Showing 39001 words to 42000 words out of 188741 words
kallo ba ya ce" Lafiya?"
A birkice ta ce" Iyi? A'a na ga kun dauketa zaku je da ita, ai summa ce kawai ba wani abun ba, idan kuwa da ita zaku je mu je tana farkawa mu juyo saboda kar su yi kiran bata nan, ka ga in kuɗi suka yanke sai ta kawo masu abinsu su bani mijina"
Bai taba tunanin zai iya haduwa da dan adam mai irin halayyar nan a nan kusa kusa a garin nan ba sai yau da Allah ya hada shi da ita, ya rasa mai zai yi tunani ko yace a kanta, ama ya fi ajiyewa ransa cewar bata da hankali ne matar nan
Kasancewar bashi da wani hadi da ita, kuma a tsayen nan dai itace kawai yar uwar yarinyar da suka dauka, duda liman din kansa ya bada amanar a tafi da yarinyar zasu zo suma sai ya dan sake cewa" Ki yi hakuri ki koma, ai zata dawo idan ta warware, Allah ya bayyana shi"
Ya juya ya bude motar ya shiga ya ga still ta kama abin motar ta bude
A haukace YUSUF ya kalleta ya ce" Ke, rufe min mota!"
A birkice ta saki motar tana ja baya tana bin motar da kallo domin tana rufewa ya tayar da motar ya yi gaba
A wajen ta durkushe cikin shiga uku da neman zaucewar tunani ta shiga kama sunayen Umar din da Rauda tana faman sambatu tamkar wace ta haukace, mutanen anguwa kuwa saboda Umar din da ita Raudar suka ringa yi mata sannu da adu'ar Allah ya bayyana shi, ama babu wanda yace ta tashi daga inda take bale ace ta je ta suturta jikinta da kyau ta dauki carbi kan Allah ya sanyaya masu abinda ya tunkaro su
Sai da ta gaji dan kanta ta mike ta nufi cikin gidan tana hada hanya
Tana shiga kunnayenta suka jiyo mata kida na tashi sama sama a yar karamar redionta
Har ga Allah sai da gabanta ya fadi, dan bata tunanin a kusa kusan nan akoy wanda zai saka mata kida a gida bayan abinda ya faru
Da sanyi sanyi ta karasa falon, nan ta samu Farisa ta dage sai dirkar rawa take yi hannaye a kugu ta juya nan ta juya cen tana bin wakar gwomja ta warrrr
Idannuwa ta zubawa Farisar kafin ta karasa ta dauki redion ta rotsa da kasa rai bace ta ce" Ke kina cikin hayacinki kuwa? Dan ubanki ubanki ne aka kawo kayansa da jinni kaca kaca ke kuwa kike rawa kina juyi bayan ba'a san a wani hali yake ciki ba?"
Galala Farisa ta yi itama da mamakin uwar Tata a fuskarta ta ce" Mama inace yanzu kika cewa kece ajalinsa dama, to dan an kawo maki cewar ya mutu ba shikenan ba?"
Mama sai da ta ji tamkar an dauki abu an datse kafafuwanta, saboda da gasken gaske mujirya ta kama kaffafuwanta ta nemi bugata da kasa daga tsayen da take
A rikice ta ce" Farisa fada nake yi dan ya daukar min kudi, ama ke kin san ina son babanki ko "
Farisa ya tabe baki ta bi bayan redion da aka rotsa ta dauke ta yi dakin Rauda da ita, dan tana so ta je ta dan bincika da wuri wuri ko ta samu na samu ta dan adana gefe kafin Raudar ta dawo, fatanta Allah ya sa ta bar wayarta da kuma jakar kudinta, kai da itama ta kile dan walahi tana ji tana gani zata ce itama saurayinta ya kawo mata iphone din, ai ba ita kadai take da damar yin saurayin ba dan wulakanci!
Tuki ne ya yi mai gaggawa, hankalinsa a kan Mahaifiyarsa dake ambaton sunnan yarinyar da yanzu yanzu ne ta ji sunnan ama kamar wata wace ta saka mata shi da kanta
Sunna karasowa ya fito dan sake daukan yarinyar ya kaita ciki kafin ma a kawo kujerar dora marar lafiya ko gadon, sai ya ga Mah ta cire mata hijabi ta cire mata ribom sai faman son tahsinta take yi tana jimke da hannunta da dayan hannun kuwa tana dan shafa gefen fuskarta a hankali tana fadin ta farka mana
Kansa ya dauke a kanta ya ja gefe har aka zo aka kamawa Mah aka dora yarinyar aka fita da ita aka yi ciki da ita
Wurin zama Mah ta samu ta zauna tana dafe kanta da hannayenta bibiyu
A nutse ya karaso ya duka gabanta ya saka nasa hannayen yana cire nata yana kallonta ya ce" kamar kin saka damuwar wace bakima sani ba da yawa a ranki Mama, Please ki sanyaya ba komai fa, zata farka ne yanzu sai mu maidata gidansu mu je gida ki huta"
Bayan zuba masa ido da ta yi sai ta samu kanta da cewa" Mu maidata? YUSUF mu maidata fa ka ce?"
Idannuwa ya zuba mata yana son gane me kennan
A sanyaye sosai Mah ta ce" matar da muka bari a gidan cen sam bata cencenci rikon yaro ba, ko nata ba zata iya ba tarbiyya ba bale wannan da take kishi da ita, Yusuf cewa fa take yi wai idan bai dawo ya kawo mata kudinta ba itace ajalinsa kuma itace ajalin yarinyar nan , Ni ban san tsakaninsu ba, ban san me ta yi mata da zafi har ta tsaneta haka ba, ban kuma san ko inada hurumin shiga wannan rigimar ba, abu daya na sani shine daga nan yarinyar nan zata je ne gidana kuma a gobe gobe zan shigar da karra dan kar matar ta rigayeni, Yusuf ai dadinta muna da sarakai masu adalci da hukuma tsayayiya, kuma a yannayin yarinyar cen ta yi shekarun da ta isa zabarwa kanta inda take son zama, Ni dai ina ji a raina kamar taimako ne zan yi, kuma kamar idan na yin Allah zai dubeni da idon rahama nima ya yafe min kura kuraina "
Idannuwansa ya lumshe a hankali , bai saki hannunta ba a sanyaye ya dora gefen fuskarsa a tafukan hannayenta yana jin dumin hannunta yana aukawa a tunani
Lokuta da dama idan ya zauna da mahaifiyarsa sai ya ji zuciyarsa tana girgiza , hankalinsa na tashi da nasa shima laifin
Mahaifiyarsa bata taba daina neman afuwar Ubangiji ba kan abu daya tal da ta aikata wanda bayan aikatashin ta rike abinta har ta haifi abinta kuma ta so ta raini abinta Allah ya amshi abinsa
Ama a haka a kulun idan ta budi baki zaka ji tana tsoron haduwarta da mai sama kan wannan abu, to ina ga shi jama'a?
Ya mayar da mace abin shigarsa dan samun nutsuwa
Yana yi yana hawayen bakin ciki da tashin hankali
Bai rasa abin ajiye hudu idan yana ra'ayi ba, ama ya kasa tsayawa waje daya bale ya ajiye din, ya yi nan ya yi cen da ransa
Kwarai shi din ya kasance mai aikata aiki mai munin gaske, wanda idan ta ji wa'azi wani lokacin yakan kasa rintsawa
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya dago idannuwansa yana kallon mahaifiyarsa
A ransa yake aiyana 'ni kuwa zan tsaya maki har sai kin kai ga cikar burinki dan samun nutsuwar zuciyarki Mah '
"Sir, ta farka, ama ta ki tsayawa mu mata allurar barci duba da bugun zuciyarta ya yi yawa ko ma samu ya dan daidaita mu yi mata gwaje gwajen da ya dace dan mu dorata kan traitment"
Mikewa ya yi , Mama ta bi bayansa suka nufi dakin
Budewa ya yi ama ya ki shiga sai Mama ce ta shiga sannan ya bi bayanta ya tsaya yana kallon Mama
Gadon Mama ta karasa da sauri ta zauna ta dago kan Rauda ta janyota ta rungumeta a jikinta da dan karfin da ya saka Rauda dawowa duniyar mutane har ta dan saurara daga rizgar kukan da take yi hancinta na shakar sansanyan turaran ruwan mama kunnayenta suka shiga jiyo mata kalamai a sanyaye kamar haka" me yasa zaki rikita kanki har haka ne? Kina son kamuwa da wata cutar ne? Waye ya fada maki ya rasu ne? Da ace sun kashe shi da wahala su kawo wayar nan, ina mai kyautata zaton yana raye sun yi haka ne dan su rikita mutane ya zamo da zarar sun yanke kudin da suke so a basu dan a amshe shi, kuma kin ga Honorable ya amshi wayar yanzu haka da ya ajiye mu ya tafi wajen commisiona na police dan ya masa maganar, Haba Rauda sai kace ba musulma ba? Koda rasuwar ya yi sai ki kasa yin tawakali ne? Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi RAUDA, idan har Allah ya so zai dauke maki kowa ne ya barki ke kadai, saboda wannan sai ki kashe kanki kema? Hana Rauda ki yi hakuri kin ji?"
Tamkar wace Mama ta tuno mata da wani gibi, ko kuwa kalmar hakurin daga bakin uwa ne bata saba ji ba ta ji a yau? Ko rungumeta a rarasheta ne bata saba samu ba? Abin dai ya shige mata zuciya har ya saka ta dago idannuwanta ta zubawa fuskar Mama mai dauke da ni'ima da haske mai daraja kallo kafin a hankali ta fashe da kuka tana saka hannayenta a hankali ta rike na Mama ta kai kanta a hankali ta ɗora saman kirjin Maman tana sake riƙe maman tana kuka irin na cikin makogwaron nan mai zafi da ratsa zuciya muryarta na sarkewa ta ce" Dama iyayena da kanaina sun rasu, shine kawai gareni sai Abdul, shine kawai gareni , su ne kawai dalilin da yasa nake tafe da karfina, idan na rasa su Ni na san Bani da karfin dazan iya jurewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, dan Allah Hajia ku taimakeni a samo min Abanmu, ko nawa suka yanka min zan biya su bani shi, ki nawa suke so zan basu Ni dai su bani shi"
Mama, tausayi, tashin hankali, mamaki duka sun hadu sun rufe mata zuciya, haba koda ta ji ta san wannan kam da wahala idan ta haɗa jinninda yarinyar irin yadda ta ringa jaza mata alkaba'i, haka kuma jin iyayen yarinyar duka sun rasu sai ya sake daga mata hankali, uwa uba kuma jin wai ko nawa ake so zata bada, aikin me take ne?
Shigowar docter da baban file a hannunta ya saka Mama bada hankalinta wajen docter, har zuwa lokacin kan Rauda a kirjinta tana dan dadabata a hankali, Yusuf kuwa yana tsaye ne yana sauraronsu
" wannan ba itace aka kawo jiya ba? " Docter ta tambaya
Mama ta tabbatar mata itace
Docter ya fita , jim kadan ya dawo tana sake bude takardar hannunta ta ce" To ai a jiya duka abinda ya dace na gwaji mun mata, sai dai idan kunna da bukatar a sake wasu to, dan jiya sir yace a mata komai dan lafiyarta"
Murya a shake sosai Rauda ta ce" Lafiyana kalau, gida nake so na je, Lafiyana kalau "
Mama ta dago daga kallonta ta kalli YUSUF dake tsaye bai ce masu komai ba, a tausashe ta ce" Eh yanzunma summa ne ta yi shi yasa muka dawo saboda wani abu da ya daga mata hankali, idan ba damuwa sai mu juya gida ?"
Likitar ta karaso ta fitar da abubuwan aune aunenta ta shiga auna RAUDA, wace lebenta ya yi Jajajir, hakama saman hancinta da wajen idannuwanta du sun kumbure sosai hakan ya sa da kyar take daga idannuwan , leben kuwa sai haske yake yi na abin kukan da ta ci
Da kula sosai likitar ta ce" kunna iya tafiya Madame, ama a sayi wannan maganin ta ringa shan daya idan zata kwonta na tsayin sati guda saboda bugawar zuciyar nan, kuma ta yi kokari ta cire damuwar dan yawan yanke jiki a fadin nan daga nan ake haduwa da mugun hawan jinni mai naci, Allah ya bada lafiya"
Daga nan ta yi gaba da kayan aikinta a hannunta
Mama ta dubi Rauda bayan ta dago kanta a tausashe ta ce" Kin ji abinda likita tace ko? Ki daina kukan hakanan, mu je gida ki huta za'a ganshi kin ji?"
Shi kam mamakin mama ya fi komai damunsa, su mata me yasa suke da saurin sabo? Haka kawai daga gannin yarinyar sai rungumeta take yi tana faman neman dagawa mutane hankali a kanta? Kai shi kam bai san me zai ce ba kam, ama Mama akoy rigima Allah kuwa, meye hadinta da wannan ne? Shi ba abinda ya bashi haushi sai jadadawa da take yi wai ko a je ko nawa ne zata biya? Shin aikin uban me yarinyar take yi da bata jin kunyar kowama ya ji? Kai subahanallah ashe rashin jin maganar mace haka yake da kayan haushi? Shi haushima take bashi kamar ya buge mata baki yake ji idan tace din nan ko nawa ne zata biya, aikin banza aikin wofi yarinya tunda ya santa cikin kaya kaya take? Shirme kawai!
Da kyar mama ta iya ganar da ita dalilinta na ta bita, sai da ta nuna mata ta ji furucin maman Farisa sannan ta yi gumm ta kasa cewa komai, sai alfarmar da ta nema kan zata je wajen kanninta gobe? Mamah kuwa ta nuna mata zata kaita ne da kanta dan haka ta samu yin shiru ta koma kukan zuci da addu'a ga wayarta a kirjinta wajen da za'a kaita kawai take jiran gani dan ta samu ta yi kira, ba zata iya rintsawa ba in har bata san inda uncle dinta yake ba, kuma ta san idan ta fadawa mutumen ta zai taso ko me yake yi ya zo ya nema mata shi, kuma ko nawa zasu yanka masa zai biya ne dan ta samu nutsuwa da kwonciyar hankali......
A lokacin da YUSUF ke tuki har ya dauki hanyar gidan Mama kira ya shigo wayarsa na Mahaifinsa
Dan rage tafiyar ya yi dan a tunaninsa ko ya zo asibitin ne bai gansu ba? Dan ya sanar masa sun taho gidan Mama
Yana dauka ya saurara yana jin Muryar mahaifinsa yana fadin" Yusuf, ka ganni na zo fada , ina tare da commitiona aka yi kirana cewar sarki ba lafiya, Hajia ce ta yi kiran nawa wai ba dama, shine na zo ka ganmu nan ance ba za'a kai shi asibiti ba, ama ana tsaye kansa ga likitoci nan, Ni ina ta lafiyarsa ne Hajia tace wai na yi kiranka in me kake yi, in a ina kake ka je maboyarka ku zauna har Allah ya tashe shi"
Tsai ya yi yana sauraron maganar ,.
Maboya?
Shi walahi ya manta cewar akoy maboya da aka masa wace abin ya bashi dariya a lokacin da akace a dukkan lokacin da wani abu ya taso ya je cen
Waje ne wanda zuwansama hatsari ne a yanzu dan dare ya shigo
Gashi sun ce idan suka ambata masa ya saki hanya kar ya bi cikin gari
Ikon Allah me kennan?
A tausashe ya ce" Abu, me ya hadani da wata maboya dan Allah? Gamu fa zamu je gidan Mah ne "
Mahaifinsa dake tsaye shi da Hajia wace ke zaune tana kallonsa ta masa alamun ya tirsasa shi, dan haka ya ce"
Sako zuwa gare ku masoya kuma mabiya wannan littafi nawa mai taken AZAL
*In sha Allah da zarar na gama free page zamu koma posting a telegram ne, dan haka wa'inda suka saye shi su yi kokarin sauke telegram, telegram, zamuna yin posting dinmu a cen ne, na gode*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*15*
*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*
*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
Mahaifinsa dake tsaye shi da Hajia ta masa alamun ya tirsasa shi, dan haka da yannayin nada umarni ya ce" Ka san idan akace ka je da dalili, ka je din sai na bukaci ka fito ka fahimta?"
Dan jim ya yi kafin ya bashi amsa da to
Hanyar ya dauka cikin tuki mai gagawa da kula, yana tafe yana kiran wa'inda ke ba wajen tsaro ya sanar masu shine zai shigo layin har ya karasa layin gidan da aka yi a cikin jeji wanda zaka dauka wani waje ne daban aka ware a cikin gari aka dankara wannan fasali da tsari na tsaro a wajen
Yana shigowa wasu maza hudu suka saka