Showing 186001 words to 188741 words out of 188741 words

Chapter 63 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9851

ya ja din wahalar sai ta fi ta farko yawa


...........Ta sha radadin azabar da duk wata kamilaliya cikakkiyar budurwa ke sha a daren ta na farko.........., bale ta hadu da Malamin abin, sai ya zamo ya zama nama daya jal a saman tuwo , ya ririta karshe ya cinye sumul dan ko a yanzu da ya kuma maidata ruwa a karro na biyu suka dawo saman shinfidar da ya cenza da kansa suka sake kwontawa a saman kirjinsa ya dorata idannuwansa a lumshe, jikinsa gaba daya na sake sakewa da lamarinta, babar godiya tana karra tabata ga Ubangijin talikai, wanda bai haifa ba, ba'a haife shi ba, mai rayawa a cikin matace mai kuma kyauta da karri, a rikon nan da ya yiwa RAUDA a saman kirjinsa a irin wannan lokacin , ya sani ne mai kwatarta ko yi masa wasa da lamarinta wanda ya bashi ita ne, ya sani cewa Allah ya dubi lamarinsa ya bashi ba dan halinsa ko isarsa ba, shi yasa zai rike, zai rike da dukkan karfin da Allah ya bashi da kuma adu'a, zai riketa ta hanyar yin takatsantsan, zai bata dukkan kular da ta dace da ita......, in sha Allah zai zamo amini , dan uwa, yaya, aboki kuma miji a duniyarta, zai goga da duk wanda ya nemi lalata farin cikinta, zai girmama wanda ya girmamata!

Hucin numfashinta mai dumi dake sauka a jikinsa yake ji har ransa, a hankali bayan ya sake shafa gashin kanta ya budi baki dan karra jaddada mata kalmar da ya fada ya fi a irga a yau, a tausashe cikin nutsuwa ya furta" I love You so much baby........"


(☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗😌😌😌😌😌😁😁😁😁😁😁😁😍😍😍😍😍😍😍😍😍)



67
Azl PAJIN KARSHE
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

tallah2


*MAGANIN KARA KIBA 3IN1*

*Ina meneman kiba ido rufe Kuma tanason maganine ingantacce Wanda baida illah kokadan to tazo gadama tasamu yar uwa indai kibace da gyaran nono dakara hips toga Mganinmu nan 3in1 cikin kwana 7 kacal👌🏻 zakiga yadda Zaki fara murmurewa insha Allah mungwada mungani munbayar angwada munsayar angode insha Allah kawata Zaki godemin da 3500 dinki kinhuta da gorin rashin kiba munan cikin Gombe Kuma munatura kaya ko ina kedai tuntumebi ta Whatsapp ko kikirani Kai tsaye ta 08030861857 sai kunzo🥰*

*MAGANIN HIPS*
*Wannan Maganin anyisane tamasu neman hips sunsha wannan sunsha wannan to gatamunan insha Allah guarantee nakebaki hajiya inada yakini akanta matsala indai tarashin hips ne to anwuce gun 3500 kacal kinhuta kijuya kiwarwasa kisaka kayan gayu kijuyawa Oga yayikallo kawata har yanga saikinmasa ninafadamiki wannan nemeni kisamu naki 08030861857*

*MAGANIN NONO*
*Itama akwaita me inganci kamarta 3in1 data hips wasu suna korafi nifa nono kawai nakeso yaciko yayi bulbul gwanin sha'awa yadda Oga zaiyaba nasa breast cup suzauna das Amman abun yacitura Nasha Nasha magungunan Amman haryau ba chanji to ganamu Nan yakine ne Dani akansa ba Dan kadanba alhamdullahi duk Wanda yasaya saidai godiyace tsakaninmu kema zokigwada Kuma kigodemin location Gombe 08030861857*





Tabas ta wayi gari cikin cenza dukan tunaninta da duk wani yinkurinta na tada bali wa aminanta Atu da saleema , a lokacin da ta wayi gari a cikin jikin mijinta abin kaunarta bayan ya sake jaddada mata abinda ya gana mata tsakiyar dare ya kuma bita da zazafar kula sai ta sake jin cewar lalle zata iya jurewa duk wani motsinsa koda kuwa hakan na neman fin karfinta, zata jajirce ta koyi karatunsa dan zamtowa wajen da zai ringa kawo duk wani motsinsa da bukatarsa ya ajiye, A wannan ranar shi da kansa sai da ya fito daga masalacin sallar la'asar ya leka bangaren Hajia saboda ta bar masa sako a waya cewar Mama zata tafi da Dayana dan kaita asibitin kamar yadda aka bata shawara, kuma tana rokon alfarmar ya mata hanyar samun takardar zaman garin itama dan idan Dayanar ta samu sauki zata so su zauna su jima a cen ta yadda zasu sake samun lokacin karra kusanta kansu da ubagngijinsu, shi yasa ya je da kansa ya kuma basu lokacinsa dan a yau din sun fado a kan daidai, ya kuma da lamarinsu sosai har sai da kunya ta saka maman zubar da hawaye da gaza kallonsa, Allah dai ya nuna mata YUSUF sarkinta ne, kuma dole zata yi masa biyayya ko bata so, ko dan yadda yake kyautata mata ya gama mayar mata da aniyarta a dole suka dawo ita da shi sai gaisuwa kai a kasa dan kunya

Mah kuwa dama tunda ya je gaisheta da asubahi ta gane yarensa a dunkule, hakan ya sa ta dauki nauyin girkinsu aka girka aka kawo da ta kula ba zai bar RAUDAR ta zo wajenta ba a yau din sai ta basu lafiya ya kula da matarsa

A hankali jikinta ya samu sauki, sabon su kuwa sai da ya zama tamkar zai hanna shi fita fada, abinda ya shafi wayarsa ajiyewa ya yi Taj ne ke kula da shige da ficen abinda ya shafi kasuwancinsa , fada kuwa Bah ne da kansa ke kula da shike da ficen komai, domin kowa uzuri ya masa ya bashi lokacinsa


Sannu a hankali ta idasa kwace duk wani gurbi da ya yi saura a tsakaninsu, ya zamo shine ita itace shi, sannan ta dauki duk wani girma da aiyukan da ya dace ace ita ke gudanarwa cikin aminci da kwonciyar hankali, har ya zamo Hajia da kanta ta gama samun sukuni a zuciyarta da tunanin kwarai ko yanzu lokacin ta bar duniya ya zo alhamdulilah Gimbiyar Tsatsunburum gimbiya ce mai adalci, mai riko da addini, mai tausayin talaka


Bayan sati Uku da wannan rikicin da kyar Bah ya daina fushi da Mah, suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin cencana tsufansu da kare hakkokin junnansu, abokan zamanta kuwa murna ta karra komawa ciki, ya zamo a ci gaba da zaman doya da man jan da suka zabarwa kansu, sai dai na wannan karron ba wani daraja domin wanda suke yi dominsa bai nuna ya san sunna yi ba, sarakuwarsu ta yi watsi da su , kuma sun ci gaba da ci a hannun d'an wace suke yiwa kallon makiyiya, domin basu da yadda zasu yi da zakaran da Allah ya nufa da cara, sun riga sun gane ko ana ruwan mazuru sai ya yi, shi yasa suka koma bakin cikinsu na nukurkusarsu a hankali yana lalata lafiyar jikinsu

tsakaninsa da ISHAK sun yi zama mai anfani, domin sun zauna Ishak din da kansa ya bayyana masa tarin damuwar da aka saka shi saka shi, ama a ciki daya bai samu nasarar saka shin ba, domin ko harkar biyan mata ba shine ya saka shi ba shi ya wayi gari a ciki tsundum sanadiyyar ziyartar wajajen da basu da anfani, irin club ɗin da suke zuwa a da, sun yi magana irin ta fahimtar junna sun ci gaba da zumunci da harkar kasuwanci, ama wani ikon Allah kwata kwata baya son Ishak a lamarin da ya shafi RAUDA, sam baima taba bashi damar yin maganar RAUDA ba sai dai su yi na abinda ya shafe su iya su

NAJEEBA ta kawo ziyara da yin Barka da tarewa, sun kulla zumunci irin wanda ya dace tsakaninta da RAUDA, ta ji haushin rashin samun wace ta so lakadawa na jaki, haka ta juya Damagaran da jama'arta

Tsakanin Mah da Rauda soyaya ce ta uwa da y'a, da farko bayan RAUDA ta fara fita ta so saka matsananciyar Kunya tsakaninta da Mah, sai dai Mah ta ki amincewa da haka, ta ture mata wannan tunanin ta nuna mata ita uwa take a wajenta sarakuwarta Hajia ce ba dai ita ba, dan haka karma ta fara, a ranar ne kuma suka yi shawarar maida auren uncle dinta da tsohuwar matarsa mahaifiyar Abdul idan ya dawo, Mah ta yi amana da haka da farin cikin hakan da kuma adu'ar Allah ya idasa masu nufinsu

___________________________________


Gashin pizza take yi a ovun , dan yau gaba daya da ita ta wuni a ranta, ji take yi idan bata samu ba komai na iya faruwa, shi yasa bayan ta kula ya yi barci ta samu a hankali ta sadado kicin din ta shiga aikin pizzar daga ita sai yar yololuwar rigar barci da Safar hannu dan aiki da ovun din da take yi, hankalinta gaba daya a kan gashin, gani take yi gashin ya fi jimawa fiye da hadin kayan pizzar

Har ga Allah bai san ta fita ba, sai da wayar tasu ta tsakiyar dare ta tashe shi shi da Shaheed ya ga ba matarsa, hakan ya sa ya mike ya nufi bayi dan baya jin motsin ruwa da tunanin ko na tsakiyar dare ya kama y'ar gidan Mah ne? dan kawai ya tsokaneta domin har yanzu boyen abin nan take masa abinta, wato sindirki uban dawa mai dawa mai rikita kanshin waje ya koma kanshinsa oga baba mai saka tsoho gudu😌
A lokacin da ya leka ya ga bata nan ne ya ji kamar hankalinsa zai tashi, a hankali ya ce" Shaheed matata bata nan"

Shaheed dake masa firar abin haushin da matansa suke son guma masa ya ce" Karta yi nan din mana, aikin banza ai gwarama ace bata nan din, ina maka maganar wulakancin nan na tabata NAJEEBA ta san da maganar yarinyar nan, wai ace ni Shaheed nine suka yiwa kashedin kar su kar su gani ance zuwan yarinyar nan nawa ne? sun manta waye ni? Nine Sarkin damagaram fa, Nine nan mai wukar yanka , kuma mata hudu aka halatta min aura ba biyu ba ko?"

Shaheed na fadansa shi kuwa yana leka duk inda ya san zai ganta, ama bai ganta ba, dan bai taɓa kawowa ransa cewar da tsakiyar daren nan y'ar Mah zata je kicin ba, muryarsa a raunane ya ce" Shaheed Allah bata nan, wayo Allahna kirjina ya fara daukan zafi, kai ina matata kar dai aje an shigo an dauken mata"
tunanin wannan ya saka shi yin hanyar fita da mugun sauri, gaba daya bai dubi hanyar da zata kai kicin din Bama bale ya gane wani abin

Budewa ya yi da sauri bayan ya saka cod ya fito, gaba daya masu bada tsaron nan masu kwana yau suka yiwo kansa , Taj ne gaba gaba suka yi gaggawar zubar da gwuiwowinsu muryoyinsu a tare sunna furta" MALEEK"

Taj ya yi gaggawar fadin" Allah ya ja da rai...."

suka amshe da " MALEEK "

"Allah ya taimaki uban mai uba, marar ubanma ga ubansa nan!" Taj ya sake fada da karfin murya,
Tasu muryoyin suka amshe wajen sake furta" MMALEEK"

Hannu ya daga masu yana duban Taj kasa kasa ya ce" Kai dilla, ina matata"

Taj ya dago ya sake duban idannuwansa da wayar dake hannunsa da alamun bai gane tambayar ba ya dan yiwa girarakinsa alamun karin haske sannan ya furta" Na'am?"

Yusuf ya sakar masa harara ya juya dan ya ga sunna son tara masa mutane a nan shi kuwa wa bilahilazi ya zube masu baya ce masa komai a kan RAUDA

da sauri Taj ya bi bayansa zai sake tambayar bai gane bane suka jiyo motsi a kicin din cen ciki da alamun aiki ake yi a cikin

ido ya dan kura ya nufi hanyar, da sauri Taj ya ce" Allah ya taimakeka, ka bari in fara zuwa, karfe biyu da rabi fa yanzu, kuma bamu da beran daji a gidan nan, motsin kuwa ya yi yawa"

Da sauri YUSUF ya riko rigarsa ta sojawa dake jikinsa kiiiii ya juyo shi baya yana sake sakar masa harara ya ce" Kai dila, ka dakata daga cen in beran ne zan yi ihu sai ka shigo, idan matata ce a ciki fa?"
Ya karasa fada yana yin cikin, wayar nan a kunne bai kashe kiran na Shaheed ba, shi kuwa ya zauna yana sake zarro ido yana sauraron YUSUF din

A nutse ya karasa ya bude kofar kicin din, daidai RAUDA ta duka sosai tana son ciro prmpan din

"ALLAHU AKHBAR !" YUSUF ya fada da karfi

Shaheed daga cikin wayar ya furta" Beran ne!"

Taj ya taho da sauri yana fadin" Subahanallah beran ne, sir dan kauce yau ko Ni Ko shi, manya ne berayen nan na jeji tabas abinci suka biyo!"

Juyowa ya yi da sauri ya tare shi yana tura shi baya yace" Kai fita, wai ban hanna kato shigo min nan ba? haba jama'a beran uban wanene Ni, Baby ce!"

Da sauri Taj ya fice, Shaheed kuwa ya ringa hailala yana karrawa da kansa ya kashe kiran ya talabe kuncinsa yana tunanin shi kam a aminansa na kusa shi kadai ne mai jin tsoron Allah

Saman abin kicin din ya ajiye wayar yana dubanta kamar yadda take dubansa bayan ta ciro din kuma tun da guminsa da komai ta ringa saka abun yankawa tana yankowa a hankali ta kai wajen bakinta bayan ya karaso ta yi bismillah ta cira har tana lumshe ido kasa kasa ta ce" Babyn bae, yinwar ne kaima?"

YUSUF ya karaso yana kallon yadda take ci kamar bata ci komai ba, ya yi murmushi yana jin wani boyayan farin ciki a cen kasan zuciyarsa da firar da suka yi da Hajia dazu da safe, tana cewa ya kula da lamarin RAUDA ya bi ta a hankali domin ga dukkan alamu ba ita kadai bace akoy ajiya a tare da ita, kwarai maganar nan ta saka shi farin ciki kuma ya ci gaba da adu'ar Allah ya sa haka din ne, wannan yannayin da ya ganta a ciki ya saka shi jin tabas asibitin fada zai shigo gobe a dubata

"Bae, na tsorata fa, da na ga bakya nan, yinwa ce ta tasar min ke? me ya hanna ki kirawo chef ta dafa maki?"

Kai ta girgiza ta kawo bakinsa ta ce" Tst it , Tst, ka ji dadinsa kuwa?, wata irin yinwa ce ta hanna min kwonciya shi yasa na fito, kai baka jin ta?"

kai ya girgiza ya zauna yana dorata saman cinyarsa a hankali ya ce" Bana ji gaskiya, ama yanzu ina ji"

sake kawo masa bakinsa ta yi, ya kuma girgiza kai kasa kasa ya ce " Ba shi ba fa"

Tura abinta ta yi a bakinta ta cinye ta hadiye tana jin kwadayin na fada mata a nutse ta ce" To bari in dafa wani abin, me zaka ci?"

Idannuwansa da suka gama kadewa ya dora Mata cen cikin makoshi ya furta" ke..........hhhhhhhh"

ido ta rintse cike da jin kunya , shi kuwa ya saki murmushi ya mike da ita a jikinsa ya nufi Part dinta dan shi ya fi kusa idannuwansa na sake rufewa.............








Alhamdulilah 🤗😍😍😍😍😍😍

Alhamdulilah



Nd💓

nd

nd

nd



Mu hadu a sabon littafinmu mai taken *WATA TAFIYAR* Wanda mukai haɗaka Ni da kwatena, wato samira Haruna marubuciyar Badakala,
A wata tafiyar tabas akoy wata tafiyar mai ban mamaki, rikici, hargitsi, rikitaciyar soyaya, da sauransu..............................................ku tuntubemu a kan numba kamar haka 93811618 sai mun hade😍😍😍😍😍😍😍😍😍



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login