙafarta ta hagu, sai hakan ya bada wata dama ta musamman, ya zama suna ɗaga ƙafafuwan su, a tare kana suna taku a jere.
Sai dai shi ɗin ya ɗan kereta kaɗan.

"Masha Allah. Tabarakallah,". Sune kalaman da Umaymah ke Maimaitawa, lokacin da take biye dasu a baya.

Lamiɗo da kanshi da Galadima sunga wani irin dacewa na musamman a tsakin Muhammad Jabeer da Aysha.
Abba kuwa murmushi yakeyi mai baiyana jin daɗi.
Malam kuwa, Addu'o'in yaketa jero musu na fatan al'khairi da zaman lafiya da nitsuwa da samun zuriya ɗayyiba.

A hankali suke taku yayinda kowa zuciyarshi ke bin takun sawunsa,
A haka suka fito babban falon Gimbiya Aminatu nan suka samu Ummi. Tana ganinsu ta miƙe da tsauri tayi gabansu, hadimai hudu cikin na Gimbiya Aminatu kuwa, sukayi bayan Umaymah dake bayansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer suna fitowa yayi wani irin saurin sake hannunta tare da janye nashi,
Sabida shi ji yake tsikar jikinsa na tashi tamkar ya riƙe wutan lantarki ne sabida masifar tsuma da yaki naman jikinsa nayi.
Murmushi Umaymah tayi ganin still dai suna tafiya a jere a jere suna wani irin taku mai ƙayatarwa.

Suna fitowa, suka samu sallama a bakin mashigar wurin.
Nan ya shaida musu, duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga.

Tafiya kaɗan sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu, ta gefen hagunshi,
suka ɓullo farfajiyar wani babban part,
Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu.
A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya.
Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru.
Cikin murmushin da muryar tsufa tace.
"Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa."
A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita.
wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima.
Cikin kula yace.
"Barka da safiya Innano". Cike da kula tace.
"Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko".
Kanshi ya gyaɗa mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta.
"Cikin muryar tsufa tace.
"Allah ya sanya al'khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya ɗayyiba."
Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki ɗayansu.
Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta ɗan kalli tsohuwar tare da cewa.
"Ina kwana".
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace.
"Lafiya lau, ya baƙu ta?".
A hankali tace.
"Alhamdulillah". Jakadiyarsu ce ta ɗan rusuna tare da cewa.
"Mun barki lfy".
Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi.
Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta.

Kana suka miƙe suka fita.

Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga.
Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne.
Saida suka gama da sashukan manyan masarautar.
Kana suka nufi sashin Hajia Mama.
Tuni tasan da zuwansu.
haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata.
A matsayinta na uwar ango.
Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya.
Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi,
Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara'a tace.
"Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy".
To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.

Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.

Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
"Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike".
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
"Ina kwana Mama".
Cikin kula tace.
"Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta".
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
"Gashi ɗiyata amshi kisha."
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
"Alhamdulillah".
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
"A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi."
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
"A a Shatu amshi kisha kinji ko?".
Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Bana shan madarar".
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
"Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi".
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
"Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne".
Cikin rawan murya tace.
"Bana sha".
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
"To gashi kai kam kasha naka".
Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
"Kawo hannunki ko ɗiyata".
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c...!




Ƙaƙa tsara ƙaƙa
By
*GARKUWAR FULANI*


Tsayuwa tare da kasa kunnuwanta.
Tana jin sautin zazzaƙar muryashi.
Yana kudba.
Akan laduban fuskantar watan Ramadan wanda zuwa yanzu kwanaki ne suka rage.

A hankali ta fara taku tana
Nufo inda Hibba ta shimfiɗa musu sallaya.
Ita kuwa Hibba ido ta zuba mata ganin yadda ta kasa kunne.
Cikin murmushin tace.
"Aunty Aysha me kikeji".
A hankali tace.
"Wannan me sunan malamin da yake huduban nan. Kamar inada wa'zuzzukanshi amman kuma, ban san sunanshi ba, kamar dai kam nasan wannan Muryar".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Lallai ma kam Aunty Aysha wai muryar Hamma Jabeer ɗin ne ma kike cewa kamar kin santa, kamafa kikace, lallai kam my Aunty".
Da sauri ta kalli Hibba domin zuwa yanzu ta gane waye suke cewa Hamma Jabeer, Ko Sheykh, ko Jazlaan, ko Muhammad wani lokacin Umaymah na kiranshi haka.
Ta kuma fahimci wai shine mijin da aka aura mata.
Ta kuma gane sun taɓa haɗuwa sau biyu kafin yau.
ganin tayi nisa a tunnine yasa Hibba cewa.
"Aunty Aysha".
Murmushi ta ɗan yi tare Dasa hannun ta amshi hijabin da Hibba ke miƙo mata.
Cikin ranta take mgnar zuci.
"Uhumm mutun duk rayuwarsa tana cike da ƙalubale da matsaloli Magauta sun sashi a tsakiya kota ina ya juya suna tare dashi.
Amman bauɗewa ta hanashi ganewa, sai anyi mgn yace wai anayi mishi ihu a kai.
ko shi kunnen macijine dashi da yafi kowa jin sauti.
sai iya lillibka ɗika-ɗikan al'kyabbar yanata ɓoye jiki kamar wani mace".
Mitsss ta ɗanja gajeren tsaki tare daci gaba da zancen zuci.
"Yana nan jiki duk matsaloli ya bari mutun yaga iya inda abunda ke kan yatsunshi ma, ya gagara, shine kullum cikin al'kyabba har ƙasa uwa shine limamin harami.
Sai an kasheshi a banza yasa ƙannenshi da iyayenshi a matsala.
Danni matsalar rashin yayuna har huɗuma ya isheni damuwar duniya bazan ƙarawa kaina damuwar waniba".
Da sauri ta juyo ta matso kan sallayar sabida jin har masallacin sun sallame sallar, sabida ta daɗe a tsaye tana zancen zuci.

Nan dai sukayi salla, kana Hibba ta miƙa ta fita
Ita kuwa Shatu, sabuwar wayarda aka saya mata jiya da sabon layi aka haɗa mata komai ne, tasa hannunta,
ta jawo.
tare da komawa ta kwanta bisa sallayar.
Layin Bappa tasa kana ta kira.
Jin bata shiga bane yasata gane, sun tafi kenan.
Cikin sanyi ta kira ɗaya layin na wancan ƙasar tasu.
Cikin sa'a kuwa ya shiga sai dai ba'a ɗagawa.

Sau uku ta kira jin ba'a ɗaga ba, ta haƙura.
Number Rafi'a tasaka ta kira.
Tana ɗagawa tace.
"Rafi'a Garkuwa ce".
Cikin tsananin jin daɗi Rafi'a tace.
"Alhamdulillah Garkuwa ya kike? Ina kike? Ashe kuma abinda ya faru kenan.
Alhamdulillah mun rabu da matsalar Ba'ana, jiya naje Rugar Bani, wai yau su Bappa zasu tafi Lardi".
Cikin murmushi tace.
"Kai Rafi'a kimin mgna da ɗaɗɗaya mana zanfi ganewa".
Cikin dariya tace.
"Eh kyace haka mana kinyi bulunbuƙui a masarautar Joɗa".
Cikin sanyin jiki taja numfashin tare da cewa.
"MASARAUTAR Joɗa ko matsala, komai a bai-bai yake Rafi'a, bana fahimtar komai, tunda nazo cikin wannan masifeffen masarauta kaina a juye yake. Jina nake kamar a rami".
Cikin rauni tace.
"Rafi'a abubuwan sunmin yawa, da wanne zanji.
Tabbas nayi farin cikin tsira daga tarkon ya Ba'ana, to amman ƙaddara batayi min adalciba data kawoni wannan wurin.
Kin sani Allah ya sani ina son Ya Salmanu".
Da Sauri Rafi'a ta katseta da cewa.
"Kice Astagafirullaha kada ki mance da auren wani a kanki kike cewa kina son wani".
Hawayen da suka cika mata ido ta share tare da cewa.
"Bana sonshi! Bana ko son ganinshi, kuma shima hakane baya sona baya son ganina. sauƙina ɗaya da shima ba sona zaiyiba, kowa zaiyi rayuwarshi babu ruwanshi da wani shiyasa hankalina bai tashi sosaima, sai dai ina cikin tarin damuwa Rafi'a, babu Ya Giɗi,Gaini, Seyo, Lado, Inna. Sannan Junainah,Ummey da bappa da nake gani inji sanyinma wai sun tafi Lardi,
ya zanyi inji farin ciki, ga wannan gida mai mutantani daban-daban wasuma naga tsanar shi wancan mai jajayen kunnuwan zasu ɗora a kaina, ko uwar meye haɗina dashi, da magautanshi zasu haɗa dani a ƙiyayyarsa, suji dashi mana, tunda bansan meya shuka musuba, dan shima na lura ba kanwar lasa bane bakine dashi, kan ace ɗirin yake ce musu konɗi, rashin tsoronshi na bani tsoro."
Murmushi Rafi'a tayi tare da cewa.
"Yanzu dai ya batun karatunki?".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Zan gayawa Umaymah".
Cikin shaƙuwarsu Rafi'a tace.
"To sai na shigo, dan mgnar bazata ƙare a wayaba".
Da sauri tace yaushe zakizo?".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"In sha Allah dai kafin azumi zan shigo".
Cikin sauri tace.
"Kafin azumi kuma azuminfa da ɗan saura bama kice gobe ko jibiba, Rafi'a in bakizo minba wa nake dashi da zai zomin?".
Ta ƙarishe mgnar cikin rauni,
Cikin tausayin Rafi'a tace.
"To gobe ko jibi in sha Allah".
Cikin jin daɗi tace.
"To sai kinzo."
Daga nan sukayi sallama.

A ranar da yamma Haroon ya wuce jiharsu Jannart inda nanne masarautar sarkin musulmai take.

A hankali dai kwanakin sukayi ta gungurawa suna cuɗewa Ramadan nata ƙara gaba towa.
Yayinda duk al'ummar Annabi suketa shirye-shiryen tarban watan Ramadan.

Yau dudu saura kwana bakwai ne ake zaton za'a fara azumi, in bai cikaba ma kwana shida.
Tuni Umaymah nata shirin komawa Jihar Tsinako sabida Abban Haroon ya matsa ta dawo sabida shirye-shiryen Ramadan.

Ita kuwa Umaymah tana jiran kayan auren data aika a haɗo mata a Dubai su isone.
wanda ƙawarta ce ta bawa aikin kuma ƴar nan cikin jihar Ɓadamaya ne!

Yau Lahadi ne, ta kama ranar bautar al'jihun baya ne.
Wannan yasa duk manya-manyan Coci na cikin garin Ɓadamaya ya cika maƙil da mabiya bayan addinin Kirista ci.


A hankali motocinsu suka fara fitowa cikin masarautar Joɗa, suna kama babban hanyar da zata sadasu da asibitin taraiya na jihar wato Genaral Hospital Ɓadawaya.
Kamar kullum haka tawagar take, Lamiɗo zaije kai ziyarar dubiyar marasa lfy kamar yadda ya saba duk ƙarshen mako.
A ƙalla motocin sun kai goma.
Suna tafiya a jere a jere.
Har suka iso yankin da asibitin yake, inda nan babbar hanyar hada-hadan cikin garin ne, wanda babbar kasuwar jiharma take kan titin.

Wani tabkeken cocine mai zaman kashi a bakin babban titin LCCN, yana ta hannun hagu.
Kana ta hannun dama kuma wani tsabtaceccen masallacin juma'a ne mai ɗan karen girma, haka ya zama suna fuskantar juna masallacin da cocin.
Kana sai an wuce ta gabansu za'a ratsa konar shiga asibitin.

To kasan cewar duk ranar jumma'a ƴan agaji na toshe hanyoyin daga ƙarfe sha biyu da rabi zuwa kan a idar da sallan jumma'a su buɗe,
sai kafuran nan suma suka tsiri duk ranar Lahadi tun shida na safe zasu,
Toshe hanyoyin nan, sai shida na yamma.
Wanda hakan ke jawo cinkoson ababen hawa ata yankin wuri. Sai ya zama duk masu son yin salla a wannan masallacin jumma'a to ranar a sai tsare musu hanya,
sai dai masu zuwa da ƙafa.

Wannan abun ya damu musulmai, koda aka kai ƙorafi ga gwamnatin jihar sai cewa tayi.
"Ita bata son fitina, a bar kowa yayi addininshi salin alum".
Haka musulmai suka haƙura dan a zauna lfy. To masarautar Joɗa bata da wannan lbrin sai yau da suka fito ranar lahadi da yake kullum asabar suke zuwa.

A jere a jere motocin ke tafi kasan cewar da sanyin safiya ne,
lokacin sun gama rufe hanyoyin kana sunata tsastsafowa gabas da yamma kudu da Arewa.
Cikin Mamaki motar su Lamiɗo da saura duk suka tsaya, sabida ganin motocin gaba sun tsaya.
da sauri Sallama ya fita, tare da dawowa baya.
zuwa gaban motar Lamiɗo yayinda Motar Sheykh Jabeer kuwa take can bayansu, shi sauri yake zaije Valli Hospital dan yiwa wata mata aiki.

Rusunawa Sallama yayi tare da cewa.
("Allah rene halkaleru en mabɓi labi mai".) Allah rene kafurai sun rufe hanyoyin".
Da sauri sarkin ƙofa ya fito yazo ya buɗewa Lamiɗo marfin yadda zasuji juna da kyau.
Cikin mamaki Lamiɗo yace.
"Lfy meya faru zasu rufe hanyoyin".
Da sauri dubagari yace.
"Ai haka sukeyi duk ranar Lahadi, su hana mutane sakewa su rufeshi tun safe sai yamma".
Cike da Mamaki Galadima da yanzu ya iso wurin yace.
"To duk hakan na menene?".
Cikin sauri Duba gari ya ɗan rusuna tare da cewa.
"Wai sabida musulmai na rufe hanyar duk ranar jumma'a sabida bada tsaro wai suma shine suka tsiri, hakan ankai mgnar wa gwamnatin kuma ta goyi bayansu".
Cikin ta ajjudi suka kalli juna,
kana cikin bada umarni Lamiɗo yace kaje kace, su buɗe hanyar yanzu nan.
Kuje da sarkin aike".
Nan take suka juya suka nufi can inda yaransu ƙananan ke tsaye su kakkafa Road closed and stop.
Suna zuwa jim kaɗan suka dawo.
Tare da cewa ai yaran sunƙi sabida sunce Gwamnatin jihar ta amince musu da haka.
Wannan mgnar yayi masifar tasa zuciyar Lamiɗo.
Cikin ɓacin rai ya zaro wayarshi ya danna mai girma Gwamnan kira.

Inda yace maza, ya bawa kafuran nan damar buɗe waɗannan hanyoyin da suka rufe.
Ba kunya gwamnan yace, to ai. Dokace Allah rene da kunbi wata hanyar ai yafi ko."

Cikin tsananin tarin takaici Lamiɗo yace.
"Muje duk ku shiga mota, mu canza hanya."

Sun shishiga kenan sai kuma sukaji.
matasa irin wanda suke gefen wurin suna cewa.
"Jahan! Jahan!! Jahan!!!".
Da Sauri Duk suka fara leƙawa suna kallon wanda ake kira da Jahan, ɗan jarida mai zaman kanshi wanda jihar Ɓadamaya da kewaye ke alfahari dashi. Duk da ya kasance Musulmi mai sunaga ba nasu bane, kafurai kuma suna alfahari dashi a matsayin nasune.

Cikin isa da karsashi yake taku cikin wasu irin zafafan ƙananan kaya masu masifar kyau. Jahan kekyawane aji ƙarshe a kyau, fari ne ƙal hanci har baki shiyasa da yawa kance shi iyamurune, idanunshi farare ƙal-ƙal gashin kansa gwanin kyau sai dai kafurin askin dake kanshi.

Yaran suna hangoshi suka matsa.
Shi kuwa Jahan da kanshi ya buɗe hanyoyin gaba ɗaya.
Kana ya nufi motar fadawa dake gaba.
Haɗe hannunshi yayi wuri ɗaya tare da.
Musu alamar suyi haƙuri kana ya musu alamar su wuce.
Daga nan motar Waziri ya nufa, suma ya basu haƙuri. Haka yayi tayi har gaban motarsu Lamiɗo,
cikin sanyi ya rusuna gaban marfin motar, tare da jinjinawa Lamiɗo kana yace.
"Tuba muke Lamiɗo, ga hanya an buɗe".
Wani irin sanyi da daɗi Lamiɗo yaji, gashi duk da Gwamnatin ta kasance ta musulmi siyasa ta hanashi adalci.
Gashi wanda ba nasu ba ya zantar da adalci".
Haka ya rinƙa bawa mutanen cikin motocin haƙuri suna wuce.
a haka har yaje mota ta ƙarshe,
Yana isa yasa hannu ya buɗe marfin motar.
Wani irin kallo mai cike da ma'anoni yakeyi mishi.
sai kuma yayi wani munafukin murmushi.
Ganin hakane ya ja motarshi ya tafi.



Washe gari ranar Litinin. Da hantsi Hajia Kubra aminiyar Umaymah ta iso.
da yan rakiyanta.

Kai tsaye har bakin part ɗin Sheykh Jabeer sukayi parking.
Kana ta shiga cikin

Cikin farin ciki suka ruggume juna ita da Umaymah cikin dariya Umaymah tace.
"Hajia Kubra amman kin shamma ceni".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ato ai naga kin zaƙu kina son ki koma Tsinako ne nace bari dai in hamzarta indawo".
Ta ƙarishe mgnar tana zama tare da miƙa Jalal car key ɗin ta tace.
"Yauwa Jalal Jamil ku shigo da kayayyakin."
To sukace kana suka amshi key ɗin suka fita.

Nan suka buɗe motoci biyun wanda tazo a ciki da wanda drever'nta yazo a ciki.
Nan suka rinƙa kwatsar akwatunan suna shigarwa.
Set biyune masu fasifar kyau da tsadan gaske.

Umaymah kuwa tuni tasa Juwairiyya ta cika Hajia Kubra kayan kwalam a gabanta.

Robar Inabi ta ɗauka tana buɗewa ta kalli Umaymah cikin raha tace.
"Hajia Khadijah ina ɗiyar tamu".
Cikin murmushin Umaymah ta ɗan juyo ta kalli ƙofar falon Shatu tare da cewa.

"Hibba! Hibba!!".

"Na'am".

Hibba ta amsa tana miƙewa tsaye
Kizo keda Aysha ga Mommy Kubra tazo".
Cikin jin daɗi Hibba ta miƙe tare da cewa Shatu.
"Wayyo Aunty Aysha tashi muje".
Cikin nitsuwa ta miƙe tsaye,
mayafin Arabian gawd ɗin dake jikinta ta gyara.
Kasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login