Showing 114001 words to 117000 words out of 188741 words

Chapter 39 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9860

mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo


Sai da ya gama daidaita abinda zai isar ya ce" tabatar da an hanna kowa shigowa, ka je ka sanar wajen Hajia baba a sauke amarya a bangaren kakar marayu, ka sanar mata umarni ne daga uban marayu!"

"An gama ranka ya dade, a huta lafiya, Allah ya karra nisan kwana mai wukar yanka" ya fita yana kirari, shi kuwa ya gyara zamansa ya shiga tunanin yadda zai yi da wannan jirgagen abokin nasa, yadda zai koya masa hakuri da halin mata, ya kuma fada masa sai ana taro su, idan har akace za'a yi da su yadda ake yi da namiji tsaf zasu hada maka cutar da likita zai kasa gani, a zo ana maka dan turare ana fadin ai jifa ne, bayan ba wani jifa a balakin mata ka afka!

Sako na isa wajen Hajia da gagawa ta sa aka Hau mota aka nufin gidan su Amarya, a nan cikin gidan kuwa ta sa aka bata wayarta ta yi kiran layin Mah ta sanar mata cewar bangarenta amarya zata sauka maza a shiga shirya mata wajen zama

a lokacin da aka sanarwa Mah, sai ta rasa me hakan kuma yake nufi, bangarenta dai bangarenta?, sai ta shiga neman layin YUSUF din, ama bata shiga, dan SHAHEED na tura sakon ya kashe wayoyin dan ya tabata sai an yi ka je ka zo da maganar dan kuwa rigima ce wannan ai yake son saka mutane a ciki!

Gannin bata samun layin sai ta saka alkyabarta ta nunawa yar uwarta tana zuwa ta bi ta hanyarsu dake sada su da junna ta nufi bangaren Hajia

tana zuwa ta tarda Hajia ita ke taro, domin dankam ana ta Kai kawo tsofafin yan gayu sun cika wajen Hajia gaba da baya sai sha'ani ake na kakar sarki da kawayenta

Bayan ta gama gaishe su sai ya je dakin Hajia ta zauna tana jiranta dan ta gabatar ta gane wajenta ta zo
mintina ฦ™alilan tsakani Hajiar ta shigo, ta sha lesh dan ubansu da gold a wuyanta da hannayenta har ga Allah Mah sai da ta yi mamakin yadda aka yi ta iya jure shigar nan a jikinta duba da shekarunta

Da matukar girmamawa Mah ta ce" Hajia, dangane da maganar sauke amarya a wajena ne, nace me zai hanna a same shi a ji dalilinsa? duba da yannayin yadda aka saba, lafiya kalau ba a saba kawo amarya a sauketa wani wajen da ba dakinta ba, kar aje wani abinsa ke damunsa ya yanke hukunci haka ya cutarwa yar mutane"

Sai da Mah ta dasa aya sannan Hajia ta sauke ajiyar zuciya, itama abin a ranta sai dai ita kam babu abinda zata iya yi a yanzu da ya wuce a bi abinda ya fada din, dan haka da kula ta ce" Kin gane, a sauketa inda yace din, tunda ya yi biyayar nan aka yi auren nan na fi so a bi shi a hankali har zama ya zaunu, idan aka watse sai ku tatauna in ya yarda sai ta je cen din, in kuwa ya kiya sai ta yi zamanta a nan din, kina gani saboda kayan dakin cen sai da na yi kiran mahaifinta da kaina nace masa ya dace ya tsawatarwa duk wani mai son sako min kace nace a tafiyar nan, domin ba zai taba yiwuwa ba a saka shi surutu a kan abinda ya yanke, da yace kar a zo masa da komai dan gardama da nuna ana da shi sai da aka zo din , Ni kuwa na saka an sauke a cen dan ba zan taba bari ya sani ba Ni kam!"

sosai ta yi mamakin wasu kalamai a furucin Hajia, sai dai bata nuna ba ta mike ta koma bangarenta ba tare da ta Musa ba, ama abu daya ta sani idan har ta same shi kafin a kawo matarsa babu mai sauke mata ita a bangarenta gaskiya, ta yaya zata iya zama tare da sarakuwa?, a'a kar ya fara yi mata haka, bata din fitina ita kam su je cen su shirya kansu su tatali junnansu

A gidan su amarya

biki bidiri, a nan ake bikin mai sunnan biki domin babu ce kawai babu a wannan rana, dan tun daga kan uwar amarya har zuwa autar gidansu babu wace bata cenza tufa sau biyar zuwa wannan lokacin ba
dama bikin gidansu haka ne
idan aka ce ana sabgar da ta shafe su zaka ga sunna cenza tufa tamkar a cikin rijiya suke janyo kudaden siyansu
makida kuwa kala kala tun daga na Nijar har na makotanmu wato Nigeria sunne ke wake ahalin gidan baki daya da wakokinsu kala kala na amaryar da angonta

Ana cikin wannan shagalin sako ya iso masu cewar idan an je da amarya a bangaren mahaifiyarsa za'a ajiyeta

yayar Amnah ce aka fara sanarwa sakon, a gigice ta mike daga wajen kidan nan ta nufi ciki tana fatan samun mahaifiyarsu dan bata jima da komawa ba daga wajen kidan ta fito ta zuba cefa iya cefa

a lokacin da ta sameta tana cikin kawayenta bata sanar mata ba sai da ta kirayeta ciki, dan a rayuwar da suka saba da mahaifiyarsu ta koya masu ko aminanta bata lamunce su ji sirinta ba bale mutanen gidan da zagaye

sunna shiga ta sanar mata wannan bayanin da ya saka uwar yin turus kafin ta dan yi wani yannayi da fuskarta sai kuma ta kai wajen kujerar dakinta ta zauna tana fadin" Bani wayata na yi kiran Hajia, a'a fa, ba zai yiwu ba, dama ta fada min in shirya Amnah sosai dan uwarsa ta fi karfinsa ta gama shanye shi sai yadda ta yi da shi, dan balaki Bama zata bari ta je dakinta daren farko ba sai dai a sauketa a wajenta? ta yi mata uban me? a'a fa, kar matar nan ta saki ta shigo lamarina dan na yi watsi da ita baya ce min komai a kan yarinyata, kuma tunda Amnah ta nuna ta ji ta gani tana son sa an gama, sai dai ya manta da ita uwar tasa ba dai Amnah ba!"

wayar ta miko mata, cike da isa ta danawa Hajia Rufaidah kira , wato mahaifiyar su Salima, ita ta sani a famillyn, tare suka yi karatu, kuma a rayuwa ta yau da gobe idan wani abu ya same su sukan ziyarci junna, a yanzu da maganar auren nan ta kullu kuwa sai zumunci yake son dawowa sabo dal , saboda Hajiar ta fada masu gaskiyar lamari cewar sai sun yi da gaske saboda mahaifiyar Malik muguwa ce , kiri kiri su ta raba su da mijinsu, haka kuma d'anta ta gama shanye shi sai yadda ta yi da shi

da takama, kalar yadda take ji da kanta a matsayinta Na matar gagarumin mai kudi ta amsa salamar Hajia, ta dan ja iska cike da isa ta ce" Hajia, yanzu magana ta zo min, kishiyarki tace wai a part dinta za'a sauke Amnah, ta san kuwa da wa take tafe?"

Hajia da bata san bama maganar sai da ta mike zaune tana mutsike idannuwanta saboda tun dazu ta shige da nufin zata yi sallah ta yi kwonciyarta tana hutawa dan ta gaji sosai da hayaniyar nan gashi yanzu komai ya zama na balaki jiranka kawai ake yi a ga ka yi wani abin yanzu a rikita maka lissafi

A nutse itama da kalar nata isar ta ce" Wai Ameerah din ta fadi haka?, yaushe kuma?"

cike da basarwa irin ta masu kuษ—i ta ce" Yanzu mama ta zo min da maganar, Hajia ba da zan yarda da abubuwan nan ba fa, gaskiya na san darajar yayana kuma mun san yancin kan mu, tun kafin ta shiga zata fara gasa mata aya a hannu?"

Hajia ta tabe baki tana gyara zamanta ta ce" Kadan kika gani a tarin muguntar matar, idan kika yi wasa sai an rikita maki lissafin yarinya kuma tana ji tana gani sai mijin ya gagareta!"

"lalle, uhum....lalle, sai dai ita d'anta ya gagareta, zan yi kiran ki Hajia, ama ki shirya tarbata dan kuwa tunda na ji haka nice zan kai AMNAH dakinta!" ta datse kiran tana wani murmushi abin tsoro tana kada kafa ta dubi mama, wato y'arta mai sunnan mahaifiyarta ta ce" Mama, je ki ce a yi a tashi kidan nan AMNAH ta shigo da wuri dan a shiryata da wuri, in sha Allah Ni zan kaita dakinta"

Wucewa Mama ta yi tana ta kada mazaunai tana tunanin ai Bama zai yiwu ba walahi ace za'a tafka masu wannan rashin mutuncin, ina , sun shirya tsaf shiga gidan nan ba dan su fito kwana kusa ba! kuma duk wata matsala dake iya Kunno masu a shirye suke tsaf da tararta ko Wacece!


Yama na yi aka shiga hada hadar kai RAUDAH bangaren Hajia
Mah da yan uwanta ne suka kai RAUDAH suka mikata hannun Hajia sannan suka koma falo, domin wankan amarya Hajia ce zata yi da kanta da shirya amarya, shirin da sun sani ba'a digawa amarya ko kwali bale a yi zancen wani mak'up na rashin tsari, domin Hajia a kulun takan kalubalanci irin rayuwar nan, takan ce ina anfanin wannan rayuwa ka wanke budurwa zaka mikata dakinta ka bari a kwaliye mata fuska kamar wata wace ta gama watsar da kanta a titi?

Su dai sunna waje suka yi salolinsu na magariba sannan aka shiga har fira ana jiran isha

A cikin dakin Hajia kuwa Rauda na cikin wani hali na matsanancin mutuwar zuciya da tunani, sai dai tunda Hajia ta zo hankalinta ta koma kan Hajia, domin, tunda take magana ta kusa da kusa bata taษ“a hadaya da Hajia ba, Hajiar dai ta santa itama karya take tace bata san Wacece Hajia da dukkan sauran halayarta ba, sai dai a yau sai take ganninta daban, bale da aka gama yi mata wanka irin na amare Hajiar ta bata wata jalabiya da hijabinta ta umarce ta ta saka ta yi sallah, bayan ta gama ta umarce ta kan ta hau abin kanshi, ta hau ta yi zaune a nan ne Hajiar ta shiga yi mata nasiha, kwarai nasiha ce, nasiha ta zaman duniya wace idan ka yi abinda aka fada maka lalle ka tanadi harda ta lahira, domin bata taba tunanin Hajia zata dubeta ba bale wai har ta damu da yi mata nasiha da fada da kakkausar murya a kan aure da darajarsa sai da Hajiar ta dubeta ta sanar mata a yanzu darajarta ta karu, idan har ta kiyaye ta yiwa mijinta biyayya lalle ita ke da riba, ribar dake iya shafar su su marikanta, Hajia ta yi mata nasihar da uwa da uba ke iya yiwa ฦดaฦดansu, a lokacin da ta zo rufe magana tana dubanta ta ce" RAUDA, ke jikata ce, ke din ahalina ce, ki rike mutuncin kanki, aure shi ne darajar da Allah ya luluba maki, ki kuma da shi sosai ki tsira gobe kiyama"

Hawayen dake zubo mata suka sake wanke mata fuska, Hajia ta yi murmushi tana kallonta, bata taba jin mutun ya shiga ranta irin na yarinyar nan ba, yau kafin ta yarda ta cire rigarta ta zauna da sket karami da breziya a yi wankan nan na nonon raฦ™umi sai da Hajia ta yi mata jan ido, kuma ana yi tana kuka, ba kamar wasu daga cikin ya'yan gidan ba, ana zuwa suke tubewa tik sai Hajiyar ta ce su rufe ba fa tik zasu yiwa mutane ba, kuma idan ana wankan nan ana yi sunna fadin inda bai samu ruwan ba, kuma har a yi nasiha a gama kiri kiri sunna kallon mutane , ama y'ar nan tunda aka fara har kawo yanzu da Hajia ta yiwa Mah magana ta shigo kuka take yi kanta a sade du ta fice a hayacinta

Hajia ta yi murmushi tana kallon Mah, a tausashe ta ce" Yaya aka yi baki zo min maganar filinta da nake ba jikokina ba idan zan aurar da su?"

da mamaki Mah ta kalli Hajia, sai kuma ta yi murmushi ta ce" A yi hakuri Hajia mantawa na yi"

Hajia ta yi murmushin itama tana kallonta ta ce" Na yi, ama gobe gobe ki zo a fitar da takardar ta a ba Uban marayu ya saka hannu a bata, sannan ki kaita dakinta da kanki dan Allah, Allah ya baki ladan riko"

Mah ta karra kamuwa da mamaki mai girman gaske, tana amsawa ta kama RAUDA ta mikar da ita, Abin mamaki Hajia ba biye da su har wajen mota tana sake fadin a kula da ita, sannan ta tabatarwa Mah zata karbi amaryar Malik idan bata dawo ba har aka kawo ta , dukda a yadda al'ada take babu wanda ya isa ya san da shigowar amaryar, ama kuma sun ce wai zasu yi ko amaryar doka ko me?, zata je dai bangaren na Mah ta tarbi amaryar kawai

Tun a wannan lokacin motocin tafiya da RAUDA suka fice a gidan, ciki harda aminiyarta da Salima, da sauran jama'ar dake nan dan taya Mah murnar aurar da y'a, Bah kam da Aba an ce zasu ganta idan aka kawo ta sati da ake kawo amarya ta wuni gidansu a yi mata kunshi da kitso, Hajia tace idan an kawo ta zasu yi mata nasihar su ta iyaye maza

Tunda motocin Su RAUDA suka fita , Hajia ta juya da nufin komawa bangaren Mah aka shiga shelar a marmatsa za'a shigo, sai ta dan ja ta juyo dan hangen mai shigowar ko Malik ne domin yau a idonta bata ganshi ba, rabonta da shi tunda asubahin nan

kade kaden da suka fara shiga kunnayenta suka sakata sake maida hankalinta tana mamakin waye kuma da kida? Bayan tun na daurin aure da aka yi aka soke kidan akace kar a kuma shima na daurin auren ba zata suka yiwa mutane, rasuwar marigayi ba wani jimawa ta yi ba, ya kamata ace an tsagaita wasu abubuwan, shi yasa wunin an yi shi na biki ne kawai ama ba wasu kade kade da abubuwan nan na sabga

jerin motocin dake shigowa da irin iface ifacen da suka shigo ya tabatarwa hajia ko su waye Wadinnan baki ne a masarautar nan da har zasu zo su yi wannan rashin da'ar a irin wannan lokacin

bata gama mamaki ba aka ringa fitowa daga mota, yannayin ado da kwaliyar matan dake fitowa ya fadar mata da gaba
da sauri ta juya wajen da ta ji murya kamar ta dan daudu yana fadin" Ku gafara a bude motar Hajia, hajiarmu maganin kukanmu, tabas mun yi kamu, kuturun kare, wannan gidan ko a Saudiya ai ginane ne, jama'a ga inda ake barin kudi da sarauta, Ni na san AMNAH dinmu sai ta yi baban kamu, sarki kika dauka tawa fito mu kashe, sarkinma uban sarakai ne dan uban mutun!"

Kiris ya hanna Hajia summa, a lokacin da ta ga an bude bayan wuleliyar motar nan wata ta fito da doguwar riga ษ—inkin nan da ake yiwa amare na yanzu, daurin kalabin kanta yadda ka san panka haka ya bude, hannunta rike da wani abin fifita, kafarta sanye cikin dan uban takalmi takani na karye!, a lokacin da masu daukan vidion da suka zo da su da masu hotuna suka shiga gabatar da aikinsu, a lokacin ne wannan zabiyar yan daudu ya kuma bude baki yana fadin" MRS YUSUF BELLO kennan, AMNAH, yar kudi, jikar kudi, yanzu kuma ta gama gogewa Yan uba harda ta zama matar kudi, kuma matar SARKI, yau dole mu tsole idon makiya da yan yatsunmu, ku kauce uwarku ce ta karaso!"

har ga Allah, ashariyar da ya kyatsa sai da Hajia ta rintse ido, gaba daya sai ta ji kamar ita daya ya ware ya durawa ashariyar nan...... , LA'ILA HA ILALAH Muhammadu RASULULAH Sallallahu alaihi Wa sallam





๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ wayo abu ya same mu, ku zo mu jajanta Hajia me kika dauko mana? ...

a ringa yi ana amsar bonanza๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

Azl 42
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login