Showing 57001 words to 60000 words out of 188741 words

Chapter 20 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9875

huta sosai"

Tana fada ta mike ne, Har Rauda ta mike itama Salima da kula ta ce" Mah, ki barta a nan mana, na ga ke kike kula da Bah, kar a barta ita kadai a dakinki, ama in ta fi son cen din to"

Mah ta dubi Salima da murmushi a fuskarta, ta sake bin dakin Salimar da kallo, kwarai yana iya isar su koda su biyar ne bale su biyu kadai, ta sauke dubanta a kan RAUDA a tausashe ta ce" Zaki zauna a nan din kuwa?"

Da kula sosai Rauda ta gyadawa Mah kai, Salima kuwa ta fice da carbinta ta nufi bangaren mahaifiyarta dan ta sake gannin jikinta sannan ta mata sai da safe

Mah ta amshi wayarta ta saka mata numbarta ta ce" Ga numbana, idan kina da bukatar wani abu ki yi kirana ko wani time ne kin ji?"

Rauda ta kuma gyada kai tana gannin abin wani iri

Mah ta sake dubanta da kula sosai ta ce " dangane da neman babanki, ki kwontar da hankalinki kuma ki yi ta addu'a, in sha Allah da ba ga an samu dan sarari zan sake yiwa YUSUF maganar, na tabata zai maida hankali kin ji? Ama yanzun ki yi hakuri ki yi ta saka shi a addu'a, zan yi iya yina dan kar abin nan ya zama wani iri, kin ga babanku ya kai maganar ana ta bincike dan comissiona ya sanar min ko jiyan nan marikiyarki a wajensu ta yi rabin wuni dan shi bai yarda da ita ba, wai ko har sai da aka zane kanwar nan taki? Ni dai abinda na sani shine bi izinillah za'a same shi , sai mu yi ta saka shi a addu'a ya zamto a same sshi a cikin hayacinsa"

A sanyaye RAUDA ta ce" In sha Allah Mama na gode"

Mah ta yi murmushi sannan ta tafi ta barta zaune bakin gado

Bayan fitar Mah ta jima sosai a yannayin nan tana ta saka da warwara, daga bisani ta gyara kwinciyarta baki bakin gadon ta yi addu'a ta shiga neman barci, dan a hankali ta ringa jin sauki a zuciyarta da samun tabbacin in sha Allah za'a ga uncle dinta , a lokacin karfe goman dare tuni ta gabato dan saura yan mintuna ta cika Salimar kuma bata dawo ba,
Cen barci ya kusa daukar ta Salima ta dawo, tana jinta tana addu'a kuma tana ji ta rufa mata lalausan bargo itama ta kwonta nesa da ita ta rufan bayan ta kashe fitila, daga nan barci ya fara awom gaba da ita


Sai kusan sha biyu ya nufo bangaren Bah, tare da mutanen da suka rako shi, suke tafiya tamkar ta kurame domin tunda ya shiga gabansu suka yi shiru suke tafe kowane na mamakin taku baban taku irin na rikaken sarki a tare da sarkinsu
Sunna zuwa wajen get din ya dakata ya juyo a nutse da idannuwansa masu tsauri da girma da kaifi ya ringa bin su da kallo yana jin yadda suke masa salama da yare mai tafe da kirari sunna duka masa da yi masa sai da safe

Ko a da idan ana masa irin haka ba baki yake budewa ba bale yau da yake ji kamar an dinke masa bakin ne?
Da idannuwansa ya ringa masu alamun amsawa sannan ya juya ya nufi ciki mai gadin get din ya duka yana gaishe shi har sai da ya bacewa ganninsa sannan ya mike ya rufe get din yana murmushi a bayane ya ce" Yan garina tabas yanzu kuka hadu da daidai da ku, daga manya har yara yanzu zamu san mecece sarauta"

A nutse yake ta takawa har ya karasa kofar dakin Bah

Budewa ya yi ya shiga da salama ciki ciki yana kai dubansa saman doguwar kujerar da ya hangi farare tas din kafafuwa

A nutse ya karasa yana jin sanyi na ratsa zuciyarsa sakamakon gannin Mah na bude idannuwanta jin tafiyar mutun da ta yi a kunnenta

Dubanta ta sauke saman fuskarsa lokaci daya tana sakin murmushi a tausashe ta furta" MALIK"

Idannuwansa ya lumshe yana jin sunnan da daraja a bakinta ya mika hannayensa ya tayata tashi ya zauna gefenta a nutse a hankali ya shiga ware rawanin dake kusa da habarsa sosai yana jin wata iska na ratsa shi ta ac, a tausashe ya ce" Mah, hw Are You?, yaya jikin Bah"

Mah ta sauke ajiyar zuciya itama a tausashen ta mike tana fadin " Da sauki, likita yace wai zai tashi, "

Tana fada ta karasa ta dauko kular abincin da ta tanadar masa ta kawo ta ajiye a baban plate mai dauke da su cokula da sauransu

Yana kallonta tana zubawa har ta gama ta dago plate din tana kallonsa ya fara magana kamar haka" Zan fita da shi, in sha Allah zuwa gobe nake so da yama"

Ido ta zuba masa sosai ta ce" Ka manta yanzu ba da bane?, koda za'a fita da shi sai dai Ni na fita da shi"

"Mah,"
Ya fada yana kallon kafarta mai yi mata ciwon

"Babu mai jinyarsa ne? Ina sauran suke?" Ya fada yana kallonta

Mah ta yi shiru tana bashi abincin ta masa alamun ya ci, dan ko rantsuwa ta yi ba zata yi kafara ba yau bai ci komai ba

Abincin ya ringa tabawa yana ta tunanin abinda ke ransa

Sai da ta ga ya ajiye ta zuba masa ruwa ta mika masa ya sha ya miko mata kofin a tausashe ta ce" Ka yi hakuri da duk wani abu dake iya taba maka zuciya, zan iya jinyarsa tunda ba daukanshi ake yi cikin dare ba, ka yi hakuri bayan adu'ar bakwai sai a fitar da shi din tunda a yanzuma ba wai ciwonsa ne ya hanna shi farkawa ba, alluran da ake masa dan ya samu hutu mai nauyin gaske ne, ina adu'ar Allah ya sa kafin nan ya farka da kansa cikin nutsuwarsa, ka ji?"

Kai kawai ya iya gyada mata, suka dan tattauna, gaba daya firar danarsa ne take yi, da bashi hakuri da nuna masa hukuncin ubangiji kennan, ta sake sanar masa ya bari mahaifinsa ya dawo hayacinsa ta tabata komai zai zo masa da sauki
Karshe dai ita da kanta ta raka shi har dakinsa wanda Salima ce ta yi tsaye aka masifar gyara dakin har aka gama tana tsaye dan fitowar nan da ta yi ta ga jikin mahaifiyarta sai da aka yi gyaran ne ta koma shi yasa ta cika dare

Da kanta ta kunna masa AC harda tunatar da shi addu'a kafin ya kwonta sannan ta tafi

Tana tafiya ya samu ya tube ya shige bayi yana ta tunanin Allah ya sa kayansa dake dakin nan sa shiga jikinsa , a killace dai suke , sai dai a ajiye suke sun jima haka

Tawul ya bude ya ciro cikin wrdrb din dake bayin mai madubi yar madaidaiciya
Bude shi ya yi daga cikin ledarsa sannan ya nufi waje ya rataye ya shiga wanka

Alwallah ya dauro ya fito ya haye salaya

A yanzu YUSUF ya san ya shigo wani fage da barci bai ganshi ba, shi da kansa ya san a yanzu ya zame masa wajibi ya yi sallah ya yi addu'a ya daga hannu ya roki Ubangijinsa kariya da taimako a kan baban abinda yake wuyansa

Ya jima saman salayarsa, kansa a kasa yake, ya sani a yanzu yana gaban wanda ya isa ya kifar da duniyar da yake ciki baki daya a cikin second daya, ya sani ne yana gaban wanda ya cenza masa zanen Kadara cikin yan sekwani, bai taba garajen wasa da ibada ba, dan ya yarda da kalmar LA'ILA HA ILALAH, ya kuma shaida MUHAMMADU RASULULAH SALALAHU ALAIHI WA SALAM MASOYINSA NE, ya san cewa akoy lokacin da rai zai yi halinsa domin ya yarda Kulu nafseen za'ikatul m'aut, kuma ya san akoy kwonciyar kabari bayan fitar rai, akoy ranar tsayuwa gaban Allah, kawai ya zamo cikin bayin nan wa'inda ta yiwu ba zasu samu rabauta ba? A yadda yake tunani kennan dan kuwa ka san zaka je ka fadi me ka yi? A ina ka yi? Saboda me ka yi? Kai da wa ka yi? A wajen wanda ya halicce ka, yake da ikon saka ka a wutar jahannama, ama kuma *KAKE YI DIN*.......( ASTAGFRULLAH WA ATUBU ILAIK)

Yana ganawa ya je saman gadonsa ya dauki babbar wayarsa ya danna yana kallon tarin miss call din da aka jera masa

Kai ya gyada yana tunanin ina shi ina iya amsa wadinnan tarin call din? Yana shirin aikawa ISHAK kira kiran SHAHEED ya shigo wayar

Kwonciyarsa ya gyara ya daga kiran kasa kasa ya ce" Yaya da kiran mutun tsakiyar dare kuma ?"

Murmushi SHAHEED ya yi shi dinma ya ce" kai da baka ajiye NAJEEBA da Nadia ba ai baka da time din da za'a kirayeka"

YUSUF ya yi dan shiru, cikin yannayin maganarsa ya ce" Nine zaka cirewa rawani dan ka rantse sai an nadani ko?"

"MALIK alkawarin Allah ne fa" SHAHEED ya fada a tausashe dan ya sani sarai YUSUF yanzun yana bukatar a tausasa masa

A tausashe ya dora da fadin " kai ka san tana binka, YUSUF saboda ka guje mata ne ka kaura nesa da ita, kai ka san na san wannan ne dalilin da ya sa ka fito daga garin nan , dan ba wani rikici da ya isa ya saka ka yin nesa, ama kuma abinda ka ki yarda shine , ita fa danko ce, du inda ka yi tana biye da kai"

YUSUF ya bude idannuwansa da suka yi ja saboda gajiya da tunani kala kala, kasa kasa ya ce" Kai ka san sarauta ba tawa bace, ba rayuwar da nake iya yi bace"

SHAHEED ya yi murmushi ya ki bashi amsa a kan maganar nan, saima tambayar da ya masa kan awon hular dake masa

YUSUF ya ce" Hula kuma? Me za'a yi?"

SHAHEED ya yi murmushi ya ce" Dinkunnanka ne sun yi nisa sosai, bani da awon hularka ne ranka shi dade"

YUSUF ya dafe kai, hakane fa yanzu sai ya yi dinkunnan nan ko? Da hulunan, tunda ba'a zaman fada da gajeran wando
Firar dai ta dan dauki lokaci kafin su yi salama ya kwonta yana sake yin
addu'a


Washe gari tunda duku duku gidan ya dauki haya haya, wato bangaren Honorable

Tunda gari ya fara haske kadan aka ringa shigo da takardu na neman son gannin MALIK
takardun dake sauka hannun matar Honorable mahaifiyar Salima saboda a lokacin dole baki daya kowa ya fito falo baba dan a karya a kuma jirayi fitowarsa, dan sun sani ba maganar su fara neman fitina a fili bane, koda zasu yin sai dai su samu makami ba dai fito da fito da YUSUF dan BELLO ba!


RAUDA na daya daga cikin wa'inda suka farka da wurin har aka yi yan aikace aikacen kayan kari da ita, a daidai lokacin sunna wajen diner baba, diner din da tabas in har zai karya a nan ne zai karya sunna ci gaba da kimtsa wajen dan Mah ta fito tuni ta kawo mata sutura ta yi wanka ta cenza , sai dai bata zumbula hijabin da Salima ta bata ba, ta dai yafa gyalen mayafin a kanta sunna dan dauki ajiye da Salima da kuma su Musulima wa'inda suka ba Salima mamaki ainun, domin a lokacin da suka shiga kicin yan matan nan uku kowace ta tambaya a bata girkin MALIK ne ta girka, hakan ya ba Salima mamaki dan a tsakaninsu a lokacin suka shiga yiwa junna kallon ke fa? WHO Are You da zaki nemi a baki girkin Malik? Me kike nufi da hakan? ................karshe dai sun zamo iyayen gida ne dan babu wace ta taษ“a girkin sai bin su Salima da suke sunna kokarin saka su ko hannasu da son basu order na yadda zasu shirya komai har sai da hakan ya saka RAUDA yin murmushi ta girgiza kai dan kwarai ta gane shirmen yaran nan da abinda suke nufi, hakan sai ya bata dariya da mamakin yan matan zamani, to ita akoy wani girmemen katon da zata gyara dan ta birge? Sam mata basu san abin so bane Bama, uhum wahala!.......





๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”
Azl 21
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo




Sunna cikin hada haษ—ar nan Mah ta fito dauke da kaskon turaren wutar da ta fito da shi daga ษ“angaren YUSUF,

Itace ta ringa gaishe da matan Bah da girmamawa da kula, su kuwa sunna amsata kadaran kadahan harda wace ta shiga jiyan ta saki tsaki ta fito falon itama, kana gannin yannayinta ka san kamar wace aka yiwa dole, ga abin karin ruwa a hannunta

Mah ta ajiye kaskon dake dauke da tsumamen turaran wuta na Dolars a lungun kujeru ta zagayo ta zauna saman kujerar nan tana dan sauke numfashi, dan ta ci aiki harda na mamaki, domin tunda ta yi sallah ta kamawa YUSUF ya kimtsa mahaifinsa tas, ya dauke shi ya kai shi saman doguwar kujera suka cenzawa gadon dakin zama suka yi shinfida mai kyau, ta yi shara ta wanke bayi tas ta saka turare ko'ina suka kimtsa hatta labulaye sai da suka cenza, sannan ya maida mahaifinsa za kwontar wanda ke numfashi ama jikinsa da gumi, kuma yannayin kwonciyar da ake masa irin ta masu ciwon zuciya ne sannan ya tafi nasa dakin dan Hajia sai kira take yi tace kar ya amshi bakuncin kowa yau kuma kar ta saki ta yarda wani ya dafa masa abinci ya bashi ya ci ciki harda mutanen cikin gidan da sauransu sannan ta sanar Sarkin rawani zai zo da tufafinsa a masa rawani ita kuma zata kawo abincinsa, a haka dai suka yi salama da Hajiar Mah ta rarasheshi ya je ya yi kwonciyarsa domin a wannan lokacin da ake ta kai kawo din nan shi barcima yake yi a dakinsa, gashi har karfe tara ce zata yi

Da kula sosai Mah ta ce" Ku yi hakuri jiya na kwana dakin cen ban tsaya mun daidaita ba, na yi ta jira ko wata zata shigo har barci ya daukeni, yaya kuka tsara jinyar tasa ne Hajia?"

Hajia ta dago dubanta tana kallon Mah, ita abinda ya fi bata mamaki da ita kamar bata taษ“a haihuwa ba caras da ita, ga shegen gayu, koda yake abin nata koda ba wanka ta dauka ba sutura na yi mata kyau ne wannan komai koshenka ba zaka kushe wannan ba

Kanta ta dauke ta ce" Ai kawai ki yi jinyar , idan kuwa da Maman su Khalifa zaku raba ba damuwa dan Ni ba lafiyar gareni ba nima"

Maman Khalifa ta juyo tana yiwa Hajia kallon lallema, ta dauke kai tana tabe baki dan walahi ita ba zata furta masu koda a ba a wannan shirmen, jinyarsa? A'a ita matar so ta je ta yi ama ba dai su ba!

Gannin haka ya sa Mah yin dan murmushi ta mike ta nufi kicin bata kuma furta masu komai ba, ba zasu gane bane, a da ta dauki wulakanci ama banda yanzu, su da kansu sun sani banda yanzu, ba wai dan YUSUF ya hau kujerar nan ba, a'a, tun kafin ya hau ta yi watsi da wulakancin su ta fuskanci rayuwarta tunda ta gane ba zaman mutunci ake yi da ita ba ta dangana da su!

Su Dukansu sun yi mamakin yadda bata basu hakurin a raba jinyar Honorable ba, sai kuma suka watsar dan sun san dama abinda take so kennan, maman Khalifa ce kawai ta kudiri a ranta ba zata bar mata mijin ba, zata hannata zaman lafiya da kai kawo tana watsa masu hannu da Bara masu kanshi kamar ita kadai ce matar BELLO ba!

Mah na nufar wajen Diner ta ja ta tsaya da mamakin yan matan dake tsaye kowace ta sha kwaliya su ukun nan tamkar wa'inda suka zo gidan biki bayan gidan rasuwa suka zo

Amsa gaisuwar da suke rige rigen yi mata ta yi a jimulce ta dauke dubanta ta ษ—ora saman RAUDA a tausashe ta ce" To nan babyn Mah"

RAUDA kunya ta ji ta kamata, sai kuma wani abu da ya sakata daga kafafuwanta ta karasa daf da Mah ta nemi dukawa dan gaisar da ita, wani abu mai kama da shauki da jin wani iri kamar idan wani mai daraja a duniyar ka ya nuna maka kulawar nan

A nutse Mah ta tareta ta dagota tana murmushin tsokanar da Salima ke yiwa RAUDA din, dan Salimar cewa ta yi" Iyeah, kin ga mamanki kin saku? Mah y'ar nan taki bata fira sai da ke kadai ama ko?"

Mah ta sakar masu murmushi zata basu amsa kunnayensu gaba daya suka ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login