Showing 102001 words to 105000 words out of 188741 words

Chapter 35 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9838

a yanzu ba lalle ne na iya bari wani abin ya rikita masa lissafi ba, sai in ya fi karfina!"

Mah ta dafe kai cike da zulumi, karshe dai daren nan wani iri suka kwana dan kowa da tarin tunani ya kwonta har kiraye kirayen sallar asubahi ta saka kowa ya kama gabansa dan gaisar da Ubangiji

kamar yadda ta saba zuwa gaishe da Mah tun da duhu duhu kadan hakan ne yauma ta je ta duka gaban Mah ta gaisheta

har zata mike Mah ta saka ta koma ta zauna, sai da Mah ta gama abinda take yi ta fuskanceta, da yannayin kula sosai ta ce" Baby, yauma zan sake yi maki tambayar da na maki sau uku a baya, dan ina son amsa ta karshe, domin hakin hakan a wuyuana yake, ki fada min, kina son ABDALLAH sosai zaki iya yin rayuwar aure da shi?"

RAUDA ta lumshe idannuwanta da suka yi mata nauyi, a hankali ta gyada kanta muryarta a raunane sosai ta furta" Eh Mah "

Mah ta tsura mata ido, haka kawai take ji a ranta abinda take fada ba gaskiyar abinda take son fada bane, sosai take son tambayarta da gaske ba komai tsakaninta da wanin bayan Abdallah, ama ta gaza, dan haka ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Allah ya tabatar mana da alkhairi, daga yau mai gyara zata zo a fara gyara min y'ata in sha Allah, je ki huta kafin a jima zan kiraye ki mu shiga kicin mu fara girkin Larabawa"

Mikewa ta yi tsaye tana jin idannuwanta sun ciko da kwallah ta juya ta fice, Mah kuwa ta rakata da kallo tamkar tace ke zo nan, karya kike ki fada min gaskiya, sai dai ta gaza dan bata san yaya zata hau yarinyar da fada ba, bata iyawa, tana kaunarta tana jin tausayinta sosai a rayuwa

kasancewar coridor ne kafin a fito falo karami sannan a nufi wani corridor din a tafi dakin Salima ya sa take tafe a hankali har ta zo daf da fita daga corridor din ta ja da karfi , kirjinta na mahaukacin dokawa , a hankali ta sada kanta daga kallon tsararan rawanin dake zagaye da ni'imtaciyar fuskarsa , jikinsa dauke da manyan tufafi na dakarun sarakai, sarakai masu aji, sarakai masu ya'yan banki, suturarsu kadai abin girgiza zuciya ce bale idan Allah ya halice su da iza, da kwarjini, kallon su na hadasa danshi a ido da bugawar zuciya koda baka so ba, girmama su ya zame maka dole saboda Allah ne ya basu ba wani ba
kan da ta sada yake kallo, kafin ya bi yan yatsunta dake dauke da jan lalle da kallo

a hankali ya furta" Raudah......?"
Gabanta ya sake faduwa, ta dago dubanta a raunane ta saka cikin nasa

idannuwansa ya janye kadan daga cikin nata , kasa ya furta" Ya yi kyau"

jikinta ta ji ya fara rawa, tsigar jikinta na tashi, gumi na son wanke mata fuska, da sauri ta sada kanta dan ba zata iya duban idannuwansa ba

Sai dai bata tsira ba, domin dukar da kanta da ta yi ba shine ya rabata da shi ba, har sai da ta ji amon muryarsa wannan karron daf da ita ya sake furta" RAUDAH?"

"innalilahi Wa inna ilaihi raj'une..." ta fada a hankali saman lebenta kirjinta na bugawa da karfi
Sosai ya karanci abinda ta furta, ama bai sace masa gwuiwa ba, to shi meye kuma ya rage tace masa? wannan ai tabataciyar kalma ta maimaita dan tace daga Allah muke gareshi zamu koma, ta fa taba ce masa shedani har ta nemi tsari da shi fa ko? , a hankali ya hadiye yawun dake son busar masa da makogwaro kasa kasa ya furta" Nace ya yi kyau RAUDAH"

idannuwanta dake cike da kwallah ta dago ta saka cikin nasa, da karfi ta ja numfashi ta sauke sannan ta kausasa dubanta, da karfin ikon Allah ta sakar masa zazafan harara sannan ta ja baya ta yi tsaye hadi da dukar da kanta zuciyarta na tafarfasa, bata san me yasa ba, gani take yi babu wanda ya taba wulakantata irinsa, ita a yanzun gani take yi kamar baya jin tsoron Allah, ashe shi aurema zai yi nan da sati biyu? tirrrrr tirrrrr tirrrrr da wannan hali, tirrrrr da fitinanen hali, kuma tana tausayawa matar dan kuwa ta iya ganganci, aikin banza Allah ya sa a Daura masa hudu a tashi daya kowama ya huta, itafa dama tunda ta ga idannuwansa ta gane za'a yi biye biye a nan, shi yasa ta zabi auren Balarabe dan yanzu ko bahaushe ka shige tsaf zai maka kishiya, ita kuma ba zata taba zama da kishiya ba, bata so, bafa ta so, bata so!, aikin banza wai aure zai yi , hum!

ya jima a tsaye yana kallonta, kafin ya tabe baki ya yi ciki shima yana jin wani tukuki na kama masa rai, shirme kawai, karma ta yi maganar ma mana, y'ar cen gwarama a yi a mata auren nan ta tafi ko kowa ya huta, dan ta galabi kowa da kowa a gidan nan, sai rashin kunya da rashin girmama manya, aikin banza kunshin Bama wani kyau bane ya yi fa, kawai dai ya dan haska hannun ne, kuma sal ba'a yaba dan wani abin ba, shirme, dala shigowa ya yi ya ga Mah sannan ya wuce wajen wace tsohuwar su gama magana tace tana neman sa,

juyar da kai RAUDA ta yi ta wuce kamar ana korarta ta nufi falo baba tana sake turo baki da maganganu a ranta da jin haushi, ta kuma yi alkawarin ita da shi ido, tunda dai haka yake!

bai jima ba ya fito ya fice da jama'arsa suka nufi bangaren Hajia baba

sunna zuwa suka tsaya a waje ya shige dan baya shiga wajajen nan da su

yana shiga ya tarda Hajia na magana ranta bace tana fadin" Kin ga, ki tashi ki tafi ciki, ko ki koma bangaren ku, dan bana son fitina, bana son fitina, ki cire wannan tunanin a ranki, dan abu ne da ba zai yiwu ba, ba tsanarki na yi ba, ba kuma hamayanki nake zagi ba, ama ba zan taba yin haka ba, kin ga tuni an kawo min hotunan wa'inda zan zaba masa , na zai yiwu ki kawo min wannan maganar ba, tashi ki shige ciki nace!" Hajia ta fada a tsawace, hakan ya sa ta mike da sauri ta nufi cikin tana fashewa da matsanancin kuka da tarin bakin ciki hadi da alwashin da ta barwa ranta, dan bata tunanin za'a yi macen da zata zauna da YUSUF in dai tana raye!

murmushi ya yi ya karasa shigowa yana salama ciki ciki ya karasa ya zauna a ransa yana ayana' Hajia Nana, na fada maki sai na galabeki, ki jira Ni!'

harare hararen da yake ya sa Hajia sake tausasa muryarta ta ce" Dama ka ga hotunan da aka kawo, walahi in fada maka a nan ya'yan limami da manyan mutanen kirki ne, to ban zaba ba nace ka zaba da kanka ka ji dan arziki?"

harara ya sakar mata kafin ya dauke kansa ya ce" Kiran da kika min kennan?"

Hajia ta yi tsuru tana kallonsa
ya girgiza kai yace" Ke dai tunda iyayena ke jin maganar ki ai kin gama da Ni, kika saka tunda asubahi ya tisoni a gaba na zo dan wannan abin? ki zaba kawai ai kin gama magana, Ni tafiya zan yi inada ayyuka "

Hajia na murmushi ta ce" Allah ya huci zuciyarka, to shikenan ama dan Allah in baka so fada min mi kashe mu birne abinmu a nan ka ji? babu wanda ya isa yace ba haka ba!"

mikewa ya yi yana ciro wata takarda mai dauke da check na kudi ya ajiye sannan ya dubeta ya ce" Idan basu isa ba, ki kirayeni"

Daga nan ya wuce, Hajiar kuwa ta dauki kudin ta duba sannan ta yi murmushi tana furta" Ko y'ar Sarkin Saudiya ce ai sun isa a aurota, kudin nan sun isa MALIK"

Tun daga wannan lokacin aka shiga hada hada na shirye shiryen biki, bikin auren mutun biyu, MALIK da amaryarsa sai kuma RAUDA da ABDALLAH

ana saura sati guda a yi daurin aure aka shiga kaura sabon ginnin fadar
ginnin da gaba daya Nijar harda kewaye suka dauka, domin yan zuwa gannin sabuwar fadar Sarkin garin Tsaburim sun dauki vidio da hotunna na waje waje, Bama kamar balbalin sarki wanda du abinsu babu wanda ya samu shiga cikin falon bale har ya kai ga dakunan da saura wajajen bangaren, abinda dai ake cicirawa shine an ce faloma biyar ne, wasu su ce shida , abubuwa dai gasunnan ba'a cewa komai, domin ba'a karra rikita kan mutane ba sai da aka fitar da kayan tsohuwar fada aka ringa sadaka da su, kayayyaki masu kyau da tsari, kai MALIK ya sha adu'a daga bakin talakawa domin sosai aka taimaki mutane da ayyukan yi a sabon gidan Sarki

a cikin wannan tsakin, sam bai samu lokacin kansa ba, dan kuwa yana fada ne amma aikin da yake yi ba na wasa bane, dan sun bude manya manyan shagunan na furniture, su Taj na kai kawo a kan harkokin shi kuwa yana magana da mutanensa na waje , ga kuma kayan sabon gidan da ake zubawa dan kamar yadda aka yiwa kowa bangarensa sai da aka zubawa kowa abinda zai bukata na rayuwa domin ba'a far kaurowa ba sai da komai ya gama kamaluwa sannan aka kauro,ciki harda Nana domin har ita ya yi mata nata bangaren, dan ba zai taba so su yi nisa ba, ya fi so tana kusa da shi ta yadda zai idasa nufinsa a kanta!

ana kaurowa shiga shiri mai sunna shiri, domin ana saura kwana uku daurin aure da bikin sarautar tuni abubuwa sun kankama ba'a kama hannun yaro

a irin wannan lokacin na farin ciki zukata da yawa na cikin tashin hankali da rauni na firgicin abinda suke dannewa, tun daga kan MALIK, MAH, BAH, SALIMA, RAUDA, NANA, da y'ar NANA, sai daidaikun masu boyayar manufarsu kowa na nasa sharafin har zuwa yau da aka wayi gari y'ar gidan Nana na zubar da kumfa ta bakinta sanadiyar abinda ya yiwa zuciyarta yawa a sashen yayanta wanda ya maidata wajensa tun lokacin da aka kauro nan ya kauro bisa umarnin MALIK domin a tsakaninsu akoy kyakywar alaka ta zumunci da girmama junna, dan ko shi MALIK ya yarda da kaunar da RISLAN ke yi masa, yannayi ne ya zo da hargitsin da ba zasu mori zumuncin yadda suke so ba, gashi a yanzu gannin MALIK ya yi mugun wahala, dan tsarin Sarautar wannan bawa na tare da mugun karfin gaske ta yadda idan a da ganninsa na arha a yanzu ya zama baban aiki ko ga ma'aikatan bangarensa bale na waje, shi yasa yake samunsa a masalaci su zanta , daga nan kuma sai wata sallar dan baya rasa sallar jam'i a baban masallacin cikin fadar wanda yake iya zuwa a cikin yan sakwani dan ba nisa sosai da shashinsa

hankali tashe ya nemi layin Nana ya sanar mata, sannan ya shiga neman agajin duk wanda ke iya taimaka masa, ciki harda HAJIA BABA;





washhh yan yatsuna๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚

Azl 36


*KADA A YI BA KU, BONANZA TA NOVELS DINA A KAN FARASHI MAI SAUKI, WATO 1K SU 22 CIF IN SHA ALLAH.....KU GARWAYO DAN SAMUN NAKU A BISA FARASHI MAI RAHUSA .....KU TUNTUBI NUMBARNA 93811618*


*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo


A lokacin da sako ya iso wajen Hajia kwarai hankalinta ya tashi, a lokacin ne kuma tana tare da Bah, wanda nasa hankalin ya fi na Hajiar tashi, domin a fitowarsa sun ci gaba da mu'amala ta yan uwantaka tsakaninsa da y'ar uwarsa sai dai ba irin na da ba, ya so kwarai ya san ba'asi ama harta Hajia sai ta nuna masa ba wani abu, shi dai abinda ya sani daya ne tsakaninta da yaronsa ya nuna mata babu wata mummunar magana kuma, dan shi ba yaro bane ba kuma munafiki bane da zai tsaya wani kwane kwane, abinda aka yi a da har shima aka dora shi sama ya yi yanzu ya gane ya daina, yana so a mutunta masa yaronsa ko a zuba masa ido, ta yiwu shi yasa zumuncin nasu ba irin na da bane, ama duda haka sunna gaisawa sosai

ya rigayi Hajia karasawa bangaren na RISLAN, tuni likita ta karaso domin Hajia ta bada umarnin komai tsanani kar a fita da ita a haka a kawo likitar cikin gida ta sirri, domin a baban bangaren da suka baro aka yi tsarin madaidaiciyar asibiti aka zuba kayan bukata da kwararrun likitoci wace ke anfanin da ciki da na waje

Tunda ya shigo ya zauna daf da Nana yake bata baki, domin fuskarta har ta haye , idannuwanta sun kumbure sundume kana ganninta ka san hankalinta ba a jikinta yake ba, takan kalli dakin da suke ciki sai ta ja numfashi da ajiyar zuciya, domin DAYANA itace y'arta daya kwalin kwal mace, kuma tana son abarta sosai shi yasa duk abinda zata yi take hakuri ta rungumi abarta, sai gashi DAYANA zata kashe kanta saboda namiji?

kiraye kirayen sallar magariba ya saka Bah mikewa ya mata alamun zai je sallah ya dawo

tare suka fita da RISLAN suka nufi masalaci bayan sun yi alwallah

sun gabatar da sallar sunna hanyar dawowa bangaren na Nana Bah na gwada kiran layin matansa gaba dayansu yana ji a ransa kamar ransa na daf da bacewa sakamakon rashin ganninsu bayan da aka sanar babu wace bata ji ba, ama shiru basu zo ba RISLAN ya dukar da kansa zuciyarsa na sake neman tarwatsewa saboda irin yadda suka zamo tamkar mujiya a cikin familly din saboda halayar mahaifiyarsu, babu mai yi da su, babu mai daraja su, domin a lokacin da ta yi abin nan yadda kuka san yaษ—uwar mutuwa aka abin ya yadu, kafin kace kwabo kowa ya ji kuma kowa ya sani nan da nan aka shiga tofin Allah tsine domin wannan abu da ta yi Babu abinda ya kai shi abin kunya da muzantawa, karrara ta fito ta nuna son kai a kan abinda bata da tabas, koda tana da tabas a kan ษ—an dan uwanta uwa daya uba daya? hakan ya sa a yanzu dai mahaifiyarsu bata da wani abokin hulda a cikin garin nan sai masu hali irinta, ita da kanta du a takure take ga matsaloli na yau da gobe, domin ba matsalar son a dora su a mulki kadai ke yayube da rayuwarta ba, ga ta yaya ga ta wajen aiki.

Bah na gama kiran daya bayan daya ransa bace yana fadin me kennan?, me yasa bai gansu ba, yana huci ya kalli RISLAN ya ce" Wai me yake damun yarinyar nan har ya kaita da shan guba? me yake damunta a rayuwa ita kuma da har ya fi karfinmu muna zaune a cikin gidan nan?"

kai RISLAN ya sake sadawa yana fitar da hucin numfashi mai amon "HUMMMM." Ama ya kasa fadin komai

Bah ya sake dubansa a lokacin da suka shiga dan get din bangarensu yana hangen daidaikun kuyangin da ya tabata na Hajia baba ne ya ce" Tana da wata matsala ne da ban sani ba?"

RISLAN ya rasa yaya zai yi, domin irin yadda Bah ya tsaya yana nufin sai ya ji abinda yake damunta kennan?

kai ya sake sadawa a nutse ya furta" Bah, shirme ne kawai ta sakawa ranta da abinda bata isa ta bawa kanta ba, da ace ta bi maganar da na fada mata ta fawalawa Allah na tabata da ta ji sauฦ™in abin cikin ruwan sanyi, domin tabas da Allah ya bata mafita nagartaciya, idan har abinda take yiwa din dama nata ne sai ta ga ba tare da ta daga hankalin kowa ko zubar da wata kima Tata ba Allah ya kawo hanyar da shi kadai ya isa ya kawo ta samu biyan bukata,ama sai ta ki, a kulun da irin abinda zata fito da shi, a kulun da irin fitinar da zata bilo mana da ita, shine na dawo da ita nan tunda maman rashida na nan koda yaushe tana hankalce da ita, shine yau ta yi anfani da damar nan da ta ga ta fita anguwa gidansu ta sha abinda zata bar duniyar gaba daya, ko me take tunani, ko ina karatunta? ko bata san du wanda ya kashe kansa ษ—an wuta yake ba? Ni dai abin ya matukar gigita min tunani"

"To ai baka sanar da ji damuwar da take sakata hakan ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login