Showing 132001 words to 135000 words out of 188741 words

Chapter 45 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9831

dan walahi walahi babu shegiyar da zata rabar min miji idan ya shiga hannuna, zan ci gaba da nuna masa ban san ciwon kaina ba har ya shiga hannun nawa, a nan ne zaku san *AZAL* ta shigo maku gida

Rai bace ta ringa neman layin abokinta, abokin sharholiyarta, dan daudun nan

wayar na fara ringin ya daga a lokacin yana restaurant dinsa, domin abinci yake yi na siyarwa, da kararamba ya kama kirari yana fadin" Barka da yamaci uwar dakina, amarya kike kuma uwar gida a gidan SARKI SULTAN MALIK YUSUF DAN BELLO, ke dama matar manya ce bale kin gama tabatar mana, ci uban kannanun kwari masu rike jakar jaka dari, ke ce uwar masu gida, ke ce uwar masu kudi ke ce......."


"Habu!" Amnah ta katse shi, duda irin yadda take jin dadin yadda habu ke wasa ta, a yau sai ta ji batta bukata, ta fi son jin abinda take son ji

Da yannayin bada umarni umarni ta ce" Ka hau whatsup zan turo maka hoton wata yarinya, ama ban sani ba a yadda na dauki hoton ko zaka gane ta?, ka dai hau ka gani na dauki hoton ne ranar da ake sadakar satin mijinta dan ina son Sannin Wacece a yau yau!"

rigar dafe dafensa ya shiga kuncewa yana fadin" Yanzu kuwa"
Dan yannayin muryarta ya sa ya gane akoy wata gwarama tare da uwar dakin nasa, shi kuwa ba zai yi sanya ba dan a duniya ita fa uwarta ne gatansa, sha nawa yake karyewa, su ke tada shi a nemansa na yau da kulun,

Zama ya yi ya bude data sannan ya shiga wajen sakwaninta

bude hoton ya yi, ya shiga zooming din hoton a ransa yana ayana' in dai ta kwana ta tashi a Tsatsunburum ba zata boye min ba, kai ko a Damagaran ne makociyar Tsatsunburum da wahala ta bace min'

Zooming din hoton yake da mamakin Wacece dare dare a saman cinyar Hajia baba? Hajia wato kakar MALEEK, domin halayar Hajia babu wanda bai sani ba bako da dan gari, an san wace Hajia a fannin tsaurin halaya da kamewa da kin yin wasa da jikoki, an sani a duniya YUSUF kawai ke rikitata ya yi yadda ya so da ita, bayanshi babu wanda ya isa har baban shi

Fuskar yake kallo yana karawa
Hoton ya dauka ya turawa Nafeesa yana sake dan zarro idannuwansa da tunanin kai anya? kai a'a, ba haka bane

ya yi katari Nafeesar na online, yana tuna mata ya dana mata voice note ya ce" Wannan kamar RAUDARIYA y'ar larabawa?"

Nafeesa sai da gabanta ya fadi jin sunnan RAUDA, kawarta a da, ko tace kawar kawarta wace a yanzu bata fatan ko hanya daya su hada bale wani abin ya haษ—a su, hoton ta sake kallo, ita dai bata gane Hajiar ba, ama kuma ta san cewa lamarin RAUDA a yanzu ya fi karfin ta tunda ta koma rayuwa gidan su Ogan oganta wanda yake sarki a yanzu ta san ita dai ta sai hange
Voice note din ta danna itama ta sanar masa kwarai itace

kasancewar ya fi son ya tura mata rikakakiyar sheda sai kawai ya sake danna wani voice din yana fadin" Dubata da kyau Nafee tamu , itace wanda ta yi maki shashawar nan? dubata da kyau fa"

Nafeesa ta maida masa amsar cewar itace ko mutuwa ta yi ta dawo na zata mantata ba, dan haka ya tura mata voice din baki dayansu, a lokacin har an fara kiraye kirayen sallar magariba, ama babu wanda ya yi alamun zai tashi dan gabatar da abinda zai kwace su gobe kiyama, sai suka fi gane karasa zancen da suke gannin shi ne a gabansu a yanzu

Da yannayin mamakin jin abinda ya sake fada mata na Wacece RAUDA kamar yadda Nafeesa ta sanar masa a lokacin da ake rade radin an yi mata shashawa ya je ganewa idannuwansa tsaf ya zube mata, ya dora da fadin" Ni baban abinda ya dameni shine ganninta a jikin Hajiar sarakai, to me hakan yake nufi?"

Da wani bacin ran da kuma mamakin karfin halin Rauda Amnah ta danna masa kira, yana dagawa ta ce" Kana ji? ka tambayi kawar nan taka ta sanar maka dalilin da ya hadata da dangin mijina, ina jiranka komai dare ka ji?"

Sosai ya gane akoy baban abinda zai hada Amnah da RAUDA, dan Amnah bata cika bin didigin abu ba, idan ka shiga hanyarta ka kure bata mata rai a sawake zata saka a koya maka hankali ne, dan ta zuba makudan kudi a daukeka a baka wahala baya ce mata komai, dan haka da gagawa ya dannawa Nafeesa kira, ya ringa yi mata tambayoyin har ta dire masa aya, ayar da ta firgitashi, dan tunda akace Balarabe mai kyautar manya ya rasu, kuma dukiyarsa ya barawa matar da ya aura gaba daya dukiyarsa yake cigiya da neman Wacece, dan kuwa burinsa ya ji ko Wacece ta yadda zai je ya zama ษ—an dakinta, dan ya san idan ya samu karษ“uwa ya warke daga cutar talaucin dake damunsa, sai dai wata cutar ba dai wannan ba

Bayan ya kashe kiran ya jima yana tunanin amsar da ya dace ya sanarwa AMNAH, dan kuwa ya fi so ya fara jin musababin neman Sannin Wacece RAUDA da Amnah ke yi kafin ya san irin amsar da zai bata, saboda nasa aljihun ba dan komai ba!

A lokacin da ya yi kiranta sanar mata ya yi gashi ga Nafeesa ama tace sai an dire mata kudade zata fadi wacece RAUDA


Amnah kuwa a lokacin an zo yi mata kwaliyar be kamar yadda ta buฦ™ata, a dole ta sasauta maganarta kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata, cewa ta kula daga nan har a sadata da dakinta ta kiyaye duk wani abin da zai sa ta shiga ido ko bakin makiya, ta bari har ta je ta ga takun uban kowa kafin ta maida martani daidai da amsar kowa

A hankali ta furta" Ka ajiye min accunt numba, ama ka tabatar har tarihin uban ubanta ka jiyo min da kuma abinda ya hadata da dangin mijina ka ajiye min labarin a nan zan saurara idan halin saurarar ya kama!"

Jiki na bari ya tura mata account numbar, sannan ya fice a restaurant din ko sallar bai yi tunanin yi ba yace sai ya gama kashe wannan wutar zai yi, ya haye mashin dinsa ya nufi gidan su Nafeesa, dan samun cikakken bayani daga bakinta ya sanarwa AMNAH, dan ya san yau sai ya shaki kudin da bai taba shaka ba a zamantakewarsa da ita, tabas ya san akoy balaki kuma in sha Allah sai ya karu da wannan balakin!


Tana yin transfer na makudan kudi ta maido hankalinta kan mai kwaliyar da aka kawo mata

kwarai ta san masu kwaliyar, sun iya kwaliya sosai domin yarinyar a wajen Hajia NAJEEBA ta koyi kwaliya ta bude saloon a nan garin, sai dai ta so ace HAJIA NAJEEBAR ce da kanta ta zo yi mata kwaliyar, dan ta nuna mata a yanzu fa ba maganar da ta taba fada mata wani lokacin da dan karamin abu ya hado su, ta ce a sanar mata ba zata iya taba fuskarta dan kwaliyewa ba, kuma tace a sanar mata eh lalle kwaliya sana'arta ce, ama fa bata cika yiwa wa'inda suka tsinci kudi daga sama kwaliya ba, dan basu iya barnar kudi ba, sunna zubawa sunna tuna sabulun da zasu saka su wanke hodar ne, wanda ke cikin hajar kuwa ya shafa hoda yanzu ya wanke baya ce masa komai, sosai maganar nan ta mata zafi dan a lokacin kawai cewa ne ta yi a ce mata ko nawa ne kudin kwaliyarta ta fada mata ama so take ta zo ta yi mata har Tsatsunburum , a lokacin batama auri SHAHEED ba take iya yin nan, ta so ace itace aka turo mata yau, dan ta maida mata magana walahi, sai dai ba laifi, zata sanarwa wannan dinma dan ta tabata sako zai je inda take so ya je!


Bayan ta zauna ta cire hular dake kanta mai dauke da katon ribom din da ta makalawa gashinta tana kallon mai kwaliyar da yaranta biyu masu kama mata aikinta dan ta zo da su ne saboda Salima tace harda gyaran kai zasu yiwa Gimbiyar , dan su gama mata da wuri,
cike da isa bayan ta wani watsar da su din nan ta ce"
Azl 47
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo


DA isa ta ce" Kina da abinda zaki saka min a kai ne? ko in sa a kawo? koda yake na so ace uwar gidanki ce ta zo dan ban sani ba ko ke kin iya abinda ta iya?"

Kallonta mai gyaran ta yi tana sake maimaita "UWAR gidana?"

Amnah ta dan dage kafadu ta ce" Eh NAJEEBA"

Ido ta dan zarro tana dubanta, sai kuma ta yi murmushi kawai bata ce mata komai ba, dan kuwa wannan amsar ba zata bata ba walahi, san ta sani NAJEEBA ba sa'ar yinta bace, , a ranta kawai ta ayana' Ikon Allah, dama haka kan Amnah din nan yake? to wai isar nan da take yi na menene? koda yake haka akace halinta, dama ance yan gidansu sun ce sun fi karfin saloon dina ko me?, sai dai ki yi hakuri Ni ba zuwa na yi ki bani sadaka ba, kuma a yadda na yi aiki karkashin Hajia karya ne dan zan maka aiki ka raina Ni, ta koya mana Sannin ciwon kanmu, Hajiarmu kuwa daidai take da ke ki yi haukanki ya kai kunnan ta!!'

A bayane mai saloon tace" Muna da atach natural, in kuwa basu miki ba sai a sa a kawo "

Amnah ta dan dubeta, gannin ta bata amsa kai tsayen nan, ama bata ce komai ba ta sa suka bude atach din nasu
kwarai manya ne masu kudi ne sosai, dan haka kawai sai ta zabi wata mai kama da gashinta sak, kuma mai tsayin gaske ce ta basu dama suka shiga kimtsata


A cen wajen Habu dan daudu kuwa yana zuwa wajen Nafeesa har gidansu ya shiga, a falonsu ya zauna suka fara zancen, gannin tana zazagayewa ya bata jaka na bin jaka har ashirin , kyautar da ta bata mamaki, dan da wahala ka ga ko jaka guda ce dan daudu ya cire ya baka, sai dai bata tsaya masa kwana kwana na, da banzarta ai zata sanar masa dukkan abinda yake son ji hankali kwonce ne

Dukkan wani bayani da yake son ji sai da ta sanar masa, bata sani ba recoding dinta yake yi daya bayan daya, tun daga kan accident din iyayen RAUDA, rikon da uncle dinta ke yi mata da matarsa, sanadiyar komawarta hannun Mah, da aurenta da Balarabe da mutuwar auren ta karashe maganar tana fadin" Kamar yadda ka sani ko ka ji ana fadinta a gari hakane, mutun ce mai shegen son kudi , bata soyaya da kannanu, kai ko hulda bata yi da talaka ka yarda da ni, na yi mamaki ainun da na ji inda ta koma rayuwa, sai Ishak ke sanar min mahaifiyar sir ce ta dauketa sanadiyar accident din da suka yi shi da ita a adaidaita, duba ka ga Sa'a irin ta yarinyar nan fa? kuma lokaci guda ABDALLAH din nan ya aureta, kuma wata muguwar sa'ar mijin ya mutu ya bar mata komai? kai mu dai mu muka wahala ba soyayar ba ba neman kudin ba!"

Yana sakarwa Amnah labarin ya sake bararajewa bayan ya sauke data ya ringa jin sauran firarakin dake iya gyara shi, misali mu'amalarta da mutane da sauransu, yana ji a jikinsa shiga FADAR TSATSUNBURUM ta kama shi koda a matsayin dan aiki ne dan shima ya samu nasa rabon, kuma ya karra yarda akoy wani abin da ya hadata da Amnah, wanda yake son sani , kuma ya san AMNAH zata fada masa ne da kanta, zai dai je ya daki cikinta cikin hikima har ta zayane masa komai ba tare da ya sha wahala ba, 'Hum, ina tsoron wannan karron uwar dakina ta janyo abinda yake iya rinjayar hannayanta ko ya makata da kas, domin idan dai takamar ta kudi ce bana tunanin mai yinta da na wani da mai yinta da nasa su zo daya, dan kuwa malan bahaushe yace da namu gwonda nawa, ba za'a taba hada mai yi da na iyayenta da mai yi da nata ba gaskiya!' Shine abinda ya yi ta ayanawa a ransa

.....................................................


Abincin take zubawa a plate plate da miyar zabin da ta yi,

Har yanzu jikar girarta bata bushe ba, dan tana gama daidaita miyar ta shige dakinta ta yi wanka ta cenza tufafi zuwa sket da riga na atampa ta saka hijabi ta yi sallah sannan ta cire ta yafo mayafi dan madaidaici ta dawo falon dan idasa aikinta, domin tunda suka dawo Salima ta sanar mata Mah tace a karra yawan miya saboda bakin da zasu raka Amnah dakinta


A hankali take aikin , Salima kuwa na dauka tana kaiwa bakin dake cen karamin falo da kuma daki wajen yan kwaliya, wa'inda ke aikinsu ka'in da na'in

Tana gama zuzubawa ta juyo dan duba agogo saboda maganin Mah da kuma lipton dinta na dare da take sha, sai ta ga Mah din tsaye a kofar shigowa ta harde hannayenta tana kallonta

Murmushi ta kakaro tana dan buda idannuwanta ta ce" Lah, Mah tun yaushe kike tsaye a nan? ban fa ganki ba"

Mah ta idasa shigowa tana murmushi, a ฦ™alla ta kai minti biyar a tsaye a wajen nan, ama RAUDA bata san ta zo wajen ba, ta afka tunani ne ko aiki ne ya mata yawa?, dan haka da kula ta ce" Na jima a tsaye fa baby, ki je ki huta aiki yau ya maki yawa, je ki yi sallar isha'i ki huta kin ji?"

Murmushi ta yi ta karasa ta dauki abin dafa lipton din Mah, ta je ta bude wajen kayan shayin ta harhada dukkan abubuwan bukata, dan shayin ba wai Mah din kadai bace ke sha, harda MALEEK, tana juyowa Mah ta ce" Lah rage kayan nan, yau ki dafa iya nawa, shi da za'a mika masa matarsa yau ai zata dafa masa abinsa ya sha ko? ko aure zan masa in ci gaba da bashi tuwo?"
Mah ta karashe zancen tana sakin murmushi, RAUDA kuwa sai ta tsaya cak tana kallon Mah din har sai da Allah ya sa ta tuna tsayuwa ne ta yi sannan ta juya da sauri tana lumshe idannuwanta ta koma wajen abin shayin ta bude ta ringa rage kayan, inda Mah ta bita da kallo tana kausasa idannuwanta kafin ta girgiza kanta ta juya ta fice a ranta tana ayana' Lalle zaku san kun yi da mamanku, daga ke har shi mararsa wayo kawai!'


RAUDA kuwa kayan shayin ta rage ta koma wajen abin ruwan nan ta wanke su tas ta zuba ruwa ta dora sannan ta ja ta tsaya a hankali ta rungume hannunta a kirjinta, tana jin ranta na tafarfasa

sam bata san har ya dahu ba, sai da kukan butar ta sakata juyawa da sauri ta mika hannu ta kashe gaz din sannan ta dauko abin juyewa ta juye komai ta juya da su ta fito a nutse ta nufi dakin Mah ta kai mata shayin da kuma maganinta

Maganin ta tsaya sai da Mah ya sha sannan ta ajiye sauran ta nufi dakinta ta shige ta rufe da ky

Tana rufewa ta ja ta tsaya kanta na sarawa , idannuwanta na yi mata nauyi, kirjinta kuwa na yi mata zafi

A hankali ta karasa wajen madubin dakin ta ja ta tsaya ta tsurawa fuskarta ido

dan kwalin kanta ta cire a hankali ta ajiye gaban madubin sannan ta saka hannu ta cire ribom din kanta dan siriri fari shima ta ajiye kafin ta zubawa fuskar tata ido

Hawayen da idannuwanta suka tara take bi da kallo, zuciyarta ba tsintsinkewa da wani fitinanen tashin hankali

Ta sha tsayuwa ta dubu kanta tace da kanta RAUDA kin ji kunya, RAUDA kin saka kanki a uku tunda kika ce wannan rayuwar zaki yi, me kike nufi RAUDA? Yaushe mijinki ya rasu, abin kaunarki, wanda ya nuna maki so da gata tunda ransa sannan ya rasu ya kuma Bara maki wani lasisin so da gatan a duniya wanda koda yau kika rasa mai kama hannayenki da izinin Allah ba zaki tagayara ba in dai kin kiyaye dokokin Allah, sai dai kashh, tun kafin a shafe shekara ke RAUDA shine kike tunanin wani abin da ba zai taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login