Showing 69001 words to 72000 words out of 188741 words

Chapter 24 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9832

kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo




ISHAK ya jima a tsayen nan kafin ya kai zaune saman kujerar yana dan shafa gashin kansa irin na samari da suke tarawar nan, duda shekarunsa sun wuce misalin na saurayi normal bai daina tara gashi ba yana askin yan duniya

Wayar dake aljihunsa ce ke ta alamun msg na shigowa, msg din kuwa har da gagautawa

Janyo wayar ya yi ya duba msg a jejere, gaba daya kuma abu daya msg din yake dauka shine " Na kira ka? "

Idannuwansa ya rintse yana jin amsar dake yawo a zuciyarsa wace ya jima da jin haka tun daga lokacin da ya jima tare da shi yake jin haka a ransa.....da kyar ya iya maida amsa da "ina tare da bos!"

"Me kuke yi? Ina fatar da zaka zo ka zo masa da abinda ya fi so? " aka maido masa da amsa a abinda bai fi yan sekwani ba

Ajiyar zuciya ya ajiye yana jin zafi a zuciyarsa sosai
Uhum, dama ace mai wannan farauta ya gane cewar har yanzu ramin da suke ginawa bawan Allahn nan bai samu zurmawa ba ya ba kansa lafiya? Ama lalle su din *AZAL* ne a duniyarsa, dan ko ba komai sun samu galaba daya a cikin dumbin mugun nufinsu a kansa, a yanzu bai san shi me zai kirayi kansa ba a cikin tafiyar nan, sai dai ya sani ya jima da baro layin mutanen nan daga son tura AMININSA a ramin mugunta, har a ransa yake jin baya ra'ayin wannan tafiyar, kuma burinsa Allah ya bashi damar da zai daina

A takaice ya bada amsa da "Eh" , sai ya kashe wayar gaba daya ya turata cikin aljihun wandonsa ya ci gaba da zaman jira yana jin tsoron kar dai wani abin ya same shi, karshema dan ya dauke kewa da zulumi sai ya dauki wayarsa ya bugawa NAFISA da ta tafi kauye wajen Kakaninta suka shiga fira sama sama


Lalle dajin mai sunnan Daji ne, dan tunda suka shigo shi basu hadu da mutun daya mai rai ba, sai wasu irin shuke shuken da suka ki bada hankalinsu a kai har suka kai wajen da zasu ajiye ababen hawansu da fatan Allah ya sa idan sun dawo su tardo ababen hawan

Kasa kasa sosai Taj ya ce" Oga , bani da tabbacin samun su a nan fa, ina kyautata zaton sunna nan din ne duba da yannayin da muke ciki na zafi, dan jejin da suke zama uku ne, yanzun zafi ne sukan zo nan cikin dare tare da babys din su"

Gadanga ne ya amshe da fadin" kwarai bosss, ama ina kyautata zaton samun cika a nan wajajen dan ya kwana biyu bai shiga birni ba, na tabata yana neman kudi ne, nan din kuwa makwoncin shege ne, shi yasa nace mu je a kasa dan na san hanyar bi wace ba za'a zagayemu bamu shirya ba!"

Murmushi YUSUF ya yi ya basu dama suka shiga tafia da dan gudu gudu da hannanenyu suke magana tunda suka shigo wajen da basa so a gane sun tunkaro taron da suke hangen wuta irin ta karraruwa na tashi da kidan kalangu ga hayaki na tashi dan tun daga nesa in dai hancinka bai saba jin kaurin hayaki ba tsaf zaka kasa tunkarar wajen

Tun daga wannan warin hayakin YUSUF ya rayawa kansa ba taron komai bane sai na yan jagaliyan yara masu shaye shaye, dan kuwa ya tabata in har taron nan na wani jijigegen dan ta'adda ne da ba zai yi wannan shagalar ba ace har a zo inda yake bai ankara ba yana shirme?, ai manyan yan fashi da makami sun jima da daina kwalewa cikin dare a labe a daji, sukan kwale a cikin iyalansu a lokacin da suka yi niya ta yadda ba za'a ritsasu ba, sai ya ji dama ya ji maganar gadanga da yace masa ya bari su je su gane masa ama ya kiya , koda yake shi dinma yana so ya dan ware hannayensa ne

Alamun da Taj ya yi kan zai fara zagayawa ta wajen da yake kyautata zaton uban yan iskan na nan ya saka su su kuwa bi ta gaba

Da sanda Taj ya karasa ta bayan wanda ke zaune saman kujera gabansa zagaye da kayan makuwa da yan mata cikin shiga ta kannanun kaya sunna ta shegantaka a tsakaninsu ya samu ya dago ya damki wuyansa ya dago shi hadi da mikar da shi tsaye

Lokaci daya yan matan suka saka ihu, hakan ya sa samarin dake tare kowa neman wawurar mabuginsa dan basa harbi domin karar bindiga na iya ankarar da mutane wajen zaman nan nasu wanda suke kauna sosai dan tarin ni'imar wajen na shuke shuke da kuma tsoron shigarsa da ake yi dan ana cewa jeji ne mai dauke da aljannu da kuma macizai, dan ko yan kauyen dake makotaka da wajen sunna tsoron shigowarsa shi yasa du suka saye yan farautar kauyen suka daina farauta a jejin sai wani jeji daban

Har ga Allah YUSUF sai da ya ji mema ya kawo shi nan to? Abin na yara kawai ya gani dan a tunanin sakarkarin Yaren nan zasu shigo wajen nan ba bindiga ne?
Wani tsagera irin na hannun damar ogan ne ya nufo shi a haukace da wuka sharbebiya yana ta wani dire dire irin kwararan nan ne, ya kyale shi sai da ya matse masa waje sosai ya karbe wukar tashi da wajen fadinta ya kasa masa mari da ita sannan ya cira shi ya makawa sauran dake kokarin yin ayari dan su rufa masu

Da gagawa ya ciro bindigarsa ya dagata sama da nufin harbawa

A rikice ogan nasu dake hannun Taj ya ringa ihun kowa ya tsaya kar ya yi harbi, basa son harbi, kar ya yi harbi basa son karan bindiga!

Da mamaki kadan YUSUF yake son ganewa, da gudu gudu Gadanga ya sanar masa ai basa son a gane wajen ne dan waje ne da suke da sirika a boye sosai da kuma wajen hutawarsu, harta mutane idan sun kama a nan suke boye su

Hakan da ya ji ya saka shi gane lagonsu a fili da kuma yarda cewar lalle kannanun yan iska ne dake iya zama manyan yan iska nan gaba, dan manyan ai basa tsayar da wajen zama guda daya saboda tsaro, dan zama a waje guda ai hatsari ne ga mai laifi

Bai ajiye bindigarsa ba dan kar yara su ritsa kato har ya karasa wajen ogan nasu dake ta tambayar su wanene su me suke so? Me suka masu?

A daken da yakan yiwa duk wani bayan Mah da Bah magana ya ce" Dan sakar masa wuya Taj"

Taj ya dan sassauta masa rikon, ama bai sake shi ba dan ko ba komai shine baban malamin su, Gadanga kuwa rike yake da tasa bindigar hankalinsa a kan kowa dan gudun kar a yi ba dadi

Kallon YUSUF yake yana magana a ransa yana ƙaryata tunaninsa, dan a ganninsa an ce fa Sarkin gidan mashaya ya zama sarki me zai kawo shi nan? Duba da yannayin sarautar garinsu ba karamar sarauta bace, ama kuwa da shi din ne da ya ji dadin ganninsa dan a duniya yana girmama mutumen nan, sun sha shiga basu da ko sisi ya dauki nauyin su harda guzurinsu fa, ai baba sunna jiran ranar da za'a basu damar su kai ziyara fada Allah za'a sha shagali dan sai sun yi masa yar karya karya ta musamman

"Akoy wani mutun dake hannunka, wanda ya fito daga masalaci ka kama shi da kudi a hannunsa, mai sunna Umar, ka turawa iyalansa suturarsa da komai, ka bani shi ka janye duk wata alaƙa tsakanin ka da shi da iyalinsa!" YUSUF ya fada a kausashe yana dubansa

Da yannayin son kawo raini ya ce" Ban gane ba, a kan aikina fa nake, ka san me ya hadani da shi,? Kudi nake binsa a gidan giya ya hadu da Ni ya ranci kudadena karshema yace zai shuna Ni in ban bashi lafiya ba, na jima ina dakonshi sai da aka kwana biyu na samu nasara na cafke shi, shine zaka ce na baka shi? "

Taj ya saka bayan bindigarsa ya maka masa a keyarsa da hargagi ya ce" Kai dan ubanka daidaita muryarka karamin shege, ubanka ne wannan in a wani fanni ka dauko takamarka, ka san waye Ni kuwa? ....." a haukace Taj ya ja hular fuskarsa fuskarsa ta bayyana a gaban shugaban yan ta'addan, lokaci daya YUSUF ya dafe goshi yana kallon Taj da irin yadda shugaban yan ta'addan ya rikice yana juye juye a rikice ya ce" Oga Taj innuwar Sarkin gida in an ganka an ga sarki YUSUF gagara gagarare, Allah ya sa ba rashin jina ya sa na yiwa ubana rashin da'a ba!"

Taj zai kuma yin magana YUSUF da ya rasa to su kuwa a ina suka san shi ya masa alamun kar ya saki su gane shi ne, sai kawai Taj ya ce" Sakon da muka zo amsa zaka bamu ka kuma saki wa'inda ke hannunka, ka san Allah in ka yi wasa tsaf zan yi maka jagaliyanci in kai karar ka gaban Oga bossss, dan ka fara kawo raini fa!"

Da gagawa ya ringa gyara rigarsa da ya sake shi gannin fadan ashe na cikin gida ne ya yiwa yaronsa ihu da karfi yace" Kai dan ubanka fitar da mutanen nan"

Sannan ya maido dubansa kan Taj ya ce" Taj, kai ka san bana kisa , ban taba kisa ba a harkar neman nan, ka san manyan basa bamu aiki, shine muke dan samowa ta wannan hanyar ama dan Allah tsakaninmu ne ka san fa yanzu oga ba zai iya saurara mana ba duba da ya zama uban kowa ko?"

Shi dai YUSUF magana ya ki yi, dan tsaf ya san a yanzu in ya yi magana yana iya gane shi, sai kawai yake biye da su kamar ba shi ba har aka fitar da mutane su uku cif, gaba dayansu maza ne, daya ne alamun a jigace yake dan ko tafia kasawa ya yi jikinsa du a kumbure babu wajen da ba rauni a jikinsa, rigar jikinsa wata jalabiya ce mai dati da wani irin wando wanda du a cicire kana gani ka san ba suturarsa bace a jikinsa

Da kyar ya iya matse muryarsa yana kallonsu ya ce" Ina Umar din?"

Da hannu ya nuna shi Yana sake tsare Yusuf da kallo dan gaba daya wannan din ya kasa gane ko waye kuma sai yake tunanin ko dai ko dai?

"Ka maida kowane gidansu, ka bamu shi din,........ka maida kowane nace gidan su, kuma ka bamu shi din, in dai da gaske kake rashin sana'a ta saka ka wannan aikin ka zo fada mu zauna, idan wasa kake yi kuma na yi maka alkawarin zamowa abokin gabarka, yadda kake satar mutane sai na sace ka!" YUSUF ya fada a kausashe bayan ya dan bude hular fuskarsa sun yi ido cikin ido, dan takaicinsa ya ji ya kama shi

Da hannu ya masu alamun su tafi da Umar din sannan ya cire abinda yake bakin bindigarsa mai hanna bindigar yin kuka da karfi ya dagata sama ya yi harbi har sau biyar da ita , harbin da ya hargitsa mutanen wajen hatta Umar ya zube a summe dan shi ya zata yau kuma kashe shi za'a yi tunda sun yi ta kiran layin da suka kai wayar ba'a dagawa kuma sun samo numbar maman Salaha sun ce sun yi kira wata yarinya ta daga ta zazzage su, lalle zasu kashe shi a madadin kudin da bai taka kara ya karya ba, kudin giyar da ya sha ta fitar da shi a hayacinsa ba ta saka shi aikata aikin alkhairi ba, lalle ya karra tsinewa wannan rayuwa ya yi Allah wadai da ita, idan yana tuna halin da Rauda zata shiga sai ya ji kamar ya yi ta kuka da ihu, shi kam me zai ce ya zama a duniyar ta? Matsalar ta da damuwarta, bai tsinana mata komai ba sai tashin hankali a gidan duniya

Harbin bindigar nan ya rikita kowa har ya zamo bai ga wucewar su YUSUF ba domin a rikice duk wani dake wajen ya shiga wawurar kayansa dan guduwa domin sojan Nijar ba abin wasa bane idan ka yarda ko takalmin ka ka bari wani ya gane naka ne ka fito kuma ka bayana shikenan sai yadda Allah ya yi da kai, shi yasa du suka tsorata suka ringa guduwa ciki harda abokanan shashancin nasa, domin dama iya shegen bai gama bin jinnin jikinsu ba, ana yi ne dan an dandani shaye shaye wanda dama daga kadan din ake zama manya manyan,


A saman babur din daure yake da shi a jikinsa a summe suka nufi garinsa direct ya wuce ofishin yan sanda

Yana zuwa aka bude masa get aka zo da gagawa aka kama Umar dake summe aka yi cen bangaren asibitinsu da shi sannan ya wuce ciki wajen da baban su ke jiransa a tsaye

Yana shiga da mamaki sosai ya ce" Wai dan Allah da gaske kai ne?"

YUSUF ya yi murmushi yana cire hular fuskarsa ya bashi hannu suka gaisa da kula ya ce" Abokina ka ɗan daga kafa kadan kafin ku je jejin nan, saboda ina son basu dama kankannuwa , an san ko su waye idan abinda nake son yi bai samu ba zamu bi su daya bayan daya mu kame su"

"In sha Allah namiji, ama ka mana garage gaskiya, ka daina dan idan wani abin ya same ka yanzu ai muna cikin kwaramniya kaima"


Murmushi Yusuf ya yi ya masa alamun ya wuce, ya fito yana biye da shi har wajen babur din, ya bar Gadanga a wajen Umar suka wuce gidansa dan ya maida kayan nan ya koma masarauta

Kafin Yusuf ya koma masarauta ya cika dare sosai yana zuwa ya sake saka kayansa ya fito ya nufi bangaren su ya shige ya karasa dakinsa ya shige wanka, yana fitowa ya gabatar da nafilar da ya yiwa kansa alkawarin ciwo kawai zai hanna shi yi , ciwonma mai tsanani ya yi adu'o'insa sannan ya kwonta yana tunanin ta yiwu Mah na cen ta kasa barci dan yau ya hannata kwana wajen Bah tunda likitansa na nan,
Murmushi ya yi yana mamakin soyayar mutanen nan, wato mahaifiyarsa da mahaifinsa, yana masu addu'a da fatan alkhairi a rayuwa barci ya dauke shi

Washe gari tunda duku duku aka tafi da Bah, cikin yan rakiyarsa da Hajia da Mah da kuma Yusuf, kafin gari ya waye tarrrr sun dawo saboda asibitin ba wace ake barin majinyata bace, kuma ga likitansa nan da ya zo dominsa kawai yana tare da shi tsakaninsu da shi sai addu'a da fatan Allah ya tashe shi lafiya sai ziyara da zasu ringa kai masa da dare kadai na minti talatin har Allah ya tashi kafadunsa

A wannan ranar wajen karfe goma babu kowa dake gilmawa a falo sai Mah da Rauda da Salima dake kicin sunna taya Mah girki saboda Hajia da MALIK da wani mutun mai zane na falon zaune sunna zanen tsarin ginin da za'a maida masarautar , YUSUF din sanye da pyjamins masu ruwan kalar blue da suka jiza sosai, riga da wando masu santsin nan, kansa ko hula babu yana saman kujera ƙafarsa daya tankwashe dayar a kasa yana kallon yadda mai zannen nan ke nake basira yana ta zanen bangarensa wai


A daidai lokacin da Mah ta fito dauke da dan karamin plate dauke da bitar shayinsa da yan kofunna na kwalba, bayanta RAUDA ce rike da plate baba dauke da manyan kuloli, sai SALIMA itama dauke da manyan kulolin , a daidai lokacin ne Hajia ke dan rage girman idannuwanta tana kallon zannen ta ce" Malik, bangaren mata fa? Kwaya nawa za'a yi?"

Yana kallon Mah ya mike ya amshi abinda yake hannunsa a tausashe sosai ya furta" HUDU " ba wani damuwa ko wani abin da zai dan dakatar da shi ya juyo sai ya ga sun zuba masa ido da Mah din, da Hajiar harda Salima, ciki RAUDA ce kawai ko kallonsa bata yi ba ta ajiye kayan abincin nan ta mike ta nufi kicin ta gabansu bata cewa kowa komai ba har sai da ta shige ya dan lura da ya bita da kallo ya dauke dubansa a lokacin da ta dawo dauke da wasu kayan abincin kasa kasa ya ce" Jiya fa, an ga baban yarinyar nan!"

Da sauri RAUDA ta dago idannuwanta ta sauke su cikin nasa, shi dinma a lokacin ita din yake kallo, shi kuwa gashin idannuwanta yake son gane wai yaya ake yi kulun suke a jike? Kukan dai ne Allah ya sa ta kware a shi ko menene? , ita kuma fuskarta lokaci daya ta ringa bada wani annuri ta bude bakinta tana kallonsa, a gaban Hajia wace tun maganar mata hudu ya sakata yi mata kallon kurame dan son gane jikan nata yaya dai?, da Mah da ta girgiza kai da mamakinsa wai mata hudu ko a ina zai wani yi mata hudun?, sai Salima dake kallon zanen da mai zanen nan ta ce" Dan Allah fa? Uncle dina kake nufin ka gani?, wayo Allahna dan Allah da gaske kake?"






Kashhhhhhhhhhh☹️☹️☹️☹️☹️🤗🤗🤗🤗

Azl 25
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login