Showing 36001 words to 39000 words out of 188741 words
ranar Litinin in sha Allah?"
Zubawa fuskarta ido ya yi sai kuma ya kalli mahaifinsa
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Zan duba na gani in sha Allah"
Daga haka ya wuce shima ya bar mahaifinsa na sake yi mata sai da safe dan yauma ba zai kwana a nan din ba, kuma ba zai kwana gidan maman Yusuf ba dan ba kwananta bane, fushi yake da matansa biyu kuma sai an bashi hakuri koda zai hakura
Yana fitowa ya samu Yusuf a tsaye yana duban agogo, magariba ce ta shigo dan suka nufi masalaci bayan sun sanarwa maman Yusuf din dake cikin mota tana kallo a wayarta hakan ya sa itama ta fito ta koma ciki dan yin sallar
Sunna gamawa suka shiga motar Yusuf ke ja Abu na waya da Aminu yana fada masa daidai inda zasu tsaya yana daidai wajen
Sunna karasowa wajen suka dauki Yusuf sai godiya yake yiwa su Mama kan adaidaitar da Yusuf ya sa ya je ya amsa sabuwa dal da ita harda karin kudin awo, sai fatan alkhairi yake yana fadin lalle Yusuf din sarki ne kuma uban talakawa
Shi dai tukinsa yake yi yana jin dan feeling na abinda ya kwana biyu bai yi ba, rabonsa da nanikar jikin wata kwana biyu fa cirrrr, kuma har mantawa yake yi saboda rashin lafiyar mamansa, ama yau sai yake jin wani feeling na neman damunsa
A nutse suka karasa cikin anguwar har kofar gidan
Sunna tsayawa Aminu ya nuna masu gidan yana faɗin " Ga gidan nan sir, ama inaga shi uncle din nata baya gidan dan yanzu a masalaci liman na fada min ko na ganshi? Yace sau biyu tana zuwa nemansa wai tunda ya fita dazu ransa a bace"
Honorable ne ya dube shi da kula ya ce" Ransa a bace? Kwananta a wani wajen ya saka ransa bacewa ko ina iyayenta ne ko hutu ya zo wajen uncle din nata?"
A hankali Yusuf ya jinginar da bayansa jikin kujerar motar yana sauke dubansa daga kan Mahaifiyarsa dake kallonsu yana jin Aminu na maimaitawa Honorable cewar RAUDA marainiya ce gaba da baya a hannun uncle din nata take
Shiru wajen ya dauka, na tarin alhinin jin maganar ne ko mene?
A sanyaye Mah ta sauko kafarta daga cikin motar bayan ta bude ta ajiye wayarta baba tana fadin" Bari Ni na shiga ka ga idan yana nan din sai ya maku iso"
Haka kawai ta ji zuciyarta ta buga mata jin labarin yarinyar, sai ta ji bari ta shiga ko sa ga marikinta su sanar masa ga asalin inda ta kwana ta yiwu da akace ya fita hankalinsa tashe ya daina fushi ya yi hakuri
Da ido YUSUF ya bita har ta bude karamar kofar gidan ta shiga sannan ya dawo da dubansa kan Aminu dake dan yiwa Ana shinfidar wasu daga cikin abinda Rauda ke ganni a gidan rikon nata
Salama Maman Yusuf ke yi tana karawa, ama ba amsa, sai murya dake tashi sama sama da alwashi kala kala wanda ya sakata dakatawa a dole tana tunanin ta koma ne ko ta shiga?
Ta daga kafa da nufin shigewa ciki ta ji sama sama murya na fadin" Rauda idan har ubanki ya shanye giya da kudina nice ajalinsa, kuma kema nice ajalinki ki rubuta ki ajiye, munafuka algunguma, ki bani kudina nace , ki tashi du gidan ubanda kika san zaki je ki samo min kudina ki je ki samo idan ba haka ba na wulakanta ki na je na dauko dayan shegen na yanka shi!"
Hankalin Mah ne ya mugun tashi, da sauri ta juya har tana jin kafarta zata tashi na ciwo ta fito ta nufo mota tana haki
Da sauri YUSUF ya bude motar ya fito ya kamo hannayenta yana kallon yadda take haki hankalinta tashe, Abu ma dake tsaye shi da Aminu gefe sun nitsa a labarin Rauda da sauri ya karaso yana kamota ba wata wata ya rungumeta a jikinsa yana fadin" Hey Madame, menene, me ya faru?"
Hankali tashe har hannayenta na rawa ta fadi abinda ta ji da ta shiga, da sauri ta ce" Wacece RAUDA? Inace wajen yarinyar da muka zo ne , me ta yiwa Mamanta take fadin kalaman nan a kanta innalilahi Wa inna ilaihi raj'une"
A nutse ya mayar da hannunsa ya rufe motar ya juyo yana kallon mahaifinsa dake faman fada mata kar ta daga hankalinta ba komai bane bari ya shiga ya gani
A tausashe ya ce" Aba bari na shiga na gani"
Yana fada ya juya ya nufi hanyar shiga, da sauri Aminu ya biyo shi yana fadin" Biya Muradi da zaka yi hakuri na tabo wata mace ta shiga, ka san matar nan da sharin tsiya, gashi bata gannin girman kowa kar ta lika maka wani sharin a banza a wofi"
Murmushi YUSUF ya yi masa ya nausa kansa ciki yana salamar da ta zame masa jiki ciki ciki
Yana shigowa Farisa ga fito daga bayi ta gama aikata kashinta na magariba da ya zame mata jiki suka yi ido hudu
Ido ta zuba masa kafin da sauri ta dubi kafarta dake dauke da dati harda zannin jikinta, zannin da ta wuni da shi shekaran jiya da jiya ne , yau fa har zata cenza tace bari dai ya karra kwana biyu sai ta cenza dan bata kayanma ai ba kyau,sai gashi an yi rantsatsen bako?
Da sauri ta wuce shi ta yi cikin gidan har kamar zata kifa
Tana shiga ta ce" Mama, wa bilahilazi Balarabe a cikin gidanmu, Allah ka sa bakona ne , Allah Allah Farisa Allah amen"
Uwar dake daure da zani saman munafata ta dubeta itama yau din dai wankan nan bata yi shi ba, ta wuni a daki ko abinci bata ci ba ta ce" Balarabe kuma?, Farisa zan ci uban ubanki idan har baki daina kawo min shirme a yau ba, me zai kawo Balarabe anguwar nan dan ubanki?, ko wajen wannan ya zo ai ba zai shigo min gida ba ko?"
Da sauri ta tari uwar tana fadin" Allah ya sawaka ya zo wajenta ki ji kai mugun fata , kina ji ina adu'ar Allah ya sa wajena ya zo ki wani ce wajenta, ke Rauda gaskiya tashi ki shiga ciki kar ya ganki ki masa asirin da kika saba da munafukan idannuwan nan naki, Ni dai kuma kar ku bari ya gane ana neman baba Umaru gaskiya kar ku zubar min da mutincina!"
Magana take yi tamkar ta sako da sako, magana take yi ta rashin mutunci tana hantarar uwar da Raudar baki daya domin du ta gigice
Mikewa Rauda ta yi idannuwanta ko gannin kirki basa yi
Sama hijab ne a jikinta mai ruwan anta har kasa ama bashi da hannu ya dai kama fuskarta das ya fitar da zagayen fuskar nata, hakan ya sa fuskar ta fito fayau da ita sai lebenta da ya dan bushe da kuma idannuwanta da suka kara nutsewa suka yi luhu luhu
Niyarta ta sake komawa masalaci daga nan kuma ta nufi gidan giyar da yake zuwa, in dai yana cen shikenan sai ta dawo ta nutsu ta kuma ci gaba da yi masa addu'a, dan jikinta na bata mugun abin da ya ringa bata a ranar da zata iya kiran ranar da Azal ta fadawa ahalinta
Da sauri Farisa ta riko hijab din tana fadin" Rauda nace kar ki fita fa!"
Da kyar ta iya yiwa idannuwanta luuuuuuu ta bude bakinta ta fara magana ta ga an daga labule an shigo ama bata ga mai shigowar ba, a hargitse ta ce" Idan kika kuma taba min sutura da kazantar nan taki sai na karya maki hannu, idan kika kuma daga mun murya sai na janyo makogwaronki FARISA!"
Da sauri ta yi baya tana neman yin kusa da mamanta, dan ita ta sha'afa kan Wacece RAUDA ita kuma Mama tunda ta ga wanda ya shigo sai itama ta shiga kunce hijabin dake daure a kugunta tana kokarin sakin fuska ta ce" Barka da zuwa baki muka yi ne?"
A hankali Rauda ta juyo da niyar zagayesu ta fice idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa ya zuba mata ido shima sannan ya dauke ya sake kallon hoton dake dakin daya kwal wanda kwarai ya san fuskar mutumen, ama a inda ya san mutumen a waje ne marar kyau, wajen da su mutanen suke kwalewa shi kuwa yakan je ne dan ya yi nasa kalar kwalewar shima
"Ba wajenki na zo ba" YUSUF ya fada a hade yana kaucewa daga nufo shin da Mama ta yi da kujera
A hade ya ce" Ke ?, menene ?"
Rauda dake tsaye bayan ta dauke kanta tana tunanin me kuma ya kawo wannan gidansu ta dago yana kallonsa
Kwarai da ita yake,
Ke ? Menene? Eh lalle da ita yake , sai ta ji ba zata iya amsa shi ba ta sake dauke kanta da nufin ficewarta ta tafi suka ringa jiyo salama daga bakin kofa ta muryoyi masu dan yawa kuma maza ne
Gaban Rauda ne ya yanke ya fadi, daga tsayen da take sai ta matsa sosai ta yi ciki kadan dan ana amsawa masu salamar salamarsu ne Mama na fadin" To wai kuma su waye da daren nan Ni yau sai bakin mutane ke zuwar min!"
A tausashe Liman ya ce" Ba baki bane maman yara, su liman ne"
Itama sai ta samu kanta da yin tsittt kafin ta taho jiki ba kwari tana jin zuciyarta na dokawa jin su liman ne, su liman? Idan tana da tunani ba zata tuna yaushe liman ya taba sako ƙafarsa gidan nan ba, haka kuma ita dai ko a hanya ba abokin gaisawarta bane bale tace sunna gaisawa
Abu daya ta yi tunani an zo ne a mata nasiha da Umar dan kamar ai ana haka a anguwar sukan je dan wani tsirku su yiwa mace da mijinta nasiha ta rainin hankali, namijin dake zaune da matarsa bai isa ya mata nasiha ba sai sun je da wasu wandunansu tsalau tsalau wai sun zo nasiha
Tana fitowa bayan YUSUF ya fito ya ga harda iyayensa a yan shigowar da sauran mutanen da bai san su ba ama suma sunna ganninsa da mutuntawa sosai suka bashi hannu suka gaisa da daraja junna sai kuma ya ga fuskar mahaifiyarsa tamkar wace ta jike da hawaye nan take ya ji tamkar hankalinsa zai tashi, ama kuma ya yi iya yinsa ya dane yana kallon kowa ciki harda Rauda da ta fito da tabarma jin ana fadin a kawo tabarma, jikinta na rawa ta shinfida masu ta tsuguna tana bin ledar dake hannun Liman da kallo gabanta na ci gaba da faduwa
A tausashe Liman ya ce" Ina fatan na same ku lafiya, sannan ina baku hakurin zuwan da na yi maku a irin wannan lokacin"
Shiru ya yi yana neman dukan hanyar da ta dace ya sanar da abin dan shima hankalinsa a tashe yake sosai
A hankali ya ce" Wunin yau mun fita da malamai, sai da yama da na zo aka shaida min mai gidan nan ya je nemana sau biyu bai sameni ba, sai kuma RAUDA da ta je ita dinma sau biyu nemansa baya tare da Ni, a lokacin gannin yama ta shigo magariba ta kusa sai na yi adu'ar Allah ya sa lafiya kuma Allah ya kawo shi masalaci sai mu gana, to bayan an yi sallar magaribar muna zaune da su malan da datijawan anguwa a bakin masallacin muna karatu kamar yadda muka saba wani mashin ya tsaya zo da gudu aka wurgo mana wannan ledar aka wuce dan ko tsayawa mashin din bai yi ba bale mu tantance mai shi da kuma kalarshi mun dai san baki ne kuma masu tuka shi da shigar baki a jikinsu har fuskarsu"
Ledar da ya nuna kowa ya zubawa ido, ciki harda Rauda da Mama wa'inda hankalinsu ya fi tashi, domin kar ku manta duk rigimar mama da uncle tana son mijinta, irin matan nan ne masu mugun halin da duk wani wanda ya rabe su ba zai ji dadin zama da su ba
A sanyaye Liman ya ce" A dole muka bude ledar bayan an tabbatar da ba bom bace, mun ga sutura ta namiji ba kyan gani da waya yar karama, a lokacin aka yi kiran mu aka sanar mana kayan ko na waye kuma akace mu saurari kira, abinda dai muke zato ta yiwu yan garkuwa da mutane ne ko wasu wa'inda rikicin su ya hado su da shi, fatan da muke yi Allah ya sa lafiyarsa kalau "
A rikice Mama ta rarafa ta warto ledar, duk irin yadda aka ringa kokarin hannata budewa ta farke ledar ta zarro rigar uncle caba caba da jinni, da wandonsa sai wayar nan ita dinma duk abin jinnin ya bata ta
A haukace ta saka ihu hadi da sake daga Kayan, Rauda kuwa da zuciyarta ta yi bugawa daya tak tana mikewa dan karasowa ta gani kaffafuwanta suka dauketa suka yumata da kas
A rikice mahaifiyar Yusuf ta janye hannunta daga cikin nasa ta ririko Rauda jikinta, dan wasu sun nufi mama ne wasu sun nufo Raudar ama ba damar su masu rikon da Mace zata iya yi masu
Idannuwan Rauda luuuuu suke yi numfashinta na yin sama sama,
A hankali ta wani irin nisa dan neman sakin kuka, sai dai ba kukan sai nishin dake fita mai haɗe da zazafan numfashi
A birkice da kyar ta ce" Ya mutun shima? Haukacewa zan yi, in har ban mutun ba nima haukacewa zan yi, ya mutun ko? Shi dinma an kashe shi? Ya mutu ko? Shikenan sai Ni sai ita? Haukacewa zan yi kwakwaluwana juyewa zata yi, haukacew zan................." Dif maganarta ta dauke , gaba daya jikinta ya saki, kanta a kirjin mama ta saki rikon da ta yiwa lafayar maman ta summe
Da sauri YUSUF dake tsaye kikam yana kallonta ya duko ya tare Mama da ta fashe da wani irin kuka
Hankali tashe ya ce"
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*14*
*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*
*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
A rikice ya ce" Dan Allah, kar ki yi, kar ki zubar da hawayenki kuma i beg You mama"
Hannayensa ta jimke kirjinta na bugawa tana kukanta kunnayenta na jiyo mata salalamin su Liman dake fadawa Mama ta daina mana ba fa mutuwa ya yi ba dan sun ce zasu kira, kuma basu je wajen yan sanda direct bane dan dole su fara sanar masu, in sha Allah za'a ganshi kar su daga hankalinsu mana, gashi Rauda har ta summa dan Allah a daukota a kaita asibiti
A rikice Mama dake kuka tamkar zata zauce ta ce" Idan da mutun a nan kuwa sun fitar da shi a hayacinsa, ku duba ku ga yadda jinni ke zuba daga jikin rigarsa harda guda guda? Wayo allahna Umar, muna zamanmu ka fita da kudi , shin da barayi ka hadu ko me? Wayo allahna ya tafi ya BARNI da duniyar da ya'ya, Umar dama da wuri zaka mutu ka barni? Yauma muna rikici ya fita, da kudin da wancen tsinaniyar ta kawo ya fita dan na amsa ya amshe ya fita da su, ko dai a gidan giyar aka kashe shi? A ina suka kashe min shi?"
Su liman kam sai suka koma yan kallo, domin su dai ba ririketa zasu yi su rufe mata baki ba, kuma babu mai hurumin yi mata tsawar ta kamawa mutane baki su kam an ce za'a yi kiransu hakan na nufin da wahala idan Umar din ya rasu, ama sai wasu abubuwa take yi kamar ba musulma ba? Ga furucin bakinta ya yi tsauri da yawa
Mikewar YUSUF da Rauda a hannunsa sukutum ya saka su liman din kallonsa
Ba da wani tsaye tsaye ba ya ce" Asibitin za'a kai ita wannan din"
Daga haka ya yi gaba mama na biye da shi da sauri, abansa kuwa ya karra tsayawa suka sake yin bayani da su Liman
A lokacin da mahaifinsa ke neman fitowa Mama na binsa tana faman taro zani ta biyo shi har wajen motar ta kama abin motar hakan ya sa ya dakata bai wani kureta da