Showing 165001 words to 168000 words out of 188741 words
idannuwansa na neman rufewa ya dawo inda ta zauna tana zuba abincinta ya sake bin shigarta da kallo ya ce " Ke da wa kuka yi girkin nan?"
RAUDA ta kalli fuskarsa jin amon muryarsa kamar ranar da yake mata fadan nan, dan haka ta bashi amsa tana fadin" Ni da masu aiki"
Hannunsa ya kai wajen goshinsa ya shiga murzawa da dan karfi sai kuma ya juya da sauri ya nufi hanyar nan ta baya da suka shigo shi da ita jiya ya dadana wasu numbobi ya bude ya fice
Mikewa ta yi tsaye da sauri tana kallon kofar, gannin an rufo ya sa ta yi kasakai tana tunanin mutumen nan kamar wanda yake tare da almatsutsai masu saka shi shiga halin fushi da sauka a lokaci daya? kai ita kam ta fi kowa shiga wani hali a rayuwa gaskiya
YUSUF na fita Taj ya karaso da gudu ya kawo gaisuwar da ya saba kawo masa kansa a kasa
YUSUF ya rintse idannuwansa dan ba zai so jin amsar tambayar da ta zama wajibi ya yi ba, sai dai dole zai yi tambayar nan , dan haka ya ce" Masu dafa abincin nan maza tare suka dafa da RAUDA?"
Kai Taj ya sake sadawa a hankali ya girgiza kansa ya ce" A'a sir, tunda chef din kicin din ta sanar min Hajia ta fito tana kicin na suka bar wajen lambu ina fatan ban yi laifi Allah ya kara maka lafiya"
idannuwansa ya lumshe yana fitar da huci mai sanyi daga zuciyarsa,
ya jima a tsayen nan kafin ya ce" Ka cire su a harkar kicin tunda tana son shiga,nd......"
ya dan dakatar yana bin manyan talo talon dake yawo da kallo ya ce" Nd ko da wasa, kar wani ya shigo inda za'a iya haduwa da ita........Doka ce"
Da sauri Taj ya amsa yana sake dukawa, shi kuwa ya juya ya nufi dakin da suke rufe masu laifi kirjinsa na masa zafi da wani tunani da ya yi a kan maganar da ake cewa idan ka bi ta wani sai an bi takan nan?
' innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, ya Allah ka yafe min abinda na ringa aikatawa, ya Ubangiji ka yafe min kurakuraina kar ka kamani da RAUDA.......' shine abinda yake ayanawa har ya kama karfen da Habu dan daudu ke ciki ya yi tsamo tsamo kamar kazar da aka saka cikin ruwan zafi
A lokacin da AMNAH ta shige dakinta direct bayi ta nufa ta haye saman wc cikinta na kurdawa tamkar zata zubar da hanjin cikinta hankali take hannayenta saman kanta
Tuni ta cire abayar nan dake jikinta ta Yar a nan ta saka hannayenta tana sake sosa kanta dan sai ta ji kamar tafia ake yi mata a cikin kan nata
*Clinik lafiya, docter Papalo* kunnayenta suka jiyo daga bakin MALEEK? wannan wani irin tashin hankali ne? dama ya san Papalo? , Da karfi ta ja ruwa ya kora abinda ta aikata ta janyo pampon nan ta wanke jikinta ko sabulu mantawa ta yi da sakawa tsabar tashin hankali ta kuma fitowa dakinta ta duka ta warto wayarta tana dane dane hankali gaba daya yana daf da barin jikinta, domin ya zamto mijinta ya san rayuwar da ta yi da Papalo shine abinda ba zata taba so ya faru ba a rayuwa, dan kuwa da wahala idan har ya san haka ya iya zama da ita, ita kuwa in har akace zata bar daular nan komai na iya faruwa da ita, ta riga ta shigo rayuwar nan bata tunanin akoy wata bak'ar kadarar da zata fitar da ita, ko mecece, shi yasa ta kudurta aniyar a kwana kusa sai ta san yadda ta yi da yarinyar cen, sai ga wata fitinar na son bilo mata?
Ringin take yi ama ba'a dagawa sai da ta yi ya kai sau biyar sannan aka daga kuma aka yi shiru aka ki yin magana har sai da ta ce allo sau uku sannan aka amsata da murya kasa kasa mutumen ya ce" Lafiya kike kirana?"
Itama da yannayin a tsorace take ta ce" Kai zan tambaya lafiya na ji sunnanka a bakin MALEEK? ya sanka ne dama?"
A zaune yake, sai da ta sa ya mike tsaye yana fadin" Ni? ya san Ni? a ina? a'a fa, wani irin sanina?"
Amnah ta ja wani irin numfashi mai zafi tana fadin" Wani irin bai sanka ba, bayan yanzu yace min idan ban warke ba zai sa a kaini wajen ka ya san kana da maganin ciwona?"
Shima sai ya samu kansa da shiga tashin hankali, a rude ya ce" Wani ciwon? kina nufin tun aikin da muka maki wata da watanni baki warke bane shine kika kama sunnana a gaban mijinki?, ba mun yi da wajewa ba mun gama neman junna mun gama nunawa mun san junna ko a lahira ba?, a kan mi zaki kama sunnana a gaban mijinki Amnah? kin san da yana iya lalata min dukkan abinda na tara ko? kin san da yana iya sakani a prison din da za'a manta da na taba rayuwa a duniya ko?, inace tarayar mu ban taba tirsasaki ba ko? shine zaki watsa min kasa a ido ki tona Ni a wajensa?"
Itama muryarta a daukake fiye da tasa ta ce" Kai dan Allah ka rufe min baki ka bar ambaton abubuwan nan kuma ka daina kama sunnana kai tsaye kar wani ya gane wace Amnar ake nufi, an gaya maka banda hankali ne da zan yi maganar nan da wani ma bale mijina?, Ni yanzu na ji sunnanka a bakinsa bayan a nan palas muna da asibiti baba wace ta dame clinik dinka inma maganar asibitin ce yake, kuma kai likitan mata ne me ya haɗa fatata da kai?, a dole zan kirayeka dan in san abinda nake ciki, in haukanka, karamin haukanka ya sa ka bude sirrin abinda yake faruwa Ni da kai walahi sai na yi ajalinla, kuma kaima ka san ba Ni kadai ce zan shiga uku ba!"
Shima ransa ne ya ji ya ɓaci, ya ce" Kin ga, ina gannin ba Ni kadai ne zan shiga ukun ba tabas, harda mahaifiyarki walahi, kuma maganar ki yi ajalina karya kike baki isa ba na rantse, ke dai zaki cire sunnana a ciki dan kuwa kin san in na budi baki sai na fada cewar da kika zo wajena neman maganin infection dinki da kika kwaso a wani wajen bayan na yi treatment din ki kin warke kika ci gaba da zuwa wajen nawa, ke ce kika fara nemana, kuma ana gobe aurenki ba Ni nace ki kwonta da Ni ba, ke ce kika kwonta da Ni daga baya na maki aikin nan ai ba Ni na kawo kaina ba , sannan mahaifiyar ki itace ke........."
Dif ta kashe kiran tana zarro idannuwa cikinta na sake murdawa, a dole ta shiga kiran layin mahaifiyarta dan kar fargaba ta kasheta ita kadai a daki, gaba daya tsoro ya gama mamaye mata zuciya da tashin hankali
A irin wannan lokacin kuwa mahaifiyar Tata sunna zaune a falon gidansu ita da abokin mahaifinta da mahaifin nata sunna maganar abinda yake faruwar nan, su duka burinsu su gane ya ji abinda banzar jarababiyar tsohuwar nan ta fada ne ko bai gane komai ba?, hakan ya sa wayar ke ta ringin bata gani ba kasancewar a silent take
matarsa uwar gida ce ta shigo dauke da jus da kayan kari ta ajiye, kanta kasa ta gaishe da su ta juya ta fice, a zuciyarta tana adu'ar Allah ya sa su ci abincin kamar yadda akace a saka adu'ar nan WARAFA'ANA'U MAKANAN ALIYA da aka rubuta dubu tara da casa'in da tara, akace idan da hali duk wanda ake tunanin da saka hannunsa a lamarin ya sha, to kuwa in sha Allah za'a fara gannin haske a maganar asiri, domin adu'ar nan waraka ce sosai bale a harkar samu, shi yasa da sakon ya zo yau daga fada ita kuma ta maida hankali ta yi girkin nan da jus ta kawo tana ta adu'ar Allah ya sa a dace
Hankali kwonce Hajiar AMNAH ta mike ta zubawa kanta abincin ta koma da abinta ta zauna, shima mahaifinta da kansa ya zuba nasa ya zauna hakama abokinsa da ya bararaje tamkar gidansa ya zuba ya fara cika jus din ya koma ya zauna ya shiga shan jus din sannan ya dora girkin
kusan kowane ya sha jus din nan, sai dai wani ikon Allah sun a sha ciwon kai ya saukar masu gaba dayansu
gannin da gaske ciwon kan yake ya sa mahaifin Amnah mikewa, dama jikinsa du wani iri yau din, tun dazu da Hajia ta fara fadan nan jikinsa ya yi wani irin sanyi, ya mike ya nufi dakinsa yana fadin"
😍😍😍 *MAGANIN KARA KIBA 3IN1*
*Ina meneman kiba ido rufe Kuma tanason maganine ingantacce Wanda baida illah kokadan to tazo gadama tasamu yar uwa indai kibace da gyaran nono dakara hips toga Mganinmu nan 3in1 cikin kwana 7 kacal👌🏻 zakiga yadda Zaki fara murmurewa insha Allah mungwada mungani munbayar angwada munsayar angode insha Allah kawata Zaki godemin da 3500 dinki kinhuta da gorin rashin kiba munan cikin Gombe Kuma munatura kaya ko ina kedai tuntumebi ta Whatsapp ko kikirani Kai tsaye ta 08030861857 sai kunzo🥰*
*MAGANIN HIPS*
*Wannan Maganin anyisane tamasu neman hips sunsha wannan sunsha wannan to gatamunan insha Allah guarantee nakebaki hajiya inada yakini akanta matsala indai tarashin hips ne to anwuce gun 3500 kacal kinhuta kijuya kiwarwasa kisaka kayan gayu kijuyawa Oga yayikallo kawata har yanga saikinmasa ninafadamiki wannan nemeni kisamu naki 08030861857*
*MAGANIN NONO*
*Itama akwaita me inganci kamarta 3in1 data hips wasu suna korafi nifa nono kawai nakeso yaciko yayi bulbul gwanin sha'awa yadda Oga zaiyaba nasa breast cup suzauna das Amman abun yacitura Nasha Nasha magungunan Amman haryau ba chanji to ganamu Nan yakine ne Dani akansa ba Dan kadanba alhamdullahi duk Wanda yasaya saidai godiyace tsakaninmu kema zokigwada Kuma kigodemin location Gombe 08030861857* 😍😍
Mahaifin Amnah ya kusa shiga dakinsa yana rike kofar dakin ya ce" Idan ka tashi tafia, ka fadawa Ilu mai shagunna ya saki shagunnan nan Please"
Daga haka ya shige dakinsa yana jin kansa sai sarawa yake yi
Furucin ilu mai shago ya saka abokinsa binsa da kallo sannan ya kalli Hajia da ita dinma ta kalle shi da sauri,
Dukda yannayin da take ji a jikinta bai hannata fadin" Ilu mai shago kuma?"
Shima abokin nasa yana kallonta ya ce" Lafiyarsa kalau kuwa? a shekara goma ma ya yi maganar dukiyarsa? idan akace da su Ilu su tashi ace masu a kan wani dalili bayan sunna biyan kudi a kan lokaci?, ki binciki mijin ki fa, wani iri nake ganninsa"
Dan shiru ta yi tana kallonsa, sai kuma ta mike ta nufi ciki wajen Elhaji a ranta tana tuna maganar wanda ya bata rantsatsen aikin nan, bata tunanin kuwa gawa na dawowa duniya bale har ta ciro abinda yake bakinta a dinke wanda aka dinta mata saboda aikinsa, kawai tana kyautata zaton dawowa ne abin ya dan masa sama sama, bayanshi ba dai ace wai ya dawo hayacinsa ba
Tana shiga ta same shi yana ta barci, sai zufa yake yi, dan haka ta ficewarta ta barshi tana dan fitar da tsakin zai bata mata lokaci a kan shirmensa
____________________________________
Taj ne ya zo inda yake tsaye tun dazu ya kurawa habu dan daudu ido, wanda tunda ya tsaya din nan shi kuwa ya duka hannayensa a hade yana duban kasa sai rizgar kuka yake yi wanda shi da kansa bai san ko na meye ba
Da girmamawa Taj ya ce" An saka sakon a hannun uwar gidan nasa, kuma an tabatar da ta tabatar da sun sha"
Ya jima kafin ya iya budar bakinsa yana duban Taj ya ce" Thank you, Please kar a daina har sai Allah ya tabatar mana da maganin da muke nema , sannan a sake kaima babar abinci"
Taj ya amsa yana risinawa
har ya juya YUSUF ya yi kiransa
dawowa ya yi ya sake dukawa
A hankali ya ce" Taj, sirina ya zama siri a gareka"
Taj ya karra sada kai a hankali shima ya ce" Mudin raina MALEEK"
Daga haka ya salame shi, ya ciro ky din wajen da Habu yake ya bude ya shiga ya rufe daga ciki ya nemi waje ya zauna yana kallon Habu
Ajiyar zuciya ya sauke, gaba daya karfin jikinsa ya bar jikin nasa ne tunda tunanin nan ya shiga zuciyarsa
A tausashe yana kallonsa ya ce" Zo nan ka zauna"
Habu ya kalli inda ya nuna masa,, ya karra sada kai a raunane ya ce" Ranka ya dade, dan girman Allah ka gafarta min, Ni ban san laifina ba sai ganina na yi a nan, ka yi hakuri ranka ya dade"
YUSUF ya sake dubansa a tausashen ya ce" To Ni na zo ne?"
Da sauri ya girgiza kansa ya mike ya je ya duka kusan kaffafuwan YUSUF kansa a kasa
Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" Ka ga, ka daina sada kan nan, bashi da wani anfani, dan ban haliceka ba, wanda ya haliceka na jiranka, ruwan ka ka shiryu ko ka je masa a haka, abinda nake so da kai tambaya gareni , na san kai aminin matata da mahaifiyarta ne, tunda na ganka da idona ranar da muka gaisa a falona"
A haukace Habu ya dago yana dora hannayensa saman kansa, jikinsa na karra daukan rawa
YUSUF ya dan sauke ajiyar zuciya shima yana kallon nasa ya ce" Ka daina abin nan mana, kai fa namiji ne......"
Sai kuma ya dan yi murmushi a saman lebensa ya ce" Au ashe ba haka ba, ka ga, ina so ka fada min sirrin asirin da ya saka Elhaji zama kurma kuma makaho a kan abinda ke tafe a gidansa"
Wannan karron kam, ya san tasa ta kare,dan kukan na dazu ba ihu na yanzun harda ihu yana sake dora hannayensa saman kansa ya ce" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une na shiga uku, Ranka ya dade ka ga daga Allah ba wani? Ni nan dan aike ne kuma yaro a wajen Hajia, walahi du abinda za'a aikata Ni dan rakiya ne dan na samu dan abincin ci a bakina bayan wannan babu wani abin, dan Allah ka min rai ka yafe min shiga gidanka da na yi da kuma zamowa tare da matarka, idan na fita daga nan ko sunnanta ba zan kuma kamawa ba"
YUSUF ya yi shiru, sai kuma ya girgiza kansa kawai ya mike yana ciro ky din aljihunsa ya nufi kofar
A rikice Habu ya rarafo yana fadin" Innalilahi ranka ya dade dan girman Allah kar ka barni a nan, ka ceci rayuwa.........."
"Kai ja baya dan ubanka kar na datse maka hannaye!" Taj ya fada da hargagin da ya sa Habu saurin yin baya fitsari na sake kubce masa a wandonsa, dan a zamansa a wajen nan fitsarin da ya yi a wando ya fi a irga, ranar da suka likira shi ya saki fitsari Taj cewa ya yi ashe yanada alkalami a jikinsa yake daura zani
Murya na rawa, jikinsa kaf na rawa, kana ganninsa ka san ya gama fita a hayacinsa ya ce" Ranka ya dade zan fada dan Allah kar ka barni da su, walahi kasheni zasu yi, ranka ya dade ko muryarsu tsoro nake yi, dan Allah kar ka barni da su, walahi a wata gawar wata budurwa da ta rasu a anguwar su Hajiar aka dinke layar da aka basu, sunne suka yi wankan gawar Hajiar ce ta saka da kanta dan aminiyar Uwar yarinyar ce, ita ta fada min cewar daga baya ta biya aka bi gawar aka dinke mata bakin dan kar layar ta fadi, ranka ya dade na san gidan su yarinyar, ama ban san inda kabarinta yake ba, dan Allah a sakeni zan nuna"
Kansa banda sarawa babu abinda yake yi, a hankali ya lumshe idannuwansa ya bude din ya fice yana jin ihun Habu ya nufi bangaren Mah idannuwansa na neman rufewa
Da kyar ya iya sada kansa da dakin Mah, a lokacin tana zaune tana shan maganinta ta dago da sauri tana kallonsa har ya karaso
Maimakun ta ga ya haye gadon ya zauna daf da ita sai ta ga ya zauna a kasa sannan ya dora kansa a saman kaffafuwanta
"Kai lafiya?" Mah ta fada da sauri tana dubansa
Sai dai bai dago kansa ba daga irin yadda ya dora kan nasa a cinyar nata
Da sauri ta saka hannayenta ya dago kansa sakamakon jikar da ta ji cinyarta ta yi , jika mai dumi , jika mai nuni da hawaye ke sauka a kan cinyarta na Yusuf
Da sauri ta sauko ita dinma daga saman gadon tana talabo fuskarsa ,, muryarta na rawa ta ce" Menene? subahanallah me yake faruwa? ina Bah dinka? ina Hajia? ina baby? ina Amnah ne? menene Ishak ne? ko Taj? menene YUSUF?"
Da sauri ya mayar da kansa cikin tafukan hannayenta ya ja wani irin numfashi hawayenshi suka sauka sosai yana rike da hannayen nata
gannin tana daf da sumewa dan shiga a halin kidima a dole ya budi bakinsa yana dubanta a hankali ya ce" Lafiyarsu kalau Mah"
Mah na dubansa idannuwanta sun gama cikowa da kwallah ta ce" Mememenene to? kuka fa kake yi fa"
Yusuf ya langwabar da kansa yana dubanta, a hankali ya ce" Mah, anya kuwa zan iya?"
Mah ta sake rikicewa tana dubansa ta ce"Mene? meye ba zaka iya din ba? sarautar kake son ajiyewa?"
Kai ya girgiza a sanyaye ya ce" Inama ace sarautar ce nake son ajiyewa, sai na ajiye dam na dauke ki mu gudu, kin ga abin nan ya fi karfin wannan Mah, walahi ya fi karfin wannan rigimar"
Zuwa yanzu kam Mah ta gama rikicewa, da dan karfi ya ce" Kai, wai uban meye?, zaka fada min ko sai na fala maka mari?"
Idannuwansa ya sada kirjinsa na dokawa, a hankali ya ce" Idan fa abinnan ya bi Ni har yayana?, Mah idan rashin jin da na ringa aikatawa na biye biyen mata ya bi Ni har yayana? yaya zan yi?"
Mah ta yi dif gabanta na faduwa tana kallonsa, ta kasa furta koda kalma daya ce
A hankali ya sake fadin" Kin ga, tun ba'aje ko'ina ba, matata , uwar gidana, bata jin magana, ta yiwu fiye da rashin jin da na aikata a da, dan abubuwan da nake gani a hankali da wa'inda na gani sunna karra rikita min lissafi, a yanzu Ban