Showing 45001 words to 48000 words out of 188741 words

Chapter 16 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9818

ta ce da mahaifiyar ta " dama akoy wanda ya cencata bayan RISLAN ne?, nagartar yana da ita, makaranci ne, malami ne, mai jin tsoron Allah ne, ba'a taba kama shi da wani laifi ba, kuma daidai gwargwado yana da kudi, me ake so a daurawa talakawa? Kar dai ace mashayi mazina................."

Harshenta ya datse saboda zazafan marin da Hajia ta sauke mata a saman kuncinta, rai bace sosai ta ce"








Asalamu alaikum, alhamdulilah mun tsaya bakin nan a free page, zamu nausa cikin labarin, domin AZAL din na gaba, rikicin na gaba, zazafar soyaya mai rikita zukata na gaba, darasi na gaba, kai ba zaka gane ba sai ka shigo mun tafi tare in sha Allah


Azal 16


A sanyaye sosai Hajia ta ce" Nana, dukda sarauta ce, hakane, a lokacin da aka ɗauki kukan rasa wani ake naɗa wani, sai na ga kamar kin yi gagawa da saurin neman zurowa cikin abinda yake iya zama shafafe sannan wanda ke wanze da maza a gabanki, Wacece ke? Shin bushewar zuciyarki har ta kai wajen nan ki dubeni ki kirayi YUSUF da sunnayen nan?, kar ki saka na zama yarinya kuma wace bata tsoron a je a dawo ya zamto na zauna nima ina tada maki jiya i yau, mai kashi a jikinsa ne zai zagi wani? Ko menene shi an jima da fadin waye shi a doron kasa, tun kafin a san zai girma aka gargadi garajena a kansa, dan shi din shine tsayayen namiji tsakanin maza, ko mahaifiyarsa ba zan iya gani in kyale tana wulakanta shi ba bale ke , ki kula, ki kuma godewa Allah a zaune nake yau, da ace kaffafuwana na iya tashi a daren nan sai an nada wanda ya dace da sarautar nan kafin a yi kowace irin magana, Nana ba zan so ace a rikicin rai da rai harda jinni daya ba, na fi so ace rikicin daga wajen gida yake fitowa, ama ki zage damtse shi din cen da ya tsole maki ido muruci ne, haka kuma Allah shi ke zamani idan har da rabon RILSAN ya hau mulki zai hau a gobe goben nan ama kar ki manta a kasar nan in har d'an mace ya hau mulki sai abin ya zamo babu mazan ko daya, ki sanyayawa ranki kar ki bari a gane abinda ke zuciyarki wanda nima nake daf da ganewa a yanzu!"

Gaba daya ƙafafuwan Nana nauyi suka yi mata, ta gaza motsawa daga inda take har na tsayin mintuna, sai da ta ga dare na karra yi ta mike ta fice ba tare da ta sake saka idannuwanta a cikin na mahaifiyarta ba ta nufi wajen da ta tabata RISLAN na nan ta saka aka yi mata kiransa

Tunda ya karaso ya ga yannayinta hankalinsa ya fara tashi, a tausashe bayan ya bi bayanta sun karra yin nesa kadan ya budi baki ya ce" Ki yi hakuri mama, Allah ya jikan aba sarki Allah ya sa ya huta, dama mu dukkanmu lokaci muke jira, Allah ya sa bakin wahalarsa kennan, ama a gaskiya iyalinsa basu kyautawa kansu ba,mama dama yana cikin wannan halin ama suka boye?"

"RISLAN, ba wannan ya kawo Ni ba, dangane da kujerar nan nake tsaye, domin kai nake so ka hau mulkin nan!" Nana ta fada kai tsaye tana katse maganar da yake yi a wani tausashe da wani karya harshe kamar mace, shi ba zai yi abu kaza kaza ba irin na maza sai da wani laluma da sanyaya magana

A dan tsorace ya kalleta ya ce" Mene? Mulki? Ni kuma?"

Zata bashi amsa ta yi dif sakamakon nufo hanyar da YUSUF ya yi hannunsa daya a wajen kunnansa ya aika kira , dayan hannun kuwa a dan jimke da alamu jira yake yi kawai a amsa masa kiran da ya aika

Da hannunsa ya dan dagawa RISLAN wanda ya nufo shi da sauri , hakan ya sa ya dan dakata yana jira ya gama wayar

Daga dayan bangaren RAUDA dake zaune idannuwa sun yi mata fulu fulu ɗan tashin hankali da tunani, ga wata bakuwar rayuwa, ko tace sabon tashin hankali na nufin nufota a tsiyace, dan Mah dake kwonce cikin wani irin yannayin da ya sakata shiga halin tsoro har ta dago kanta ta ɗora saman cinyarta a hankali tana mata karatu tana jin zafin jikin matar ya yi yawa hakan ya sa du take neman fita a hayacinta dan bata san yaya zata yi ba kuma, abin nema yake ya yiwa zuciyarta da tunanin ta yawa, sai take neman ta idasa fashewa da wani kukan da ya gama rike mata kirji da bakinta gaba daya, a irin lokacin ne wayar Mah ke ruri cikin kira'a tatausa tana neman agajin a daga

Kiran farko kasa dagawa ta yi, dukda ta ga sunnan mai mahimmanci ne a jiki, sai a kira na biyu ne ta daga muryarta a cen kurya ta furta" Asalamu alaikum"

Shiru ya yi da farko, a hankali ya kai dubansa fuskar RISLAN shi dinma muryarsa a tausashe sosai ya ce" Ina take?"

RAUDA ta dan hadiyi abinda ke mata kai kawo a wuya, ta dubi Mah da idannuwanta ke lumshe a hankali ta ce" Gatanan"

Duk irin yadda yake cikin zakuwa da son ta ba Mah wayar bai nuna a muryarsa ba, dan yanzunma Muryar wata iri da take bugun kanta ya furta" Please bani ita,"

A sanyaye ta cire wayar daga kunnenta ta dan dago hannun Mah da yake da dumi shima sosai ta dan matsa kasa kasa sosai ta ce" Hajia, waya ce, wannan da ya kawo mu ne, na saka maku a kunne?"

Mah ta lumshe mata ido, dan kanta sarawa yake yi sosai , sannan ta dan jimke mata hannu, hakan ya tabatar mata tana nufin eh ne

A nutse ta kara mata wayar tana kallon yadda Mah ke bude idannuwanta a hankali muryarta cen ciki sosai ta ce" Baka kyauta min ba"

Bata san me yace ba, ta dai ga ta gyada kai, sai kuma a raunane ta furta" Allah ya jikansa, ka zo gida YUSUF"

Magana ya yi mai dan tsayi, tana gyada kai kamar wani yaya da kanwarsa har dai ta saka hannunta ta dago wayar da hannun RAUDA ta kai wajen kunnen RAUDA sannan ta sauke kanta daga saman cinyar RAUDA din ta kwonta a nan dan gaba daya jikinta ya yi kamar ba nata ba ta lumshe idannuwanta tana ta addu'a a ranta

Rauda dake rike da waya tana jin saukar numfashin mutun, ama gannin ba'a yi magana ba itama sai ta ki yi ta ringa sauke numfashinta a hankali

Sai da ya yi niya dan kansa ya ce" Zan iya Bara maki amanar mahaifiyata kafin gobe da safe?"

Idannuwanta dake lumshe ta bude da sauri tamkar wace ta yi maye ta tsaida dubanta waje daya ta kasa furta koda A ne

A tausashen da yannayin yau ya haifar masa na rashin da suka yi da halin da mahaifinsa ke ciki da halin da kakarsa ke ciki ya ce" Ba zan iya fita daga inda nake a yanzu ba, ita kuma bata da lafiya, zaki iya zaunawa a gefenta ki rike wayar nan a kusa da ke, idan jikinta ya kiya ki sanar min?"

Yanzun kam ji ta yi ta gaza yin shirun, a dole ta budi baki tana kallon Mah ta ce" Yaya zan yi mata?, bata da lafiya fa"

Shima ya dauke numfashi a hankali ya ce" Addu'a zaki yi mata, zaki iya?"

Rauda ta ja numfashi a hankali ta ce" Zan iya in sha Allah"

Shiru ya yi na dan lokaci, kafin ya iya budar bakinsa kasa kasa sosai ya furta" JAZAKILAH"
Kalmar da ta sa RISLAN sake zuba masa ido har ya katse kiran ya maido da hankalinsa kansa

Hannu ya bashi suka yi nusabaha cikin alhinin rashin da ya zamo na su duka suka yiwa junna jaje a takaice sannan ya juya ya nufi ciki ba tare da ya karra koda kalma daya ba, sai a lokacin RISLAN ya juya ya koma wajen da mahaifiyarsa ta yi tamkar zuciyarta zata buga dan bakin ciki
Yana zuwa bata tsaya wata wata ba ta saka hannunta ta make gefen keyarsa rai bace ta ce" Haka ka zabarwa kanka? Yana tsaye kana jira tamkar uban gidanka? Ka fi shi nasaba dan a jikina ba dati!, idan har haka kake so ba damuwa ka je ka bi shi kamar kare da mai gidansa, ba daraja ba mutunci, yadda yake takamar yana da jinnin sarauta a jikinsa kaima haka, kuma kai ka fi shi duk wata daraja dan baka wulakantar da kanka ba!"

Kasa cewa komai RISLAN ya yi, kansa a kasa har ta gama fadan da bai san dalilinsa, fadan da baya so sam ace mahaifiyarsa ce ke yinsa, domin fada ne na rashin gaskiya, a gaban idannuwanta a dazun motocin wa'inda koda babu su baba BELLO a doron kasa kafin ya hau sai sun hau suka ringa shigowa, a irin wannan lokacin ya dace ne ace tana cen wajen Hajia an gama kimtsa wajen dan karbar bakin da tabas da yawa sun kamo hanya, ga wata rigimar da ta bilo ta rikicin sai an gurfanar da iyalan mamacin a kan rashin hankalin da suka yi na kin fadin rashin lafiyarsa, rikici dai kala kala wanda a tunaninsa a matsayinta Na mace daya a tsakaninsu zuwa yanzu tana cen tana neman mafitar da ta dace da su baki daya, sai ga wani gihitacen zance a bakinta? Allah ya yiwa wannan buri nata tsawa dan ya tabata zata jazawa kanta fitinar da ta fi karfin ta da su ƴaƴanta baki daya

Gaba daya shi ya wakilci mahaifinsa , hankalinsa ya rarabu gida uku, yana yi yana lekawa wajen mahaifinsa wa'inda matansa ke zagaye da shi hankalinsu tashe baki dayansu, domin babu wace zata so ace wani abu ya same shi daga nan zuwa safe dan bakin labarima irin wannan shine ace ɗan matar da suke yiwa wani gani gani ya haye karagar mulkin nan, kai wata har ta mutu a cikinsu domin abu ne da zai iya dukan zukatansu baki daya, hakan ya sa ba su ba, ba ƴaƴansu ba, kowane rike da carbi sunna masa addu'a kuma sunna jira karin ruwan da likita ya jona masa ya kare ko ya dawo cikin hayacinsa
Shi dinma wannan addu'a ita ta fi komai tsaye masa a zuciya, ba zai taba misalta halin da zai shiga ba idan muguwar Kadara ta biyo da shi ta hanyar nan, shi ya san ba zai taba yarda da wannan tatsuniyar ba, shi yasa hankalinsa gaba daya a tashe yake, sau uku yana dora hannunsa wajen kan mamacin nan a ransa yana rokon Allah, Allah ya sa ya ga alamun doguwar summa ce ya yi, haka kuma idan ya je wajen mahaifinsa ya duka daf da fuskarsa a sanyaye yakan ce" Abu, dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, Abu rasuwar dan uwanka na san dole zata gigitaka, ama ka tashi ka ji? Ka tashi ka masa addu'a sannan ka hau mulkinka, Abu Ni din gaba dayana yaushe ka haife Ni? Dan Allah ka tashi kar zuciyata ta buga ka ji Abu?"

Idan ya mike ya fito har duhu duhu yake gani, ga wasu masu tsaron da Hajia ta karro da taimakon commisionan yan sanda da sarakan da suka isa tuni an zagaye masarautar haka kuma kiri kiri idan ya motsa sukan motsa ne da shi, abin har ya fara neman zautar da dukkan tunaninsa dan ba zai iya misalta wannan tashin hankalin a kansa ba, ina ba dai shi ba

Yakan kirayi RAUDA ne a dukkan motsinsa, tun tana amsa shi idannuwanta biyu, har barci ya dauketa a bayan Mah a kwonce bayan ta shinfida masu bargo sun kwonta a falon tana yi tana taba goshin Mah din da yi mata sannu har barci ya yi gaba da ita itama bai hakura ba, a cikin barcin take dagawa idannuwa a rufe ruf dan ta gaji sosai ta amsa shi sannan ta mayar da idannuwan ta rufe har aka fara kiraye kirayen sallar asubahi ta farka sakamakon farkawar da Mah ta yi suka yi ido hudu

Da sauri ta shiga lalaubar hijabinta a dan birkice ta ce" Hajia kin farka? Yaya jikin?"

Mah da ta jingina da jikin kujera ta sauke ajiyar zuciya tana kirkiro murmushi a tausashe ta ce" Ki daina ce min Hajia, ba zaki kirayeni da Mama ba? Ko bakya so na zama mamanki?"

Kafeta Rauda ta yi da ido ta kasa cewa komai, tana kallonta ta ciciba ta tashi ta nufi ciki dan yin wanka domin ta dauri niya sunna gama sallah zasu kama hanya zata ga ubanda zai hannata fita yau a masu tsaron nan dan ba zata iya ba , zuciyarta na iya bugawa

RAUDA ta dauke ajiyar zuciya ta juya zata mike wayar nan ta kuma daukan kara

Sai da ta dafe goshi dan abin ya ishe ta ita kam sannan ta daga , tun kafin ya yi magana ta ce" Ta fa tashi , ta shiga wanka fa ka bar kiran hakanan mana ai da sauki ko?"

YUSUF dake zaune a dakin mahaifinsa kansa na sarawa , domin su har sun fito daga masalaci, baki sun gama cika ko'ina, mutane ta ko'ina, abinda ya fi daga masa hankali magangannun dake yawo cewar shi YUSUF shine magajin garin kai tsaye , ba kwane kwane, a irin wannan lokacin da ake ciki ba'a san halin da mahaifinsa ke ciki ba kuwa ba za'a nadawa mahaifinsa sarauta ba, ba zai taba yiwuwa ba, bale uwa uba sarakai sun iso ba za'a taba dora masu tsarin da ba daidai yake da sarautar garin ba, hakan ya idasa rikita shi har ya rasa halin da yake ciki, sai gashi ana masa magana a sama sama ana fadin ya daina kiran mahaifiyarsa?

Wani irin Gwauron numfashi ya sauke, bai iya cewa komai ba, duk irin abinda yake bakinsa bai iya furta wa ba, ya sake kai dubansa kan mahaifinsa wanda yake gannin tamkar da gangan ya ki amsa shi, sai dai ba maganar gangan jikin mahaifinsa ya rikice tunda suka kawo shi suka kwontar, kirjinsa bugawa yake yi gashi dama yana da ciwon zuciya dan tun a lokacin da aka so hanna shi auren mahaifiyar Yusuf aka tabatar da ciwon zuciyarsa wanda idan abu ya dake shi yake zubar da shi, sai gashi jiya wani abin ya dake shi kai tsaye wanda YUSUF yake gannin bai masa adalci ba idan har ya ki amsa shi ya mike ya amshi sarautar shi cen ya karata da ita

Mikewa ya yi har kamar zai kifa ya fito falon gidan, nan ya samu matan mahaifinsa biyu, sunna ganninsa ya ga sun sada kawunansu, kuma har ya wuce basu dago ba, hakan ya sake daga masa hankali, kennan da abinda yake faruwa?

Yana fitowa babbar harabar masarautar mai filin gaske wace ta fara cika da mutane masu bin nan nasa suka kuma biyo shi, a birkice ya nufi bangaren Hajia, shi ba ya dakatar da su ba, shi ba ya dakatar da mai sanar da jana'izar Sarki karfe goma na safe, da kuma nadin sarauta *MAGAJIN MAGAJI?, KAN UBANCEN BABU WANDA YA ISA YA DORA MASA WANNAN RIKICIN, INA BA ZAI YIWU BA, BA ZAI TABA YIWUWA BA!*

A rikice ya shiga, ko salama bai iya yi da karfin da za'a ji shi ba sai ganninsa aka yi

Da sauri tsofafi da iyaye da tarin matan dake wajen suka ringa gaishe shi da girmamawar da ta dake bata masa rai sunna barin falon har ya zama daga Hajia sai NANA a falon sannan ya kalli mai biye da shi ya mashi alamun ya koma waje

Yana tafia ya karaso kan kujerar da Hajia ke zaune, cikin shigar hijab mai ruwan blue har kasa dan ya yi mata zubul da yawa har kafarta mai dauke da abin karayar a ciki ta rufe ruf hannunta rike da carbi tana ja hankalinta a kansa ya zuba mata ido a hankali ya kamo hannunta mai rike da carbin nan yana kallonta a tausashen da rabonta da ta ga ya yi mata magana a haka har ta manta ya ce" Dan Allah ki katse wannan rigimar ba zan iya ba, dan Allah ki rabani da wannan fitinar ba tafiyata bace, ki dora wanda kike so ama ba Ni ba, ku yi hakurin ya tashi , ciwon zuciyarsa ne ya tashi ba tsufa ya yi ba, ba kuma ciwon da zai hanna shi mulki bane, Hajia ba zan iya ba, bana so!"

Hajia ta lumshe idannuwanta tana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da karfi, a sanyaye ta ce" MALIK!, kana nufin Ni na isa na nada ko na sauke?, kana nufin kace a cikin wannan tsarin ka ga maganar mutun a ciki? YUSUF a jiya ko Ni ban san zan rasa d'ana ba, bale har wani d'an nawa ya fadi rashin lafiya, kana tunanin inada ta cewa a wannan tsarin? YUSUF na sha fada maka, ka sanyayawa zuciyarka ka kuma dawo da hankalinka dan babu tamtama abinda ke yawo a jikinka tabbatacce dai dai idan lokaci ya rigayi fata......"

"Dan Allah ki daina min magana kamar Ni kadai na yi saura a cikin jikokin ki, kin san ko ina yaro abinda na fi gujewa kennan, ko aure ban yi ba , ban san darajar abin ba, girma ne da ya fi karfin mutun irina, Ni dan kasuwa ne, Ni mai tafiye tafiye ne, rayuwata ba irin ta sarauta bace!" Ya fada wannan karon a kasashen da ya saka Nana dubansa ta dan matso ta tausasa muryarta tana dubansa da kyau ta ce" Haka nake ta kokarin kwatantawa Hajia, ama har ta mareni, na fada mata ga RISLAN nan, ama ta kasa yarda, ko kasar nan ba zasu yarda da sarautarka ba, tunda baka boye waye kai, ka fita ka ji yanzu haka cikin rigimar da ake a kan maganar nan, Hajia, Hajia...."

Ta fada tana duban Hajia ta sake fadin" Hajia kina da damar fada koda a kwonce kike a aikata maki, dan kin isa, ki bashi abinda yake so ki dora wanda ya cencenta "


"Tabas a kan maganar nan, kowa zai gane Wacece Ni, na rantse maku a kan wannan sai dai raina ya fita daga gangar jikina, ku rubuta ku ajiye a yau idan girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login