Showing 180001 words to 183000 words out of 188741 words

Chapter 61 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9828

yan kaso

Da sauri ya nufi wajen, dan bata tunanin zata iya jiran dawowarsa ko ina zai je

"Sir, Sir" Ta fada da dan karfi, Da sauri Taj ya yi baya ya tsaya , shi kuwa ya ja ya tsaya har ta karaso

jikinta na rawa ta shiga fada masa lalle lalle zata je gidansu ba lafiya kuma ya taimaka mata ya tura wani a yiwa samarin anguwarsu tsawa sunna son kawo raini gidansu

Ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta, a tausashe ya ce" Amnah, ki nutsu, ki fuskanci komai a nutse yadda ba zai ji maki wani ilar ba, babu wanda zai shiga gidanku ba za'a bari kowa ya tarda mahaifiyarki ba, ki kula, idan kika dauki abin ta wata fuskar tabas zaki lalata goma biyarma bata gyaru ba, baban abu ne ya tunkaro ki, in kika yi wasa da ganganci zai cin maki, maganar laya gaskiya ne ta aikata, za'a gurfanar da ita, idan kin san kina ciki ki shirya dan babu wanda zan kyale , Amnah ki nutsu kar ki janyowa kanki idannuwa a lokacin da kurarki zata yi kuka, ki guji baki, shine kawai abinda zan iya fada maki"

Daga nan ya juya ya fita Taj ya maro kofar ya saka mata sakata

A tsaye take a daskare tamkar ta summa, da kyar ta iya tuna abinda ya fada ta maimaitawa kanta, hakan ya sa a rikice ta zarro ido ta kama kofar ta ja ta ja ta kasa budewa

da gudu ta juya ta nufi dayar kofar itama ta kama ta ja ta ja ta gaza budewa, ashe nan din ya fara bada umarnin a garkame kafin inda ya bi,

A haukace ta zube ta tartsatsa wani irin ihun da ya sa RAUDA mikewa a zabure ta nufo falon tana ajiye wayarta da suke yi ita da ATU tana sanar mata zuwan Mama hudu tana sake yi mata magiyar dan Allah ta yi mata hanyar da zata ga RAUDA din, mama ciwo ya cita ya gama cinyewa, bata da lafiya kuma tace wai a asibiti ance ba'a ga komai ba, gidan haya an koresu saboda a bayane Salaha ke kawo maza tana lalatarta, karshe salahar yanzu bata san ina ta shiga ba, ita kuma sai dai ta kwana a inda dare ya kamata idan safiya ta yi ta ci gaba da bata, aikin aikatau ya gagareta samu duk inda taje kyankyaminta ake yi ana yi mata korar kare, harda wajen da aka yi mata lakabin marainiya daga zuwa neman taimako, wannan lamari na shiga kunnenta a kwoncen nan ne ta ji ihun nan na RAUDA

Da sauri ta karaso tana kallonta , da kula ta shiga kokarin kamata tana fadin" Subahanallah, lafiya? menene? ke? menene?"

RAUDA ta kasa daina ihu da burgima, a bayane kuwa fadi take yi "


azl65


*MAGANIN KARA KIBA 3IN1*

*Ina meneman kiba ido rufe Kuma tanason maganine ingantacce Wanda baida illah kokadan to tazo gadama tasamu yar uwa indai kibace da gyaran nono dakara hips toga Mganinmu nan 3in1 cikin kwana 7 kacal👌🏻 zakiga yadda Zaki fara murmurewa insha Allah mungwada mungani munbayar angwada munsayar angode insha Allah kawata Zaki godemin da 3500 dinki kinhuta da gorin rashin kiba munan cikin Gombe Kuma munatura kaya ko ina kedai tuntumebi ta Whatsapp ko kikirani Kai tsaye ta 08030861857 sai kunzo🥰*

*MAGANIN HIPS*
*Wannan Maganin anyisane tamasu neman hips sunsha wannan sunsha wannan to gatamunan insha Allah guarantee nakebaki hajiya inada yakini akanta matsala indai tarashin hips ne to anwuce gun 3500 kacal kinhuta kijuya kiwarwasa kisaka kayan gayu kijuyawa Oga yayikallo kawata har yanga saikinmasa ninafadamiki wannan nemeni kisamu naki 08030861857*

*MAGANIN NONO*
*Itama akwaita me inganci kamarta 3in1 data hips wasu suna korafi nifa nono kawai nakeso yaciko yayi bulbul gwanin sha'awa yadda Oga zaiyaba nasa breast cup suzauna das Amman abun yacitura Nasha Nasha magungunan Amman haryau ba chanji to ganamu Nan yakine ne Dani akansa ba Dan kadanba alhamdullahi duk Wanda yasaya saidai godiyace tsakaninmu kema zokigwada Kuma kigodemin location Gombe 08030861857*

A rikice take fadin" Na shiga uku, na shiga uku, wayo Allahna waye ya fada masa, wayo na shiga uku waye ya fada masa? kar dai saboda wannan abin a kashe min aure, kar a hadani da mijina a rabani da gidana, sun rufe sun hannani fita gashi ina kiran maman dan in fada mata bana samu, wayo Allahna!"

Ihu take yi tun karfinta da kuka, du yadda RAUDA ta so kamata ta gaza, hankalinta ya tashi ainun, domin abinda Amnah ke yi ba wai abin wasa bane, dole mutun zai tausaya mata,

Da sauri ta je dakinta ta dauki wayarta ta shiga ta nemi layinsa dan ya mata salamar ya fita ta waya, ta shiga bugawa, ama ba'a dagawa, a dole ta nemi layin Mah dan har yanzu ihun Amnah bai rage ba, tamkar wace aka cewa iyayenta sun rasu? subahanallah hankali tashe ta shiga sanarwa Mah abinda ake ciki

Mah dinma muryarta a dan birkice ta ce" Baby, ki zauna a dakinki za'a zo a rako ki, itama za'a kawota kar ki damu ba komai bane in sha Allah"

Mintunna ƙalilan Jakadiya baba ta zo ta baya aka bude mata bisa umarnin Mah ita da wasu ma'aikatan bangaren Hajia baba suka tafi da Amnah dake cikin halin fitar hayaci, domin ta daga kiran yayarta ta sake daga mata hankali itama ta sanar mata abinda yake faruwa ta dora da fada mata wace gawa ce Mamansu ta sakawa magani?, har abin ya zo kunnen MALEEK?, baban tsoronta da firgicinta Sannin waye MALEEK, domin koda basu zauna zaman aure na mata da miji normal ba ta ji waye shi ji na gasken gaske ba jin hasashe ba, kuma ta ga wasu aiyukan a aikace, itafa tunda aka fada mata marisha babu irin haukan da bata yi ba a kan MALEEK tun yana matashin dan kasuwa ta ji ta sake riƙe shi a zuciyarta, domin marisha din nan babar mai kudi ce dake zaune a baban birnin Nijar wace ke cikin gwamnati kuma take tare da manyan kasa, wace ta san ta dame babansu ta shanye a kudi bale wai su, ta ji lalle ta kai , tunda yau za'a dubeta ace itace matarsa?, idan har aka rabata da shi bata tunanin in zata iya rayuwa, ta sanarwa yayarta ko me Mamansu ke yi na asiri sai ta fada sannan ta nemi ita a cireta a cikin rikicin nan dan walahi ba zata yi saken rasa MALEEK ba!

Ita din suka fara kaiwa, sannan suka dawo Jakadiya ta raka RAUDA har wajen Mah dake daya daga cikin dakunan bangaren Hajia tana kwonce dan saboda yannayin jikinta

Amnah kuwa a dakin Hajia aka sauketa, cikin ikon Allah tun kafin Hajia ta nemi Sannin wani dogon bayani a wajenta ta ringa tona mata sirin mahaifiyarta har sai da abin ya gigita Hajia, domin bata taba tunanin rayuwa na iya kasancewa haka ba, a dole ya nemi sheda a kusanta da kuma wanda zai zamo wanda zai yi magana da Amnah, dan ita yarinyar ta fara bata tsoro, irinsune ke shiga haukan karfi da yaji idan suka rasa wani abin da suke so, shi yasa ta fito ta yi jiran zuwan Bah wanda ya baro wani rikicin a babar fada da ake tafkawa da jama'ar gari kan a basu mahaifiyar Rauda su konata da ranta, domin irinsu barin su a doron kasa tamkar busa guba ne a cikin iska, sai dai du abinsu basu iya shiga baban dakin taron da ake ta dauki ba dadi da mahaifin Amnah wanda ya summe tunda aka kona layar da aka ciro du ta yi hijoji cikin tsuma ya kai biyar, sai dai layar na nan bata lalace ba, shi yasa baban malamin masallacin Masarautar ya sa aka hada garwashi yana ta adu'a ya kona layar da hannayensa, sai ga mahaifin Amnah dake rikicin karya ake yiwa matarsa shari ne ya fadi kasa sumame , da kyar aka samu numfashinsa ya dawo jikinsa, sai dai yana ta wasu irin abubuwa kafin a samu ya yi wani irin tashin da aka hanna shi mikewa tsaye cirr bisa umarnin malan, ana ta masa karatu, malamai zagaye da shi, YUSUF na zaune saman kujerarsa ta mulki, sojawan da suka kamo su maman Amnah na zazaune kowa yana jiran wannan abin da akace a fara warwarewa kafin a hau shara'ar

Cikin ikon Allah ya dawo hayacinsa, cikin wani irin yannayi ya ringa bin mutanen wajen da kallo, hankalinsa na neman sake dugunzuma ya tashi, du kamar wanda bai sansu ba bai taba Sannin kowa ba, bakinsa na buduwa a rikice mahaifiyarsa ya fara tambaya sai matarsa auwar gidansa
Tun da mahaifiyar Amnah ta ga haka ta nemi zubewa, aka nuna mata ba dama domin kiri kiri ana nuna mata ko gawarta ta shiga uku bale ita, a dole ta ringa rusa kuka a zaune hannayenta saman kanta tana fadin ta shiga uku, karshe dogari ya tsawatar mata cewar ta masu shiru a gaba dai zata shiga ukun


Tun daga lokacin tone tonen abubuwan da ta aikata suke bayyana a hankali har zuwa kan maganar ya'yan da ta haifa da shi su biyu yan mata, ta tabatar da ba nasa bane na abokinsa ne, wanda hakan ya sake rikita mutanen wajen da tashin hankali da Allah wadai da suke yiwa abokin nasa, shi kuwa zuwa lokacin ba baka sai ido, domin abin ya gama tsoratar da shi, ya zamo harta dukiyar da ta janyo masa kuda tamkar sun ga zuma ta shiga bashi tsoro hannayensa cikin na Mahaifiyarsa, matarsa uwar gidansa a gefensa zuciyarsa na karra karyewa irin yadda shi mutun mai zumunci, mai kiyaye dokokin Allah da hidimtawa addinin musulunci ya samo shi ba kafuri ba shi ba Musulmi ba yana rayuwa da makiyansa a gefensa, su basu kashe shi ba, su basu barshi ya rayu ba

hukunci aka yanke masu mai tsanani ita da abokin aikata masha'ar Tata, da kyar polisawa da dogarai suka tare mutane aka samu aka fita da su aka tafi da su , hakan ya sa rikici sake balewa sunna nuna a basu su su koyawa masu irin halayarsu hankali, sai da MALEEK ya fito da kansa ya yi tsayuwar sarki a gaban su, tsayuwar ja gaba a gaban su, tsayuwar malamin su, tsayuwar uban gidansu idan fannin a fito na fito din, sannan tsayuwar aboki a gaban su, cikin Yaren da zasu fi ganewa na nasiha da kuma tsauri ya tsawatar sannan ya bada umarnin a yi hakuri a koma gida, mai aikin yi ya koma bakin aikinsa, hukunci ba a hannayensu yake ba, an riga da an yanke masu hukuncin da sarki yake da ikon yankewa, sauran zancen yana kotu domin iyayen marigayiyar idan sun daukaka kara sai a je a kalli Shari'a, sannan ya rufe taron da kakausan kashedi da alkawarin yankewa duk wani wanda ya taka doka hukunci in dai a cikin garin TSATSUNBURUM yake!

Dan karamin hauka Amnah ta tadawa su Bah bayan duk irin nasihar da ya yi mata da tausarta da nuna mata irin kular da za'a basu ita da yayarta da kuma inda za'a tura su rayuwa duk dan ya tabatar mata a yanzu ba zata kuma amsa sunnan mata a wajen MALEEK ba, sai dai ta yi hakuri Allah ya bata malamuncinta tabas su zasu daura mata aure idan wani ya fito mata

Da kyar suka samu abin ya koma rizgar kuka kawai da cimuimuyar hijab da tarin tashin hankali marar misaltawa a lokacin da ta samu yayarta itama ba yadda take suka ji tamkar ace basa raye a duniya da wannan tashin hankali, gashi sunna ji sunna gani a cikin gidan mahaifin da a da suka fi kowa isa da tunkaho a yanzu sun boye sun rasa inda zasu saka ransu domin uban da suke takama da shi aure ne ya bashi ama ba nasa bane, kuma ya nuna idan sun so zama ba zai hanna ba, sai dai shi kam bai san wani irin zama zai yi da su din ba, abinda ya sani kawai zai kiyaye hakinsu a kansa, shi yasa shi dinma ya fi yarda da maganar fitarsu daga garin, domin ya riga ya san cewar a yanzu zaman garin nan ya fi karfinsu, rayuwar da suka yi a da tamkar su suka haifi kansu a yanzu ba zai taba iya zuba masu ido su maimaita ba , dan haka duk inda za'a kai su zai yi iya yinsa dan gannin ya fita hakinsu, wannan tashin hankali ya karra saka Amnah a mummunan halin da ya nemi jirga tunaninta, ba ruwanta da halin da mahaifiyarta ke ciki, domin ba itace a gabanta ba, abinda ya fi rikitata damuwarta da asarar da ta gane cewar ta tafka ta rayuwa fiye da komai, asara ta duniya da kiyama idan bata tuba ta koma ga Allah ba, ba mutunci, ba usuli, ba MALEEK, kadararta mai zafi ce wace ta hannata sukuni sai kuka da maimaita kalaman mahaifiyarsu ta cuce su da ta bi wani mutumen har suke hayayafa da aurenta, fadi take yi ita ta san ba zata rayu ba ba MALEEK........
(Allah ka hanne mu aikata aikin dana sani, ka rabamu da muguwar Kadara)

Sai bayan isha RAUDA ta koma bangarenta bisa rakiyar Jakadiya, wace ta yarda ta tafi da kyar bayan Mah ta tabatar mata jikinta da sauki suka shigo har baban falon daga nan Jakadiya ta duka cike da girmamawa ta yi mata salama, ita kuwa ta rasa yaya zata yi dan gaba daya yanzun sai take jin bangaren ya yi mata wani irin girma, a dole ta lalubo wayarta ta dannawa salima kira suka shiga dan zantawa tana yi mata nacin ta zo bangarensu, ita kuwa tana fadin wane ita, ba yanzu ba, Bah ya masu kwakwaran kashedi cewar ba yanzu ba, karshema firar ta ki dadi dan Rauda ta rasa yaya zata yi da ita kan dan Allah ta zo ita gidan ya mata girma, a dole suka yi salama ta sake dokawa Atu kira, ama take ringin ba'a daga ba sai a kira na biyu ne Atun ta daga kamar wace ke barci ta ce" Sweetheart "

A hankali, cikin yannayin sanyin jiki da Muryar da ta wuni da shi ta furta" Atu, kin yi barci ne?"

Atu ta sake bude idannuwanta da kyau ta ce" Ina kwoncen dai, yannayin nan na saka kasala sosai, yaya kike, lafiya nake jin muryarki wata iri?"

RAUDA ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Atu , Bana tunanin zan iya, karfina karewa yake kokarin yi....., Atu ke kin san burin irin mijin da nakeda a rayuwa, Atu sarauta ba tawa bace, gaba daya rikicinta da irin yadda na shigota nema suke yi su karar da karfina "

Da kyau Atu ta zauna tana sauraron Rauda, ta bata dukkan kulawarta saboda ta sani idan har Rauda ta budi baki ta fara magana haka tana cikin babar damuwa a zuciyarta
a tausashe ta ce" Subahanallah, wani irin ba zaki iya ba? me yake faruwa? wani abin yayan ya maki?"

RAUDA ta lumshe idannuwanta tana jin irin yadda take son yin maganar kamar ba za'a fahimta ba

A hankali ta ce" Babu abinda ya min, Ni dai nake tsoron kasa zamowa abinda nake son zama, "

"Tl me, me yake damun ki, Please ki min magana dala dala mana " Atu ta fada a tausashe dan zata so ace RAUDAR ta yi kokari sun yi maganar yadda ya kamata saboda ta cire mata damuwarta

Huci Rauda ta fitar mai dan dumi a hankali ta ce" Na riga na yi saken da kadarar zuciyata ta cafki wanda ya zamo gogage a lamarin kwaliyar mace da duk wani abin da take iya birgeshi da shi, uwa uba yake da ya'yan banki , da kuma RAWANI Atu...."
Ta ajiye tana lumshe idannuwanta dan jin nauyin abin sosai a zuciyarta da harshenta

A hankali ta ɗora da fadin" Dan son kai irin nawa, nake jin haushinsa da matarsa bayan na san wanda aka aura min ko bayan mata idan yana da bukata zai iya ajiye kwarkwaraye su amsa kiransa a duk lokacin da ya so...., Atu tana iya kasancewa ganninsa ya min wahala a lokacin da na so, kuma magana da shi ta zamo aiki a lokacin da na buƙata,......Atu ina tsananin kishinsa wanda ke neman yi min ila , bayan na san wa nake aure....uwa uba na fara shakun in har zan iya birge shi ko na ga abinda nake son gani da ji ƙarara ba ta wani yannayin da nake jin ana iya ba wata dina ba!, Atu ban san yaya zan kwatanta maki ba, ina iya cewa ina jin kaina tamkar ba mace ba a gabansa........duba ki gani yau kwana na na h..........."

Dif ta dauke maganar sakamakon bude kofar nan ta baya ta wajen hanyarsa ta sirri da aka yi aka shigo

A hankali numfashinta ya shiga sauka daya bayan daya sakamon gannin bayanuwarsa a cikin idannuwanta a irin wannan lokacin da ya shigo yannayinsa a gajiye, sai dai daga tafiyarsa ba zaka gane ba sai ta idannuwansa da suka yi wani irin lumtu, shigar jikinsa kuwa banda daukan ido da shiga ido babu abinda take yi, domin ta hau jikinsa das ta zauna Bama kamar alkyabar dake jikinsa

A hankali wayar dake hannunta ke neman subucewa, duk bayanan da Atu ke kwararowa ta daina fahimta har sai da Atun ta dawo maimaita hello hello ama tamkar ba kowa a wajen, bayan ga call din bai mutu ba kuma takan ji abin Ac dake dan tite tite lokaci zuwa lokaci wanda ke tabatar mata ba network ya datse kiran ba

Idannuwansa a kan fuskarta suke, tunda ya shigo din
Gaba daya fuskar yake kallo da zagayayen hijab dinta wanda ya matukar bi kyan fuskarta ya kawatata.....shi fa a da yana yiwa hijab kallon abinda in za'a yi sallah ya dace a ringa sakawa dan a ganninsa in rufar ce ai abayama sutura ce, sai dai tunda ya santa ya ringa ji a ransa idan zai samu ta ji komin girman suturar da zata saka ta dora baban hijab da nikab, zata fi kyau a haka.........


Idannuwanta ta sauke saboda dokawar da kirjinta ke yi, cikin yannayin sanyin nan ta dan dago zata kuma kallonsa da sauri ta lumshe idannuwanta sakamakon maganar da ya fada dazu da safe kafin matarsa ta katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login