Showing 168001 words to 171000 words out of 188741 words

Chapter 57 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9855

san ta ina zan fara ba, dan kuwa tsoro ya gama kashe min duk wani kuzarina da yunkurin daga nake iya yi"

"Rashin jin, na menene? kana nufin bayan da igiyar aurenka tana kara ci gaba da rashin ji? ko menene girman tashin hankalin da kake fadi dan Allah?" Mah ta fada a sanyaye tana dubansa, zuciyarta kuwa cike da tsoron amsarsa

Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana dubanta ya ce" A yanzu, ai bata fita Bama bale ta aikata, koda ace zata iya ci gaban bayan auren, wanda ya shigo da sunnanta kuwa dan daudu ne anya zata iya zubar da kanta har haka?"

Gaba daya Mah sai 5a dawo bata gane yarensa, kallonsa take yi ta kasa gane komai, sai take gannin kamar wanda yake yi mata wata maganar ta wasu daban, dan haka a tausashe ta ce" YUSUF, dan Allah ka min bayanin yadda zan gane ko zan iya taimaka maka da addu'a, sannan na yi maka nasiha? domin na sani ko menene ba zai gagari yafiyar ubangiji ba in sha Allah "

"Mah, mahaifinta fa ba shi ya haifeta ba, kuma ana jibi aurenmu ta aikata zina da likitan da ya yi mata aiki ya dinketa bisa jagorancin mahaifiyarta, Mah kin ga dai mahaifiyar Amnah ko ta gama kuncen kaina da na ji cewar wannan hali da mahaifinta ke ciki wai asiri ne kuma a gawar y'ar kawarta ta anguwa suka saka, to yanzu Ni gaba daya na gama rikicewa, inaga da wahala in Allah zai yafe min, tunda da ace mutumen kirki nake da wahala Allah ya hada hanyata da mutanen nan, Ni da kaina na daina yarda da kaina yanzun Mah....." Ya karashe yana rike hannayenta , ta yadda zafin tafin hannayensa ke ratsa nata da irin yadda bugun kirjinsa ke shiga kunnayenta kawai sun isa su tabatar mata tabas a mugun yannayi yake ciki

A hankali ya dora da fadin" Na rasa ina zan kama, dan kuwa na san ba zan iya zama da ita ba Ni dai, wannan tashin hankali dake tare da ita ya fi karfina, ina bibiye da su ne a hankali tun daga ranar da Taj ya zo min da magana a kanta kan binciken da na sa ya yi, domin a ranar da aka kawo ta fa kanta ta kai cen bangaren tace min wai gata, sai na ji tsoron kar aje banda rashin kunyar akoy wani halin ko na tabuwar hankali ko makamancin haka dai, sai kawai abubuwan nan ke fitowa, Mah a sanadiyar asirin da mahaifiyarta ta yi , mahaifiyar Elhaji ke daka daka dan ta ci abinci a daya daga cikin kangonsa, matar nan tana ji tana gani, ba zata iya taimakawa wannan baiwar Allahn ba ko dan rabata da ta yi da d'anta, sai da muka ji ne aka kawo ta nan take zaune har mu ga abinda Allah zai yi, yanzu Mah wannan ai ba tsatson hada zuri'a da su bane ko? shi yasa nace kawai tunda malan ya tabatar min akoy aurena a kanta sakinta zan yi in komai ya daidaita"

Mah ta jima tana innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, da kyar ta daidaita tunaninta ta kalle shi har ta iya sauke ajiyar zuciya tana sake dubansa ta kuma sada kanta sannan ta dago a tausashe ta ce" Ka saketa ka ce?, to kai kana tunanin kowa zai so hada zuri'ar da kai ne Yusuf?, kaima fa abin gudun mata da yawa ne in fada maka gaskiya, kuma a bayanan nan da ka yi inaga in dai ba ta san dukkan shiga da fitar mahaifiyarta ba laifinta daya ne irin sana'arka wace idan Allah ya sa ta shiryu ne ta dalilinka sai ka ga ka kilaceta har Allah ya sa ta zama abar kwatance gobe, domin da yawa a rayuwa ai ana aikata laifi idan an tuba ka ga an yi kyakkyawan tuba an shiryu har an zama abin kwatance, in ba wannan ba YUSUF ai da an halaka sosai a duniya, dan kuwa da yawa sun ci gaba da aikatawa kansu tsaye tunda dai tubar ba wani anfani ko Yusuf? ko dan Amnah mace ce ta aikata irin halayanka zai zamo abinda za'a yi riko da shi a kasa yafe mata har a bata second chance din da zata rayu itama rayuwa mai kyau? ko so kake ka nuna min cewa lalle kai din jinnin Hajia ne da basa yafe irin wannan?"

Da sauri ya kalli Mah, hankalinsa na neman tashi ya ce" Mah, a'a fa, ya Salam ba haka nake nufi ba fa,Mah ki duba ki ga halayanta, ki kuma dubi iyayenta, inace addini ne ya koyar da mu samawa yayanmu iyaye na gari dan gobe su yi alfahari da mu ba? halayarta nake ta dubawa, ina ta yi mata uzuri , Mah sai dai bata da wasu qualities da zan so, kin san da na san bata son ki, haka bata son Hajia, kin san da na san Hajiar su Salima ce aminiyarta wajen zuwa shawararta, idan fa aka wayi gari abinda ya kasance da mahaifinta ya kasance da Ni na yi yaya? Mah bayan ku da kuke a wuyana garina ke wuyana, idan na zama sai yadda mace mai son kanta ta yi da ki ai na bani na lalace ko?"

Mah ta sake lumshe idannuwanta, kwarai dukkan abinda yake fada gaskiyar kennan, sai dai tana so ne ya zamo ya yi sadaukarwa ya kuma bata dama saboda rayuwa, da kuma fatan Allah ya dubi aiyukansa na kirki ya yafe masa na banza, dan haka tana dubansa ta ce" Ka ga, a duniya babu abinda mutane basa yi saboda dukiya da mulki, kuma a abinda ka fada sai an zauna za'a gane in ƴaƴanta sunna tare da ita kuma in sun san abinda yake faruwa da su, bayan wannan Ni uwa ce, kuma wace na ga rayuwa kala kala, ba zan tashi tashi guda in hade kowa da kowa a laifi ba, kwarai iyayenta sunne tushen tarbiyarta, ama kuma Allah mai shiryar da bayinsa ne, idan ita din da rabon hakan sai a bata dama, haka din baban jihadi ne, idan kuwa ta yi nisa a tafiyar bata jin kira sai a salhance mata ta hanya mai sauki ta yadda Allah zai yi duba da halayan da aka aikata dominsa masu kyau ya yi yafiyar wa'inda aka aikata marar kyan, ka fahimta?"

Kai ya gyada yana duban Mah

Mah ta dora da fadin" a duniya bawan da zai ringa aikata sabo yana sane ya kasa tuba ne abin tausayi, da kuma bawa mai yin tuban muzuru, bayan wannan duk wani wanda ya aikata laifi ya koma ga Ubangijinsa to ya ci gaba da astagafari in sha Allah Allah zai yafe masa......... ka yi rashin ji YUSUF, ama ka daina right?"

YUSUF ya gyada kansa yana kallonta da sauri

Mah ta yi murmushi ta ce" To ka bar sake saken munanan tunanin da suke iya tsayar maka da numfashi, idan ka haihun ka saka albarka ka kai makaranta ka yi nasiha ka yi hakuri, dukkan sauran abinda Allah ya yi mai kyau ne ka fahimta?"

Yusuf Ya ce" Eh"

Mah ta ci gaba da fadin" Dukkan wani wanda zai zageka da shi kuwa ka saka masa ido ko wanene, domin farkonsa ya sani bai san karshensa ba, idan ya zamo mai isgili sai Allah ya jarabce shi da farkon ka, a lokacin zai gane cewar jarabta ce ta Ubangiji, ka ci gaba da taimakawa baiwar Allahn nan, ka kuma jajirce wajen kwato mata yancinta, Amnah ka yi hakuri ka gyara zamanku, kar ka sauta sai idan ya zama dole, kar ka wulakantata saboda abinda ta aikata ko iyayenta suka aikata, idan ka tashi yi mata shara'a ka yi mata cikin sirri saboda iyalinka ce, ko yau ka rabu da ita ta taba zama matarka, maganar bata son mu kuwa ka bata lokaci in da rabon ta so mu fine, idan bata son mu YUSUF normal ne ba wani abu tsakaninmu da ita mu, domin iyayenta muke daga wannan ba wani abin, YUSUF zaka iya yi min haka kuwa?........."









🥹🥹🥹🥹 Allah ka gafartawa iyayenmu


Azl 62

*MAGANIN KARA KIBA 3IN1*

*Ina meneman kiba ido rufe Kuma tanason maganine ingantacce Wanda baida illah kokadan to tazo gadama tasamu yar uwa indai kibace da gyaran nono dakara hips toga Mganinmu nan 3in1 cikin kwana 7 kacal👌🏻 zakiga yadda Zaki fara murmurewa insha Allah mungwada mungani munbayar angwada munsayar angode insha Allah kawata Zaki godemin da 3500 dinki kinhuta da gorin rashin kiba munan cikin Gombe Kuma munatura kaya ko ina kedai tuntumebi ta Whatsapp ko kikirani Kai tsaye ta 08030861857 sai kunzo🥰*

*MAGANIN HIPS*
*Wannan Maganin anyisane tamasu neman hips sunsha wannan sunsha wannan to gatamunan insha Allah guarantee nakebaki hajiya inada yakini akanta matsala indai tarashin hips ne to anwuce gun 3500 kacal kinhuta kijuya kiwarwasa kisaka kayan gayu kijuyawa Oga yayikallo kawata har yanga saikinmasa ninafadamiki wannan nemeni kisamu naki 08030861857*

*MAGANIN NONO*
*Itama akwaita me inganci kamarta 3in1 data hips wasu suna korafi nifa nono kawai nakeso yaciko yayi bulbul gwanin sha'awa yadda Oga zaiyaba nasa breast cup suzauna das Amman abun yacitura Nasha Nasha magungunan Amman haryau ba chanji to ganamu Nan yakine ne Dani akansa ba Dan kadanba alhamdullahi duk Wanda yasaya saidai godiyace tsakaninmu kema zokigwada Kuma kigodemin location Gombe 08030861857*




Muryarsa a matukar sanyaye yana kallon Mah, zuciyarsa cike da sake saken abinda Mah ke son a yi wanda yana kyautata zaton da wahala ya tabatu ya amsa mata a tausashe kamar haka" In sha Allah, Mah zan yi, in dai na tabatarwa kaina cewar a abubuwan nan da na zayana din, laifin Amnah abinda ta yi a baya ne, kuma baya da niyar yin wani zan dubeta, koda kuwa na taba zmbatar kalmar haramtawa a gareta a kankin kaina zan sake neman malamai su daidaita lamarina da ita, Allah ya sa hakan ya zamo silar gogewar zunubaina "

Mah ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta cike da rauni ta amsa shi da Amen

Zaman nasu kasa daukan lokaci ya yi, ita da kanta burinta ya tashi ya fita dan tuni ta yiwa Bah msg din tana son ganninsa yanzu, burinta ya tafi ta iya daidaita nutsuwarta, shi dinma kuma gaba daya ya sake shiga a wani yannayin daban, mai kara hargitsa masa tunani, a dole ya mike yana murmushin dole ya mata salama ya kuma komawa bangarensa dan baya tunanin a yanzun kuma zai iya zuwa wani wajen, ko a bangaren nasa ya san ba zai iya samun wata nutsuwa ba sai wani firgicin da tashin hankalin


Yana tafiya Mah ta cire hijabinta ta shiga yamutsa gashin kanta hankalinta tashe idannuwanta suka kama zubar da hawaye

Innalilahi, da ace za'a shiga zuciyarta da an ga tarin tausayin yaronta dake son halakata, sai dai duk abinda take ji in sha Allah zata jajirce ya gabatar da abinda zai tsira gobe kiyama, tunaninta a wajen da ya fi tsayawa shine *SHIN YUSUF NA GIRBAR ABINDA SU SUKA SHUKA NE, WATO YUSUF NA AMSAR HUKUNCIN ABINDA SUKA AIKATA NE HAR YA SA SHIMA YA DANDANA MASU ABINDA SUKA DANDANAWA IYAYENSU, HAR YANZU ALLAH YA NUNA MASU YA SHIRYU KO SHIMA YUSUF DIN ZAI HADU DA NASA HUKUNCIN DAGA WAJEN ALLAH????????*

Tunaninta ne ya katse da zubar hawayenta sakamakon shigowar Bah

alamunsa daga barci ya fito domin jalabiya ce a jikinsa, kuma yau yana ɓangaren Hajia ne, wato mahaifiyar Salima

shi da kansa ya san kiran nan ba na dadi bane, domin idan baya bangaren Mah bata so ya zo dan gudun rigimar matansa da suka kasa girma idannuwansu a kan dan karamin abin da yake iya zama abin a ji kunya idan aka ji ya fito daga su suke jira su yi masa daukakawar da kowa zai ji a yi rikicin da bata so ace a yanzu dai , da girma ya gama kama su, suke aurar da y'aya sunna fada a kan abin da ita rabontama da shi an jima, shirme kawai sun kasa gane an riga an zama daya fiye da tunaninsu, su suke ha baba ha karami a kan lamarin nan, ita a yanzu ta lafiyarta ai ta fi komai gaskiya

Kamar yadda ya zama abokin sirrinta, mutumen da idan abin ga yi kuka da burgima ya kama shi take yima, mutumen da koda abu bai shafe shi ba takan saka shi a ciki dan ta gama yarda cewa a nan gidan duniya shi din nan shine sirrinta kuma shine mai sauraronta ya bata shawarar da ta dace koda ba zata yi mata dadi ba, ya sa a yanzunma ta neme shi a fujajan suka zauna a kan abinda yake da ruwa da tsaki a ciki kamar yadda take da shi, ta shiga sanar masa abinda ya gigita shi fiye da tunaninta harma tsoro ya shiga kamata a lokacin da ta sanar masa abinda ta fadawa d'an su, kuma Sarkin garin su, cewa eh, dukkan abinda ta zayana din nan kuma a haka zai zauna da yarinyar harda fadin a ba yarinyar chance din da ya dace dan idan ta gari ce a zauna da ita, in kuwa ta dauko maganar da ake da tabbacin in dai ta samu hanya zata dauko din sai a bata salama cikin salama ko me? ransa ya ɓaci yana kallonta, duk irin hucin zafin da jikinta ke fitarwa yau kam ya kasa hakuri yana kallonta da kausasawar da bai taba yi mata ba ya ce" NA JI, kuma na fahimci dukan bayanan nan da kika fada, sai dai abinda nake son karra tabatarwa shi ne, YUSUF ya nufo ki, a yannayin gigitar da kika ce ya yi kuka, sai kika karra tabatar masa eh hakan da yake faruwa da dukiyarsa daidai din kennan kuma dole zai dauka?"

Kallonsa take yi, gannin kamar ransa a wani iri ba yadda ta so ji ba ta ce" Eh abu YUSUF, haka na fa......."

"Dan Allah zaki iya yin shiru na second biyu?" Ya fada a tsawacen da ya sa ta zabura tana kallonsa gabanta na faduwa

Rai bace yana dubanta ya ce" Ke, kisa ake yi idan an yi shara'ar da Allah ya rubuto Allah ya yafe a yadda muke kyautata zato domin mu musulmai ne, ke Ameerah bulala kike so a masa ne? Sai na kai shi kotun musulunci a kwontar da shi da hannayena na masa, ko mu din zamu je mu sanar kafin a mana aure mun yi rashin jin da a yanzu rayuwar nan yannayin zamani da ya zama haka daidaikun samari da y'an matan ke tsalakewa suke nan kuwa su tuba su dawo su bi Allah, Allah ya dube su saboda dama d'an Adam Ajizi ne, kuma Allah yace da ace dan Adam zai rayu ba yin laifi ya tuba, da ya shafe duniyar ya zuba wasu, ko baki dan cewa ka yi laifinma ka daina babar daraja bace da zaki ringa rayuwa a matse, a takure, ki kuma takurawa yarona a kan haka har ki budi baki ke AMEERAH ki ce da YUSUF zai rayu da yarinyar nan?!" Ya karashe muryarsa a sama saman da ya saka Mah sake shiga a halin tsorata tana kallonsa

A kausashe ya ci gaba da fadin" Inaga dan kin haife shi, yana karkarshin yi maki biyayya ne kika kasa yarda da darajarsa da kuma girman da Allah ya bashi, ina tunanin dan YUSUF bashi da wajen zuwa ya zubar da hawaye sai jikinki ne kike aiki da wannan damar a tunaninki so din ne kina karra daba masa wuka a zuciya, Ke Ameerah da yawa sarakan ne suke badalar kuma da matayen na kirki sun kilace, manyan masu koyar da tarbiyyar ke aikata badalar kuma sun kilace iyalansu, ban san me iyalansu ke aikawa a boyen ba, abinda na sani shine Allah gafurun rahim ne, ban ce d'ana bai yi laifi ba, d'ana ya yi laifi sosai, kuma na fi kyautata zaton dan na taba y'ar wani Allah ya jarabceni da d'ana mafi soyuwa a zuciyata ke wannan halaya marar dadi, yake fitinar kowa a da, kuma Allah ya amshi adu'ata har aka wayi gari YUSUF ya bar aikatawa ke kin san ba dan yana tsoron dan Adam ba ya daina dan na wannan tsarin a duniyarsa, dan yana tsoron Allah ya daina, kuma mun yarda da tubansa domin baya rayuwa dan ace ko a gani, shine zaki duban min yaro ko rikita shi?.......... AMEERAH!"
Bah ya sake fada yana dafe kansa da hannayensa bibiyu

ya sake dubanta idannuwansa sun gama yin ja, ya ce" Inaga Nine baki yafewa ba, da ace kin yafe min da baki min haka ba, Ameerah a me kika dauki sarauta?"

Mah tana kallonsa hankalinta gaba daya a tashe ta ce" Bello, dan Allah ka kwontar da hankalinka mu yi magana, a ganina d'a ai duk na kowa ne, kuma yarinyar nan idan an bata dama an rungumeta ina ga ai aikin lada aka yi ko?"

" Tabas baki san menene sarauta ba, kuma kallon nan da kike yiwa d'anki a bagas ya sa kike tunanin irin kowani mutun ne da yake iya daukan wannan rayuwar!"
Bah ya sake katse Mah, sannan ya juyo ya fuskanceta ya ce" Ki yi hakuri da kiyayar da Hajia da ahalina suka nuna maki koda kuwa mu din nan mune ke dauke da gagarumin tabo na rashin ji a gidanmu, sai dai kuma sarauta gare mu!, ki yi hakuri da kika ga sun kasa yafe maki da wuri yadda ya kamata ba dan kin fi kowa laifi bane ya sa yadda lamarin ya zo mana ne, ki gane Nine na ja maki tsana da na kasa hakura da ke na kasa baki lafiya, na kasa barinki ki yi rayuwarki da wani, tunanin wanina na iya daukan ki bayan ke tawace, rayuwata ce ya sa na kasa baki damar ki rayu cikin farin ciki na saka maki kunci mai tsananin da har kika kasa gane Allah kika yiwa laifi ba uban wani ba da har za'a kasa dubanki a cikin al'umma bayan ke din mai kyakkyawan tuba ce, tunda kika yarda da abinda na saka ki kike kuka har zuwa yau, a haka na jajirce bayan na san in na aureki ba Ni ba sarauta, na yarda na auri abata dan na zabe ki a kan sarauta, kuma na san zaki zabe Ni a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login