Showing 78001 words to 81000 words out of 188741 words

Chapter 27 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9859

adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo






Cikin gundura da magangannun nasa YUSUF ya ce" tana ciki ne?"

Kai ya girgiza da sauri kansa a kasa ya ce" Tana bayan motar, ai baka ce na kaita ciki ba Allah ya karra maka lafiya"

Dan tsai ya yi, ya dan dube shi , kasa kasa ya ce" Ka kaita ciki?, dama kai ka dauketan?"

Wannan karron dagowa direban ya yi ya dan kalli MALIK, kafin ya maida kansa kasa, da girmamawa sosai ya furta " Allah ya taimakeka, a sume take ne, gashi Hajia ba zata iya daukanta ba, shi yasa na sakata a motar"

Kai YUSUF ya dauke yana tabe bakinsa ya nufi motar

Salima na ganninsa ta bude bangaren da take zaune kan Rauda saman cinyarta, Abdul kuwa ya kwontar da kansa a kirjinta , gashinta a fili ta cire mata ribom dinta ga jinnin nan har a jikin rigar Salimar da kuma gaban goshinta

Wani irin bugawa ya ji zuciyarsa ta yi, hakan ya sa ya dauke dubansa ya kalli direban dake dan nesa kadan , kasa kasan nan sosai ya furta" Ko ta mutu ne?"

Da sauri direban ya girgiza kansa ya ce" Wahala ce kawai ta sha, ai abin ba karami bane kuma inaga an shamaceta ne sosai fa"

YUSUF ya dauke idannuwansa daga kansa ya sake kallon Salima dake ta share hawaye hannayenta du jinni ne, sannan ya mika hannu ya furta" Bani ky"

Ky din motar ya ciro ya duka yana miko masa, ya amsa ya juya yana masa alamun ya tafi da yan yatsunsa sannan ya bude gidan gaban ya shiga hankali kwonce yana jin kamar ya cire rawanin a nan ya ajiye dan yadda yake jin tamkar numfashinsa na masa nauyi, bai san dalili ba, ya dai san kawai yana jin isla na neman yiwa kofofin hancinsa kadan

Idannuwa ya sauke kan polise don da ya shige gefen direban yana fadin" Sir ka kawo na yi driving Please"

Bai ce masa komai ba ya tada motar ya nufi hanyar get din, sauran suka ringa bin su da gudu, dogaran dake gadi suka bude get din sunna risinawa tare da kirarin da suka saba har motar ta shige gaba daya ta wuce cen gaban kofar shigewa ya parkerta a nan

Kashewa ya yi a nutse ya ziro kaffafuwansa ya fito domin tuni police din nan ya bude masa motar

Bayan motar da ya kalla ya saka police din budewa sannan ya tsaya yana hankalce da yannayinsa, shi dinma dan tsayawar da ya yi kawai nazarin police din ne yake yi da mamakinsa

Uhum ya dan fitar daga kirjinsa yana kallon Salima, wace ke kiciniyar kamo Abdul ama yana girgiza mata kai da nuna mata RAUDA, yaron ya jigata har muryarsa bata fita sai yake yi kamar bebe yana nuna mata

A sanyaye ta ce" Abdul, ciki zamu shiga a duba auntynka ka ji? Ka yi shiru hakanan kaima ka ga baka da lafiya ko?"

Kai ya ringa gyadawa ya kama hannun da take bashi suka sauko da dan hanzari ta kauce tana rike da hannun Abdul tana so ta ga police din ya yi ya dauko Raudar su shige ta ga ta bude idannuwanta ko hankalinta zai dawo jikinta

YUSUF ya dan daga ƙafarsa kadan dan aikata abinda ya yi niya , sai ya ga Police din da sauri yana nade hannun rigarsa ta kaki yana masa alamun ya dakata shi zai daukota ne ai

A ransa ya ayana' toh fa'
A bayane kuwa sai ya ki dakatawar ya saka hannunsa gashin nan nata dake baje da ya fi bashi haushi , a ganninsa in ta san fadanta zata je yi ta saka hula mana? Yarinya kamar wata kura du in ta fita sai ta daku? Yau dai an sha duka su uwar fada ta yiwu a daina.
Gannin police din nan ya bude dayan bangaren ya saka shi zura masa ido, ta wajen inda kaffafuwan uwar Abdul yake ko wa police din ya je, shi kam ta yiwu an hadda shi da tababe kuma, yake ta ayanawa a ransa, kasa kasa ya furta" Bari mana, kar ka dauketa"

Dakatawa police din ya yi, har ga Allah bai gane shine zai dauketa ba, shi yasa ya shirya iya shirya wa dan kar ya daukota aje tana da mugun nauyi ta kada kato a shiga uku, sai gani ya yi Sir da alkhyabarsa ya cicibo RAUDA ya mata daukan jaririya domin a hannayensa ya daukota ya juya ya nufi ciki, shi kuwa daga nan ya tattara kakayayakinsu ya ba Salima da ya dakatar sannan ya ja motar ya fice da ita dan sai ya mata sumul zai dawo da ita ya ajiye a muhallin ta sannan ya ba direban dake janta ky dinsa

A nutse yake nufar dakin Mah, tunda ya shigo din, likitar kuwa na take masa baya bayan ta risina ta masa Barka da karasowa hannunta rike da jakarsu na likitoci sannan ta bi bayansa kamar yadda ya mata alamu, yan matan dake zaune a falo na biyu kuwa suka yi mutuwar zaune suka bi abinda suke ganni da ido, dan babu wani abinda ya shafe su da reton da hannunta yake yi, abinda idannuwansu suka gane masu shine MALIK dauke da wannan budurwar da Mah ke kira baby, wace Mah ke yawon nuna mata kulawa a gaban kowa, Wada Mah tace y'arta ce bayan iyayensu sun sake tabbatar masu basu san lokacin da ta haife ta ba, ya nufi dakin Mah da ita , likita na biye da su, Salima na dafe mata baya....kusan sai suka rasa abin yi a zaunen nan, domin a dan zaman nan da suka yi sun riga sun fahimci in dai so suke yi su sayi wata zuciyar da zata iya kusanta su da YUSUF sai dai su sayi ta mahaifiyarsa, dan duk irin yadda aka nuna masu mutumen mutumen mata ne, abin na neman gagararsu, dan ko da wasa su dai abin nan bai tabata a kansu ba, sai gani sai hange tsakaninsu da shi, kusanci ko na kwabo sun kasa ciyowa daga fadarsa, ko a yanzun gaba dayansu tsoron karasawar inda yake ya saka su tsayawa da zubawa sarautar Allah ido!

Tunda ya bude dakin Mah Musulima ta dago daga vidio call din da take a saman kujera ta ji tamkar zata summa ta zuba masa ido, lokaci daya kuma ta mike tana daukan hijab dinta dake ajiye ta ware shi za saka ta fice a dakin dan tunda ya kalleta sau daya ya ja tunga ta san me hakan yake nufi, a dole ta saka hijab din da aka saka su saka shi dan dole a cikin gidan ta fice tana jin zuciyarta tamkar zata fito daga kirjinta, dan Allah yana ganni ita a zaman nan da farko an nuna mata wannan miji ne da ya dace da duniyarta dan sarautarsa da kudinsa, a hankali ta idasa gane ko bayan su, miji ne da ya dace da ita dan ya isa a so shi, ya haɗa qualities na mamaki, ya kasance jaruminta burinta, mafarkinta, ita fa ta jima da kamuwa da so din da koda bashi da komai tana iya rantsewa cewar zata iya zama da shi, bale ga ya'yan banki ga sarewa jama'a, kwarai a matsayinta Na yar Sarkin kasuwa ya dace ta zama matar MALIK, a nan sarautar zata gama haduwa gaba da baya

Direct bakin gadon ya kaita ya shinfidata sannan ya juya ya koma wajen kujerun nan ya zauna yana duban agogonsa da auna lokacin da Mah ke iya shigowa a zuciyarsa

Likitar kusan du Salima ta yiwa tambayoyi ita kuwa ta bata amsar gaba daya abinda ta sani dan haka da gagawa ta juyar da RAUDA ta shi bata taimakon da zai taimaketa ta hanyar fara duba ciwon da ya hadasa mata zubar da jinnin nan dan ba sumar ta fi damunta ba , ba kamar ciwon dan in har ya taba wajen da ba'a so dole a kaita asibiti a shiga bincike, domin ita summa ai ko da hannu ana iya summar da mutun in dai aka daki keyarsa bale da wani makami.
Ajiyar zuciya ta sauke gannin ciwon , cikin kwarewa bayan ta hade gashinta ta daure mata shi ta yi maganin ciwon sosai ta saka mata dukan abin bukata sannan ta daure mata shi da farin abin pansama sannan ta juyata ta dora kanta kan matashin kai mai laushin gaske ta shiga duduba jikinta sai dan balshe a cinyarta nanma ta saka mata magani sannan ta nemi jijiyarta ta saka mata karin ruwa dan kadan na dauke zafin ciwon , yana karewa ta cire mata ta yi mata allurar dake iya dawo da ita sannan ta zauna daf da ita tana rike da hannunta mai dauke da allurar nan dan sai ta farka ta ga zata ci gaba da yi mata ne har ta ji sauƙin ciwon ko daga wannan ya wadatar?

Bai fi mintina biyar ba Rauda ta ja wani Gwauron numfashi hadi da shedar da ya saka shi dago kansa a hankali ya zuba mata ido
Da farko tamkar a lokacin take shirin barin duniyar mutane ta farka, a hankali a hankali ta samu tana jin maganar likitar nan sama sama a kanta tana jimke da hannayenta bibiyu har ta gane a duniya take kuma magana ake yi mata a daf da ita

Idannuwanta ta bude da sauri tana waige waige, a birkicen nan da kake farkawa idan ka summa, lokaci daya kuma ta shiga kiran sunnan Abdul

Da sauri Salima ta karaso mata shi tana kallonta hawaye na cika mata ido ta saka mata hannunsa cikin nata tana fadin" Gashinan RAUDA ga Abdul din fa"

Shima tunda ya ga ta farka ya dora kansa a kirjinta yana fadin" Aunty, auntyna, auntyna"

Tunda kunnayenta suka ringa jiyo mata amon muryarsa ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idannuwanta hawaye na zubowa ta gefe da gefensu dan sarai ta gane a dakin Mah suke, kuma ta gane likita ce ke kanta

Baki ya tabe yana dauke kansa a ransa ya ayana' ka ga wani rusheshen d'a ta lalata shi, wannan katon saurayin yana wani runguza mata kai a kirji? Lalle su uwa masu dadi , shi dai soyayarsa da Mah ido ne ta tsolewa mutane ama ai wasu iyayen sun iya shagwaba ya'ya, shi bai isa ya dora kansa a kirjin Mah ba yanzu zata ture tace kai meye haka dilla kauce kar ka fasan kirji!' ( wai Ni ina hadinka da mu ne mai martaba?)

Dukkan kular da ta dace likitar nan ta bata sannan ta dawo wajen da yake ta masa bayanin zata dawo dole a gobe dan ta ga yannayin jikinta, idan da sauki shikenan sai ta cire mata allurar karin ruwan in kuwa dole sai an ringa zuwa saka mata magani har ta warware shikenan, abinda dai yake wajibi idan ta warware sai ta je an duba kan a na'ura dan harkar kai ana takatsantsan da ita.

Daga nan ta tafi, shi kuwa ya mike da hannunsa ya yiwa Salima alamun ta zo

Da sauri ta mike ta je, yana sake duba agogonsa ya ce" Ki zauna da ita har Mah ta dawo, zan je part dina"

Da to Salima ta amsa ya fice shi kuwa ya nufi nasa bangaren domin a yau zai yi transfer na kudaden kayan aikin da zasu shigo na ginnin fadar baki dayanta, dan a satin nan za'a fara aiki jajir , domin ya samu da kyar ya lalaba Hajia ta yarda a yi ginnin fadar a mamakeken filin dake jikin tsohon gidan fadar, nan din ya nuna mata yana so a bar shi matsayin gidan dukkan wasu da suka shafi fadar, su waziri da sauransu......

Sunna zaune ne Salima na fama da Abdul kan ya ci kwan da ta soyo masa ama ya kasa cin wani abin kirki dan hanjin cikinsa sun gama kulewa da horon yinwa Mah ta shigo da sauri tana masu salama hankalinta a kan RAUDA dake barci Mai nauyi da kuma Abdul da Salima

Jakarta ta ajiye da sauri ta karaso ta zauna tana dubansu zuciyarta na tsintsinkewa tana jin wani abu kamar tsanar matar da bata santa ba, itama bata santa ba na taso mata daga cen cikin zuciyarta

Dubanta ta kai kan Salima idannuwanta a kausashe ainun ta ce" Matar nan ce ta yiwa yarinyar nan dukan nan? Lalle yau ba zan iya hakura ba, sai na kuleta!, kennan ita ta dauki kannin na RAUDA? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, lalle akoy mutanen da basa jin tsoron Allah, na yi ta kiran numbobinku bana samu na yi tunanin baku ji ba ashe ku tashin hankali kuka tarar a cen din? Ba zata ci bulus ba walahi , dan na daina hakura kowani banza yana takani da ahalina dan son zuciya!"

Salima dake ta rike hawayenta muryarta a raunane ta ce" Mah, Ni ban taba jin tsoro irin wanda na ji yau ba, ba imani ba tausayi ta ringa maka mata abin nan, ga magangannu tana ci na alwashin itace ajalinta da yaron nan, yaron nan duba ki gani, har yanzu ya kasa zama waje daya du a tsorace yake da kowa, Mah da ace bamu je da direba ba na tabata sai ta idasa nufinta sai ta kashe tan.... ......."
Sosai ran Mah ya bace, kuma a yanzu haka in ba dan ta ga cikin aikin da ta baro YUSUF ba walahi da a yau yau sai ya dauki mataki ba sai gobe ba, ama da kyar da rarashi Mah ta dangana har goben, kuma ta amshi kiran da balaraben Rauda ke ta yi a wayar Salima domin ya jima da samun numbar Salimar saboda in yana kiran Rauda wani Sa'in baya samu, nan take shaida masa Raudar ce ba lafiya ama da sauki kuma wayar Tata basu san inda take bane, shima da kyar suka yi salama yana ta aukin fadin dan Allah ta rokar masa Mah ya zo gobe ama Mah fir tace zai zo ama ba gobe ba sai ta ji sauki, da wannan Salima ta je nata dakin ta tarar da yan matan Mah sun baje abinsu sunna sharar barci ta shige bayi dan yin wanka ta bar Mah na ta rarashin Abdul wanda da kyar ya yarda ya yi wanka Mah ta rasa abinda zata bashi ya saka , a dole tufafinsa ya maida ta kwonta da kudirin gobe in sha Allah an je a yi masa siyaya

Mah kwana ta yi tana taba goshin RAUDA har kiraye kirayen sallar asubahi suka farkar da ita

Kamata Mah ta yi ta shige bayi dan yin wanka, da kyar ta kyaleta ta yi sai da ta rantse mata tana iyawa, da dabara ta yi wankan dan har ga Allah ta daku fa

Tana fitowa daure da Tawul Mah ta bata doguwar riga da hijab itama ta shige bayin dan yin wankan domin ita har ta yi sallarta

A dadafe ta yi sallar ta gama, tana cire hijabin Mah ta fito, ta karasa wajen wando da rigar da ta dauko mata na barci ta miko mata, kaya ne mararsa nauyi ta umarce ta ta saka harda turare sannan ta kama Abdul dake gyangyandi suka fice dan tunda ta bashi wainar kwon nan jiya a baki ya yarda da ita, suka fita tare

Da kallo Rauda ta raka su, a hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dauki kayan nan ta saka cikin dabara, sai dai du yadda ta so kar daurin kan nata ya kunce sai da ya kunce, gashin ya bazun mata a jiki

A hankali ta duka dan daukar ribom din, kunnayenta basu ji mata bude kofar dakin ba, ta dauko ta mike tana dan lashe lebenta da ya yi fari fat ya bushe sosai ta gyara tsayuwarta cikin dabara ta shiga kokarin kame gashin, ama ta ringa jin juwa na yawo da ita
Ta kama abin gadon nan a hankali zata zauna Muryar Mah na yar dariya ta bude kofar ta shigo tana fadin" Baby yau na sha kokowa da Abdul, wai ba zan masa wanka ba, ga yaro to ko YUSUF ba sai da ya kai shekara goma ina darje shi a bahon wanka ba....."

Ido ya zarro ya juyo da dubansa ya zubawa Mah, wace ke dariyar abin tana bada labarin da a tunaninsa bai taba hasaso ko Bah ta ba shi ba, sau yau shi Mah ta budi baki tana masa tone tone

Shi da kansa bai san ya dan shagwabe fuska yana kallonta hadi da zarro ido ba, ita kuwa da bata san ya shigo dakin ba ta kame bakinta tana furta" Au, ashe bosss din na kusa"

RAUDA kuwa ta samu kanta ta zubawa fuskarsa ido, yadda ya yin da yadda Mah ta fada din sai ta ji dariya na son kubce mata duda halin da take ciki, hahahaha wannan garjejen karin shima an taba yi masa wanka? Uwa kennan....., sai dai bata yi dariyar ba ta dai saki murmushin da shi da kansa sai da ya gani har ya dan so shagala da kallonta dan bai taba ganninta a irin yannayin nan ba, yawanci ko tana fada, ko tana rizgar kuka haka dai

Mah ta rike caputuno din da ta yiwa RAUDA ama yake son karbewa tana fadin" ka ga ba fa naka bane, yauwa me ya taso ka da sassafe haka kamar ka san a raina ka kwana? Son ko ka kai karar matar da ta sak3ar min yarinya sannan ta sace min yaro ko yanzu na fita na je na kai, dan sai na rufe ta ta je ta hadu da yan daba irinta ko zata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login