Showing 147001 words to 150000 words out of 188741 words
bale ke"
Daga nan Hajia ta yi shiru tana mikawa Mah hannu har sai da ta yi mata kiran Bah ta bata sannan ta mike da kyar ta yi cikin dakinta
Zaunawa Mah ta yi a sanyaye ta sada kanta, zuciyarta na bugawa cike da wani irin tsoro na abinda ke iya zuwa ya dawo, ta san da wahala Rauda ta ƙi auren nan, sai dai ba RAUDA ta fi ji ba a yanzu kamar matarsa, kai ita fa yarinyar na bata tsoro Allah kuwa, ba zata so ta kai yarinyarta karama a wahalar ba, ba zata taba iya hakuri a cutar mata da RAUDA ba, a yanzun ma sai ta mike ta nufi bangaren su Salima dan ta amshi wayarta ta sanarwa baby su juyo duk inda suke, dan ta sani ya san inda take abu ne mai sauki koda bata tare da ma'aikatan sa, bale tana tare da direban dake aiki karkashin sa, bata so ya yi wani abin da yarinyar nan zata koma jin haushin sa , bata san a me ya dauki y'a mace ba, abinda ta sani daya ne yana iya shan wahala saboda so, dan ba kowace mace bace zata yarda wai da Yaren ido da hannu!
A lokacin da Mah ta karasa baban falon Hajia ta yi ya salama, ama abin mamaki babu kowa a falon, hakan ya sa ta nufi karamin falon tana tunanin ko Hajiar na cen, dan ba zata iya shigowa ta nemi Salima ta fice ba tare da ta gaisar da ita ba
A lokacin da Mah ta tunkaro karamin falon Hajia ta ringa jin magana da wani irin iya yi, da isa isa , da wani kalar takama, maganar ba muryar Hajia bace, hakan ya sa ta dan dakata sannan ta so juyawa dan bata cika son shiga sabgar kawayen Hajiar Salima ba, dan mutanen sam basa mutunta ta, sai iya bin mutun da kallon raini,
A lokacin da ta juya din ne Muryar AMNAH ta shiga kunnenta, Muryarta da wani irin yannayi na bacin rai ne da cin alwashi ko menene? ita dai ta ji muryarta ta fara magana, yakan ya sa ta dan ja ta tsaya da mamakin dama Amnah na kawo ziyara nan ama bata kaiwa cen wajenta?,
A lokacin ne AMNAH cike da wani gagarariyar magana ta ce" Ba zaki gane bane mom, bana tunanin akoy wani mahaluki da zan iya bari ya shiga tsakanina da mijina!, kin ga ki daina min maganar wancen gawa ta ki ramin dan walahi ni a mataciya nake kallonta matar nan fa kusan kulun sai kin ji an ce wani ciwon nata ya tashi, lokaci dai ama na tabata zata yi gaggawar Bara min d'anta in yi yadda na so da abina,
dama dama wannan masifafiyar kakar tasa, itama zan san yadda na yi da ita, dan wahali sai na maida ita mahaukaciya tana ji tana gani, abinda yasa nace ki zo yarinyar nan da ya dauka nake so a batar, mom ba zan iya kuma tunani mai kyau ba in dai tana doran kasa, a batar da ita dan ta shiga abinda bai dace ace ta shiga ba, ko ni da yake aure bai dauka ya ajiye ba sai ita? ba zan iya hakura ba, ba zan iya yafewa ba mom!" Ta idasa tana dantse lebenta, hakan ya sa Mah zarro ido, jikinta ya dauki rawa, tashin hankali ya ziyarce ta har ta so gaza taka kaffafuwanta sai da kyar fa sidin goshi ta iya juyawa ta nufi hanyar fita kirjinta na dokawa fiye da kima
Da kyar ta kai kanta falon ta, tana zuwa ta zube saman kujera tana cire hijab dinta jikinta na rawa tana jin kamar ciwonta zai tashi
"innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Azl 53
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo
Mah ke fada jefi jefi a hankali, har bata san shigowar Bah ba, sai da ya karaso da sauri ya zauna yana saka hannayensa ya kamata sosai da kula da tarin tausayinta kamar yadda ya saba ya ce" Subahanallah, Anmi YUSUF menene? jikinki ne? ko saboda maganar daurin auren ne Hajia ta fada min yadda kuka yi, bakya tunanin a Daura din ya fi alkhairi maman Yusuf idan ya so sa daidaita kansu?"
Kanta ta ɗora a gefen hannunsa idannuwanta a rintse tana tunanin anya maganar nan abar ta yi 'e da shi? duba da wace ta yi jan ragamar zaman watsa ahalinta matarsa ce,
A Raunane ta dago tana dubansa, muryarta a tausashe sosai ta ce" Ba'a daura auren bane?"
Yana dubanta ya gyada kai a hankali ya ce" Shedu muke jira, Shaheed yace min gayanan zuwa, kuma liman baba ne zai wakilci YUSUF, bakya so a Daura ko?"
Mah ta lumshe idannuwanta a hankali ta furta" Ina so, ina so a Daura, idan da hali a Daura shi yanzu yanzu, kuma a sanar a lasifika, ka bani wayarka ka samo min YUSUF din, Ni zan sanar masa sannan in bashi umarnin ƙafarsa kafarta, ka ji?"
Da mamaki yake kallonta, sai dai bai yi mata gardama ba, ya dauka cewa adu'ar da aya yi ta yi kwana biyun nan ne Allah ya amsa, dan haka ya shiga neman Layin YUSUF, sai dai bata shiga, aka sheda masa yana waya, ya dan jima ya sake bugawa wannan karron aka ki dagawa, ya rasa dalilin da ya sa ba'a daga din ba, dan ya buga ya kai sau hudu ama ba'a amsa ba , a dole ya mike bayan ya daukowa Mah maganinta ta sha yace ta je dakinta ta kwonta ta nuna a'a bata jin barci akoy abinda take jira, shi kam a dole ya fice dan ana ta nemansa a waya a masallacin Masarautar
Bayan fitarsa Mah ta samu ta daidaita kanta, ta je ta dauro alwallah ta zo ta ajiye salayarta ta maida gabanta gabas ta yi raka'a biyu sannan ta zauna rike da carbinta tana ja idannuwanta lumshe, dan tunda ta nemi kadaicewa din ta nuna bata son damu daga kowa sai ya zama ko yan aiki dake lekowa jifa jifa sunna karra kimtsa waje da karra turaran wuta basu shigo ba, hakan ya sa ta samu nutsuwar da take da Muradi ta ringa yiwa Allah kirari, tana ta karra neman kusanci da ubangijinta, ba ji ba gani tana karra yiwa Annabi salati , shauki da nutsuwa na ratsa ta kunnayenta n sauraron babar lasifikar Fada, lalo lalo har ta fara tsinkayo ana gayatar duk wani namijin dake iya halartar daurin aure yanzu yanzu.....hakan ya sa daurin auren ya ringa dan jan lokaci , ama a inda take bata motsa din ba, dan bata tunanin tana iya motsawa in ba kunnayenta suka jiyo mata abinda take son ji ba
......................................................
A lokacin da motarsa ke yin cikin Damagaran ya dauki hanyar gidan Bara'atu kamar yadda direban ya sanar masa ga inda suke, a lokacin ne Shaheed da yan rakiyarsa suka je taron daurin auren sa ba tare da ya sani ba
Zuciyarsa yana iya rantsewa ta kumbura a irin yannayin nan da yake ciki, gumin da bai daina ba kuwa ya tabatar masa gudun jinninsa ya jima da wuce ka'ida, idannuwansa kuwa yana iya rantsewa hudu hudu suke gani bama bibiyu ba
'Shin me yasa ake tayata kaucewa umarninsa?, me yasa mahaifiya a gare shi ta kasa taya shi daidaita kansa ya zama cikakken da ake so ya zama?' Wannan sunne tambayoyin da yake yiwa kansa a zaune cikin mota, a harabar gidan Atu, domin yana isowa ya yiwa abokinsa texte cewar yana kofar gidansa, shi kuwa ya yi kiran mai gadi yace ya bude masa gayanan zuwa yana gidan dayar matar tasa ne ba nisa, hakan ya sa ya shigar da motar ya samu waje karkashin wata innuwa ya parker motar ya salami direbanta da tsoro da mamakin ganninsa da kansa yana tuka kansa kuma a nan kuma ga dukkan alamu Hajia da ya tuko ya zo nema? shi dai bashi da halin yin wata tambaya a dole ya juya din ya bar gidan ba tare da ya yi mata salamar cewa an ce ya tafi ba
A cikin falon Atu, zaune suke a tsakiyar falon sun baje, RAUDA ta cire lesh dinta tunda ta zo Atu ta bata wando irin mai lafewa a jikin nan da riga katuwa sosai budadiya ta saka ko dan kwali bata saka ba ta yi masu danwake a kicin din Atun sun baje sun zabga masa yaji sunna ci sunna ihu da fira da dariya irin ta aminan da suke aminan junna din nan na kud da kud, dan Atun ta tabatar mata mijinta yau yana gidan uwar gidanta shi yasa ko hijab basu dauko kusa ba
Atu na dubanta a lokacin da ta gama shan ruwan sanyi da kyar yaji ya bar harshenta tana haki ta yi yar dariya ta ce" Ina son tambayarki wani abu Ni kam, wai yaya usulin mesg din ku da MALEEK?"
RAUDA ta saka birki a kokarin sake kai dan waken nan bakinta, sai kuma ta tabe baki ta ce" Dama bakina da naki nace maki Shi ya min message?"
Atu ta dan zarro ido tana kallonta ta ce" Kar ki raina min wayo mana, Ni dan Allah gaya min, dan matar nan tasa tsaf na nemo wace ita, dan a ranar da kika so sakawa ya zane mu ta bani mamaki, ke kin san kirarin da ake yiwa uwarta kuwa? baiwar Allah kishiyar Mamanta tunda aka auro uwarta ta zama kamar hoto a cikin gidan, ke su fa harda tsafi kina ji suke yi, kuma duk daraja irin ta babanta kina ji mamansa surfe take yi a garin nan, dan gaba daya ya manta da tana raye fa, ke Ni sai da na tsorata da na ji wannan abin nace Allah , Allah ga MALEEK ya rab ga Mah, kuma ga RAUDANA, Allah ka sa su fi karfin mugu ya Allah!"
RAUDA ta tabe baki tana kallon ta ta ce" Ba zaki gane bane, ki daina hada sunnana da shi da matarsa, dan Ni bana iya cin sauran tuwo!, kuma kina maganar tsafi sai dai lamari na Ubangiji idan har ya kadarto hakan wa Mah dina, bayan wannan Ni so nake na zane yarinyar nan walahi, haka kawai nake tashi da muradin in zaneta, na dai yiwa kaina alkawarin ba Ni ba su ne, da ba wannan ba yarinyar nan so nake in dauraye mata jiki ta yadda man nan da ya gama jika mata fata ya sa ta zama kala biyu, wajen man da kuma wajen bulalar ke dai kamar bayan kado dai ya dace fatar ta zama ko?"
Atu ta zarro ido cike da mamaki zata yi magana RAUDA dake kallon wajen kofa a rikice ta duke tana hade jikinta da dan karfi ta furta" Innalilahi, aminin aminiyata kar ka shigo dan Allah!"
Ja ya yi ya tsaya ya juya bayansa gaba daya, hakan ya sa Atu mikewa da gudu ta shige ta dauko mata zumbulelen hijab ta dawo ta miko mata ta zurma tana fadin" Aban karima dama kana dawowa warhaka ban sani ba har muka baje? bismillah kai ɗaya ke tafe"
Juyowa ya yi yana murmushi,
idannuwansa ya dan sauke kan RAUDA, sai kuma ya dauke zuciyarsa cike da matsanancin mamakin abinda ya tarar yau a wajen MALEEK
a tausashe ya ce" Eh Ni daya ne aminiyar, aminiyar aminiyata shine kika so ki kawo ziyarar ki gudu Ni ba'a yi zumuncin da ni ba ko?, to tashi ki je Mah ta turo sako wai, zaki ga motar cen wajen shukokin cen na mangwaro a parker "
Jin an ce Mah ya saka ta mike da sauri, ko wayarta bata dauka ba ta nufi wajen tana fadin" Sako? ko wani aiken Mah gareta ? ama bata yi kirana ba, ina zuwa Atu"
Daga haka ta fita
Sai da ta tsaya ta dan dafe kugu kadan tana duduba filin gidan, hakan ya sa ake gannin wandon dake kasa karara sannan ta gano motar ta nufeta a ranta tana ayana' Kai motoci sai a gidan Mah, duk wayewarka sai ka bi watan da kallo alkur'an '
Gannin ba'a bude aka kawo mata sakon kamar yadda aka saba idan wani abin ne ya sakata tunanin ko ba kowa a motar? hakan ya sa a nutse ta karasa ta saka hannayenta wajen madubin dan ta ga ko zata iya gannin ciki, duba da motar a lulube take da bakin madubin nan
Har ga Allah kukan kwakwa din gidan suka hannata jin an bude barin zaman direban har an zagayo inda take, sai da ta ji an kama damtsen hannunta an juyota, ta zabura tana ruko ido ta daga dubanta ta sauke a kan fuskar da ta sa gabanta yankewa ya yi matsanancin dokawa a firgice ta gaza wani motsi sai jinta ta yi wannan karron ma an zaunar da ita cikin motar nan sannan aka rufo ta gaza wani motsi sai hannunta da ta dan dago a firgice tana juyawa tana binsa da kallo har ya bude motar ya shiga ya rufo da karfin da ya saka cikinta murdawa zuuuuuu, ta rintse ido da karfi ta jimke hijab din na jikinta saboda irin yadda ya warci motar sannan ga shiga adu'a a cikin zuciyarta har ta bude ido ta ga inda ya nufa ya dauki babbar hanyar Tsatsunburum ne dan haka ta ringa daidaita hakinta har ta dan samu kwarin gwuiwa a hankali ta ringa kallon yannayinsa zuciyarta na dokawa da tarin tsoron yannayin, kasa kasa sosai ta furta" Yayanmu, lafiya dai ko?"
Idan har ya tankata to kuwa motar nan ta tankata, gaba daya sai tsoro ya sake lulube ta, ta yi tsuru tana murzar hannayenta kirjinta na dokawa, baban tashin hankalinta ko waya bata dauko ba bale ta sanarwa Mah inda take, ya Allah, kar dai wannan mutumen ya ilata ta? to wai mema ta masa ne fisabililahi? me ta yi masa ne?
A lokacin da suka karaso Tsatsunburum yama ta yi sosai, a haka ya tunkari hanyar fada, sai dai sunna daf da karasawa ta ga ya dauki wata hanyar, hakan ya sa ta sake tsorata tana ta kallonsa, sai ta ga an bude wani makeken get da yake da irin kwaliyar get din fadar
Idannuwanta tamkar zasu fado wajen kallon dogaran dake wajen da sojawa Bama polisai ba
Tana kallon nan suka karaso Cikin gidan, wanda ya nuna mata ginnin kamar na part dinsa, sai dai ai kamar ba cikin fadar ba
kasancewar duk sun dauki yannayin jiran ya fito dan su miko gaisuwarsu ya saka shi dakatawa ya dan sauke madubin motar kadan
Da sauri Taj ya karaso ya sauke ƙafarsa daya a kasa daya a duke hannunsa a jimke ya furta" Barka da warhaka ubangidana"
A cen ciki muryarsa ya furta" Su koma bakin aikin su"
Da sauri Taj ya mike ya koma wajen da suke ya sanar masu, sannan shima ya ja ya tsaya ya raba kaffafuwansa ya ba motar baya
Idannuwansa dake lumshe ya bude a hankali ya sauke a kanta, a lokacin ta gama marairaicewa ta matso kwallah mai zafi irin ta sa ya ji tausayin nan nata tana kallonsa a hankali ta sada kai ta ce" Yayanmu, dan Allah idan na maka wani laifin a rashin sani ka yafe min, walahi a sanina ba zan bata maka ba, ka yi hakuri ka maidani wajen Mah dina, in sha Allahu ba dai Ni na kuma bata maka ba ka ji?" ta karashe tana matsar kwalar harda dagowa dan ya gani
Jajayen idannuwansa a kanta tunda ta fara maganar har ta dakatar,
A hankali ya ce" Bani wayarki"
RAUDA ta dago da sauri, sai kuma ta sake maida kan kasa, kasa kasa ta ce" Tana gidan Atu walahi ma kuwa"
"ina da ina kika je?" Ya sake katseta, yana fitar da huci daga zuciyarsa
RAUDA ta dago ta zubawa fuskarsa ido, a hankali ta sake raunana idannuwanta ta yi raurau ta ce" Yayanmu"
"ki ce YUSUF din ki Please, yaushe kika fara boye sunnana?" Ya fada yana sake dauke kansa
A raunane ta dan duko kadan a cikin motar tana kallonsa ta ce" Na rantse da Allah na san ai kai yayanmu ne, kuma duk abina ai ba zan kama sunnanka ba, dan Allah ka yafewa abinda na maka a baya , idan na kuma ka batar da Ni gaba dayama kowa ya huta ka ji?"
Kai ya girgiza kawai ya bude motar ya fita
a rikice ta bi bayansa da kallo, da sauri ta bude ta fito ta karasa wajen Taj tana tattare hijab dinta tana waige waige dan samun wajen da kafarta ke