Showing 3001 words to 6000 words out of 188741 words

Chapter 2 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9815

nan ne? Yan matan amaryar nan Akoy jan aji fa, har karfe hudu na neman shigewa baku kaiwa mutane abinci ba?"

Rauda ta mike tana mika hannu ta dauki dan madaidaicin mayafinta ta ɗora saman kanta, domin gashinta a bude yake dama ta saka dan karamin ribom ne ta daure shi, ko kitson bikin Babar aminiyarta bata yi ba, hasalima tunda ta samu ta dinka shadar fatiha sai atampar ranar nan daga su bata karra komai ba sanadiyar abinda ke mamaye da rayuwarta

Tana mikewar kusan yan matan dake wajen sai faman hoto da vidio suke yi sai da suka yi mata kallon kasa kasa, gatanan dai a yannayin shiga sun dameta sun shanye, sai dai wani irin tsari da Allah ya yiwa halitarta mai zubaben sanyi da jiki luwai luwai yakan zamo abin kallo a wajen du wani mai son kallon abu mai kyau..........

Murmushi ta sakarwa auntyn kawarta ta ce" Yanzu zamu tafi aunty"
Sai kuma ta juya wajen Bara'atu ta ce" Ki sanar ma wa'inda zamu je da su Ni Bara na yi gaba"

Daga haka ta wuce da yar karamar jakarta a hannunta wace ke dauke da wayarta

Takalminta plate ta saka baki mai nutsatsen kyau sannan ta karasa wajen motar da aka saka abincin wajen mazan tun dazu ta bude gaba ta shiga ta zauna ta janyo earpeace dinta ta makala a kunnenta a hankali ta lumshe idannuwanta tana sauraron wakar dake cikin wayar

Jim kadan wasu yan matan su uku suka fito, ciki harda wace ta bada numbarta wato Nafisa, dan tunda safe da suka zo ta so tada mata zancen ama Rauda din bata zauna ba, ita kuma ta daukarwa kanta alkawarin sai ta tada mata zancen nan dan ta fada mata me take nufi? Kai ba kowa ba, ba dan kowa ba sai wani isa da takama ta rainin wayo, ta tabata ko waye ke son numbarta ba karamin mutum bane tunda wanda ya tambayarma ba karamin mutum din bane shine zata wani rainawa mutane wayo?

Sunna karasowa suka ganta zaune gidan gaba ta wani hade rai , da kyar Nafisa ta yarda ta shiga bayan nan ranta a mugun bace, ta daukarwa kanta alkawarin a zuwa ba ta shiga gaba ba? A dawowa Sai dai baya dan uban ubanta!

Da wannan direban gidan su Bara'atu ya ja motar ya nufi gidan su angon da su da niyar kaiwa angwayen abincinsu kamar yadda al'adunmu suke a garinmu, ranar wunin biki yan matan amarya na yiwa angwaye girki gwargwadon iyawarsa su tafi su kai su zuzuba masu idan aka ci aka gama sai a basu tukwuicinsu mai tsoka mai kashi😂

Gaban wani makeken vila suka ja suka tsaya a Anguwar kwaliya dake cikin Damagaran
Tunda suka tsaya yan matan nan hankalinsu ya rabu gida biyu, domin ta yadda suka ga jikakun motocin dake parker a kofar gidan nan hankalinsu ya karra tashi, nan fa kan mai fitar da jan baki da madubi daga jaka sai mai fitar da hoda suka shiga sake gyagyarawa, dama kwaliyar yau ta musamman ce, mijin Bara'atu dan kasuwa ne sun san ko ba komai sa jimki kudade da kuma nasu summa abokin rayuwar ko abokin shashancin, lokaci ne Alkali, abinda suka sani a fitowar nan tasu sai sun yi wufff da ɗan wata ko uban wata

Ficewa direban ya yi ya je ya bubuga bisa umarnin RAUDA wace kasa kasa sosai ta ce" Baba buga masu kofar Atu tace Akoy kare , idanma daga nan zamu sauke masu mu juya fine"
Tana kiransa da baba ne saboda yana dauke da sunnan mahaifinta, sannan mutun ne mai daraja dan Adam, a kulun idan ya dauki Atu sai ya biya ya daukota ya ajiye su a makaranta, tun tana kiyawa har Atun ta kai kararta wajen Mamanta sai ta mata fadan a kan me zata ki shiga a kaisu da kawarta? A dole take shiga har ya zamo kamar yar gidan du inda zasu je tare ake kai su a motar

Bugawa ya yi ya fi a irga , gannin ba'a bude ba ya dawo yana fadin" HAJIA Rauda Inaga sai an yi kira ko kawai mu tura mu shiga?"

Rauda ta girgiza kai ta ciro karamar wayarta tana masa alamun tana zuwa

Numbar mijin Atun ta dannawa kira
Wayar na fara ringin ya daga yana fadin" Da girman kujerarki aminiyar aminiyata"

Murmushi ta yi , da salon muryarta ta ce" Muna kofa fa aminin aminiyata"

Mikewa ya yi da wayar a hannunsa daga cikin mutanen da basu wuce su shida ba, dan kuwa a dole ya tsame daga cikin taron hayaniyar jama'a ya kilace Wadinnan, domin mutanensa ne na kusa sannan abincin da za'a kawo daga gidan su amaryarsa yake so a kawo masu su, dan na jama'ar da aka yi ya tabbata da wahala a dadada masa rai, duba da ba kowa ke maraba da auren nasa ba

Da kula ya masu ja gaba har baban falon, yan matan amaryar saura sunne a gaba, sai Rauda dake rike da wani kula madaidaici tana tafiya cikin yannayinta na sanyi sanyi da kuma tsarin salon tafiyar da Allah ya haliceta da shi har ta karaso kan dokin kofar daidai direba zai juya da kula ta ce" Baba kar ka yi nisa, ba jimawa zamu yi ba"

Angon ne da kansa ya juyo yana fadin" Haba aminiyar aminiyata, ya koma idan muka gama ci sai a maidaku gida ko?"

Ajiyar zuciya ta sauke ba dan ta so ba tana jin dari darin shiga falon, bata yi tsamanin a falo zasu samu angwayen ba maimakun filin gida, sai dai bata ki shiga ba gannin ba ita kadai bace mace a cikinsu, kuma ita dai ba jimawa zata yi ba gaskiya

Takalminta ta cire a kofar dakin, kasa kasa tana binsu da kallo ta yi salama sannan ta sako kafarta mai haske da tsafta tana taka tiles din ta nufi wajen da aka ajiye abincin ta ajiye coolar ta sake juyowa dan neman wajen zama

Idannuwanta suka sauka cikin na Ishak da Nafisa

Shi Ishak din ba zata iya tantance kallon da yake yi mata ba, ama na Nafisa zata iya ajiye shi a matsayin kallon jin haushi ko na laifi? Allah masani, abinda take hangowa dai kamar tarin jin haushi ne, ta yiwu laifi ta yi mata bata sani ba? Ko ita dinma a wajenta bakin jinnin ta dauko? Dan kuwa ta kasance budurwa mai bakin jini a cikin yan mata, ba kowace budurwa ke mata magana ba, akan ce wai ta cika girman kai , da sauransu, ita kuma tana rayuwarta ne daidai misali

Kujerar da ta nufa da nufin zama ce ta ga wata tanfatsetsiyar waya ajiye, a hankali ta dauke dubanta ta dan juya dan zaunawa a wani wajen tana dan sakin murmushin abokin ango na mata tayin gefensa

Idannuwanta ne suka sake sauka bayan wani saman salaya, hannayensa harde a kirjinsa, kansa sade kasa , a hankali ta dauke dubanta a kansa ta juya ta karasa saman kujerar dake facin din wace ke dauke da wayar ta zauna ta maida dubanta wajen angon dake miko mata ruwa na cikin jarka yana mata fira a ranta kuwa ta ayana' Na tsani na ga namiji har namiji yana Sallah a daki, dan rashin mutunci ko yana aikin uban me aka yi sallar aka barshi?'

Salamce sallarsa ya yi a hankali ya sada kansa yana addu'a har ya gama ya shafa sannan ya mike ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi wajen zamansa ya dauke wayar dake ajiye ya zauna yana sake hade rai gannin natacen kallon da yan matan nan suka bi shi da shi, kai subahanalah ya ki jinnin irin wannan hadin da ake yi yan mata da maza, su ba yara ba, ba komai ba ama sai a hadu wai a ci abinci a biya yan matan su tafi, shi kam idan ya tashi dauko hudun nan ba za'a yi wannan badalar da shi ba, yan matan kowace zata yanka ainahin abinda take so a biyata sai a biyata ba sai an zauna ana rainawa junna hankali ba

Dubansa ya kai wajen daya daga cikin abokan ango mai sunna Idriss a lokacin da ya miko masa ruwa yana fadin" Biya maradi Allah dai ya kaimu ranar aurenka, a wannan rana ban san wa zai iya amsa sunnansa ba, Allah ya karra lafiya namu"

Yannayin fuskarsa bai cenza ba daga daurewar ya amshi jus din ba dan zai sha ba ya ajiye gefe kasa kasa ya ce" Ku salame su mana bafa ba son damuwa"

A lokacin da yake furta kalmar "ku salame su mana...." a daidai lokacin ne ya sauke dubansa a kan wace take face da shi tak tak kamar an ajiyeta ne hankalinta sam ba a kan kowa ba, tana rike da goran ruwa bata bude ba , kuma bata ajiye ba

Dubansa ya so daukewa tashi daya daga kanta, sai ya samu idannuwansa da dawowa suka sake sauka a kan fuskarta a daidai lokacin da take karanta sakon Bara'atu wace mijinta ya sanar mata mutuniyarta fa gatanan ta daka fuska bayan harda biya maradi a taron, shine ta mata msg din da ya sakata sakin tautausan murmushin da ya saka gefen idannuwanta kadan suka lotsa hancinta ya sake dan budewa kadan sai kuma ya koma yannayinsa saboda gimtse murmushin da ta yi ta dago dubanta a hankali ta kai kan angon kasa kasa ta ce" Kai ko?"

Dariya angon ya yi yana fadin" Eh, ba zaki dago mu yi fira ba? Zan kuma kai kararki ne "
Murmushi ta yi tana dauke dubanta ta juyo da nufin kallon hanyar kofa, dan mamaki ke neman kasheta na abokanan tafiyar tata, yaya za'a yi su zo waje su wani saki jiki haka a gaban mazan da basu sani ba su ringa fira haka da iya yi? Tun ba'a ce su raba abincin ba har sun bubude sun shiga zubama abokan angon a plate plate sai wani irin iya yi suke yi da Gwali, ita abin har daria ya so bata, ina ajin? Ina jiji da kan? Zamani ya zo mana da sabon salo mai wuyar fasara, ace yanzu mace itace zata yi iya yin da namiji zai gane ta? Lalle wahala bata bar wasu matan ba, WALAHI tsakaninta da namiji sai dai ya bita ba dai ta bi shi ba!

A hankali idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa, sai dai abin mamaki ko second biyar bata yi tana kallon gefen da yake zaune ba ta dauke kanta tare da nunin alamun bata san da zaman dan Adam a wajen Bama bale ya isheta kallo

Mamaki ya kama shi mai girman gaske
Har angon da wanda ya sanarwa a salami yan matan suka dawo dan waje ya ja shi ya sanar masa sakon *YUSEF* din cewar a salami yan matan nan baya son takura

Rasa yadda zai yi ya yi, a dole cikin murmushi da basu daraja ya ce" Amare, har kun fara raba abincin? Ai da baku ba kanku wahala ba, so nake a maida min ku da wuri ku shirya min hajiata a kawota da wuri wuri, sai kuma na ga har kun fara hidima da mu?

Nafisa ce ta yi gagawar dagowa tana sakin fari hadi da murmushi ta ce" Haba elhajinmu, ai ba dawainiya, an riga an zama daya, mun fara ai bari mu gama ku ci idan kun gama sai a maidamu, amaryarka kar ka damu kaima ka san tana hannun manya dole ta sha gyara "

Sai da ta dasa Aya Rauda ta dago da mamaki ta zuba mata ido
A hankali ta lumshe idannuwanta ta maido dubanta kan Elhaji, yannayin muryarta kasa kasa sannan da sanyin nan ta ce" A'a , a maida mu ya fi, sai ku samu sarari ku ci abinci cikin nutsuwa aminin aminiyata"

Da sauri Nafisa ta juyo tana kallonta, duk yadda ta so Hanna kanta nuna bacin ranta sai da ta ce" Mu zamu Hanna su sakewa ne? Ko dama an taba yi basu ci abinci ba mu mu juya? Me muka yi Kennan?"

Rauda ta sake tsareta da duban dake nunin abinda ke cikin zuciyyarta, ama bata yi magana ba, sai da ta sake bude baki zata yi magana sai ta ga Rauda din ta mike hankalinta kacokam a kan angon da ido ta masa alamun ita fa tafia take so bayan fuskarta ta wani irin nuna lalaci irin na shagwababen yaro , sannan ta masa nuni da agogon hannunta siriri mai ruwan zeba cewar lokacin ta tafi ya yi

Daga yadda yake ya sake dagowa ya zuba mata ido a tsayen da take tun daga yalolon jan mayafin dake yafe saman gashin kanta har zuwa yatsutsanta masu ɗauke da abin lalle irin na mata

Kansa ya sake daukewa ya kai dubansa kan Ishaq, sai ya ga shi din ma shi yake kallo da kuma wannan dake tsayen

Elhajin ne ya samu da dabara ya nunawa su Nafisa ai ba komai sannan ya rako su har wajen motar dake parker ya mikawa kowace embulop da ya zo kan RAUDA ya miko mata Tata du ta fi tasu girma da alamun ta fi tasu nauyi yana fadin " sai mun hadu da dare wajen kawo min aminiyar ko aminiyar aminiyata?"

Murmushi Raudat ta sakar masa tana ajiye kudin da aka bata saman cinyarta a saman labanta ta furta" In sha Allah"

Direban ya ja su, matashi da shi irin matasan nan masu zuciyar nema dan yaro ne a shagon Elhajin , haka kuma direbansa ne da gidansa baki daya

A lokacin da motarsa ta tsaya bakin Danja kunnayenta suka ringa jiyo mata shewace shewacen su Nafisa dake baya, ama sam bata jin abinda suke fada har sai da motar ta tashi suka dauki hanyar gidan bikin kasa kasa ta jiyo magana kamar haka" Ke kuwa, meye a ciki banda gayar tsiya? Itace fa jarin matar marin nata, shi kuma marikin mashayi ne kuma mazinaci!, Wai nan bikin aminiyarta ake yi ta kusa da kusa ama bakin ciki da bakin hali ya hannata ta yi kwaliya irin na sauran yan mata, ki duba ki gani sai hade rai da jiji da kai na banza , isar baka isa ba, ita ba yar kowa ba sai kwonbo da gashi da kuma kirar nan wace a wannan zamani du mai son ajiye kira irin nata tsaf zai ajiye in ya shiga wajen masu magani, aikin banza bata san yanzu maza yan kyale kyalen yan mata ke jan su, ba wai ire irenta ba?"

Kanta ta dauke , bata da niyar tankasu, har wace ke maganar tare da Nafisa ta ce"





Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*


*PAID BOOK*


_Bismillahir rahamanir-rahim._


*3*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳



Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*




Kanta ta kawar, bata da niyar tankasu har wace ke firar tare da Nafisa ta ce" FIFI, wai dan Allah baki ga irin yadda mijin aminiyar Tata ke kure mata waje ba? Ke kudinta fa ta yiwu ya fi namu yawa!"

Nafisar ta ja dan tsaki ta sake rage murya, domin magana ce suke yi kasa kasa sosai dan kuwa direban dake jan su ko kadan baya jin abinda suke fada , ama ita Allah ya mata karfin ji shi yasa dukkan furucinsu a kunnayenta, kasa kasa Nafisa ta ce" Na zaki gane ba, wannan fa da kike ganninta babbar yar hannu ce, idan kin ga tarin samarinta sai kin sha mamaki, ba za'a ce a'a ba in akace shima yana soyayya da ita din, bata da haram fa, kuma tsaf zata rabaki da saurayinki sai dai ki yi hakuri, gashi ita iyayenma bata da su bale a kai kararta wajensu, iyayenta hatsari suka yi suka mace harda yayarta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login