Showing 42001 words to 45000 words out of 188741 words

Chapter 15 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9823

motar a tsakiya yana tukin a hankali su kuwa sunna biye da motar da gudu da kaffafuwansu har wajen get din gidan wanda aka yi shi tamkar garun gidan, dan in dai ba Sannin wajen ka yi ba ba zaka taba gane ga get din nan ba, domin a saje yake sosai da gidan kuma tsayin kofar a hade take da wani abu da aka saka da cen kasa ya hade da kasa, babu yar hudar da zata shaida maka ga wajen da zaka bude ka shiga sai masu tsaronta da suka san cikinta da wajenta

Da gagawa wasun dake kofar suka bude kofar wadinnan na ja gabar tafiyar, sunna shiga wasu hudun ne suka sake raba motar biyu gaba biyu baya ya zamo hudu gaba hudu baya , shi dai yana tuki a hankali ne, mahaifiyarsa kuwa kana kallonta hankalinta a tashe yake, dan ta san me hakan yake nufi ganninsu a wannan waje a irin wannan lokacin

Sunna tsayawa sojan daya ya bude masa motar ya sauko , lokaci daya suka saka gwuiwarsu daya a kasa dayar a dan dage suka dora hannayensu na hagu da dayar suka cire hulunan da suka yiwa fuskarsu katanga da gane su waye su sannan suka shiga masa sannu da zuwa hadi da gabatar da kansu daya bayan daya da kiransa da sunna *SARKI*

abinda ya tsaya gani daya ne, gabatar da kan nasu da zasu yi, sunna gamawa ya bude bayan ya mikawa mahaifiyarsa hannu yana kallonta a nutse ya ce" Mah sauko"

Mah ta sake zuba masa ido, a saman lebenta ta ce" Me yake faruwa ne?"

Da idannuwansa ya mata alamun bai sani ba, dan haka a dole ta kamo Rauda wace take ta kale kalen kowa da mamakin toh, ikon Allah, wannan mutumen kuwa wai wanene shi?

Rauda na fitowa sai ta ji tsoro ya fara kamata, saboda tana fitowa sai ta ga mutanen dake duduken nan kamar ba mutane ba? Gashi jikinsu gaba daya shigar baki ne, ga bindigogi a jikin nasu kamar wa'inda zasu je yaki? Da sauri ta dauke kanta daga bin su da kallo tana bin mama da ta rike hannunta sunna biye da ɗan maman har suka karasa kofar inda zasu shiga ya saka cod dinsa suka shiga Mama ta kaita cikin wani daki wanda Rauda ta kasa zama saman katifar dakin dan har ga Allah tsoro take ji da tunanin arzikin mutanen

Da sauri Mama ta dawo inda yake ta zauna tana fadin" YUSUF me yake faruwa a cen fadar?"

YUSUF dake son ya dauki hankalinta ya fice ya ce" Mama ban sani ba, an ce dai mu zo nan, Ni yanzu yinwa nake ji mama sosai fa"

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta mike tana fadin" Bari in je kicin din naku, akoy komai ko?"

Kai ya gyada mata yana sakar mata murmushi yana kallonta har ta shige ciki

Wayarsa ya ciro ya ajiye nan da duk wani abinda ke cikin aljihunsa sannan ya juya da sauri ya fice

Yana fitowa ya samu baban mai ba gidan tsaro ya mika masa hannu

Baya ya ja kadan yana kallonsa da girmamawa ya ce" Sarki ina zaka je?"

Fuska ya hade sosai ya ce" Ka aike Ni ne? Bani ky!"

A dole ya bashi ky din daya daga cikin baburansu sannan ya bi bayan shi da gudu, dan walahi ba zai barshi ya je cikin gari shi daya ba, zai bi shi ne har inda zai je ko su mutu tare ko su yi rai tare, shi ya yarda ana neman ran bawan Allahn nan lokaci zuwa lokaci dan tare aka harbe su da bulet , ama shi sai kasada, sam baya ji idan aka ce ya yi biyayya kuwa kamar an ce baude!

Hanya suka dauka ta cikin jeji sunna keketawa da gudun gaske, bayan ya bar masu wasiyyar kar su saki su yarda a shiga a tarda mahaifiyarsa, in sha Allah zai dawo , koda shi bai dawo ba mahaifinsa zai dawo ko kuma RISLAN, domin ukun nan su kadai suke da damar shiga gidan nan bayan shi

Mah na fitowa dauke da plate wanda ta soya masa kwai kafin girkinta ya kare tana fadin" Yusuf wai yanzu baka da hakurin yinwa k.........?
Idannuwanta suka sauka saman kujerar da ya tashi da wayarsa da sauran abubuwasa nan zube

Da karfi ta ce" YUSUF! YUSUF!" Lokaci daya tana zubar da abinda ke hannunta ta saki plate din na kwalba ya fadi kasa,
Kararsa da ihun muryarta ya saka Rauda fitowa da gudu tana zarro ido ta zuba mata ido tana kallonta

A lokacin Mah ta je tana ta duduba shi bata ganshi ba, hakan ya bata tabbacin lalle Yusuf ya fita sai kawai ta nemi fita a hayacinta tana ta faman son saka cod dinsa a wayarsa ama ta kasa


Da sauri Rauda ta karaso tana kallonta, jiki ba karfi da kuma tashin hankalin menene wannan din kuma ta ce" Hajia, lafiya?"

Mah ta kalli Rauda ta sauri dan har ta fara manta tare suke tsabar tashin hankali

Da sauri ta mika mata wayar tana fadin" Dan Allah, cire min cod ki saka min numbobin nan da zan fada maki ki min kiransu, dan Allah yata"

Wayar ta amsa tana kallon yannayin Mah,
A hankali ya kamma hannun na Mah ta zaunar da ita saman kujera tana kallonta a sanyaye ta ce" Mama, ki yi hakuri, ki fada min numbar na bude maki, ama ki yi hakuri ko menene kin ji?"

Mah dai so take kawai ta bude mata ta kira mata numbar, dan haka ta shiga fada mata cod dinsa har ta cire mata sannan ta shiga fada mata numbar Honorable

Tana fara rubuta numbar sunnan ya nuna kansa da sunnan *UBANA* , ta karanta sunnan ta karra sannan ta danna kiran ta mikawa Mama ta zauna tana kallonta, dan sai ta ji anya kuwa zata iya tafiya ta barta a wannan yannayin?

Wayar ba fara ringin ya daga, muryarsa wata iri a sanyaye sosai ya ce" Yusuf kun karasa wajen?"

Muryarta na rawa ta ce" Aban YUSUF, Yusuf din baya nan ai, ban san ina ya je ba, gashi ya kawo mu gidan nan na jeji kuma ya fita, ya bar min wayarsa harda su katinsa na shedar dan kasa, ina ya je? Me yake faruwa a fadar dan girman Allah? Ka fada min walahi zuciyata bugawa zata yi"

Rauda ta kawar da kanta dan bata so ta maida hankali kan maganar Maman, ama kuma haka kawai ta samu kanta da maimaita FADA a cikin zuciyarta

"ya Salam, ya Salam, ya Salam" Honorable ya fada yana mikewa ya fice daga cikin mutane ya nufi cen bangaren matansa dan ba kowa a irin wannan lokacin , kowa yana ɓangaren Hajia tare da marar lafiyar

Yana zuwa ya sake rage muryarsa sosai ya ce" Sai fa da na fada masa ,kar ya saki ya fito, Allah kadai ya san gawar fari cikin mu da sarki da shi Yusuf, ama Hajia na gannin jikin sarki ta rikice ta ce in sanar da Yusuf in yana ina ya je gidan nan ya zauna har sai Allah ya yi yadda ya yi ji sarki ya mike ko akasinsa sai ta bada umarnin Yusuf ya fito zai fito, shine ya fito?"

A rikice Mah ta ce" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, me yake damun Sarkin? Me yasa baka fada min ba Ni ai da ka san na rike Yusuf duk abinsa ba zai fita ba ko? Wayo na shiga uku yanzu yaya zan yi?"

Shi dinma hankalin nasa a tashen yake ya ce" kin ga ki kwontar da hankalin ki, in sha Allah ba komai, wai sarki bashi da lafiya tun shekaran jiya yake cikin gudawa da amai matan suka rufe suka ki fada min, sai da Hajia ta matsa kan ko ina yake a kira mata shi ne amaryarsa ta zo a sace ta fada mata walahi bashi da lafiya bakina san wanda yake kansa ba, Hajia baba ta hanna a sanarwa kowa sai magani ake didika masa a boye wai ko zai tashi ya zamto sai sun wanke shi sun cenza masa tufafi dan baya jin fitar gudawar daga jikinsa, shine fa Hajia ta yi kirana ta sanar min, da na zo ban nemi kowa ba na je bangaren nasa na bude na shiga da karfi dan kiri kiri Hajia baba ta nunan yana hutawa baya so a dame shi, da na shiga na tarda shi yana cikin wani hali, dan ko gudawar yanzu ba abinda ke fita sai ruwa tsululu, karshema malamai ne kansa ana ta addu'a, na yi na yi a je asibiti kowa ya wani nuna min wai me za'a kai"

Wani irin Gwauron numfashi Mah ta sauke kirjinta na dokawa
Ta rasa me zata ce,
Ya Salam wannan lamari na tsoratata yana kuma daga mata hankali
A me aka ɗauki sarauta ne?
Me suka dauki duniya ne?

A sanyaye hawaye na bale mata ta ce" Ai ba Yusuf ne abin a boye ba, kai ka san in dai abinda Hajia take nufi ne kaine abin a boye ba YUSUF dina ba, su cire Yusuf a duk wani abinda suke tunani, su fida d'ana daga rikicinsu, Aban Yusuf ka san ba zai taba yarda ya zauna kai kana cen din ba ko? Dan Allah ka fito Ku zo"

"Kar ki daga hankalinki, bari yanzu in fita in gani zan ganshi na dawo da shi, Ni sam bana son fitinar nan ta gidanmu, gashi dare ya yi ama kowa sai wani irin abu yake yi, kar ki daga min hankalinki dan Allah, gan.............."

"Yaya, ka fa zo, Hajia na kira" AISHA TA fada sama sama sannan ta juya da sauri ta koma

A dole ya katse kiran yana karra tabatarwa maman Yusuf cewar gayanan zuwa, kar ta daga hankalinta plz

A lokacin da ya shigo falon Hajia, inda sarki ke kwonce, matansa na nan a dole a irin wannan lokacin, da baban malamin masallacin gidan na zaune daf da shi sosai yana maimaita kalmar shahada, hakan ya sa gabansa ya yanke ya fadi kansa ya sara da sauri ya kai dubansa wajen Hajia inda take zaune kanta a kasa da carbinta tana ja idannuwanta a rintse tana ta ambaton sunnan Allah, dan a irin wannan lokacin ko waye kai dole zaka ji tsoron wanda ya isa ya busa kuma ya janye numfashin bawa, domin kakari na fitar rai shine ya cika falon, duk irin musun da uwar gidansa ke yi bakinta ya mutu ta kafe shi da kallo ta gaza furta koda a, sauran dake zaune kuwa an umarce su su masa addu'a ko su fita dan ba'a bukatar kowa ya daga murya a wajen

Sosai kirjinsa ke dokawa ya karaso da sauri ya duka ya rike hannun dan uwansa, wanda ya zamo tamkar ya dafa wani abu marar kasashi, kamar ba tsokar naman mutun ba mai dauke da kasusuwa da nama da jini, a hankali ya amshi hailalar da ake ta maimaita masa idannuwansa na kallon wajen da ya zarce tsayuwar dan Adam, sannu a hankali har yannayin dan rike hannun dan uwansa da ya yi ya saka baki daya hannunsa ya yi nauyi a hannun mahaifin Yusuf

Jiki ba laka ya sake damke hannun, wasu irin hawaye suka taru a cikin idannuwansa suka shiga zubowa a hankali saman kuncinsa ya gaza dagowa kunnayensa na jiyo masa furucin malan na sanar da sako mafi dukan zuciyar mahaifiya, Mata, ya'ya, yan uwa, dangi, da jama'ar gari baki daya, cewa RAI YA YI HALINSA

Kukan matan ne ya nemi hargitsa masa kwakwaluwa ya ringa jin tamkar ciwon shanyewar barin jiki zai kama shi, a birkice ya dago dubansa yana jin duhu zai mamaye shi, jiki ba karfi ya kama da kyar ya mike ama ina, abin ya zo masa kai tsaye kuma a irin lokacin da bai shirya ko tsamaci haka ba, duk da ita dama MUTUWA takenta kennan, bata zuwa a lokacin da ake tsumayinta dukda babu bawan dake zama yace zo na shirya sai wanda yake cikin halin yau i yau!, Mutuwa dai wannan mai tonon asiri a yau ta dauka, ta katse jin dadin Dubai zata nada na dubai, ta katse shan wahalar Dubai zata dora ta Dubai, mutuwa mai yanke dukan wani farin ciki ko nau'in wahala, a daidai lokacin da ya yi baya zai zube A'isha ta mike ta zuba masa ido abinda ke zuciyarta na zuciyarta, mahaifiyarta ta yi ta yi ta tashi dan ta agaji wanda take yiwa kallon shi ya rage a matsayin wanda zai hau kujerar dan uwansa ko salon kidan ya cenza domin idan har babu ɗaya tsayaye sarauta zata koma hannun kannin riga ana ji ana gani, a lokacin ne kuma Yusuf ya karaso jiki ba laka dan tun a kofa kunnayensa suke jiyo masa hargitsewar da masarautar ta dauka , a dole ya karaso yana jin gaba daya komai ya fice masa a rai, hankalinsa ya tashi, tashin hankali kala kala ya ziyarce shi, ciki harda tunanin mahaifinsa da abinda ke iya damun uban nasa

Da sauri ya karasa wajen da liman ya kama mahaifinsa yana masa sannu da nasiha irin wace ake yiwa wanda ya yi rashi ya zaunar da shi daf da mamacin wanda aka rufawa zanin gado sabo dal aka kuma tsawatarwa matan dake kuka kamar zasu tada dakin da hayaniyar kukansu

A hankali ya kai hwuiwoyinsa kasa, ya kama hannayen mahaifinsa ya zuba masa ido, a tausashe sosai ya ce" KA yi hakuri Abu, kar ka daga min hankali fiye da halin da nake ciki a yanzu dan Allah"

dumin hannunsa dake shiga cikin nasa ya saka shi jimke hannun da karfi sosai hawayensa na ci gaba da zuba tamkar an bude pampo

Hajia ta share hawaye a sanyaye bayan ta gama waya da asibiti ta dubi wajen da su YUSUF suke a tausashe ta ce" Ku ne alwalinsa, kunne ja gabarsa, Allah ya masa rahama, ku yi masa shinfida mai kyau, yanzu za'a zo a bashi kulawar da ta dace sai a kwana ana masa sauka, Allah ya jikan ka uban talakawa...."
Ta karshe muryarta na rawa sosai wani hawayen na sake bale mata, da kyar ta sake sharewa tana kallon Aban Yusuf da ya karaso da taimakawar Yusuf ya duka a gabanta ya kama hannayenta, kwarai shi ya dan irin radadin da take ji, shi ya san Wacece ita, tun sunna yara sukan yi mamakin jarumcinta, ama mahaifinsu ya taba fada masu, tsarin Sarautar garinsu dole sai da jajirtaciyar mace irinta, dan kuwa a gobe gobe da safe da zarar an birne mamacin za'a naɗa wani sarkin a ci gaba da zaman amsar gaisuwa, abinda zai zamo rikici na mamaki idan har akoy masu harin kujerar, kujera kuwa tabas akoy masu harinta na wajen gida da na cikin gida

A sanyaye ya ce" Ba zaki yi kuka sosai ba? Bana so abubuwa na dira maki a zuciya Hajia"

Ajiyar zuciya Hajia ta sauke mai karfi tana kallonsa a sanyaye ta ce" Idan na fashe da kuka zai dawo min ne?, yaya zan yi? Aban Yusuf na rasa uwa, uba, miji, yanzu kuma yau na rasa baban d'a, tabas mutuwa tawa ce ban dandana ba, Allah ya musu rahama ya bamu kyakkyawan karshe"

Yusuf dake kallon mahaifinsa a tausashe ya zuba mata ido yana kallonta
Tabas bata taɓa maganar da ta shiga zuciyarsa irin ta yau ba

Kansa ya dauke yana kallo likitoci suka shigo bisa jagorar A'isha, aka dora mamacin aka fice da shi bangaren da za'a kimtsa shi a cen din ne kuma za'a masa addu'a har garin Allah ya waye

Sai da aka fita da shi Hajia ta riko hannun mahaifin Yusuf tana kallonsa ta ce" BELLO, ka san me yake jiranka, sai da na hanna fitowar YUSUF, ama ya fito, ka ja shi ku koma gidan nan, sai na neme ku"

Wannan karon YUSUF din ne ya dubeta da kula , sannan ba da daga murya ba ya ce" Inaga ya dace ku mayar da maganar buya gefe, dan babu inda zan je ko ya je ga gawa kwonce, duk mai so ya zo ya gwada abinda ya fi iyawa, Allah ne mai komai, idan har Allah ya ƙaddara tare za'a birni gawarwakinmu a gobe buya ba zai hannamu mutuwa ba hajia "

Hajia ta zuba masa ido, zuciyarta na dokawa sosai, tana hangen abinda mijinta ya fada a kan yaron da bai ga girmansa ba bai san waye shi ba, ya Allah, ya Allah

A tausashe ya sake kama mahaifinsa ya mikkar ya rike shi sosai suka fita ya nufi bangarensa da shi, dan yana so ya fara samun nutsuwa kafin ya je a kwana wajen dan uwansa,

Yana fitowa A'isha ta dawo da sauri ta shige ciki wajen Hajia, yaronsa kuwa da sauri ya zo ya talaba masa mahaifinsa suka kama Abu sosai suka fice da shi ba Dar ko tsoron wani ya nufo shi


A'isha na shiga ta karasa wajen mahaifiyarta, a daidai lokacin Hajia ta sada kai ne hawaye sun tarun mata a cikin idannuwa sosai tana ta jan carbi tana godiya ga Allah da jarabawar da ta sameta , ta rasa yaronta Bama zata iya tashi ba bale ta je inda gawarsa take, sai dai dadin musulunci addu'a na tarda bawa a duk inda yake

Da sauri ta dago jin an zauna daf da ita ta zuba idannuwanta cikin na A'isha

A'isha ta dan ja numfashi tana kallonta ta ce" Hajia, waye zai fara shiga kabarin marigayi?"

Da mamaki sosai Hajia ta zuba mata ido, da yannayin muryarta da ta fara raunana saboda kukan dake cin zuciyarta ta ce" Dama akoy wanda zai fara shiga sama da BELLO da YUSUF ne?"

Da sauri da kuma mamaki ta zubawa mahaifiyar Tata ido, muryarta ta kasa boye mamakin ta ta ce" BELLO? Bellon da ya fada cewar baya ra'ayin sarauta Hajia?"

Wannan karon hawayen dake cikin idannuwan Hajia sun samu zubowa, ta saka bayan hannunta ta share tana kallonta ta ce" Fadarsa ce, ra'ayi ne na jin dadin harshe ya fada, kuma koda baya nan inace kin san ya haihu, domin ja gabar garina kin san ko wanene ko?"

A'isha ta kasa daidaita tsuguninta saboda kaffafuwanta da suke son neman fitinarta sakamakon tashin hankalin dake son damunta na amsar da ta san me ake nufi da ita wace da wahala idan har ba zata iya yin fito na fito da dangi a kan wannan ba, sai dai da kula sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login