Showing 96001 words to 99000 words out of 188741 words

Chapter 33 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9856

da tarar duk wani wanda zai shigo ko zai fita

Bai san adadin lokacin da ya dauka ba, sai da Mah ta fito tana fada masa babansa na kiransa, ita ta tsaya a waje shi kuwa ya shiga ne ya ga ashe sun jima sunna shan firar su yan soyaya

yana shiga Bah ya zuba masa ido yana fadin" zo nan"

YUSUF ya kalli inda ya nuna masa sannan ya karasa ya zauna yana hade hannayensa yana kallon BAH

Bah ya ce" Me yake damunka?"

YUSUF ya sake zuba masa ido ya ce" Ni?"

Bah ya dafe haba yana kallonsa ya ce" Honorable Ni, nace Ni, ka ga ka rufa min asiri kar na daki sarki fa?"

murmushi ya subucewa YUSUF, shi kuwa BAH ya yi yar dariya yana kallonsa a tausashe ya ce" Ka ci gaba da hakuri , in sha Allah na kusa dawowa kusanka, zan tayaka kokawar nan, bi izinillah zaka kai ga cin nasarar rikon kasarka, ok?"

YUSUF ya lumshe idannuwansa sannan ya sakarwa mahaifinsa murmushi yana kallonsa ya ce" Allah ya aminta"

Bah ya amsa da amen sannan suka yi salama suka nufi gida

sunna karasawa gidan shi dakinsa ya wuce, Mah kuwa har zata kwonta itama hayaniya ta shiga shiga cikin kunnayenta, kuma hayaniyar da bata saba ji ba a sanyin safiya irin haka, domin yawancin lokuta sukan fice ciki koda fira zasu yi su Dukansu yan matan

dan saurarawa ta yi, sai ta ji ai kamar kuka, hakan ya sa ta mike da sauri tana daukan hijabinta ta saka ta fito da dan sauri ta nufi ciki dan sarai ta ji mamakin gannin ba a falo suke ba ashe sunna cen dakin SALIMA

da sauri ya tura kofar ta shiga da salama tana sauke idannuwanta kansu, lokaci daya ta shiga tafa hannu a tausashe ta furta" Subahanallah, menene wannan din, ke Musulima rikewar me ake yi maki? kin ga Salima saketa , kai saketa ku saurara min, meye haka, menene wannan kuke yi kamar wasu mararsa ilimi?"

sakin nata Salima ta yi tana haki dan walahi sun jijigata, RAUDA kuwa tunda ta ji ba'asin rikicin nasu ta ja tana kallonsu shi yasa rabiyar fadan ya dawo kan Salima ita kadai

Rai bace Mah ta ce" ku zauna min, a'a, me ya haɗa ku da junna kunna yan uwan junna fada harda dukan junna? ashe baku da tunani? yaushe rabon duniya da fada bale wai har a daki junna? meye ya haɗa ku da zafi haka wanda ba zaku iya tattaunawa ku ba junna hakuri Ni Ameera jikar Ameerah sai dambe?"

Akilah ta sake sada kanta zuciyarta na tafarfasa

Hindatu da suka sakata a cikin rigimar dan kawai tace masu meye na fada in dai a kan wannan ne kowa ya iya allonsa ya wanke ce ta ce" Mah, ki' ga wai dan Akilah ta yi create compte a Tiktok ta saka matar Malik shine Musulima ta gani tsakiyar dare, shine yau tunda muka tashi take masifa har sai da ta kula ta suka fara fada, Ni daga raba su ta zage Ni "

Mah ta dubeta tana fadin" ku ji 'in wani shirme, waye Malik kuma har da zai hada ku fada da junnanku? yau ko miji daya kuke aure ai inaga kun fi karfin wannan shirmen bale a sanina babu mai aure cikinku?

shiru ne wajen ya dauka, kowace ta kasa ba Mah amsar waye MALIK har sai da ta daina jiran jin waye Malik din ta aniya fada tana fadin" Yaushema da darajarku da komai, kunna cikakkun yan mata zaku tsaya kan saurayi kunna fada? waye shi Malik din? to ko waye ba ku ba shi tunda ya iya rashin mutuncin yin soyaya da yan uwan junna a tare "

Salima ta dago tana kallon Mah ta ce" Mah, yayanmu ne fa, a kansa ne suke fadan, su Dukansu ukun ne suke yin fadan a kansa ne kuma!"

gaban Mah sai da ya fadi, wajen kuwa ya yi tsitttttt dan kuwa Mah dake hakilon fadan nan sai bakinta ya yi tsittt lokaci daya tana kallon su

ta jima a haka ta kasa furta ko a, ta kalli wannan ta kalli wancen ciki harda Salimar da RAUDAR

kasa kasa tamkar mai rada ta ce" Soyaya kuke yi da shi ne dama ban sani ba?"
ta yi tambayar nan ne gabanta na faduwa, dan abinda take iya yin gudun ji daga bakin daya daga cikin Yaren nan shine amsar EH, dan bata tunanin zata iya yarda YUSUF ya auri daya daga cikin ya'yan yan uwanta da ranta da lafiyarta, sai dai idan kadara ta gama zuwa a haka, wace zata zo da rabo........na wai dan bata yafe ba, ta yafe fa, sosai da sosai, kawai dai ba zata bari ta cuce su bane su auri ɗan Yar iska da dan iska!

wannan karon ma ba amsa, har ranta ya fara suya ta dubi Salima da mugun hararan da ya saka Salimar bude baki a sanyaye ta ce" Mah, inaga shi fa baima sani ba fa"

har ga Allah sai da ajiyar zuciya ta kwace mata, tana kallonsu ta ce" Abinda Salima ke fada gaskiya ne? a kan YUSUF Ne ? Kuma bai sani Bama?"

wannan karon Musulima ce ta gyada kanta , kan nata a kasss

Mah ta girgiza kanta tana kallon su gaba dayansu ta ce" Yaushe kuka zama haka? ko dama haka kuke ban sani ba su aunty na kallon ku basu tsawatar ba?, ikon Allah da dukan junna zaku yi ta yi a kan abinda ba zai wani yiwu ba? yaya za'a yi mu yarda mu maku auren hadi auren da ba soyaya? ai ba zai taba yiwuwa ba , kai ko da soyaya mu Bama auren dangi dan gudun matsala salon ku zo nan ku yi rikici ku lalata mana zumunnci, Ni koda soyaya kuke yi ba zan bashi ba bale bakwa soyaya, ke maza ki je ki goge abinda kika dora, ke kuwa ku yafi junna ku zubar da shirme, ba soyaya tsakaninku da YUSUF kowace ta samo mijinta na wanketa ba kaita dakinta lami lafiya yadda koda gobe ya yi mata ba daidai ba na daure kugu na zabga masa mari kuma na mari banza ko baby?"

RAUDA ta yi murmushin yake ya sake dauke kanta, Mah kuwa ta mike tana sake toshe kwakwaluwarsu ta ce" Kar fa na kuma jin wannan maganar, maza a yafi junna, shima ai da matarsa kowa ya fitar da nasa maza a wanke ku a kai ku dakunan ku!"
tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, sosai Mah ta daga hankalin ƴaƴanta domin kuwa bata sani bane zaman nan na yakin duniyar YUSUF ne sai gashi tana fadin basa auren zumunci basa son maganar? kowace wayarta ya dauka dan isar da sakon inda ya dace

a lokacin kuwa Mah ta nufi dakinta, zuciyarta cike da mamakin abokanan zamanta, anya kuwa mutanen nan ko wuta dakinta ke ci sa fada mata? ya Salam, ace sunna gidan sunna jin wannan katsamniyar ba zasu fito su tsawatar ba?, ikon Allah

tana zama bakin gadon ta kuwa sai ta lumshe idannuwanta tana jin barcinma du ya watse a idannuwanta

uhum, rayuwa kennan
me yan uwanta suke nufi ne?
Allah ne masani
ama har sun manta a lokacin da ciki ya bilo jikinta, mahaifiyarta ke fadin a zo a hadu a rufawa junna asiri a fitar da ita nesa idan ta haihu ta gyaru sai ta dawo a aura mata cousin dinta, wanda ke sonta kamar me, suka dira suka nuna ina, su fa bama za'a kawo masu auren dangi ba, dan basa son fitina, kowa ya samo mijinsa a waje a aura masa, koda ace bata dauke da wani abin kunya ai ba zasu yi auren zumunci ba bale ita da ta watsa kanta salon Abu ya bude ta yaba masu abin kunyarta, a'a ba zai yiwu ba kawai ta nemo uban cikinta cen su karata.......
Kai ta girgiza tana kore tunanin dan kar ya cenza mata mood, abu daya ta sani shine YUSUF itace mahaifiyarsa, ta yanke wannan hukuncin babu mai dawo lata da shi sai idan Allah ne ya hukunta haka babu yadda ta iya!

a dakinsu kuwa, a ranar Rauda kadai ta dirki aikace aikacen gidan, domin tunda abin ya faru da ta fito ta shiga aiki bata kuma bi ta kan kowa ba, babu wanda ya san me yake damunta, aiki dai take yi ba sakin fuska, domin Salima ta dan dauke kafa dan sau biyu mahaifiyarta na fitowa dan ta ga in ta shiga aikin gidan ko a'a, shi yasa Rauda tace ta zauna inama aikin yake abinda sharar iya ta nan din ce, da guga sai girki, yan matan kuwa kusan kowace a bangarenta daban ta zauna, bisa kalar hudubar da mahaifiyarta ta yi mata, sunna nan daram a gidan, dan iyayensu sun nuna zasu zo ne da kansu wajen mai sunnan Hajiar, kula kowace ta kalubalanci yar uwarta da jin haushin junna, ita dai wace ake yi dan itan bata sani ba tana shan tana nata shagalin abinda zai fidata!

.......................................................

a cikin satin da ya gabata aka sako Bah daga asibiti, ama kuma likitansa bai tafi ba sai da ya rufa kwana na goma a garin sannan ya juya tasa kasar da farin cikin gannin an samu nasara patient dinsa ya warke

tunda suka dawo gidan baya rabo da baki, ta ko'ina, ga bangaren guda kuma ana tafka aikin ginnin nan abin har abin tsoro domin aikin an fara shi nan da nan har yana neman shan duka, dan kuwa sosai an cimma aikin , dama yanzu ginni in dai da kudi shikenan kafin kace meye wannan an gama, danma akoy hawa da hawa wa'inda ba'a masu garajen, dole ana bin ka'idarsu dan kar su tafka tsiya ai da tuni an gama aikin, dan masu ginnin nan yan Chaina ne aka dauko ginni ya gama kankama

a cikin yan zuwa gaisar da Bah, harda ABDALLAH,
wanda ya samu kyakkyawan tarba daga sirikinsa, har Bah ya sanar masa cewa an bashi ama ya yi hakuri a satin gaba za'a salami marikinta, shine mai tabatarwa, su sun nuna masa kauna ne, ama mai bashi babanta ne tunda da ransa
da wannan ya sake tafiya da farin cikinsa, dan kuwa har wajen da yake Bah ya sanar masa ya kuma bashi damar ziyartarsa idan yana da ra'ayi

a cikin wannan dan tsakin, zukata biyu na tare da gagarumin kadarar da ta rigayi fata wace kowane ya murje ya kane ya watsar dan nasa dalili mai karfin da yake gannin ko waye ya ji zai jinjinawa namijin kokarinsa harma ya bashi kyauta ta jinjinawa da girmamawa

tunda suka yi magana a kicin wata bata kuma hada su ba, domin karfi da yaji sun gane zagayewar nan itace alkhairi a gare su ba tare da daya ya gane manufar daya ba, sai baban haushin junna da ya darsu a zukatan na gannin wane bai kyauta min ba ko kuma wane ya yi min ganganci , kowa ya kama kowa da laifin da bai aikata ba wanda ya gama kashe zuciyar bege ta koma ta jin haushi da jiran laifin wani


a cikin satin da aka salamo uncle Umar direct fada aka nufa da shi, domin an sallame shi daga jinyar jiki ne, a yanzu ta magance shaye shayensa za'a ci gaba da yi , wace YUSUF ya gama sakawa an nema masa wajen da ake wannan, kwanakin nan da zai yi biyu dan ya san huta ne hankalinsa ya dawo jikinsa sannan ya daga zuwa neman lafiyarsa

a wannan rana RAUDA ta yi kukan farin ciki, hakama Baba Umar da ya ga yar amanarsa da kuma d'ansa cikin koshin lafiya, babu abinda ya karra bashi mamaki irin yadda Abdul du wasu alamu na hauka dake nuni a da a tatare da shi sun rage, wa'inda ya gama ganewa eh lalle yaron yana da yar matsala ama bata kai wajen da ta nuna a da ba, tsabar tsoro da firgici ya sa yake tafe a mahaukaci ziryan, a yanzu da yake cikin nutsuwar zuciya, ba zaka ce Abdul bane, harta kalar fatarsa ta haskaka sai hamdallah

kasancewar da rana suka tarda shi bai samu zama da RAUDA ba sai da dare bayan sun ci abinci ta sake komawa wajensa, a lokacin ne ya dubeta cike da rauni ya ce"
cike da rauni uncle Umar ya ce" RAUDANA, my daughter, dan Allah ki yafe min, ki yafewa babanki, na dauko ki daga hannun wace ta yiwu da a wajenta kike da yanzun wata maganar ake yi ba irin tawa ba, har Allah ya amshi ranta ban bata dama ta baki tarbiyya da ilimi ba, ban san makarantar ki ta islamiyya ba ban san ta boko ba, sama sama idan na dan auna ne nakan kwatanta wasu kulawar da basu taka kara suka karya ba, maimakun na rike ki sai na karra maki rikon wani a kanki bayan ke dinma riko ce, sannan na hadaki zama da macen da sam bata da tausayi bale jin tsoron Allah a lamuranta, dan Allah ki yafe m..,....."


"Aba....." RAUDA ta fada a sanyaye, ba dan ta katse shi ba, kuma ba dan maganar da yake yi bata da mahinmanci ba, sai dan ba zata iya jin muryarsa a matsayinsa na uba a wajenta yana bata hakuri a kan yannayin zubin rayuwar da shi dinma ya yita ne yadda ta jirga shi, kwarai tana cikin yannayi, sai dai a yanzu kuma me ya rage mata na fitina? Allah ya gama wanke mutanen kirki daga cikin mutanensa na kirki ya hadata da su, sunna zaune tamkar y'ar da suka haifa da cikinsu, me kuma ya yi saura?

a sanyaye sosai ta ce" Dan Allah Aba ka daina bani hakuri, baka taba yi min laifi ba, koda ka min wanda ban sani ba na yafe maka duniya da kiyama ama ka daina bani hakuri, ni yanzun hankalina ya kwonta da Allah ya sa kana raye, ina fatan Allah ya karra tsare min kai a duk inda zaka shiga Aba"

hawayen da yake ta tarewa dole sai da suka zubar masa, ama kuma har cikin ransa sai ya ji sanyi sanyi na hakurin nan da ya bata, dan kuwa ko da ana azabtar da shi a hannun samarin nan da bashin giya ya haɗa su, adu'arsa daya ce a kulun, Allah ya sa ya samu ya ba marainiyar Allah hakuri kafin ya mutu, yana ta adu'ar Allah ya datar da shi da bata hakuri kafin ya koma ga mahaliccin sa, sai gashi Allah ya nuna masa , shi kam ba zai gaji da godewa wannan baiwan Allahn da ahalinsa ba, dama ya san shi farin sani, domin ya sha hanawa a dake shi idan wani abu ya hada shi rigima da wani a gidan giya, kun san gidan giya karamin yaro sai ya mare ka in ta hado ku, shi yasa yake karra tirrr da wannan rayuwa, ya je ya ga ukuba kala kala saboda yan kudaden da basu taka kara suka karya ba

da kula yana kallonta ya ce" Ama ban manta fadan da nake son yi ba, waye ya baki kudaden nan masu yawa?"

RAUDA ta sake sada kanta, dan kuwa ta san laifinta
a sanyaye ta ce" Aba, dama Abdallah ke min ire iren kyaututtukan nan, masu yawan gaske, da su nake kashe rikicin Mama wani lokacin dan ba kulun nake iya yiwa samarin dabara su bani kudin su ba tare da sun nuna min wata hanyar ba, walahi aba ban taba wulakantar da kaina ba, ban taba ba, ko nawa zaka gani a hannuna ba haramun bane, ban taba aikata wani aikin dan na samo kuɗi ba, Allah ya kare Ni sosai daga wannan halakar "

Aba ya sauke ajiyar zuciya yana yiwa Allah godiya a cikin ransa, a sanyaye kuma ya furta" Allah ya karra tsare ki, shi Abdallah din nan balaraben nan ko?, ya je wajena sau biyu"

RAUDA ta gyada kanta bata ce komai ba kanta a kasa
Aba ya ce" Sosai Bah din ku ya nuna min eh idan har ana iya bashi bashi da wata matsala da ta danganci mugun hali ko nasaba ko addini da za'a iya hanna masa, Ni kam na fada masa bani da damuwa in dai kina son shi Allah ya tabatar da alkhairi, shine akace to wai za'a saka nan da sati biyu, ana so kafin a maida Ni wajen neman lafiyar nan ace an daura ina nan, shin kina son shi? dan in har bakya son shi ba zan taba yarda na baki shi ba, domin ba zan so ki kuma shiga wata rayuwar kaka naka yi bayan wace kika yi a rayuwa RAUDA"

kanta na kasa ne, tana jin furucin Aba tamkar wanda yake yi mata yare da yaren da ba nata ba
sosai Hausar ke son yiwa zuciyarta nauyi, har ta dan dago tana kallonsa a raunane ta ce" Sati biyu kuma aba?"

Aba ya zuba mata ido yana kallon yannayinta, da kula ya ce" Eh sati biyu yar gidan Aba, akoy wani abin ne? "

RAUDA ta sada kanta, a hankali tana fitar da numfashi daga bakinta dan sai ta ji murar dake sandarta ta toshe mata hanci nan take

"RAUDAH?" Aba ya fada a tausashe yana sake kallonta

dagowa ta yi da dan sauri tana kallonsa, sannan ya amsa

"akoy wani abu dake damun ki ne da ya danganci auren nan?, idan har akoy shi ki sanar min domin kina da dama tun kafin wuri ya kure maki, domin shi aure daraja gare shi, kuma maganar nan manyan mutane ke cikinta, koda ke din abar so ce a duniyar su ba zasu yarda ki saka su magana biyu ko zubar da kima a wajen mutane ba, *SHIN KINA SON ABDALLAH KO BAKYA SON SA?*"

RAUDA ta yi saurin sadda kanta, a hankali ta furta" Aba ina son shi"

"KINA SON SHI?" ya sake yi mata tambayar da ta fi kayar mata da gaba fiye da komai, dan bata san me yasa tambayar ke yi mata wani iri ba, ko dan iyayenta ne ke yi mata ita? Sai kawai ta sake sinne kanta ta gyada kan nata cike da jin wani rauni da kunya da kuma sake yiwa kanta tambayar menene yasa take jin wani sensation daban a kan lamarin nan?

"alhamdulilah, Allah ya nuna mana, ya tabatar da alkhairi, to wai shi Abdul din karami haka yake da son dadi? kin ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login