Showing 105001 words to 108000 words out of 188741 words
sai zagayeni kake yi da nuna min kun ishi kanku kai da mahaifiyarka ko? ba damuwa bari ita aishar ta sanar min!" ya fada ya juya ya nufi ciki dan sarai ya gane akoy abinda RISLAN ke zagayewa, sai dai ya makaro haihuwarsa ya yi ba shi ya haife shi ba bale ya zagaye shi a magana ya yi shiru ya masa biyayya!"
Bah na shigowa ya tarda Hajia zaune saman kujera, Nana na zaune saman cafet hannayenta duka biyu a saman kanta tana kuka kasa kasa Hajiar kuwa na magana mai kama da fada
har ga Allah bata san cewar Bah ne ya shigo ba, da ta yi shiru kamar yadda YUSUF ya nuna baya so mahaifinsa ya san abinda y'ar uwarsa ta aikata dan ya kula yanzu Bah yannayin ciwon zuciyarsa na so ya zama abu kankanima na tada shi, dan kuwa da ta ita ne da tuni ta sanar masa walahi, Bama kamar in ta ga Nana na fira da Bah normal sai abin ya ringa bata mamaki da tsoro, ta rasa a wani bigiri zata ajiye wannan halaya ta Nana, sosai take tsoron irin halin Nana, har ga Allah ko ita mahaifiyarta ta tabata idan abin son rai ne ya tasowa Nana tsaf zata zabi kanta ta barta, shi yasa itama ta yi watsi da ita take rayuwarta dan bata son mutun mai irin halin nan
Hajia ta ci gaba da fadanta tana fadin" Yanzu wa gari ya waya?, kin ga tun qq duniya kema Allah ya baki mai irin halinki sak, kuma ya saka maki kaunarta a ranki, sai ki ji abinda nake ji, Nana sai ki ji abinda nake ji a raina nima, kina dai ji kina gani , baki isa ki tsawatar mata ta daina abinda kika san ba zai taba yiwuwa ba, kina kallo ba zaki iya hanna y'arki son makiyinki ba"
Nana ta dago da sauri tana kallon Hajia, murya a rikice ta ce" Makiyina kuma Hajia?"
Hajia ta zabga mata harara ta ce" Makiyinki mana, azaluma! makiyinki mana, yaron da tunda ya fara wasu yan rashin ji kika sako shi a gaba, a hankali kika saka mahaifinsa ke jin haushinsa, kika saka yayanku ke jin haushinsa, sannu a hankali Allah ke nuna maku shi yake da damar yi ko hannawa ama kuka kasa ganewa, ki zage shi ya ciyar da ke, kina ji kina gani da aikin naki da gadon baki yake ciyar da ke da mijinki, duk bai ishe ki ishara ba kike ci gaba da zagi nai, a gabansa a gaban iyayensa bakya jin kunya ko tsoron zuciya, kina tafka rashin mutuncinki yadda kika so, Nana kika janyo min comitin kare hakkin dan Adam Ni? dan kawai ance ba za'a dora danki sarauta ba saboda Yusuf na raye? kika zo kika kwashi kayan kunyarki duk irin yadda kika mike gaban duban al'uma kika zage shi kika ce mashayi ne, mazinaci ne ba zai yi sarauta ba aka bashi sarautar, kika ci gaba da rayuwa karkashin sa dan rashin kunya ance ku kauro kika kauro , kika ci gaba da rayuwa karkashin sa, to ta yaya Allah ba zai kama ki ba?, Allah ya bata lafiya kawai idan da rabon ta tashi ama Ni dai ba zan taba tarban YUSUF da maganar ya auri Dayana ba, sai dai ta mutu in mutuwa zata yi!"
idannuwansa ya saka cikin na Nana wace ta dube shi a yannayin tsorace, hakan ya sa Hajia juyawa itama da sauri dan har ga Allah ba zata so ya jin ba dan itama jimawar nan da ya yi cikin rashin lafiya Allah kadai ya san Irin halin da zuciyarta ke ciki, komai sai ya so cakule mata, domin sai ta zama ita kadai ke kai kawo a kan lamarin rigimamenta, danma yana jin maganar mahaifiyarsa ai da sai ta yi kuka da idannuwanta na rikicewar tunani, sai Allah ya taimaketa yana jin maganar mahaifiyarsa, ita kuwa mahaifiyar tasa tana yi mata biyayya tamkar y'ar da ta haifa da cikinta, dan ita da kanta tana jinjina kawar da kai da biyayar AMEERAH, tana kuma godewa a ranta, bata taɓa nunawa bane.
"Bello, kun dawo?" Hajia ta fada tana kokarin mikewa dan har yanzu bata kaza kazar da kaffafuwanta , kai tama hakura da samun kuzari irin na da ta saka a ranta ta yiwu tsufa ya sa kuzarin tafiyarsa , danma tsufa ne na mai jin dadi, dan tuni daidaikun wa'inda suke raye da suke shekaru kusan daya suka yi yarinta tare tsufan ya gama kai su kassss , dan harda wanda abin shirficewa ta same shi, ama ita da sauki sosai
Karasowa Bah ya yi a hankali ya kamata ya mayar da ita saman kujerar ya zaunar da ita sosai sannan ya zauna shima daf da Hajia sannan ya sake kallon Nana yana jin irin yadda zuciyarsa ke babalewa
a hankali ya furta" Haka kika yi wasa da zumuncin Allah? ashe dama irin yadda kike aibata shi dan naki ya samu shiga ne? ama Ni ai ban taba bambanta yayanmu ba, na dauki wa'inda kika haifa tamkar Ni na haifa, ashe Nine ban iya son d'a ba ko ban san zafin haihuwa ba? shine kika so ki sa na tsine masa, Ni nawa ya bi duniya ko? ashe kema kina son taki duk irin abinda yake yi? kina mancewa da irin yadda Allah ke nuna mana YUSUF mai daraja ne?, kar ki manta lokacin da kika kaini wajen wani mutun wai mai bada magani yaro ya bar rashin ji, mutumen yace ki fita yana son magana da Ni, kin san me yace? cewa ya yi daga Ni har ke sai mun ji kunya idan bamu daidaita mu'amalarmu da wanda Allah ne ke tsaye a kansa ba mutun ba, yace mu kiyaye domin shine zai ciyar da mu a gidan duniya?, duka Wadinnan abubuwan da kike ganni basu isheki ishara ba ko?, Nana kin ji kunya, kuma kin ci amanar zumunci, ama Ni a wajen Allah nake nema, kuma ko yanzu zan yi domin Allah ne, Hajia dan Allah idan har ba damuwa ki bani dama na kwatanta sanar masa ya aureta, idan har ya yarda shikenan sai a hada da ita a Daura masa biyu, na san zai yarda ne bi izinillah , ai hannunka baya taɓa rubewa ka cire ka yar, Allah shi kyauta"
Daga nan ya mike ya ficewarsa a bangaren Nana wace gaba daya bata taba jin hankalinta ya yi mummunan tashi a abinda take aikatawa ba sai yau, wani tsoro da firgici ke neman rufeta, tunda take yin abin nan, duk abinda ake yi, mahaifinsa bai taba ganewa ba, kuma bata taba tunanin idan ya gane din zata wani damu ba sai yau....kasa dago da kanta ta yi har Hajia ta kara wanketa tasss ta leka dakin da Dayana ke kwonce tamkar mataciya ta fito tana fadin" Bari ki ji Nana, idan har ya ki yarda walahi babu mai yi masa dole, idan har ya kiya babu mai aura masa ita dole, domin duk balakin da kike rada masa a kanta ya kare, kin kire shi mashayi , kin kire shi mazinaci idan kin manta a gidan auren da ta kaso ta dawo aka kamata, ke kam kin shiga uku, kina da abin zagi a tare da ke kin fake kina zagin wani, sam y'arki ba matar auren YUSUF bace, ba zan so gannin haka ba , domin uwa ta gari ake zabarwa ya'ya ba kamar y'arki ba, ko kece uwar YUSUF ba zaki taba yarda a aura masa y'a kamar wannan ba, bale da irin abinda ke tsakani, Ni kam na tafi sai ki dage hakar ki ta cinma ruwa!"
Azl 37
*KADA A YI BA KU, BONANZA TA NOVELS DINA A KAN FARASHI MAI SAUKI, WATO 1K SU 22 CIF IN SHA ALLAH.....KU GARWAYO DAN SAMUN NAKU A BISA FARASHI MAI RAHUSA .....KU TUNTUBI NUMBARNA 93811618*
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo
a nan aka bar Nana da RISLAN , wanda ya zauna shima kansa a kasa bai iya cewa komai ba, shi kam yau ya godewa Allah da ya sa matarsa ta tafi gannin gida da yara, da yaya zai yi a gabanta ko a gaban yara irin abin nan na faruwa? ai ba mahaifiyarsa ba shima sai ta raina walahi, Allah shi kyauta Allah ya sanyaya.
akace da zafi zafi akan daki dutse, tunda Bah ya je masalaci sallar isha ya ga YUSUF ya ji ai shikenan damuwarsa ta kau dan ya tabata idan YUSUF ya yarda ko mahaifiyarsa hakura zata yi, hakan ya sa bayan sun gama sallah suka fito tare, yar rakiyar da YUSUF ke yi masa sai ya nuna masa su nufi bangaren mahaifiyarsa yana son yin magana da su
YUSUF bai kawo komai ransa ba, suka wuce bangaren mahaifiyar tasa, domin a yannayin ginnin da aka yi, bangare uku ke iya sadaka kai tsaye da wajen YUSUF, bangaren Bah , na Mah, sai na Hajia baba , tafiyar ba wani nisa kuma ba tsaye tsaye suka samu kansu a falon Mah
A daidai lokacin da suka shigo, Mah na dakinta tana saman salaya , domin bata tashi ba, RAUDA ce kawai ke yawo da abin turaran wuta tana turara falon lungu lungu , hakan ya sa kanshin gaba daya a jikinta yake , kuma tana jin dadin hakan dan haka take bi hankali kwonce tana turarawa har ta ji salamar Bah wanda dama yakan shigo fiye da uku a wuni koda ba girkin Mah bane, sun saba sosai da ganninsa a bangarensu, YUSUF Ne rabonta da shi ido cikin ido tun da zasu kauro da ya tuko su a mota shi da kansa, ita da Mah da Abdul , shikenan bata kuma ganninsa
Da murmushi ta juyo tana amsa salamar Bah , sai dai a hankali murmushin ya bace a fuskarta saboda wanda ta gani tare da Bah din ya karasa saman kujera ya zauna ba tare da ko kallonta ya yi ba
Bah ya ce" baby kirawo min mamanki"
Ajiyewa Rauda ta yi tana amsawa ta nufi dakin Mah, shi kuwa YUSUF harda tatare girarsa yana kallon BAH ama kuma ya kasa yi masa magana dan ba zai ce masa komai ba gaskiya, ya yi , su suka sani idan sunna so su dasa mata barima du su suka gano, ƙatuwar budurwar da d'anta gayanan shima katon saurayi ama a rika wani ce mata baby?
tana sanarwa Mah ta fito ta nufi kicin dan dauko masu dan abin motsa baki, Mah kuwa ta fito ta karaso falon tana murmushi ta ce" Da uba da d'ansa Allah ya sa ta samu ne aka zo a gutsura min"
Bah ya yi murmushi yana nuna mata daf da shi ta zo ta zauna tana kallon RAUDA ta kawo kayan sha ta ajiye ta nufi dakin Mah din ta yi zaune ta shiga kunce kanta da Mah ta yi mata manyan kitso kuma tace ta kunce dan tun gobe wai za'a yi mata kitso da kunshi,....uhum, idan ta tuna jibi jibin nan ne daurin aurenta sai ta ga abin kamar a mafarki
A tausashe Bay bayan sun yi yar rahar da suka saba ya gabatarwa da su Mah abinda ke tafe da shi
Mah ta jima tana kallonsa kafin ta sauke Gwauron numfashi ta dauke dubanta a kansa a nutse ta furta" KA yi hakuri Aban YUSUF, Ni kam ba da yawuna ba, ba zan lamunta ba, a Daura masa wace Hajiar ta zaba masa kawai, idan ya so in yana ra'ayi zai zabi wata da kansa daga baya"
Ido Bah ya zuba mata, kallo irin na bai zaci koyarwar daga ita za'a samu ba, dan haka ya gyara zamansa a tausashe ya ce" Ki yi hakuri maman YUSUF, na san abu ne dake iya yi maki wahalar amincewa, ama ki yi hakuri, domin Allah zamu yi, kuma mu dubi lafiyar yarinyar ba dan mahaifiyarta ba, kin ji?"
Mah ta dago idannuwanta da suka fara cenza launin kala ta zuba masa tar cikin nasa ta ce" Zai fi kyau mu bar maganar nan "
dubansa ya kai kan YUSUF wanda ke zaune idannuwansa a kansu, dan a waje daya suke zaune, shine a facing din su
gannin bai ce komai ba ya sa ya sake dubanta ya ce" Ba zan iya bari ba, ai inada damar zaba masa matar aure ko? to na zaba masa Dayana!"
Mah ta yi murmushi mai ciwo ta gyara zamanta da kyau tana kallonsa ta ce" Eh kana da dama, ta farko ma ai damarka ce, ama ka sani abinda ya sa da na fada maka yadda na yi da yan uwana a kan maganar ƴaƴansu kace kwarai na yi daidai haka zai faru da taka yar uwar, Yaushema , Yaushema YUSUF ya fita daga mashayi mazinaci daga bakin ku ku duka?"
ido ya zarro yana kallonta da sauri ya furta" AMEERAH!"
Mah ta mike dan ta kula bayan shashasha da aka dauketa ana so a nuna mata mahaukaciya ce ita, rai bace ta ce" ABAN YUSUF, nace bana so, na ce ba za'a min ba, a bar min dan iskan da ake zagi hakanan ya samo daidai da shi, ko ta farkon da na amince ka san na yi karra ne saboda UWA!, bayan wannan babu wata karar da zan yi kuma, Nana ta nemawz y'arta magani sannan ta bata miji kamilale, ama ba YUSUF ba!"
daga nan Mah ta wuce dakinta kirjinta na sama sama, numfashinta yi mata wuyar fita, dan nan da nan ta ji tamkar athmarta zata tashi
A birkice Bah ya dubi YUSUF ya ce" Kana kallo tana son daga min hankali ta dagawa kanta a kan wannan abin da ba zai wani rageta da komai ba?, kana kallo sai abubuwa take koya wai Nine zata ce ba za'a yi ba? "
YUSUF ya sada dubansa, dan ko ba komai mahaifinsa a yanzu bashi da abokin shawara sama da shi, tunda ya daina zaginsa kuwa shima yake gudun zuciyarsa
a tausashe ya furta" In sha Allah, ba zata tada hankalinta ba, ka yi hakuri, ka bata lokaci amma kar kace tashi daya zaka sakata dole, kar ka manta irin abubuwan da suka ringa shiga tsakaninsu"
A dole Bah ya yi shiru , ya kasa cewa uffan, karshema ya fice a falon dan zuciyarsa dake ta dokawa da irin yadda ta fice daga wajensu
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya mike ya nufi dakin na Mah
A hankali ya bude ya shiga, idannuwansa suka sauka a kanta saman mamakeken gadonta, kanta saman cinyar RAUDA hannayen RAUDA din rike da hannunta idannuwanta lumshe ko barci ya dauketa? Allah masani, shi dai tunda suka yi ido hudu da RAUDAR ya yi tsaye har sai da ta dauke dubanta sannan ya karaso a hankali ya duka ya kawo hannunsa a nutse ya janye na RAUDA wanda hakan sai da ya sa suka kalli junna da sauri RAUDA ta dauke idannuwanta kirjinta na rawa, shi kuwa a hankali ya rike hannun Mah kasa kasa ya ce" Mah, kin yi barci?"
idannuwanta ta bude da suka dan fara cenza kala ta dube shi
a tausashe ya furta" Kar ki daga hankalinki, a kan abinda kike da damar cewa a yi ko kar a yi, bakya so ko?"
Mah ta gyada kanta a hankali tana sake kallonsa
Murmushi ya yi ya ce" Ba zan yi ba"
Mah ta sake dubansa ido cikin ido, ya sake tabatar mata cewar ba zai yi ba, dan haka ta ringa sauke ajiyar zuciya, ama cen kasan zuciyarta cike da mamakin mijinta take, ohk shi mai yar uwa ko? ita ta ki nata saboda ba zata taba iya amincewa da wannan soyayar ta rana tsaka ba shine shi zai amince da nasa? ba zata hanna shi zumunci da Nana ba, yar uwarsa ce , ama ba zata taba amincewa da wannan abin ba! never!
Ya dan jima har sai da ya ga ta fara barci , RAUDA ta sauke kanta saman gadon a hankali ya mike ya dora kaffafuwanta sosai ya gyara mata kwonciya sannan ya dago ya juyo, nan suka sake yin ido hudu da Rauda Wace ta yi saurin sada kanta, shima ya samu damar kare mata kallo kafin ya girgiza kansa ya fice a dakin cike da takaicinta, abu daya ya sani idan har ta yarda ta yi masa gangancin da suke shirin yi jibi ba zai taba yafe mata ba! ba zai taba yafe mata ba!
.................................................
washe gari tunda safe gidan ya ringa cika da baki, jama'a ta ko'ina suna zuwa