Showing 159001 words to 162000 words out of 188741 words

Chapter 54 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9821

ya duka ya cicibeta ha cirata da karfi ya dagota daga kan ruwan cikin y'ar mutane kuma matar mutane, sai dai bai sani ba ta riko rigar daf hakan ya sa ta janyo rigar Amnah kiiiiikikik ta yaga gaban sannan kafin ya idasa janyeta a jikin Amnar sai da ta sakar mata kafa

Sauketa ya yi yana kallonta da mamaki zai yi magana ta sake yin kukan kura ta karra yin kan Amnah, hakan ya sa ya furta" Lah......" Yana sake fido idannuwa

Ihu AMNAH ke yi wanda ita da kanta bata san har ina girman amon muryarta ke zuwa ba, ita dai ihun da take yi na duk wani wanda zai iya jinta ya ji ta ya rabata da mahaukaciyar nan ne tun kafin ta rabata da ranta

A haukace ta kama hannunsa da ya riketa taf yana kallonta ta saka bakinta ta dantsa masa cizo

Ido ya rintse dan har ga Allah cizon sai da ya ratsa shi sosai , kai jama'a kiris ya rage kato ya saki y'ar nan ya zunduma ihu, Allah dai ya sa ya kai dayan hannun ya talabi keyarta ya rike yana kallonta bayan ta janye bakinta tana kallonsa dan gannin ya ki sakinta

Karra bude bakin ta yi, da niyar sake dandana masa azabar da ta dandana masa yanzun nan, a yanzu kam lokaci daya ya ja tunga da ita a rike a hannunsa ya sake kama hannayenta ya cirata ya nufi dakinta da ita

Ihu take yi a yanzu, dan tun dazu bakinta a jimke yake, tana harba kaffafuwa tana ihun ya sauketa, ama ya kiya sai da ya kaita dakin ya karasa wajen gadonta ya dagata ya timata a saman gadon

A zabure ta mike ya kuma daukanta ya timata a saman gadon yana sake kallon y'ar nan da wani balagagen fitina dake sake tsimkota niyarta kuma mikewa, dan wani tsohon neman isgili idonta idonsa ta ce" Ka barni, ka barni sai na zaneta walahi!'

Ido ya sake zarrowa yana kallonta ya ce" Ke to y'arki ce da zaki zane ta?"

Ido ta zuba masa tana mamakin yadda daukanta baya ce masa komai, ta dafa ta zauna tana furta" Wash Allahna bayana, yanzu tarayya zaku min kai da matarka ku karya Ni?"

Shima idon ya zuba mata, irin yadda ta marairaice muryarta tana nuna masa zasu mata tarayar sai ya rasa irin kallon da zai yi mata,......gaba daya ta yi kamani da kyakkyawar fulawa mai kyan kallo, a hankali ya ce" Ki ji tsoron Allah RAUDA, me ta maki ne?"

Kai ta cire daga dubansa tana mikewa tsaye gaba daya, hakan ya sa ya yi saurin tsayawa a kan hanyar

kirjinsa ta bi da kallo yadda ya yi mata kikam, kuma ta san ko a kashe sai ya kasheta ya birne babu wanda zai sani, hakan ya sa ta ja baya ta bude murya rai bace ta ce" Allah ya isana Ni da ita, kai kuma ba'a yi dacen mace ba, na zata zan ga wata zukekiyar mace a gabana ne, sai na ga wancen abar, kuma walahi haduwa koma fitar da raini goma tunda ta raina min iyaye, ita ta isa ta zagar min uwa? ita din banza? duk wanda ya yarda ya zagar min ita sai inda karfina ya kare, aikin banza,, na rantse idan na kuma ganninta sai na kumbura mata fuska!"

"Ke zo nan, zo nan!" YUSUF ya fada yana sake zarro ido da kallon bakon balaki yau shi Yusufa jikan Muntari, duk inda yayi tunaninta ta wuce nan ashe? kuma idonsa idonta tana cewa wai za'a yi mata taraya

Baki ta turo ta shige bayin da sauri ta rufo tana sake tunzuro bakinta a ranta ta ayana' Ba zan zo ba, kuma yau Ni da ita shege ka fasa, aikin banza mai kama da munafukai!'

Ya jima a tsaye, ya rasa abinda zai yi, kofar bayin yake kallo , a ransa yana tunanin ya bani yanzun yaya zai yi da wannan fitinar?, da kyar ya juya daga dakin yana tuna maganar Hajia ta dazu da take fadin yarinya saliha da ita bata cewa komai sai ido idan aka yiwa jikarta wani abin ba zata kyale kowa ba......

A bayane ya furta" Hum!" Bayan ya fito ya yi tsaye ya ga ba Amnah ba labarinta

A nutse ya nufi dakinta, dan ba zai je ya kwonta haka ba kar aje wancen rigimamiyar ta yi mata ilar da ake iya yi mata shari, dan haka ya je ya kama kofar ya murda ya shiga

a hankali ya dakata yana kallonta ta baya yadda take tsaye tim da ita bata da komai a jikinta tana waya da mahaifiyarta tana sheka kuka da zayane abinda ya faru

Idannuwansa ya dauke daga kanta ya juya ya fice a dakin ya ja ya rufe a hankali ya nufi kujerar nan baba ya zauna ya shiga yamutsa gashin kansa kirjinsa na neman cenza masa yannayi

Dan murmushi ya yi a hankali yana girgiza kansa...., a ransa yana tunanin ai ba laifi an jima ba'a sadu ba, idan yanzu an ji dan alamun bukatar hakan normal ne, sai dai koda shi maye ne wannan naman ba abincin cinsa bane, bai taba tsana da kyankyamin nama ba sai a kan wannan, tabas a kan wannan naman ya gane ashe shima yana da haram a duniyar nama

Murmushi ya sake yi ya mike ya nufi dakinsa,, dan wanka yake so ya fara yi kafin komai, ga yinwa yana ji, ga gajiya kuma ta kokowar nan da ya karra


yakan yi murmushi ne kawai ya fitar da sautin Hummmmmmmmmmmmmm, shi da kansa ya gama yarda cewar kamar kumbo kamar kayansa ne

Da sassafe kusan karfe bakwai daga daga masalaci ya wuce bangaren Hajia, ya sameta a falo zaune tana ta fama da turaran wuta a cikin hijabinta ko tsoron ya kama mata hijab bata ji

Zaunawa yayi yana shan kanshinsa da yake yi mata kwana biyun nan, ita kuwa sai faman masa sannu take da gaishe shi kamar shine baban ba ita ba

Ciki ciki ya ce" Abinci nake so"

Hajia ya zuba masa ido tana kallonsa, abinci kuma? ita batama san me zai fito da bawan Allahn nan ba da safiyar nan ya zo wajenta bayan ga y'ar mutane cen an kai masa

Baki ta dan tabe ta mike da kyar tana fadin" To bari in ha ko sun gama girkin, ama kuma na zata ko ka yi hakuri a kai maku cen din kar ka ci ka bar baiwar Allah marainiyar Allah, gashi ka barota ita kadai kar aje wannan fitinaniyar matar taka ta tarda min ita ta yi mata wani abin, dan Ni walahi Amnar nan tsoro take bani"

Har ga Allah sai da ya kalli Hajia bai shirya ba, kafin ya saki murmushin da bai shirya ba yana gyada kai hadi da dan cije lebensa ya mata shiru

Hajia ta kauda kai a ranta tana ayana' Oh, d'an nan sai ya ringa wani abu kamar wanda ke dauke da wasu halittun bayan bil'adama, bari a hada a kai maku cen din dan ba zan so ka jima a nan yau yau ba ake ta tarda baiwar Allah ta yi mata wata ilar ba!'

Yana nan zaune dogari baba ya karaso ya yi salama sannan ya tsaya yana jira a bashi damar shigowa

Jakadiya ya sanarwa Hajia wanda ke salamar hakan ya sa Hajia zuwa falon ya bada damar a shigo da shi

Shigowa ya yi ya zube kasa kansa kasa ya shiga kirari gannin YUSUF din a falon, har sai da ya dakatar da shi sannan ya yi shiru kansa a kasa ya ce" Allah ya taimaki kakar saraki, dangane da dokar da kika dora ne jiya cewar gabanan kar a ringa shigowa yadda aka so dan ana takamar an shafi gidan nan dan ana aure a gidan, to tun jiya kusan karfe daya na dare baki suka zo muka hanna shiga, da kyar suka koma sun ce ne wai iyayen Mai baban daki ce wato gimbiya ta farko, to yau ma sun dawo tunda duku duku sunna kofa mutane hudu ne da mata uku da wani akace mahaifinta ne, wai ance bata da lafiya ne sunna son shigowa shine nace bari dai na sanar maki kar mu hanna su shigowar aje abin mai mahinmanci ne"

Hajia ta kalle shi da kula ta ce" Wai kanana nufin iyayen Amnah?"

Ya karra sada kansa yana mai tabatar mata su din ne

Hajia ta rafka salati tana tafa hannu ta ce" Yau na ga balaki, uban me kuma ya dawo da mutanen nan gidan nan yau? Yau na ga dangin mahaukata haka zata yi zaman auren? a'a fa, ba sai yiwu ba, a kira min Jakadiya a je da baba baba a hadata a kai masu ita, idan sun shirya barinta yin zaman aure sa dawo da ita ta yi zaman aure!, ba zai yiwu ba, a kirawo min duk wani mai isan isa a gidan nan, bata isa ba walahi, kuma duk isar iyayenta basu isa ba , ba dai a fadar TSATSUNBURUM ba!"

Ta karashe ranta bace hadi da daga muryarta, da sauri ya mike bayan ya bayar da hakuri ya fice a falon ita kuma ta zauna ranta na tafasa tana kada kafa

Da ido yake kallonta, yana mamakin rikici irin nata, tsofai tsofafi sai iya daga murya bata ko jin wahalar ihu idan ranta ya bace

Dan murmushi ya yi ya sake gyara zamansa a nutse ya ce" Ta yiwu fa da gaskiyar zuwansu fa"

Hajia ta lalle shi da sauri ta ce" wace gaskiyar zuwansu kake fadi ranka shi dade?, wace gaskiyar zuwa? basu da dalilin da zasu nemi zuba min raini a nan, jiya fa ubanya ya zo nan da maganar dan mi za'a yi mata kishiya ko shekarewa bata yi a gidanta ba, walahi yana maganar idan ka kalle shi kamar mahaukaci, Ni kuma na tuna masa shima ai auren ya karra ba iya uwarta yake aure ba, kai dai abokinsa da suka zo tare ya koma yake bada hakuri da fadin dan Allah a yi hakuri shi bai san abinda ya kawo su kennan ba da ya hanna, Ni dai ban raha masu ba na masu sumul, me suke tunani , yau da ace wata y'ar a yi kwatance ce suka bamu sai ace masha ALLAH, ama y'ar da ita da banza shashasha duk daya, mtssssss Ni dai an bani abu a rufe ana ta cutata a banza a wofi!"

Murmushi ya sake yi a nutsensa ya ce" Kar ki ga laifinsa, y'arsa ce ai, kuma kin ga kar ki sa a kore su baki yi bincike ba, tam, dan kin ga salihar jikar nan taki? jiya zane min mata ta yi kamar ita ta haifeta!"

Hajia ta sake dubansa da kula da yannayin tashin hankali ta ce" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, Kana nufin jiya Amnah din ta dakar min RAUDA?"

Sai da ya karra yin murmushin nan da ya ki barin zuciyarsa ya gyara zama ya girgiza kai ya ce" A'a, ita dai baby din ce ya zanne Amnah"

Hajia ya zuba masa ido, gaba daya gani take yi kamar baya ganewa, dan haka ta dan matso sosai kusa da kujerarsa tana kallonsa ta ce" Baka gane ba fa, ita Amnah itace y'ar wadinncen mutanen , ita kuma baby itace wace aka aura maka jiyan nan wannan y'ar karamar da bata cewa komai, yarinyar nan fa ya wajen Mamanka fa nake nufi, itace ai RAUDA ko?"

Tsakani da Allah sai da ya ji dariya ya kama masa zuciya, ya girgiza kai yana kallon tsohuwar nan da wani tsukaken bakinta irin na tsofi, to shi in ba garaje ba waye zai ce masa wance ce Rauda? ai sai dai ya gaya maka wace ita da sauransu

yana kallon ya ya ce"







😍😍😍😍😍😍😍
yana kallon Hajia ya ce" Ita dai jikar taki ce ta zane dayar"

Hajia ya yi shiru tana nazari, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ya juya ta je bakin falon inda Jakadiya ke tsugune tana jiran abinda za'a fadawa dogari da kuma wani sakon idan akoy

A nutse hajia ya ce" Ki ce a basu damar su shigo, sannan ki isar da sakon ina son gimbiya Amnah da gimbiya RAUDA su halarci falona"

Kai a kasa ta amsa da" An gama kakar saraki" Sannan ta mike ta wuce

Jiki sanyi Kalau Hajia ta koma ta zauna tana kallonsa irin yadda ya gyara zamansa yana cin tufa hankali kwonce, ta zatama zai yi tafiyarsa ne, sai ta ga ya zauna,, ba zata so a ringa irin shirmen nan a gabansa ba, dan kuwa ba zata so ya yanke wani hukuncin abinda ya shafi iyalinsa cikin fushi ba

Shi kuwa zaunen da ya yi, ba komai yake son ganni ba sai wayewar gari da idon da zata kalli mutane ita wancen da ake kira marainiyar Allah, yakan yi murmushi ya girgiza kai, duk irin ayyukan dake gabansa baya jin zai iya zuwa ya yi idan bai ga abinda yake son gani ba, bashi da niyar furta masu A a zaman nan, ama kuma ba za'a hannawa ido kalaci ba

Su suka fara shigowa bayan an bada damar su shigo baban falon Hajia

Abin mamaki yau dinma shi da abokinsa din nan da kuma matarsa, wato mahaifiyar Amnah

Tunda suka shigo Dogari ya nuna masu wajen zama saman baban cafet din dake tsakanin cafet din da ƙafafuwan YUSUF ke sama da kuma kujerar da Hajia ke sam,, suka zauna idannuwansu suka sauka a kan YUSUF kusan kowane ya karra kama kansa harma suka so manta abinda ya kawo su

Daga kofar shigowa dogari ya koma ya tsaya bayan sun gaishe da Yusuf da Hajia Dogari ya yi aikinsa ya nuna sun amsa, Bama kamar Yusuf da ya saka Tissu ya goge bakinsa sannan ya dan zuba masu ido kadan kafin ya dauke kansa yana murmushi, gasu dai cikin shiga mai kyau, sai dai a cikinsu kowane da abinda.ke.tafe da rayuwarsa mai hatsarin gaske wanda idan bawa ya ji sai ya firgita

Hajia kam abokin nan na Mahaifin Amnah ta zubawa ido, da wani kallon da ya saka shi sada kansa yana jin kirjinsa na sake dokawa, domin dama tunda suka shigo ya ga YUSUF ya ji hankalinsa na neman tashi

Kai Hajia ta dauke a zuciyarta tana cikin mamaki mai tsananin gaske na kamanin da wannan bawan Allah yake yi da Amnah, kamanin har sun bace sosai, sai ta sakawa ranta ta yiwu da akace abokinsa ne ko d'an uwansa ne na jinni kuma abota take da karfi a tsakaninsu?........., ita dai ta ture tana duban su da kula ta ce" Shin me yake faruwa haka ne? ance jiya wajen karfe biyu kun zo, gashi yau tun dazu kuke kofa, Allah ya sa lafiya?"

Kan mahaifin Amnah a kasa, yana jin abinda Hajiar ke fada ama tamkar wanda ya afka wata duniyar tunani daban, har sai da abokin ya sake tabo shi ya ce" ana magana baka ce komai ba Elhaji?"

Da wata irin murya, wace kana ji sai ka kalli mai ita duba da Muryar sama sama ce kamar baya cikin hayacinsa ya yi maganar , irin sama sama din nan ya ce" Eh, haka ne, dole zan zo da duk wani wanda ya isa da yata, dan ba zai yiwu a kashe min ita ba kamar yadda Hajia tace ko ba haka ba hajia?" Ya karashe yana kallon mahaifiyar Amnah da hannayensa bibiyu a hade kamar wanda ke rokonta wani abin, ita kuwa ta sake sada kanta yadda ka san irin manyan salihan matan nan da ko surutu da karfi basu iya ba bale ace zasu aikata mugun abu

Shigowar dogari da sauri yana fadin" Kai, ka sasauta muryarka a nan wajen ko ka fito mu iya da kai talaka!" Ya sa YUSUF dago dubansa ya masa alamun ya fita da hannayensa, da sauri ya juya ya fita din yana jin tamkar ya warto mahaifin Amnah ya koyo masa hankali, dan ba'a yi wanda zai yiwa MALEEK magana haka a gabansu ba tare da sun datse harshensa ba walahi! ya godewa Allah ba Taj bane a wajen dan kuwa shi bashi yake bi kuma sai an biya shi!


Sake gyara zamansa ya yi a lokacin da Mah ta shigo tana kallon iyayen Amnah da mamaki ta karasa ta duka ta gaisar da Hajia, sai dai Hajia bata samu damar amsa gaisuwar ba saboda ranta ya kai kololuwar ɓaci ta budi baki da fada ta fara fadin" Ohk, shine kuka kwaso jiki kai da d'an uwanka da matarka kuka zo ku shiga fadan tsakanin abokan zaman da fadan bai yi tsauri ba , dan ita Amnah itace mai gata ita kuwa RAUDA bata da kowa ko? To ai RAUDA ita keda gata, wanda bana tunanin Y'ARKU tana da shi, domin ga Mamanta nan, Ni kuwa nice kakarta, !"

Gira ya dan dage yana kallon Hajia kasa kasa ya furta" Ko?, to wa yace maki d'an uwansa ne? ba hadinsu fa"
kallonsa Hajia ta yi, domin idan ba ita dake daf da shi ba babu wanda zai iya jiyo abinda YUSUF yake fadi, da sauri ta kalli bakon , ta sake kallon YUSUF daidai lokacin da AMNAH ta fara shigowa da abaya a jikinta fara, tana gannin iyayenta ta je da gudu ta fada jikin mamanta tana fashewa da kuka, ita kuwa Hajia abinda ya fito daga bakinta tana kallon abokin mahaifin Amnah ta ce" A'a fa, d'an uwansa ne mana, bawan Allah kai ba d'an uwan mahaifin Amnah bane? haba wannan kama ai sai jinni, sai kace a tatsuniya ai ba za'a ce tsabar abotaka bace ta sa y'ar nan ke kama da kai ko?"

Da karfi mahaifiyar Amnah dake sune sune tana ba Amnah hakuri kasa kasa ta dago ta dubi Hajia, kuma wani ikon Allah a tare suka dubi Hajiar sannan suka kalli junna, da sauri ta budi baki tana fadin" Ke Amnah yi shiru mana, ya isa haka, ke ashe fada be kawai kuka yi ke da abokiyar zamanki, wannan ai ba wayo bane, ina mijinki yake da zaki wani kiraye mu? haba dan Allah Ni bana son ka zama mutun marar sirri, duba ki ga mahaifinki ko ido bai rintsa ba tunda kika kiraye shi kina kuka, na yi na yi ya yi hakuri ko menene ke da kike gaban magabata an yiwa abin tsawa kika kiya, haba Ni na ji kunya walahi kin sa mun zo gaban iyayenki da wannan maganar, Hajia

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login