Showing 24001 words to 27000 words out of 188741 words

Chapter 9 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9863

da kaffafuwanta ta yi manicure da pedicure, kalli fuskarta tamkar santsin kwai, lebenta ga alamun taushi ne da su, idanun........................."

Kallon da YUSUF ke masa ya dan bashi mamaki har ya saka shi dan takaita maganarsa, dama ba wai wani zuuuuuuuuu bane yake yin maganar ba tsari, no a hankali ne yake yi sai dai duk abinda yake magana kansa ya kura masa ido ne kuma a hankali yake fadan cike da mamakin yannayin RAUDA da kuma yarda eh ashe da gaske ne a nanma Akoy yan mata masu classs haka

Shiru ya yi a zuciyarsa yana tunanin ko dai budurwar YUSUF ce?, wannan duban ba dan kawai ya yi magana a kanta bane, ama da mamaki yaushe ya fara yin budurwa daya kwal? Ko a Chaina ai YUSUF mai yanmata ne bale a nan kasarsa

Wani irin takaici ya rike mata zuciya a lokacin da aka bata dan litafin restaurant din dan ta zabi abinda zata ci, ba komai yasa ba sai gannin eh fa da gaske yau babu Sa'a a fitowar domin Wadinnan ukun ne kawai zasu zauna a nan din su isasu, sai kawai ta ba matar litafinta tana mata alamun ba zata ci komai ba ta maida dubanta kan ISHAK dake magana a hankali maimakun da dan karfi karfin da ya fara maganar dazu, yanzun kamar wanda baya so ta ji abinda ke bakinsa ya ce" Sir, na fitar da ita ne?"

Bai san dalili ba, tambaya aka masa da Yaren da ya ji bayan Yaren mahaifiyarsa Larabci, ama sai amsar ta so gagararsa har ya dan zuba masa ido na yan SAKWANI ya ki ce masa eh ko aa, ya dai dauke dubansa ya maido duban nasa kan bakonsa ya ce" Wannan motar da ka gani ita nake so a kawo ama kwaya biyu, daya Moma zata hau, dayar kuwa Baban YUSUF"

Yar dariya mutumen ya yi ya ce" Man kana ririta iyayenka fa, to ba za'a zuba su a park bane?"

Kai ya dan girgiza kasa kasa sosai yana sake dago kaifafun idannuwansa ya ɗora saman hannunta a lokacin da ta amsa waya tana sauke kafarta da ta dora kafa daya kan daya ya ce" Sai sun hau kafin wani ya hau a nan"

Kasa kasa RAUDA da zaman ya gundureta da tarin haushin mutanen wajen kansu take amsa wayar wani tsohon saurayinta wanda ta masa lakabi da 'ANDADI' , ba yaro bane, mutun ne mai shekaru sai dai kuma ba tsoho bane, a yadda ya fada mata shi Maraya ne gaba da baya, kuma wai bashi da Kani ko kanwa, mutumen maroko ne yanzu haka lambar ta kasar marokin ce ya yi kiranta da ita, ya yi ya yi ta gwada masa gidansu ta kiya har ya yi tafiyar nan a yadda ya fada mata zai je ne ya gama dukiyar iyayensa kaf ya siyar na SIYARWA na bayar da na bayarwa ya tattara ya dawo Nijar da zama ɗan yanzu maroko bata masa dadi tunda bashi da shakiki ko daya, ya jima a kasar Nijar yana dan jin Hausa da French sosai da larabci, ya nunawa RAUDA da gaske ya zo wajenta hakan ya sa ta sulube, dan ita kam bata ganta a duniyar aure ba , kuma fa zai kai uncle dinta a shekaru fa, ba zata so ta ja shi a kasa kamar yadda take jan kannanun samarinta, ama shi baya ji , ga kyauta irin mai gigitatan nan

A Nutse ta mike tana jan dan mayafinta da ya sauka daga kanta ta mayar ta dauki jakarta ko ci kanku bata ce da su ba, hasalima ko sake kallonsu bata yi ba ta yi gaba cikin tafiyarta mai tsarin gaske tana amsa wayar a tausashe sunna magana da Yaren freinch dan da shi tana gane komai shima haka

Dubansa ya dauke yana jin zufa na tarun masa a tafin hannuwansa, sai kuma ya bi bayan Ishak da kallo wanda ya mike har yana hade tafiyarsa ya bi bayanta

"Man, rigima kuka yi da madame ne? Na ga ta zauna bata ce komai ba kuma ta tashi ta tafi?" Abokinsa ke tambayarsa bayan ya dan tabo shi dan gannin ya kurawa hanyar da suka bi ido

Idannuwansa ya maido kansa, sai ya rasa gane yarensa, kwata kwata ya kasa gane abinda ya fada sai kawai ya budi bakinsa a Nutse ya ce" Ko a yi mana take away? I'm tired Man"

Cike da gamsuwa cewar ya gajin ne dan gannin ya fara lulumshe ido ya nuna masa ai normal ne a hada masu abincin su tafi da shi

Mikewa ya yi ya masa nunin yana zuwa ya nufi hanyar da Ishak ya bi haka kawai ba tare da ya san abinda zai tsinta a wajen ba da hannunsa ya yiwa masu dafa abincin magana ta biyo shi da sauri a hade ya furta" Ku yi emballer "
Daga haka ya yi shiru ya ci gaba da tafiyarsa har kunnayensa suka ringa jiyo masa magangannun mace kamar wace ke kuka kamar wace ke cikin yannayin tashin hankali

A hankali ya ja ya tsaya yana soke hannayensa cikin wandon dake jikinsa ya zuba masu ido su uku, ISHAK a tsakiyarsu, Nafisa na magana tana fadin" Walahi sai na kai kararki, me na maki? Me na yi maki? Ishak itace fa ta ji min ciwon nan shekaran jiya da ka kaini asibiti, dan kawai muna maganarta a mota ranar da muka kai maku abinci ta shakeni ta ja dan kunnena, kuma yanzu ta mareni? Ta fada na ciri tikiten fada da ita tunda na zagi iyayenta , hakan na nufin tana iya halakani walahi sai na kai kararta a mini tsakani da ita sannan na kaita fadar mai Damagaran ko ta sarki SANDA a mana tsakani da ita idan ita mahaukaciya ce Ni ba zan yarda ta kuma dukana ba, kema ki zagi iyayena mana dan kawai na zagi iyayenki?"
Da karfi Nafisa ke maganar, hawaye na shatata a fuskarta dan a wajen da RAUDA ta dauketa da mari YANZUN a gefen wajen da ta ja mata shatine ne, har ga Allah ita bata ganta ba da bata bari ta cin mata ba, sai jin saukar mari ta yi a lokacin da suke rigima ita da mai tsaron kofar nan yace ba zata shiga ba wace ake jira ta jima da shiga, bata san mahaukaciya bace RAUDA da bata shiga harkarta ba, ama walahi sai ta kai kararta dan ba zata ci bulus ba, yaushe rabon duniya da fadan duka in ba wulakanci ba?

A hankali Ishak ke fadin" Nafisa yi magana a hankali na fada maki bos na ciki fa , kin ga mu je waje na masu masalaha, ina amfanin fada yan mata da ku? Mu je waje na shirya ku na tabbata an samu rashin fahimtar junna ne......"
Yana fada yana damko hannun Nafisa ne, haka kuma ya miko hannunsa da nufin riko na RAUDA, a hankali ta ja baya tana sakin lebenta na kasa da ta dantse tana dubansa ta ki yarda ya kamatan ta kuma ki yarda ta bi su

Dakatawa ya yi yana kallonta, tsakani da Allah da farko niyarsa sai ya wulakanta yarinyar nan tunda ta ja masa tsaki a mota, ama a yau gaba daya tunaninsa ya sauya a kanta har ya zamto yana jin koda wani yace zai wulakanta ta ba zai barshi ba

Da kula ya ce" RAUDA ko?"

RAUDA ta sake kicin kicin da fuska ta ki bashi amsa

A tausashe ya ce" Ki yi hakuri an bata maki, ki yi hakuri ta zage ki, mu je waje na sasanta ku, a nan bana so oga ya fito ya same mu cikin wannan halin ransa na iya bacewa, ki yi hakuri mu je waje ku sasanta kin ji?"

Rauda ta dan tabe baki ta ki kama hannun da yake miko mata kasa kasa sosai ta bude bakinta cike da yannayin yangar da take ainahin asalin halitarta ta ce"


🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*


*PAID BOOK*


_Bismillahir rahamanir-rahim._


*10*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳



Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*




A Nutse ta ce" Ni babu inda zan bi ku, masalaha kuwa Ni da ita sai a gaban sarki wanda zai ja min kashedin kar na kuma in ba haka ba na rantse maki yanzu na fara tsaga fuskarki dan mai zagin iyayena ya zauna lafiya Dube shi duba, shima zan yi shiru ne ba zan amsa shi ba ama ba zan taba gannin girmansa ba...!"

Da sauri ya sake zubawa fuskarta ido da yannayin furucinta ya saka shi kafe lebenta da ido har ta dasa Aya ta juya ta fice ta babar kofar hankali kwonce

A hankali ya samu kansa da lumshe idannuwansa dan ya daidaita bugawar da zuciyarsa ke yi, yana bude idon ya ga Ishak ya rungume Nafisa a jikinsa yana bata hakuri da alkawarin tunda ta san gidan su RAUDA zasu je a sasanta su, ama ta kiyayi zagin iyayen mutun wasu fa a kan iyayensu mahaukata ne

Kansa ya dauke sanadiyar wayarsa karafa fara da ta fara vibration
Wayar mutun biyu kawai ke kiransa da ita, k
Layinma su kadai suke da shi, mahaifiyarsa da mahaifinsa dan haka tana fara vibration ya zuba idannuwansa yana karanta sunna kamar haka *MAI MARTABA*

Idannuwansa da suka dan cenza kala ya juyar a hankali ya daga kiran cen ciki ya yi Salama sannan ya saurara

Salamarsa ya amsa da sauri ba tare da ya tsaya ja masa aji ba kamar yadda ya saba, hakan ya sa ya sake gyara tsayuwarsa yana sauraro

"Uminka ce, tun jiya da dadare muka dan samu matsala ta shiga ta rufe, na zata zata bude min da safe , ta ki budewa na kasa hakura na sa aka kirawo mai gyara ya Bala min kofar shine na sameta ciwonta ya tashi, yanzu haka muna Clinik Nandu ta ki min magana shine nace bari in kireka na ga baka kirayeta ba yau"

Tunda ya fara magana kirjinsa ke dokawa, zuciyarsa na neman balowa daga bakinsa ta fito waje

Jin karshen furucin mahaifinsa bai iya ce masa komai ba sai katse kiran da ya yi har baya gani da kyau ya karaso inda su Ishak ke tsaye ya ce" Zan je Nandu Anmy bata da lafiya, ka kula da shi kawai, kuma kar ka zo ka san aba yana nan"

Daga nan ya yi gaba da sauri bai ko tsaya ya kula motar da suka zo da ita ba dan ba zai iya tsayawa har su fitar da motar Ba su tsayar da shi, a inda yake ji yake yi inama yanada wata baiwa ta bacewa a bayana a inda ake so, da ya bace ya bayyana a jikin mahaifiyarsa

Yana fitowa da sauri ya sha gaban wata adaidaita, bai tsaya jira ba ya zagayo ya shiga yana fadin" Clinik Nandu zaka kai Ni"

Mai adaidaitar ya kasa motsawa saboda budurwar dake cikin adaidaitar zaune tana amsa waya
Sannin kowa ne a garin Damagaran idan har mace na cikin adaidaita namiji ya tsayar da ita ba za'a dauke shi ba ko nawa zai ba mai adaidaitar sai in ita MACEN ce ta bada lamunin a dauke shi, dan haka cikin tausasawa mai adaidaitar ya ce" Ka yi hakuri malam ka tsayar da wata na dauko mace ce a ciki"

A irin wannan lokacin gani yake yi yaushe zai fita ya tsayar da wata? Ta yayane? Gaba dayama ji yake yi tamkar bashi da jinni a jikinsa, dukkan wata gaba ta jikinsa ta daina aiki sai dokawar da zuciyarsa ke yi wace ta wuce misali wanda ya tabbata in har yanada hawan jinni to ya hau a yau

Da sauri ya kalli macen da aka ce an dauko yana karkatawa dan lalubar kudin dake aljihunsa gaba daya ya ciro yan jaka goma goma sababi kal kal lokaci daya yana shaƙar kanshin dake jikin mayafinta haka kuma yana dubanta ya samu kansa da jin zai iya fada mata inda zai je ya san zata aminta su yi tafiya tare ko dan furucin da ya ji ta yi a kan *IYAYE*

A tausashensa yana kallonta, sai ya ji nauyin niyar da ya yi na bata kudaden nan duka, bai san dalili ba, a hankali ya ce" Mahaifiyata ce ba lafiya, idan ba takura ki bari a ajiyeni"

Bata taba jin damuwar wani bawan da bata sani ba na neman zama damuwarta sai yau
Bata taba dagawa wani gardi kafa ba komai laushinsa da tsarin halitarsa ba sai yau, bata taɓa ragawa wani dan uzurinsa ta bar nata ba sai yau

A hankali ta dauke dubanta daga saman fuskarsa ta ce" Mu je ka kai shi Aminu" RAUDA ta fada a hankali tana dauke dubanta a kansa

Tuki Aminu yake yi a Nutse ba da garaje ba,
A daidai wajen da zasu yi kwanar Nandu din kwanar da Nandun ke jikinta wani mai mota ya daki gaban adaidaitar ta su adaidaitar ta daku da jikin garu ama bata fadi ba, gabanta dai ya yi ratsa ratsa

Mai motar so ya yi ya gudu, dan a lokacin da ya ga adaidaitar bata fadi ba da sauri ya so juyar da motarsa ya yi tafiyarsa dan wajen yana kusa da police station ne, baya son bata lokaci , yanzu za'a zo a shiga surutun sai an yi aune aune an ga waye marar gaskiya a yi ta BATAWA mutun lokaci

Da karfi ya fito daga adaidaitar ya daga murya yana fadin " SANI ZAKWALAM!?"

Wanda aka kiraya da Sannin sai da ya zarro ido jin Muryar da ta kirayeshi

A rikice ya taka birki ya juyo da dubansa da kyau dan gaskatawa
Ai kam tsaf ya hango biya muradi na masa alamun ya gansa sannan ya juya ya koma wajen adaidaitar Aminu dake kiran SUNNAN RAUDA, dan kusan su mazan direwa suka yi ama ita bata iya dira daga adaidaitar ba, ga dukkan alamu ta bugu dan gefen hannunta jinni yake yi sosai

Da kyar ta ciro kafarta daya, tana shirin ciro dayar gaba daya jikinta ya kwashi rawa idannuwanta suka tafi luuuuuu suka rufe ta nemi dikuwa da kas

Kusan a tare suka tare ta, mayafinta ya fado saman hannunsa hannayensa kuwa suka talabeta dan Aminu sakar masa ya yi domin kamar ya shi kusa da ita sosai

Zuwa lokacin Duda dare ne wajen ya fara cika da mutane ana ta salalami, nan da nan aka fito da abin daukan marar lafiya dan a jikin garun asibitin ne aka maka su

Karbarta suka yi suka yi gagawar dorata lokaci daya sunna danne wajen dake jinnin suka shiga turata cikin clinik din, shi kuwa ya daga kafa a hankali yana rike mayafinta a hannunsa idannuwansa suka sauka cikin na mahaifinsa da ya'yan mahaifinsa wato sarki da kanwarsa HAJIA A'isha, sai kuma Sani ZAKWALAM wanda ya kade sun shima ya fito daga motar yana faman fadin " oga walahi ban san kunne a adaidaitar ba, innalilahi Oga mu je ciki a duba ka dan Allah"

A hankali ya so dauke dubansa daga kansu saboda a cikinsu babu mai binsa da tausashen kallo, sai dai ba dama a tsayen nan da suke idan har bai zo inda suke ba kamar ya wulakantasu ne baki dayansu

Kallo daya ya yiwa Sani kasa kasa ya ce" Ka bari mana baka gannin Ubana ne?, ka je kawai ku karata da police"
Daga haka ya karasa wajensu a Nutse ya furta" Barka da dare, yaya mai jikin?"

Mai martaba ne kaɗai ya iya amsa shi, mahaifinsa gefen hannunsa dake dauke da jinni yake kallo a zuciyarsa yana tunanin ko shima ya ji ciwo ne?, HAJIA A'isha kuwa takaici tamkar zai kasheta, ba wata damuwa ko Dar, ba wani jin nauyi ko gudun a jita ta ce" Asibitinma da mace zaka zo YUSUF?, mahaifiyar taka a kwoncenma sai ka zo da mace dan ka nunawa duniya waye kai?"

A hankali mahaifinsa ya kalleta yana jin kamar bai dace ba daga zuwansa ta hau shi da wannan balakin bayan ta ji ana fadin hatsari suka yi, shi wasu lokutan sai ya ga kamar tana nunawa son kai a lamarin BIYA MURADI, ta cika zakalkalewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login