Showing 51001 words to 54000 words out of 188741 words

Chapter 18 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9830

da jinni a kansa, hakan ya sa kowa ya fahimci ma'anar mikewarsa da kuma karshen furucinsa, ciki harda wace ta janyo dala da Gwauron dutsen wato Nana

Mikewa ta yi, a matsayinta Na mace, wace take uwa daya uba daya da uban wanda ake maganar , wace duk kunnuwa suka so jin bayanin ta dan an san idan akace YUSUF an ce ita, ta yi salama da mutuntawa sannan ta fara bayani kamar haka" Kwarai dukkan abinda aka fada a kan YUSUF hakane, sannan shi din da kansa baya son mulkin dan ya san bai tashi barin aiyukan da yake aikatawa ba, duk wani wanda ya san ahalina ya san muna dauke da jarabawar da daidaiku ke cikin tsarewar ubangiji, YUSUF duk wata masifar lalacewa ta taru a kansa!"

A wajen wanda bai dubeta a zabure ba daidaiku ne da suka san kwanan zancen, Hajia kuwa zuciyarta nan take ta ringa sukanta da karfi da ya sa ta rike kujerar da take sama ta rintse idannuwanta tana rokon Allah ya sa a gama taron nan kar ta lalata masu dan har jikinta rawa ya dauka

Cikin wata murya da ta dauka Tata ta ce" Bayan shaye shaye har aure ya ki ya yi, kuma yana son sha'anin mata tamkar wanda zai bi daba!"

Rai bace SHAHEED ya zuba mata ido, haka RISLAN

Bata ki dakatawa ba ta ɗora da fadin" Da wannan nake rokon kar a bashi mulkin kasata, dan idan aka bashi bamu san yaya zata kaya ba, ga dan uwansa RISLAN, a wajen nan babu wanda bai san waye shi ba, yaro mai mutunci mai mutunta manyansa, ga addini, gashi yana da iyali, RISLAN shine ya cencenci zama sarkin kasata "

Da wani shakiyin murmushi Jabiru ya mike yana kallonta ido cikin ido ya ce" To ko ke kika aika sakon nan ne?, kina nufin kanki ya yi cushewar da zaki sako mana zancen banza a nan?, kina tunanin Muna raye zaki dauki sarauta?"
Irin yadda ya kare maganar yana zarro mata idannuwansa da daga mata murya sai da ta ji tamkar zata kifa a wajen, sai a yanzu wani abu ya ringa zuwa da dawowa a kanta, tana tunanin ta yi nasara ashe da sauran rina a kaba? Idan har sarauta ta fita daga hannunsu ita ta san sai ta fi kowa wulakanta a ahalin nan dan kuwa ta fi kowa tunkaho da gobara saboda sarautar nan

Mai maradi kam abin ya girmami tunaninsa, takaici ya gama rike masa zuciya, hankalinsa ya yi mummunan tashi kuma ya sani ne idan har aka yi abin son rai tabas za'a samu bacin rai a wajen nan

Asalin shugaban masu kare yancin talakawan ne ya mike yana son daidaita hargitsewar da wajen ke son yi, dan idan ka dauki magana ba'a katse ka sai ka isar da sakon ka, kuma idan ka kai kara ba'a bayana wa ya kai

Yana kokarin dakatar da maganar Sultan SHAHEED ya mike tsaye yana bin kowa da kallo

Daga yanda ya jimke sandar da ta zame masa ta sarauta zaka gane irin yadda ransa ya ɓaci

A nutse ya shiga nufo filin har ya karaso tsakiya, hakan ya sa daga jibirin har Nana yin baya sosai ciki banda shugaban masu kare yancin talakawan dan dukar da kansa ɗan sarakai basu fara magana ba, kuma yana da damar rarashi idan har rai ya ɓaci, dan haka a tausashe ya ce" Allah ya taimake ka, ka yi hakuri da shige cikin maganar da aka yi, in sha Allah ba za'a kuma ba"

A tausashe, sai dai kana jin furucin ka san rai a bace yake ya budi baki yana dubansa ta saman ido ya ce" yaushe muka yi zubewar da zaka tara mu, a gabanmu, ka zagi jinnin mu? Koda kuwa kana sanar da yadda aka kawo maka karra ne bamu cencenci darajantawa ba ko dan magabatanmu?"

A tausashe ya yi maganar, ya yita be har karshe, yana ajiyewa Sarkin bulala da karfi ya budi baki ya maimaita yana iza maganar ya ce" A gaban sarakan kasarka zaka zagi ɗan sarki, jikan sarki? Kai din baka da kara da girmama masu riko da ayar Allah ko zaka mana tutse cikin ganganci ne?"

Sarki SHAHEED ya dora da fadin" Yaya zaka ajiye mu, ka daidaita abinda bai isa rabar hanyar mu ba, dan kawai ana so a kawo darajarmu daidai da kowani dan Adam bayan Allah ne ya dora mana rawani ba wani ba?"

"Kai ja baya dan talakawa ka kai uban damagarawa kurya uwar daka, ja baya dan a yi kare jini biri jini da mu ba komai bane, rayukanmu muka miko dan yaki da gaskiya babu ruwan mu da takarda, kai ja baya dai auna tsayinka da wanda ya isa kuma wanda Allah ya nada !" Sarkin bulala ya sake wage muryarsa yana fada har kamar zai fasa wajen dan kaurin murya ne da shi sosai

Rai bace sarki SHAHEED ya juya wajen sarakan nan ya dukar da kansa sosai ya furta" Ku min afuwa, idan na yi laifi a hukuntani, ama idan har kuka yi shiru ina tsoron a kai ga taba darajarmu da mutuncinmu, dan idan mai turawar wawa ne mai zartarwar ba wawa bane, ana so a shigo Mu ne a boye dan a cin mana bamu gane ba? Ko rawaninmu ya yi hawan banzar da za'a sakani saukewa a bainar nasi? Innalilahi Wa ina ilaihi raj'une kalmar da take tabataciya, mudin raina har na koma gaban Ubangiji a yau ina da ja da raini da sabon salon wulakantarwa da ake son sako min dan a shigeni ta hanyar da bana so, idan kuwa sarauta karya ce na ajiye rawanina!"

Yana fada ya sake sada kansa ya shiga kunce rawaninsa, kuncewar da ta girgiza duk wani wanda yake wajen ta nemi daga masu hankali bilhaki

Da sauri YUSUF ya dago kansa yana gannin da gaske rawanin zai sauke? Idan har haka ta tabata an yanki yakin da har shi ba zai bari ba, a birkice ya bi ayarin wa'inda suka mike suka nufi sarki SHAHEED ciki harda shugaban masu kare yancin talakawa da sauran da suka zube kasa kawunansu a kas

Yana karasawa ya damki rawanin dan sai hakuri ake badawa ama fir zai rainawa mutane hankali

Da karfi ya matsi hannunsa a hankali ya ce" Kar ka soma!"

Bayanan da ake yi na bada hakuri wa YUSUF Sultan SHAHEED ya dauka shima a tausashe yana kallonsa ya shiga bashi hakurin, wanda hakan ya saka Mah sakin kukanta muryarta a boye

Rawaninsa ya maida masa yana dubansa, a lokacin ne Sarkin maradi ya budi baki bayan an dan sassauta rikicin ya ce" Tabas ana nufo mu da rikicin da gaba kadan mu ne zamu kai hari ba tare da an hau ko an sauko ba, ta yaya da ransa da lafiyarsa wani zai yi tunanin kai rawani wani gidan? Shin sarauta wasan yara ne? Ko an fada maku sarautarmu ta yanzu ba sai mai kokari ba? Idan nace kokari ina nufin wanda zai iya ciyar da talakawansa, dan mun jima da ɗaukan nauyin kasarmu ba tare da jiran sai an bamu ba!, waye zai rike a yanzu? Idan kunna da ja din ne har yanzu ku sai takobi ta yi aiki!"

Idannuwa YUSUF ya sake rintsewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une ta tabata fa, ya Salam zata tabata a kansa? Ya san za'a hau a fado ama bai yi tunanin zasu shigo da korafin ta sigar rainin da sarakai zasu ki dauka ba,

Yana ji yana gani aka ringa ba junna hakuri, aka ba zaben damar da za'a yi shi da mutuntawa ba tare da an kawo harka ta rashin da'a ba, zaben da YUSUF ya koma gefe yana bin duk wanda ya dangwala masa hannu matsayin shi ya zaba da kallon baka kyauta min ba, abin mamaki harta manyan malaman garin shi suka zaba wanda hakan ya bashi mamaki ainun, har dai magana ta tabata a kansa aka kuma maidoshi tsakiyar filin nan kansa na sarawa sarakan nan suka zagaye shi da Sarkin nadi kowa ya mike nadi ya tabata a kansa, nadin da ana nadawa masu dauka na dauka a vidios, masu dauka na gidan rediyo na yin nasu aikin summa, abu dai ya zo a lokacin da bawa bai jira ko tsamata ba, duniyar YUSUF ta yi girgizar da bawa ba zai gane komai ba, har aka gama aka fice aka bar shi da mutun uku kawai, Mahaifiyarsa wace ita dinma kaffafuwanta ke neman gaza daukanta, hawayenta kuwa har sun kafe, kakarsa wace ita dinma ta sha hawayen kuma ta gaza dauke dubanta a kansa, sai SHAHEED wanda ya tsaya ne saboda abinda yake son fara sanar masa a kan ISHAK, sai dai gannin halin da iyayensa ke ciki ya gaza masa wannan furuci karshema ya yi doguwar addu'a ya rike hannunsa sosai sannan ya masa alamun zasu yi waya shima ya fice tare da taron jama'arsa suka tafi

Sunna fita Hajia ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa, a sanyaye cike da girmama ta furta" Malik, a tsakanin sati guda zaka shirya komai na fadarka, ya dace ka yi dogon......"

"Hajia......" ya fada da wata irin murya mai cike da galabaita da kuma tarin gajia da rauni

Kai ta sada a hankali ta furta" Allah ya huci zuciyarka, bari na je cikin gida"

Daga haka ta matsa kujerar Tata ta juya da ita ta fice da ita daga falon bayinta suka rufa mata baya da tarin jama'ar dake waje, a nan ta sake zubawa RAUDA ido, wace ke zaune tun zuwansu da Mah aka hannata shiga bisa umarnin Hajiar, sai kuma ta dauke kai suka shige ciki

Kansa a kasa Mah ta saka hannunta mai dauke da dumi ta dago fuskarsa, a hankali ta sakar masa murmushi sai hawaye ya bale mata, tana kallon rigar da aka rufa masa ta alkyaba, da rawanin da aka naɗa masa da kanshin da aka fesa masa, a yau tana ganninsa da wani irin girma da daraja ne wanda bakinta ya kasa misaltawa, a raunane sosai ta ce"







...............AZAL😍😍😍😍😍

Azl 19


A raunane sosai Mah ta furta" MALIK!"

Idannuwansa ya lumshe zazafan hawayen da yake ta danewa suka samu sauka a tafin hannayen nata, a hankali ya sake dora gefen fuskar nasa mai dauke da saje wanda abin rawanin ya rufe a hannun nata yana jin inama zai iya kuka wiwi irin na mata? Da ya yi ya ji sanyi a zuciyarsa

A hankali ya mike ya dawo da ita saman kujerar ya zaunar da ita sannan ya duka ya dago kansa ya sake zubawa ni'imtaciyar fuskarta mai dauke da ni'imar haske irin wace d'a ke gani a duk lokacin da ya ga fuskar mahaifiyarsa ya ce" yaya aka yi kika tashi? Nace kar ki fito fa zan zo na kai ki asibiti"

Murmushi ta sauke masa a hankali ta ce" Kai, yaya zaka duka , so kake a leko a dakeni ace na saka Sarki sun dukawa?""

Murmushin da bai yi niya ba ya yi, sai dai ba irin mamakeken murmushin nan bane, kadan ya yi mata ko zata ji sanyi, domin ya kula abinda take so ta gani a fuskarsa kennan, a hankali ya ce" Anya akoy wanda zai hannani dukawa a gabanki a nan duniya kuwa?......"
Sai kuma ya sake dubanta ya sauke ajiyar zuciya, so yake ya tambayeta shin yaya zai yi ne yanzun? Sai kuma ya kasa, saboda ya sani ko a yanzu tana da bukatar hutawa, sannan ya san irin tashin hankalin da take ji na rashin lafiyar mahaifinsa shi yasa ya yi shiru sai ajiyar zuciya sai kuma ya dubeta ya sake jimkar hannunta

A tausashe Mah ta ce" Bari in je wajen abanka, ka ga mutane zasu shigo wajenka yanzun, Please take care"

Kai ya gyada mata , ta mike ta hanna shi yi mata rakiya kamar yadda ya saba a da , dan ta riga ita ta yarda dole ne yanzun cenji ya samu ta kowane fanni a rayuwar yaron nata da ita din kanta, ama duda haka tana kallo bai zauna ba sai da ta ja baban kofar ta madubi ta rufe yana tsayensa ta shiga neman y'ar amanarta

A lokacin ne yan uwanta suka kuma zuwa, dan babu wanda ya tafi ashe, hakan ya bata mamaki gannin basu tafi ba, su uku rigis, maza biyu, mace guda

Da wata irin mutatawar da suka jima rabonsu da yi mata irinta ko magana irin haka suka shiga yi mata barka ba tare da sun kireta da sunnan da suka lakaba mata ba tunda Kadara ta sauka a kanta da uban ƴaƴanta wato mamar soyayya

Da kula sosai ƴaƴanta mai suna AGO yace" Mu karasa daga cen mu yi magana ko Andiya"

A yanzunma abin kallo ta maida su, ama bata ki binsu ba dan ta sakawa ranta su je su mata wankin baban bargo ne kamar yadda suka saba

Sunna zuwa da kula sosai Herde ta ce" Andiya, dangane da shirin gagarumin bikin da ya dace mu yiwa Malik da kuma nunawa duniya eh danmu yau ya kai matakin sarauta ne su yaya suka ce mu yi shawara mu ga nawa nawa ya dace mu hada sai a shiga shiri dan Bama so mu amshi ko sisin kwabo din Sarki, mune nan zamu masa matsayin iyayensa, ke a ganninki nawa nawa ya dace?"

Yanzun kam da tsoron rayuwa da mamaki take binsu da kallo har sai da autansu mai bi mata ya ce" Aunty yi magana mana yanke ko nawa ne mu je mu shiga shiri dan gaskiya Ni wanda zai yi girkima sai na dauko mutun daga waje"

Idannuwanta ta lumshe, ta rasa gane a wani yannayi take ciki, abinda ta sani shine yannayin da take ciki ba na farin ciki bane, dan kuwa wannan yannayi da ta jima tana mafarki a yanzu da yake bayyana kansa a gare ta a dalilin wani baban dalili na rayuwarta sai ta ji bata farin ciki da maraba da shi, a sanyaye ta ce" Biki kuma?, rasuwar da aka yi fa? Kuma kun san mahaifinsa bashi da lafiya , inaga ba wani biki da za'a yi da ya huci a masa fatan alkhairi da nauyin da ya hau kansa da addu'ar Allah yana taya shi riko"

Su Dukansu sai da suka yi jim, sai kuma Herde ta ce" Hakane, an yi rasuwa, ama gaskiya koda a cen baban gida ne idan abubuwa suka lafa zamu yi taron murnar nan , dan abin a yi murna ne, Allah ya ba Honorable lafiya"

A saman lebenta ta amsa, ta shiga alamun tana son tafiya

Ba wani kunya Ago ya ce" Kin ga ku je cikin ku zauna mu bari mu tafi wajen mazan mu zauna , yarenma sun ce gasunnan zuwa ai da iyayensu"

Yanzu kam abubuwan su sun fi karfin tunaninta, bata iya basu amsa ba sai komawar da ta yi ta shiga neman RAUDA, da kyar ta ganta zaune da wayarta a hannunta, yannayinta har yanzun bai koma normal ba dan har yanzu bata san yaya take ciki da batan uncle dinta ba, da kuma halin da kanninta yake ciki shi yasa take jira Mah ta dawo ta fada mata tana so ta je Damagaran dan ta ji halin da ake ciki da uncle dinta da kuma kanninta

A nutse Mah ta yi mata salama

Da sauri RAUDA ta dago, ta mike tana amsawa a hankali gannin wata mai kama da ita sosai a gefenta tana binta da kallo

Kai ta sinne dan sai ta ji kallon wani iri, domin irin kallon nan ne ba karewa mutun kallo tun daga sama har kasa

A tausashe Mah ta ce" Mu tafi ki karya"

RAUDA tun a nan ta so fada mata tana son tafiya, ama ta kasa, ta bi bayanta bayan ta riko hannunta kamar wace ta riko wata mai yan kannanun shekaru suka nufi cen baban bangaren famillyn, sunna tafe ana yi mata gaisuwa ta mamaki, gaisuwar da a da Bata samun rabin rabinta sai idan ta shigo fadar da mijinta ko da danta, sai gashi yau ita daya dinta ana gaisheta da girmamawa ta mamaki

Ajiyar zuciya ta sauke kawai ta girgiza kai, suka shige baban falon da salama a bakinsu

Yaran ne kawai a falon daga mazan har matan , sun yi jigum abinsu dan babu wani mai walwala ko sakewa a cikinsu, saboda rashin lafiyar iyayensu

A tare suka ringa gaishe da su Mah, saboda koda iyayensu na koyar da su wasu halayar a boye sunna da karfin gabatarwa ne a gaban idannuwansu, idan basa nan sunna jin tsoron yayarsu sosai dan bata cika shiga lamarin su ba, halayarta kusan na Bah karami ne, shi idan dai magana ta haɗaka da shi bukatarka ka kai ya gyada kai shikenan, daga nan ba kari ,

Amsawa Mah ta yi ita kadai da kula sosai, taba tambayar su iyayensu

Yayarsu ta sanar mata sunna daki, dan haka ta dubi yayar tasu da yar fara'a a fuskarta ta ce" Salima, Please ga y'ata nan ki saka a yi mata abun kari, sannan ga ky din dakina nan ki saka a tsaftace min na san ba dai dati da kura ba "

Da sauri Salimar ta amsa tana fadin" To Mah, bari in kira masu aiki yanzu a yi, bakuwa zo ki zauna a wancen falon "

Mah ta yi mata alamun ta je, a dole Rauda ta nufi wani falon a zuciyarta tana mamakin fasalin ginnin da irin tsarin furniture din dake ko'ina

Herde ta kasa hakuri bayan sun nufi bangaren Bah da sabon yannayin girmama Mah ta ce" baby wai wannan yarinyar fa wacece?"

Mah ta kama kofar dakin da ta dan juyo da kula ta ce" Bari in ga yaya dakin yake,"
sai kuma ta dan saki murmushi ta ce" Lah wai Raudar ce baki sani ba? Y'ata ce fa"
Daga haka ta yi shiegwarta ta bar yar uwar ta da baki bude cike da matsanancin mamaki da tunanin maganar Tata, kai ina ba gaskiya bane, bayan YUSUF ai Andiya bata kuma haihuwa ba, bata kuma haihuwa ba tabas, tunda ko yanzu ai kamar ta gabatar da wancen yarinyar ne a wajen su Salima ko? Idan yar uwarsu ce har sai an gabatar da ita anya kuwa?

Jira ta yi har Mah ta fito daga dakin idannuwanta sun yi wani iri, suka shiga ta masa addu'a ta koma falo ta zauna dan yanzu ta ga wajen zama,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login