Showing 108001 words to 111000 words out of 188741 words
ana ta shirye shiryen auren MALIK
A cikin part din Mah yan uwanta da mutanenta na arziki ta ko'ina sunne ke kai kawo ana ta hulda irin ta manya
karfe goma na yi Mah ta tashi RAUDA ta saka ta yi wanka wannan ta rakata dakin da ta ware saboda harkar kitson ta da kunshinta, karfe goma da yan mintunna Bara'atu ta karaso gidan da akwatinta domin ta yi iya yinta mijinta ya amince mata ta kwana dan ta fita daga girki yau ita da amsar girki kuma sai ya yi kwana biyu a dakin dayar matar, hakan ya sa hankali kwonce da kansa ya kawo ta yana fada mata zasu hade ne gobe ai saboda daurin auren SIR.
Tunda ta karaso Salima ta samu ta fice dan idasa shirye shiryen kayan RAUDA din, domin harkar kayan lefenta kiri kiri Mah ta nuna ba za'a kawo ba a zuba a dankareren gidan da zata zauna wanda ABDALLAH ya tanfatsa , ta nuna akoy sutura da za'a yi mata a nan , wadinncen yan kai amarya sa karba, ita kuwa ta yi masa haka ne dan sarai ta san bashi da kowa a garin sai irin yan cin arzikin nan, ba zata so a cakula mata lamarin y'a ba, in sha Allah idan an kaita gobe ta tarda kayanta kawai ya kai ajiye, Mah din kuwa tuni ya je ta ga kayan da ita da Salima da gidan da komai, harda dankareriyar motar da aka siya mata a kampanin YUSUF a parker as gift na oyoyo
tunda Atu ta zo take hankalce da yannayin RAUDA , gaba daya kana ganninta zaka gane tunaninta a rarrabe yake, duk irin yadda ta yi dan ta kawo hankalinta kanta gudun kar ta gane halin da take ciki sai da ta ringa tambayarta lafiyarta? me yake damunta? bale zuwa yamma da aka shiga shirye shiryen sakata a lalle kamar yadda tadar garinmu yake idan amarya budurwa ce ana sakata a lalle du sai ta idasa rikicewa ya zamo bata magana bata amsawa har sai da Atu ta sanarwa Mah dake cen cikin baki sai walwali take domin tun daga kan shigarta har fara'ar dake fuskarta zaka gane tana cikin wani hali na farin ciki ne
ko da Mah ta shigo ta sameta an gama wanke kunshin ya yi wani irin kyau ta zauna daf da ita dan mai kunshin ta gama shafa mata turare a tausashe ta kamo hannunta ta ce" Baby, ko dai rikicewar za'a barni ne? to ba gari guda muke ba? idan kina so du safia sai in je in ga yaya kika kwana dan Ni kam har sai an ringa yi da Ni ana cewa wata irin uwa mai zuwa gidan y'arta"
daria mai kumshin da Atu ke yi, Atu na kallonta tana karantarta, kai, ta kasa yarda cewar babu wani abu dake damun RAUDA, ta san RAUDA tun sunna yara, ko da ido ta yi magana zata iya fassara abinda ta ce, sam ta kasa samun sukunin yannayinta , wani abu na damunta, wani abu mai girman gaske, ama kuma ta ki fada, a haka har aka gama shirya sakata a lalle domin gabanin sallar magariba ake sakawar,
Tunda aka fitar da ita baban falo dan saka lalle aka zaunar da ita saman cafet aka cire mata hijabi Sarkin kida ya fara kidan nan mai hawa kai, zabiya nata , makeriya na nata, masu daukan vidio na dauka, masu hawaye na hawaye hankalinta ya idasa tashi a hankali ta kankame Atu aka shiga shafa mata lalle , kanta, hannayenta,kirjinta dai da sauransu ana darzarta har aka gama aka lulubeta luf sannan aka mikar da ita Mah da Atu suka kaita dakin Mah suka nufi bayi da ita dan yin alwallah ta gabatar da Sallah kafin cin abinci a irin lokacin ne kuma RAUDA ta dauki wayarta tana ta amsa kiran Abdallah tana tsokanarsa shima yana ramawa har ya shaida mata abinda yana fadar, kuma a nan zai kwana? ita dai ta ki bashi RAUDA har ta gama sallah ta kwonta ta ki sauraronta, dan ba yadda bata yi da ita kan su yi fira ko zata iya yi mata magana amma fir ta kiya har sai da itama lokacin nata barcin ya yi ta hakura ta kwonta zuciyarta cike da tunanin abinda ke damun aminiyarta
karfe uku na dare message ya shigo wayarta
kasancewar ba barcin ta samu ba sai ta laluba ta duba
message din na dauke da kalamai ne kamar haka
"kin san bakya son sa, me yasa kika cika kafiya ne?"
haka kawai take bin message din da kallo, wani bakin ciki na turnuko mata zuciya, ta ki ta amsa dan a tafiyar nan ta fi so ace ta tafi ba tare da ta nuna ta gane Yaren mai Yaren ba
"ki sani, idan kika yi haka, kin kuntata min, kuma ba zan taba yafe maki ba! RAUDAH tunda na fara gannin ki, na san na hadu da *AZAL DINA!*"
Yanzun kam zaunawa ta yi zuciyarta na kunna ta shiga rubutu kamar haka" kai ne *AZAL DINA* domin kafin ka ban san ciwon nan ba, kai ne AZAL DINA saboda kai ke son hadasa min fitina a duniyata, kana tunanin Ni mai iya raba makiyi ce bale wanda ya zamo tsokana? IDAN KA YARDA KA AURETA SAI NA DAME KU, WALAHI SAI NA DAME KA!" daga nan ta tura sakon a hankali ta kwonta zuciyarta na tabatar mata da lalle wanda take tunani ne,...to ama ita da kanta bata san me ma'anar furucinta ba, abinda ta sani daya ne ba zata taba iya yafe masa idan ya auri wata ba
(tambayeta itace, da kuke cin alwashin nan, shin akoy episode din da muka rasa wace kuka furtawa junna kalmar so?....π€π€π€π€)
babar rana
Rana bata karya
................lokaci na zuwa sai dai mai rai ya mace
...
........ a yau take babbar rana,
πππππππππ₯Ίπ₯Ίπ₯Ίπ₯Ίπ₯Ί
Azl 38
*KADA A YI BA KU, BONANZA TA NOVELS DINA A KAN FARASHI MAI SAUKI, WATO 1K SU 22 CIF IN SHA ALLAH.....KU GARWAYO DAN SAMUN NAKU A BISA FARASHI MAI RAHUSA .....KU TUNTUBI NUMBARNA 93811618*
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
ππΌ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunchingππ»ββοΈπΊπ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
ππΌ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ππΌππΌmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nanππΌ (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ππΌππΌππΌ (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa baπππ sai kun zo
Ranar da ta zamo baba a wannan ahalin ta farin ciki bana tunanin ta zamo ta farin cikin ga fani biyu, domin tunda aka wayi gari Mah ke kan RAUDA, har likita ta zo ta dubata an yi mata allura saboda zafin da jikinta ke dauke da shi, gata gum ta ki ta kula kowa, karshema Mah din ce da kanta ta kaita bayi duk irin yadda take nokewa ta kasa kiyawa Mah ta taimaka mata ta gasa mata jiki sosai suka fito daga ita sai Mah sai ATU dake Binta da kallo Mah ta saka Atu ta dauko wasu kayan, domin yannayin nan nata ya zama dole a kyaleta da cenje cenjen kayan da aka so a wuni ana sakata yi da mak'up, dan kuwa koda an tirsasata an yi kwaliyar ba zata yi kyau ba, karshe ana gama turareta da turaran wuta ta nade saman gado idannuwanta a rintse kanta na sarawa hannunta daya na cikin na Atu ta jimke sosai ta yadda Atun ke karra karantarta
Da kula Mah ta ce" Daughter dan Allah ki kular min da ita, zan rufe kofar nan da ky zan ringa kawo maku abinci da kaina idan ke kina son fita sai ki sanar min na kawo maki ky, dan in dai na bari a bude dole sai an cika mata dakin an dameta , ga wayarta nan akoy numbana idan wani abin ya taso ki kiraye ni Please"
Atu ta amsa Mah da girmamawa tana kallo Mah ya sake kama hanyar RAUDA ta dago da dubanta a nutse ta ce" baby , ina zuwa kin ji, yan daurin aure tuni sun taru, bari na je na dawo""
RAUDA ta gyada kanta tana lumshe idannuwanta, Mah ta juya ta fice ita kuwa a hankali ta silale ta dora kanta a saman cinyar Atu wace itama tana ji tana gani ta kasa shiryawar dan yannayin RAUDA ya gama rikita mata lissafi, ta rasa inda zata kama, kai ko bakin da ta tabata yau zata ringa yi ta ko'ina bata san yaya zata kula da su ba, dan bata san ta inda zata iya barinta a wannan yannayin ba, kuma tsaf ta ki yarda da abinda Mah ke son nunawa, wai tsoro ne irin na kowace budurwa na ranar aure ya sa RAUDA shiga wannan halin, kai, ta rasa me yasa ta kasa yarda da hakan, kwarai ta san da zata iya shiga wani hali ama ba wai na tsoron wannan ba, ta fi kyautata zaton tuna marigaya ne ya sakata a wannan halin shi yasa ta kasa katabus ita dinma
A dayan bangaren kuwa, a cen cikin dakinsa na biyu, zaune yake bakin a bakin kujera, hannunsa rike da cofee mai dacin gaske yana dan surba yannayin hankalinsa kamar ba a cikin duniyarmu ta mutane yake ba, idannuwansa sun yi Jajajir, jijiyoyin jikinsa sun yi birde birde tun daga na hannayensa har zuwa na kansa sun yi wani iri tamkar wanda yake cikin matsanancin halin rashin lafiya
Tun zuwan Bah na biyu dan ya sheda masa tawagar SHAHEED sun karaso an tafi yiwa su NAJEEBA rakiya bangaren Mah yake so ya dan motsa dan ya karasa baban falonsa, ama ya kasa daga koda Ζafarsa daya ce bale ya nada rawanin dake ajiye daf da shi wanda Bah ya zabar masa ,
yana nan zaune Bah ya shigo, ya sha shiga wace sai dai mu ce masha ALLAH domin ya dauki manyan kaya sai walwali yake tamkar shine ango, bakin nan nasa kuwa hakoransa a waje ya kasa hanna kansa sakin murmushi na farin ciki ga hularsa ta kafu a saman kansa ya zo inda YUSUF ke zaune da dan yannayin mamakin gannin a nan din dai yake a zaune? gashi bai ajiye cofee din da yake sha ba har yanzu? Sai ya ji kamar hankalinsa zai tashi yana mai tabatarwa kansa bashi da lafiya ne, da kula sosai ya zauna yana fadin " Son, ko baka da lafiya ne?, SHAHEED na baban falo, bayanshi duk wasu bakin dake daf da kai sun karaso tuni fa, ko na zaka iya halartar taron bane?"
Idannuwansa ya fara kiftawa masu nuni da yana raye dan bayansu babu abinda ke nunawa, ya kai dubansa kan mahaifinsa a nutse ya mikawa Bah cofee din ya lumshe idannuwansa ya gyara zamansa yana kallon BAH tare da bashi rawanin ya yi kokarin sakar masa murmushin da bakinsa labansa sannan yana yi ya gimtse yana kallon BAH wanda ya kasa gane abinda ke damunsa, sai dai gannin ya bashi rawanin hakan na nufin yana iya zuwa, sai kawai ya shiga yi masa nadi, nadi na gani na fada, domin Bah dama kwararre ne a fannin nadin rawani yana gama masa ya sakar masa murmushi ya furta" Masha ALLAH, Allah ya tsare KA MALIK, tashi mu je"
mikewa ya yi yana jin turaran da aka makawa suturarsa har kamar ya yi yawa, domin tun karfe hudu Mah ta zo ta yi ta yi masa addu'a sannan ta fitar da kayan da zai saka ta yi ta turare su , sai da Hajia ta iso ne ta tafi , ita kuma Hajia da ta zo ta ringa masa hade hade abubuwa masu daci tana bashi sannan ta saka masa turaren wuta da hayaki a daki, shi dai yana biye da su da ido sai da ta tafi ne ya cire jamabiyar da ya yi sallah da ita ya nufi wanka dan kaurin abin nan ji ringa yi ya karra dagula masa lissafi.
A nutse ya fito baban falonsa idannuwansa na sauka a fuskar SHAHEED, Bah kuwa ya fice dan sanar da su fitowarsu
kallon ido cikin ido suka yiwa junna YUSUF ya janye nasa yana karasawa inda yake zaune
yana gannin YUSUF ya karaso ya mike tsaye, suka kama hannun junna sannan suka yi gaisuwar nan da aminai ke yi ta hanyar dukan kafadar junna kadan haka sannan ya dube shi ya ce" Man, jikinka zafi, Are U ok?"
YUSUF ya dan kai hannunsa wajen hancinsa a hankali ya dan shafa, sannan ya masa alamun lafiya, kana suka fara tafiya, sai dai duk irin yadda ya kasance mutun mai surutu a gabansa a yau din bakinsa gum yake , har suka fito wajen ya karade da hayaniya da busa ta mamaki, ga kade kade irin namu na gida da ake yiwa sarakai kai ko kai ba dan gidan sarakai bane sai tsigar jikinka ta ringa tashi saboda abin baba ne, na manya ne
tunda suka zauna wajen daurin auren nan ya kasance zuciyarsa na karra cinkushewa
bai yarda da cewar eh lalle ta faru ta kare ba sai da aka daura nasa auren da amaryarsa , yarinya yar dangi gaba da baya, wace ko a garin ana maganar ahalinta domin sun yi fice sosai da arzikin da kuma kyau da isa, yarinya mai sunna AMNAH , a hankali kunnayensa suka ringa jiyo masa shelar daurin aurenta,
idannuwansa dake lumshe ya dago ya sauke a kan ABDALLAH, wanda fuskarsa ta cika da yalwatacen murmushi
a hankali ya dauke dubansa ya kai fuskar SHAHEED dake kallonsa sai kuma ya dauke ya ci gaba da kallo har aka daura aka gama , aka shiga shelawa ana ta taya junna murna
kansa bai sara masa da mugun karfi ba sai da aka sanar da Tabatuwar daurin auren a lasifika mai karfin amo, a nan ya idasa lumshe idannuwansa a hakimce a saman kujerarsa ta mulki ta dakin daurin aure .....a irin lokacin ne kuma ko'ina ya dauka lungu da lungu, sako da sako na baban gida, inda babar jakadiyar bangaren Mah ta shigo falon ta rangada guda mai kaifin tsiya muryarta sama sama dan zata so ace itace ta samu goron kawo albishir ta shiga sanar da daurin auren yan gata ya tabata, muryarta a bayane take fadin boyayiyar amaryar uban talakawa da kuma mijin autar Mah, a irin lokacin ne Salima dake sanye cikin mahaukaciyar shadarta tana dauke da faranti mai dauke da kayan lambu na Rauda Ta bude dakin da RAUDA ke ciki , Muryar jakadiyar ta kai kunnayensu ita da ATU
A lokacin da basu ankara ba , basu kawowa ransu ba suka ga RAUDA ta mike tsaye tana zarro ido, sai kuma ta dora hannayenta bibiyu saman kanta ta fashe da matsanancin kukan dake tukarta ta zube jikin ATU muryarta na furta kalma kamar haka" Shikenan , ba cuci kaina, shikenan na zabi taurin zuciya na halaka kaina, shikenan an min katanga da abinda nake tunanin babu katangar da zata iya shiga tsakaninmu, innalilahi wa inna ilaihi raj'une!"
A rikice Atu, da Salima da ta idasa shigowa ta ajiye abin nan suke kokarin tayar da ita , suke kokarin ganin ta tsagaita ta saurare su, ama ba hali, ta ki ta saurare su, ta ki ta tsagaita kukanta, wanda kana ganni zaka gane idan ta ci gaba da yinsa a haka komai na iya faruwa da ita
sakinta Atu ta yi ta karasa ta dauki wayarta, jikinta na rawa ta shiga call ta ringa bincikawa, sai dai duk abinda ta so ganni bata gani ba, domin furucin RAUDA ya sakata wani tunanin da ya kayar mata da gaba
har zata ajiye mata wayarta a kirawo Mah, sai ta daina ta shiga message kai tsaye idannuwanta na sauka a saman numbobin nan da idan ka gansu tabas ba numbobin kannanun mutane bane, domin su dama numbobin manya sun kasance sunna kamanceceniya da junnansu , sai ta yi tunanin ko numbar Abdallah ce, ta so ta fita ama gannin message uku ne kawai a ciki sai ta shiga kai tsaye ta shiga karanta message din
tana karantawa jikinta na rawa, idannuwanta na yin waje
da sauri ta dawo wajen da Salima ke rungume da RAUDA rai bace ta ce" Ke Salima, saketa, saketa, ke waye wannan?, numbar waye wannan nace?"
gaban Rauda sai da ya kwonci kwonci ya fadi, lokaci daya kukanta ya dauke, ta yi dif, wanda hakan ya saka Salima dake share nata hawayen gaggawar neman dagota ama ta kasa dan ta riketa taf kamar wace ke tsoron yin ido hudu da ATU
"No, no, no, ba zaki tarka ba, ba zaki taba tarkar aikata abinda nake tunani ba, domin ban ga abinda zai saka ki aikata haka din a yanzu ba, waye nace wannan da yake tuna maki bakya son Abdullah? RAUDA wani kike so daban shine kika auri