Showing 138001 words to 141000 words out of 188741 words

Chapter 47 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9836

ya manta abinda ya fi komai tsaye masa a rai, ya dubeta da kula sosai , da irin izar mulkin da yakan yiwa na waje wa'inda ba Mah da Bah da kuma Hajia ba ya furta" na san kin gaji yau ko?"

Dubansa ta yi da sauri, dan irin yadda ya yi maganar yana dubanta sai da gabanta ya fadi

Dan murmushin da ya sakata shakun anya murmushin ne? ko ba murmushin ba ya yi mata a hankali ya furta" Ki je ki huta, ga part dinki cen........sweet dream....."

Ya karashe yana juyawa ya karasa nasa part din ya bude ya shige sannan ya rufo kofar a hankali ya karasa wajen bed dinsa ya shiga kashe fitilun dakin ya kwonta yana janyo carbinsa a hankali ya rintse idannuwansa hadi da rukunkume fillon dake saman gadon yana jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa......
Bai taba zaton za'a bashi harka a bude ya kasa karba ba, bale harkar nan ta halal, matar aurensa, duk irin yadda ya rike kansa tsayin lokacin nan shi kadai ya san cikin azabar da yake shiga wasu lokutan idan yana cikin happy, na bukatar mai ษ—ebe kewa, gata ta samu ama wani lamari mai ban haushi ya hanna shi rawar gaban hantsi?.....in sha Allah zai ture, zai ture dan ya fuskanci matarsa su yi irin zaman da ya dace da su, na mutunci ko na abokin gabar mutunci dan duk abinda ta zo da shi da shi zasu kafta.....

AMNAH Kam......., sai ta ji wannan abin da ya yi wata dungumemiyar nasara ce, dukda ta so ace ta kwana a dakin, sai ta bar hakan zuwa ta hutan da yace ta juya tana jin farin ciki ta nufi dakinta ta sake kunna wayar dan tana son sauraron voice din Habu dan daudu, sai dai tsarin dakin nata ya sakata sake shagala kamar yadda ta shagala a falon nan ta ringa yiwa mahaifiyarta vidion falon haka yanzunma ta ringa yiwa dakin vidio tana turawa a wayar mahaifiyarta sannan ta danna mata voice note tana sanar mata tabas kayan nan sun ninninka nata da aka kawo, ita batama ga natan ba, kai kayan nan sun haukata ta fiye da tunani dan ta jima tana sake dauka har bayi sannan ta zauna sai kace ba itace ke takamar daga gidan kudi ta fito ba, zuciyarta ta sake cika da wulakanci da tarin dagin kai, a yanzu ta gama yarda tana iya bin Mah ko dan ta sayi zuciyar d'anta, idan yaso daga baya ta yi mata zagon kasa dan ta gama ganewa idan har ta idasa baban haja komai ya kare, a yanzu ba wai iya kasar nan ba o
ko waje ta fita daidai take da uban kowa!

Da wannan ta zauna bakin gadonta ta shiga sauraron Voice din Habu tana cire uban lulubin da aka yi mata da rigar da aka saka mata a karkashin lulubin

Tana sauraro ne bakinta da idannuwanta na buduwa zuciyarta na tafarfasa

wani irin takaici ya gama lulubeta a lokacin da ta kusa gama sauraron maganar da takaici ta datse , sam bata ji bayanin aurenta da Balarabe da dukiyar da ta samu ba, a bayane ta furta" Da ke karamar fakirar talaka ce har kika budi baki kika zageni dan uwar mijina na rikon ki?"

Idannuwanta ta lumshe cike da ture tunanin dalilin dake raya mata yana iya sakawa RAUDA ta yi mata haka a bayane ta sake furta" na san ko giyar wake kike sha ke ba zaki so mun miji ba, kuma na san ko tube ki aka yi a gaban mijina a halayan da aka fada min nasa na da ba zaki dada shi da kasa ba bale har ya tanka, domin wanda yake amini a jikinsa ya sanar min irin matan da ya yi mu'amala da su ba kannanun kadangarun bariki bane!, walahi Ni na san tunda na ga matar nan matsayin mamansa sai ta ja min matsala, ba damuwa na sayi fadan ki Ni da ke za'a ga karamin dan iska, in dai ina raye walahi sai na ga bayanki kafin na ji ubanda ya tsaya maki har kike zagina, tunda na ganki na ji na tsane ki, ashe dan talaka ce ke? mtssssss!"
Sosai ranta ya ษ“aci, hakan ya sa ta ci alwashi sosai a kan RAUDA, kafin ta yi kwonciyarta dan ko fitsari bata ji, kuma ba zata wanke kwaliyarta ba dan tana so gobe da safe ma ta birgeshi da ita, shi yasa ta gama kudurcewa ranta salolin zata hade kawai zuwa gobe ta gani ........
( Uhum!)

Washe gari haka aka yi yar hidimar girki aka kai bangaren, ama Mah ta hanna RAUDA taษ“a girkin dan tunda ta tashi da asuba ta ji jikinta da zafi, shi yasa ta sa ta je bangarenta ta kwonta, har dare a bangaren nata take sai da aka yi sallar isha'i ta sa ta je ta kwonta domin da sauki kawai dai rashin kuzari ne, Mah ta alakanta hakan da matsowar cikawar tabakarta jibi jibin nan, shi yasa take ta yi mata nasiha da rarashi har ta samu ta kwonta

a kwana na biyu kuwa su Atu suka dauke mata hankali, dan sun sakata gaba wai sai an yi mata kitso da kunshi na fita takaba ita kuwa tace ba zata yi ba gaskiya, sunna shan fira sunna ษ—ebe mata kewa har Mah ta shigo ta sanar masu zata je bangaren Hajia ta yi kiranta tace ta je SULTAN SHAHEED na son ganninsu har ya karaso, suka yi mata a dawo lafiya suka ci gaba da firarsu a tsakaninsu, Firar da rabinta kokarin nunawa RAUDA ne cewar hakuri zata yi na rashin mijinta, addu'a itace abinda zata ci gaba da yi masa har ta koma ga ubqngijinta na nuna Soyaya, ama a yanzu kuma da ta fita a takaba shikenan , duk wani abinda ya dace yi za'a yi, walahi ko bata yi kitso da kunshi yau ba sai ta yi gobe.......
Ita dai walahi zazzabin dake mata ya je ya dawo ya fi takurata, dan ta kiyewa Mah maganar asibiti ne, gani take yi daga dan zazabi sai asibiti? ama nukurkusarta yake daidai misali!


Da girmamawa, da kula ya fara gaishe da su, a kujerar da yake zaune wace take facing din su

Hajia baba bata san da zuwansa ba, sai da aka shigo aka sanar da ita, kuma yau YUSUF ya yi yar tafia tunda asubahi ko da ta kire shi, shima jim ya yi yana tunani yace yana zuwa, da ya kira shi sai yace da shi zuwa ya yi kawai gaishe da Hajiar, hakan ya sa ya sanar mata da gagawa aka shiga tarban SULTAN SHAHEED.

Mah na murmushi take sake tambayarsa takwarar Anmi Sarkin rigima, yana murmushin shima ya ce" Tana lafiya Mah, ai kam zata zo maki hutu ko na dan huta da rabiyar fada ita da yan uwanta"

Hajia na daria ta ce" Allah ya nuna mana, da mun yi farin cikin hakan"

Ya amsa da amen, sannan ya yi shiru na dan lokaci, kafin ya dago kansa da girmamawa da kalamai irin wanda zaka yiwa baba magana da su ya ce"









(๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ๐Ÿ˜จ)
Azl 49
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo



A nutse, cike da girmamawa bayan ya dago ya dube su , sannan a tausashe ya ce" Ina mai baku hakurin zuwan ba zata da na yi, na tabata idan har ya san zuwan nawa yana gari zai iya biyoni ne, idan kuwa yana zaune firar ba zata yiwu ba, bayan abinda yake tafe da Ni mai mahinmanci ne"

Hajia ta dubi Mah, Mah kuwa ta sake tsura masa ido tana addu'ar Allah ya sa ba wani abin ne ya samu YUSUF din ba, dan sukan yiwa junna haka, a baya idan YUSUF ya bata mata rai ta ki hakura shi yake zuwa ya wani kalamaiceta, shi yasa a yanzunma tana kallonsa tamkar zata ciro maganar daga bakinsa take ji

A tausashe ya dan nisa ya ce" Dangane da maganar RAUDA ne"

Mah ta dan zarro ido, Hajia kuwa ta dan matso gaban kujerar tana dafe kirji tana kallonsa, sai kuma ta shiga salalami tana fadin" Yi bayani mana Sultan, me ya samu baiwar Allah marainiyar Allah?, me ya sameta?"

Hannunsa ya dan kai wajen hancinsa kadan dan maganar da nauyi a yita da iyaye, kawai ya ga ne abokinsa akoy taurin kai shi yasa ya zo din
kai ya sake maidawa ya sada a tausashe ya ce " Tun kafin aurenta da ABDALLAH, MALEEK ke son ta", Ya ajiye maganar a hankali yana dan dago idannuwansa ya sauke dubansa a fuskar Hajia da ta saki baki ta zarro idannuwa ta kuma dago hannu kamar zata tare wani abin, sai ya ga Mah kuwa babu irin matsanancin mamakin nan a fuskarta

"Allah ya kadarto auren na farko ba shine mijin ba, a yanzu da Allah ya yi haka sai nake gannin take takensa, ya ki yarda da abinda nake son nuna masa, ina yi masa gudun yace zai nuna zuciya da girman kai a wajen da bai dace ba, shine nace zan zo na sanar sai a yi abinda ya dace" Ya idasa maganar wannan karron yana dubansu baki daya

"Innalilahi, innalilahi, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, wai YUSUF nawa? RAUDA tawa ta gidan nan? SO? wani irin SO ?, kai, Ni du na rikice, wai tsaya kana nufin YUSUF na nan?" Hajia ke fada da mugun mamaki tana tafa hannayenta da tarin tunanin kai ba wanda take tunanin bane

Murmushi SHAHEED ya iya yi yana sada kansa

Ido ta karra zarowa ta dubi Mah yana fadin" Andiya kin ji wani salamamen tashin hankali? Yanzu yana son nata yana kallo yana ji ya yi shiru har wani ya shigo ya dauka? yau da ace tana cen da yaya zan yi? innalilahi yau ga wani abin mamaki abin rikicewa, to wai dama haka abin nan yake? to ita fa ta sani ne ko bata sani ba? ita din tana son sa ne?, koda yake ai ba zancen tana sonsa, jikana ko y'ar waye idan ta gani ai zata so walahi talahi ma kuwa, kai ai ka gama d'ana Allah ya saka maka da alkhairi aure an yi an gama , ka san ba komai ke wahalar da MALEEK ba sai jinnin nan naku na sarauta, shi ya fi yi masa ila fiye da kowa dan kuwa kana ji kana gani ka yiwa kanka ila dan wani dalili naka ai bai dace ba, kai subahanallah ashe haka ake yi ban sani ba? ikon Allah ikon gaske, ALLAH ya saka maka da alkhairi, wannan zance ai faduwa ya zo daidai da zama tunda har gobe take fita sai ta sake daukan igiyar daraja, dama zuciyata a kulun dokawa take yi saboda abinda na jajibo masa, shikenan yanzun alhamdulilah!"

Duk irin farin cikin da suke yi Mah bata furta ko A ba,domin shi din da kansa Shaheed murmushi yake yi na farin cikin abinda yayi tunani ya tabata, dama ya san in dai Hajia ta ji an gama, duk wani na gidan mai yi mata biyayya ne, sai dai Hajia na kai kawo sai tafa hannaye take tana murna, shi kuwa yana shirin yi masu salama Mah a tausashe ,kanta a kasa ta furta " SHAHEED zauna, inada magana"

Daga shi har Hajia sai da suka kalleta basu shirya ba
Hajia da ta dauko waya ta dawo ta zauna tana dubanta ta ce" Andiya lafiya? yannayin nan naki bana so,me aka yi ne?"

Mah ta sake sada kanta, kafin ta dago tana duban Hajia a tausashe ta ce"Hajia,Ni na jima da tunanin haka, harma na gane eh haka din ne, ama matsalar ita din ai bata son shi Hajia"

Hajia ta tsura mata ido kamar tana son gane mutun ce ko aljan, a hankali ta ce" Ka ji wata bidi'a kuma, shi YUSUF din nawa ne ba'a so?, dama kin san da shi yana son yarinyar nan kika ki sanar min Andiya? me na maki da zafi haka?, kika kyaleni na je nake rarume rarume har na rarumo mai saka farcen matatu na aurawa bawan Allah?, haba kema Andiya to so meyema so din Allah na tuba da ake yiwa Yaren auren so din su je zama ya gagara?, ai sa so junnan nasu idan suka zama miji da mata, kuma Ni na tabata yarinyar nan zata so jikana, tana da wanda ya fi shi ne? meye aibunsa? Gaskiya Andiya ki daina wannan maganar haba , ko wani abin kikeda a rai sai ki bari ki huce a kaina Ni,ama ba a wajen da zan gaza dauka ba gaskiya!"

Kai Shaheed ya sake sadawa yana adu'ar Allah ya sa kar Mah ta kawo wani tsaiko a lamarin nan,sai dai kash tun bai gama adu'ar ba ya ji a tausashe sosai Mah kanta a kasan nan tana fadin" Ba hala bane Hajia, babu wani abin dake zuciyata, gani na yi yarinyar nan yar amana ce, kuma sunnanta bazawara yanzu, hakan na nufin tana da damar zabar mijin da ya yi mata ba a yi mata zabe ba, kuma ni na tabata bata wani sonsa, a yi hakuri kawai ya yi zamansa da matarsa, dukama yaushe ta tare? idan ya so daga baya abinda hali ya bada sai a yi in sha Allah, Ko shi din, ko waninsa "

Hajia ta sake zuba mata ido, sannan ta dago ta dubi Shaheed wanda ya gama ayanawa kansa ta faru ta kare, Hajia kuwa a yau harda mamaki sai da ya kamata na Mah, dan zata iya rantsewa tunda suke bata taษ“a ce mata fari, Mah din tace ja ba sai yau

Itama muryarta a tausashe wannan karron ta ce" AMEERAH, kina nufin ba zaki bamu auren y'arki ba dan bata son mu ko me?, kina nufin wani za'a kuma daurawa yarinyar da YUSUF ke so?, Ke fa kika haifi YUSUF , inace ko me yake so, ko a ina abinda yake so din yake ke mai zuwa ki nemo ki bashi ce, sai kawai in ga wannan abin kuma?, mu da aka mana auren hadin mutuwa muka yi? mu mazan basa son namu ma aka basu, muka rayu lafiya bale ita da ake so?"

Mah ta sake yin iya yinta ta budi bakinta wannan karron ta dago tana duban Hajia a tausashe ta ce" Hajia, ke uwata ce, kuma ke kakar RAUDA ce kamar yadda kike ta YUSUF, na san a hada din ba komai bane, sai dai ki min uzuri ki bani dama har su kawo kansu da kansu, idan suka ki za'a kuma daura mata wani shi kuwa ya yi ta rike bakinsa, dan in har yana so din zai magantu ko wani irin jinni ke yawo a jikinsa, dan Allah ki yi hakuri Hajia "
Ta idasa fada tana sada kanta, ta dan yi jim kamar yadda wajen ya yi dif, sannan ta mike jiki duk a sanyaye ta yi gaggawar guduwa dan bata san abinda zai je ya dawo ba kuma, abinda ta sani daya ne, ta shirya ja da kowa a kan maganar nan, babu wanda zai lalata mata amanar da ta dauko dan son zuciya, idan suka duba zuciyarta ta fi su murnar abin nan in dai haka din ne, sai dai ba zata so ta yi shi matsayin hadi ba, ita da kanta zata so ace ta samu SARAKUWAR da hankalinta zai kwonta a kanta, ba zai Amnah ba, Amnar nan tana tafe da kalar rashin da'ar da bata san a inda zata yi waje ta ajiye ba, abu daya tak ta sani ita da ita idan hanya ta hado su su san yadda hanyar ta ishe su, bayan wannan babu wani abu da zata nema na hadi tsakaninta da ita, dan ta kwatanta nuna mata daraja ta nuna bata san haka ba!

Tunda Mah ta mike ta fice a falon wajen ya dauki shiru, shiru mai girman gaske wanda har sai da shaheed ya ji mugun nauyi ya kama shi da tunanin dama Mah din ya samu kafin Hajia ta ji, dan shi bai taba tunanin Mah zata ji abu mai mahinmanci irin wannan amsa irin wannan ta fito daga bakinta ba, bai san dai abinda ya sa Mah din ta fadi haka, kuma shi bashi da shedar eh lalle RAUDA na mugun son YUSUF, abinda ya sani shine amsar da ya gani a wayar YUSUF amsa ce ta idan an damu da kai, sai dai bai sani ba har ina girman damuwar ta kai

Ajiyar zuciya Hajia ta sauke jikinta a mugun mace tana duban Shaheed ta ce" Ka san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login