Showing 33001 words to 36000 words out of 188741 words
ka sha abinda ka saba gashi kana neman fito min da sababin sirfa? Kai walahi in dai hakane ka fi kyau a maye, gaskiya kar ka wani tambayeta inda ta samu kudi , ai tafiya ta yi kyau gobema a maimaita"
Jikinsa sanyi ya karra yi ya sada kansa cike da kunnar zuciya
Rauda dake hawaye ta budi baki a sanyaye ta ce" Baba, walahi babu abinda na yi, kudin nan da ka gani turo min su aka yi daga......."
"Rauda ki je ki huta, zan neme ki" ya fada a harhade yana dafe kansa dake sara masa
Sosai ta ji hankalinta ya karra tashi, da kyar ta iya barin wajen ta shige dakinta ta rakube tana barkewa da kukan da take ta danewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, lalle ta bata ran marikinta mai kaunar ta da son gannin ta zama abin kirki a rayuwa, ya Allah da ta san fitar nan bata da wani alkhairi da bata yita ba, yanzu yaya zata dubi tsabar idannuwansa ta fada masa da Yaren bahaushe kudin da aka sako a asusunta akace ta saka kati kawai? Ta ina zata fara fahimtar da shi abinda yake tsoron nan ita RAUDA ta fi shi tsoronsa da adu'ar Allah ya sa baya cikin mummunar kadarar dake iya samunta, ita dai ta san bata kiyaye wasu abubuwan ba, ama kuma ta san har zuwa yanzu mutuncinta na tare da ita
, kunci ne ya sarketa sosai, kunnayenta na jiyo mata Muryar uncle dinta da Mama sunna abu mai kama da kokowa, domin tana jin lokacin da ya rantse cewar sai ta fitar da kudin nan ya kaidawa mai su , ita kuma tace bai isa ba ai hakinta ne, tana bin Raudar kudi ne,
Wannan ya karra hasala shi suka kama kokowar karfi da karfi har ya dambarata da kas ya shige dakin nata ya ringa zubar da kayan dakin yana neman kudin da kyar ya gansu karkashin katifarta dake saman gadon karfe mai runfa ya fito da su ya sameta sai ihu take wai ya ƙaryata kuma yau sai ya dauko masa motar yan sanda wai ya satar mata kudi, ga yarta zaune tana kallonsu tana tabe baki, dan ita ko a kwalar rigarta haka ya zo ya sake ficewa a gidan ya nufi inda zai ga liman domin abin nan na Mama ya masa yawa, inama ace yana da halin yin wani auren? Da ya salami matar nan ya kawo wata ko Allah zai sa ya samu mai daɗin halin da zata taya shi rike marainiyar ALLAH, a yanzu haka yana daga mata kafa ne saboda abubuwa da dama, wajen aikin nasa an kore shi dan da ya je dazu aka nuna masa dama an bashi dama ta karshe ne, dan a kulun idan aka yi albashi sai ya kusan kwana goma ba'a saka shi a ido ba, ana daga masa kafa ne saboda abokin ogan dake rokar masa alfarmar nan, zuwa yanzu kam ya gama cinye duk wata alfarmarsa ba zai ci gaba da masu aiki ba, idan har ya saketa bai riga ya riki abinda zai ringa biyan hayar da suke ciki da abincinsu ba wani halin ne zai sake saka su bayan wanda suke ciki,
Si abu na biyu ba zai yiwu ba zamansa a yanzu daga shi sai Rauda da Abdul Hakim
Eh lalle uncle dinta ne shi, ama rayuwa abin gudu ce, bale shi da ya ringa jin wa'azin da malan ke yi akan mashayi sai ya gama tsorata da rayuwar kanta, ga wani irin mugun bukatar ya sha dake damunsa, ji yake yi idan bai sha ba har kamar yana iya rasa numfashinsa, dan ko a jiya da ya rasa Rauda sai damuwar ta so fin karfin tunaninsa har ya fara tunanin inda zai samu abin korawar da kyar ya danni kansa ya hakura
A cikin gidan kuwa Mama tamkar zarariya da kyar ya iya kama abu ta mike tana ihun a taimaketa kudinta kar ya je ya sha giya da su dukansu, fadi take yi Umar tsaya na yaga maka na shiga uku ina ya nufa? Sai dai ba shi ba alamarsa, hakan ya hadasa mata muguwar juwa da ciwon kai, a dole ya yi wani irin kwonci tsakar falon a kasa tana kukan babu mai hannata rufe Umar a garin nan in har ya taba mata kudi, babu mai hannata mayar da rayuwar Rauda ta tantiriyar ƙaruwar da ko namiji mai bin mata sai ya ji tsoron ta, dan walahi sai ta maida ita tamkar karya in dai ya yaba mata kudinta!
A dole Rauda ta sake kama kanta a wurin ranar kaf, sallah kadai ke fitar da ita ta zagaya ta yi alwallah ta labe a dakinta, domin ko abinci gagarar shiga bakinta ya yi
________________________________
Cikin nutsuwa ya silala motar dake dauke da mahaifiyarsa da mahaifinsa yana jin takaicin isa irin ta Hajia, yanzu ace mahaifiyar ta yi jinya ta gama ba zata barta ta huta ba, a'a dan mulki irin na Hajia shine ta bada umarnin anna ta zo ta ga yaya jikin nata ta wartsake ne ko ciwon dama ba wani bane ta wani ja mata d'a ya yi watsi da matansa ya je yake jinyar saura, mace kulun ba lafiya sai tsomarewa take yi uwa akuyar maya
Wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa saboda gaba daya yannayin gidan nan komai ya tsufa ya lalace harda wajen parking space, ama dan bakin hali irin na Hajia da A'isha kiri kiri sun nuna gida babu abinda ya yi, shi kam yana da niya daya a kan gidan nan shine duk ranar da ya tashi ya samu isashen lokaci gidan nan sai ya saka an rushe shi sannan a tayar da gini na yayi na mamaki, ginni na sarauta ba wannan ginnin da du waje ya hade ba!
"Ku shiga wajen Hajiar , ina zuwa" mahaifinsa ya fada da dan sauri ya fice a motar ya nufi bangaren matansa biyu da yayansa na wajen su
Da sauri YUSUF ya kalleta ya sake bin hanyar da Mahaifinsa ya bi yana mamakin to ba yace masu na zai shiga ba su shiga su fito su maidata su je inda zasu je da shi su dawo? Ikon Allah, a dole ya fito ya budewa mahaifiyarsa ya bata hannu ta kama ta fito suka jera tana tafe a hankali cikin nutsuwa shi kuwa yana duban hanyarta kamar wani wanda ke janye da makauniya har suka zo kofar shiga ya duba ya dauki takalmanta da ta cire ya saka daga ciki inda ake ajiyewa idan an zo suka shige cikin da salama a bayane a bakin Mama, shi kuwa ya yi ciki ciki, duda ya ga yau zaman Hajiar ce kawai sai masu tayata zama, ba A'isha da ƴaƴanta da wasu cikin jikokin Hajiar na bangaren sarki da Mahaifinsa
Ba laifi Hajiar ta amsa ba yabo na fallasa, ko dan ta ga YUSUF a wajen ne ko ta fara yin sanyi ne? Ita dai gatanan ama tunda ta amsa lafiya wa tambayar da Maman Yusuf ta mata cewar yaya jikinta suka ja baki suka yi shiru, Hajia na kallon YUSUF dake zaune a kasa kafar mahaifiyarsa saman cinyarsa yana amsa waya yana zuba turanci yana dan mamatsa kaffafuwan nata a hankali a hankali
Kai Hajia ta dauke a zuciyarta yana ayana' yaya kike so mu shirya da ke, bayan kiri kiri kin shiga tsakanina jikana? Me na maki da zafi da kika zabi rabani da abinda na fi so a cikin zuciyata fiye da kowa? Ba zan daina gannin bakinki ba tunda bakya sona da alkhairi bakya son farin cikina'
A birkice ya shigar masu baban falon gidan, wanda yake kyautata zaton a irin lokacin yana iya samun su biyun a falon koda babu yanyansu tare da su
Ai kam ya same sun, su dukansu kowace na abinda ta fi kwarewa a rayuwa
Bai tsaya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwansu ba ya fuskance su yana fadin" Haka kuka zabawa kanku rayuwa ko? Ba zaku yiwa kanku wa'azi ba? Tun da jan sawayenku har shekaru sun ja kunna fama da abinda bashi da wani alkhairi a tare da ku ? Me zai rage ku ko ya cira a jikinku idan kun je kuma kun umarci yayanku su je su mata sannu? Babu wace zata ce min bata ji ba ko bata sani ba, ko dan yaronta dake dawainiya da ku ai kwa mutunta ta, shin me ya rage mana a zamanmu da ya wuce mu gyara makwoncinmu? Ace kunna nan idan ta kwonta sai dai Ni zan yi jinyarta? Kun san dai ba bari zan yi a turo mai jinyarta daga gidansu ba bayan nima inada ahali, shin me yasa ba zaku yiwa kanku fada bane a zamantakewar mu ku yiwa kanku adalci?" A tausashe ya ajiye maganarsa yana duban su ya dora da fadin" Walahi bakwa min adalci, bakwa min karra, kuma hakan ya bata min sosai"
Daga wannan ya fice a falon ya yi tafiyarsa ya bar su zaune sunna bin maganarsa a zuciyarsu
Hajia Rufaidah ta sake sauke ajiyar zuciya ta fara magana tana fadin" Hajia umu kin ji mijinki ko? , in ba Aban yaran nan da neman rigima ba ina hadin gabas da yama? Shi dai idan a duniya abu ya shafi matar cen bamu da damar motsa wa ko da wasa, domin kuwa cibi na iya zamto mana ƙari, kai Allah ka bamu mai son mu a aljanah"
Hajia umu mai dakin tsakiya da ta fi shaka ta ce" Ko Honorable baya sauraron wa'azi a kan adalci tsakanin mataye?, sam ba ruwansa da wannan kalma sai sama sama yake wartarta idan hali ya kama, yaya za'a ce ka dube mu ka ce mana ko dan hidimar da danta ke yi da mu ma kyautata mata? Hidima ai taka ya dauka kai ubansa bai zama wajibi mu gode ba sai idan mun yi niya, kuma shi dai Honorable gaba daya bai cika kiyaye namu fushin ba mu, ai ba dole bane sai mun kula ta, idan mun yi niya ne zamu yi zumunci da ita, Ni kuwa na rantse ko mutuwa na yi kar ta zo saman gawata haka nima ko mutuwa ta yi ba zan je ba, ai wankake baya haduwa da mai dati, Honorable kuwa sai dai ya yi hakuri shi kadai ke gannin darajar rariyar da ya siya , kuma lokaci dai, zai ha ranar da zata yi masa zuba!"
Hajia Rufaidah ta yi murmushin takaici tana dauke kanta tana sake tunawa wai sunna nan ya yi jinyarta? Hahahaha namiji kennan sai kace wani wanda da ace sun nuna zasu yi jinyar Tata zai amince ya barsu daga su sai ita ne?, Honorable kennan ......
...Wannan kennan.
😍😍😍😍
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*13*
*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*
*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
Yana fitowa shigewa ya yi cen ciki wajen Sarki dan a dole yana so ya sanarwa wani wannan abin dan ya huce
Har ga Allah ya ji haushin irin yadda matansa basu je ba basu aika yayansa su je ba
Ya san ba wani zuwa da zowa tsakaninsu, ba wani gaba na hargagi suke yi tsakaninsu ba, ama basa yiwa junna maganar fatar baki tsakaninta da su, eh lalle a lokacin da suke tare an yi zama marar dadi, zaman da ba'a so, ama daga bakin lokacin da ya raba zaman ya ga ita mahaifiyar Yusuf ta zubar da komai tana rayuwarta da abinda yake gabanta, kuma a rayuwa har kyauta tanaiwa ƴaƴansu irin idan sallah ta zo din nan da sauransu, ama su bai san me yasa suke irin haka da ita ba,, idan ya yi magana sai su bashi hakuri su nuna su basuma san damuwa bane Hakan, sam baya son haka, zumuncinsu sun kashe shi karfi da yaji to me yasa suke son dan abinda ya rage su idasa murjewa? Mutun ya kwonta rashin lafiya ka kasa yi masa sannu dan muguwar akida da mugun saka kai a abu marar dadi, wannan din bashi da wani anfani!
Kai tsaye ya je bangaren nasa ba tare da tunanin yana iya tarar da matansa a bangaren ba a irin wannan lokacin, ama matan nasa su biyu ne , uwar gidansa sai amaryarsa wace ga dukkan alamu itace da girki yau dan ta sha kwaliya harda ta a fada da fatar baki
Da sakewar fuska suka gaisa, duda uwar gidansa kana gannin gaisuwar zaka fahimci ba har ranta take yinta ba
Sunna gama gaisawar ya ce" Mai marataban yana ciki ne?"
Da sauri uwar gidansa ta ce" Eh yana amsa waya ne tun dazu yace kar mu shiga shine muke jiransa, wayar nan tasa ce mai jimawa"
Dan tsai ya yi dan kamar alamun kakari ya ji, sai kuma ya masu salama ya fice yana tunanin ko ya gama wayar ya shiga wani abin ne?
Yana fita ta kalli amaryar rai bace ta ce" Uban waye ya sanar masa bashi da lafiya?"
Da sauri, da kuma alamun kamar tsoronta take ji ta ce" Walahi babu wanda ya sanar masa Hajia, ai babuma wanda ya san bashi da lafiyar sai Ni sai ke"
Baki ta tabe tana dauke kanta ta ce" Dan na san Kun aika ku fita ku yayata bashi da lafiya ku baku san baban burinsu ya kau a karagar mulkin nan su su gaje bane, idan sarki ya mutu sai kun zama abin tausayi a garin nan, dan du wannan takamar da kuke yi sai kun dawo mabarata a wajensu, dan walahi sai kin yi asarar auren dattijo da yan kannanun shekarunki, domin abinda aka zo a cin ba'a jima ana ci ba, Ni Bara na je na samo masa magani ki rufe kar ki bar kowa ya shigo nan din"
Daga nan ta mike ta fice tana jin takaicin wannan ciwon ciki na sarki, ciwo ne mai gigita shi sosai, a da idan ya fara shi hankalin kowa tashi yake yi, yanzu ne take boyewa bata zama babu maganinsa dan bata son yadda ake cika masu waje ana masu ido ido, kai innalilahi ita fa idan aka bincika cikinta a yanzu haka tana cike da bakin cikin aurensa, ba dan komai ba sai dan rashin haihuwa ta so ace kannin ta aura da wannan banzan ko da yayane zai kau ya ba masu waje wajensu, gashi dai sunna zaune tamkar hoto mata hudu reras ya iya zuba yaukin fa sosai sai dai yaukin baya zama gudan jinnin da zai koma halitta!
Komawa Hon ya yi bangaren Hajia ya shiga da salamarsa
Hajia da Anna ne suka amsa masa a bayane YUSUF kuwa yana tsaye ne yana amsa call a lokacin
Zama ya yi daf da Hajia yana tambayarta jikinta da kuma tambayarta yaushe zasu koma a cire abinda aka daure karayar ita kuma tana bashi amsa da kular itama, domin danta kam tana son abinta, abinda suka aikata shi da mahaifiyar Yusuf ta dauki hakan a matsayin ya hadu da muguwar budurwa ne ta kai shi ta baro shi kuma ta yafe masa ama ta kasa yafewa y'ar da aka karbi budurcinta aka rabata da iyayenta, aka soki zuciyar iyayenta aka katse mata karatunta aka wulakantata a idannuwan abokai da dangi, Hajia kennan
Yana gama wayar ya dube su ya ce" Mu je Mah, daga cen zan je park ne yau ban je ba"
Mahaifinsa ne ya fara mikewa da kula ya ce" Karbi ky din yanzuma kai zaka tukamu da ka ajiye a kusa da Mamanka ka san ba zan barta tuki ba ko?"
Murmushi Maman Yusuf ta yi ta dauki Ky din dan a bayane Hajia take kallon mahaifin Yusuf da mamakin yau ya masa magana a tausashe, sai dai kuma farin cikin hakan ta ji, domin ita dama bata da damuwa da soyayarsa da d'ansa
Salama mama ta yiwa Hajia gannin ta yi kiran Yusuf , shi kuwa a dole ya je ya tsaya gannin mahaifinsa tsaye yana kallonsa
A tausashe Hajia ta ce" Dama dan na roke ka ne idan ba damuwa ka kai Ni gannin likitan